Showing 27001 words to 30000 words out of 34734 words
daidaita da Kulsum ta amince masa.
Hajiya ta yi mamaki kwarai don ba ta zaci hakan zai zo da sauki ba, ta san Turaki Kulsum ke so, don an fi karfinta ne. Ba ta so ya kasance Kulsumu ta amince da Taufeeq ne albarkacin ta. Sannan ita a wannan lokacin ba ta shirya yi wa Kulsum aure ba. Ta kyale ne sabida Taufeeq bai iya sanya abu a ransa ba, idan ba hadin kan Kulsumun ya samu ba ba zai maida kai ga aikinsa ba.
Ta nisa, ta ce, “Taufeeq na yi murna, amma kamar yadda na ce a baya ina so ka ba wa al’amarin nan lokaci. Ka yi hakuri har Kulsum ta kare makaranta, sannan ne za mu ba ta damar fidda miji, yanzu ba ta da nutsuwar da za ta zabi mijin aure, kuma ba auren ta ke son yi ba. Ina rokonka, ka ba ta lokaci”.
Taufeeq ya nisa, “O.K Mum, zan bi abin da ki ka ce. Ki taya ni addu’a Allah ya sa in jure jiran, kuma Allah ya sa ina da rabon samun Kulsum a rayuwata”.
Abin ki da Da da mahaifi, sosai ta ji zuciyarta ta tabu, ta ce, “Insha Allahu inda alkhairi Allah zai ba ka ita. Kuma ba ga waya ba? Ko ka tafi ko yaushe kana iya kiranta, sai dai bana son abin da zai hana ta maida kai a karatu don Allah”.
Dan murmushi ya yi, ya ce, “Mum zan kiyaye, zan tafi gobe ki sa min albarka”.
“Albarka kullum cikin sanya muku muke. Allah ya kara wa rayuwa albarka”.
Kulsum da Nasma a dakin Nasman, ta tura mata akwati shake da kaya, ta ce duk tsarabar ta ce. Ta bude tana daga English wears din daya bayan daya ‘yan gidan Marks & Spencer, duka babu mai fidda tsiraici za ta iya zama gida da su. Tana daga su daya bayan daya tana yabawa.
“Aunty Nasmah, duk ni kadai?”
Nasmah ta yi murmushi, ta ce, “Sai a yi ta tsantsarawa Yayana kwalliya”.
Rigar da ta daga ta sa ta rufe fuskarta.
Nasmah ta yi dariya, ta ce, “Ai kallon ku nake kar, kun dauka ban gane ba ne ko? Sai ki yi hakuri Yayan nawa akwai fada, akwai rigima. Ban sani ba ko ni da Aunty Sakeenah kadai yake yi mawa? Ke kam ai lallaba ki zai yi na sani, tunda shi ne mai nema”.
Kulsum ta shuri jakarta ta bar dakin Nasmah na fadin, “Sai fulako sai ka ce tashin Ruga”.
Ko da Taufeeq ya koma duk dare sai ya kira ta, komai yake yi sai ya sanar da ita. Tun tana jin kunya har ta saki jikinta da shi. Ita ma takan fada masa me ta ke ciki a kan harkar karatunta. Hatta Aunty Sakeenah da ke Lagos ta san zancen Taufeeq da Kulsum. Kusan ta fi kowa farin ciki da al’amarin don dai ita haka nan ta ke matukar son Kulsum.
Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta yi mata, kwanansu uku da yin hutu kawai rannan tana gyaran kayanta a closet dinta ta tsinkayi sallamar Goggo.
Goggon da ke zuwa kullum cikin mafarkinta, Goggon da ta ke kewa, kewar da ba za ta misaltu ba.
Sakin kayan hannunta ta yi ta buga wani uban tsalle ta rungume Goggo.
“Yi min a hankali, tsohon kashi ne”. Goggo ke fadi.
Da kyar ta bambaro ta daga jikinta, ta kalle ta ta sake kallonta cikin fulatanci ta ce, “Kulsumu am ondo (Kulsumu na ce wannan)?”
Dariya ta yi, ta kama hannunta zuwa bakin gado, Goggo na fadin, “Halan wankan inji na sake fata Nasara ke yi miki?”
Dariya sosai Kulsum ke yi, ta rasa inda za ta saka Goggo don murna. Ta zaunar da ita gefen gado, ta bude dan bedside fridge dinta ta dauko gorar fresh milk da ruwan sanyi na gora tana ta rawar jiki, ta ce, “Goggo wanne zan zuba miki?”
Hajiya Nasara ta shigo, a bayanta Serah ce da tray din abinci.
Ta ce da Goggo, “Ai yau kuma ba kanta tunda ga Goggo ta zo, ina jin ko runtsuwa Kulsum ba za ta yi ba”.
Kulsum ta ce, “Kamar kin sani Hajiya, kwanan zaune za mu yi”.
Hajiya Nasara ta ce, “To don Allah barta ta huta ta ci abinci, son samu ta watsa ruwa ma, sun sha hanya”.
Nasmah ta shigo ta gaida Goggo, Goggo ta ce, “Ita ce auta ko?”
Kulsum ta ce, “Goggo kada ki sa Aunty Nasmah ta kara shagwaba akan wadda ta ke yi, idan ta ji kina kiranta auta”.
Dariya suka yi, Nasma ta ce, “Ni ce nake shagwaba ko? Zan gamu da ke ne. Goggo ki je ki watsa ruwa ki yi sallah, ki huta ki rabu da ita”.
Goggo da Kulsum ba su samu kebewa ba sai da daddare, Kulsum ta dage a dakinta Goggo za ta kwana bayan already Hajiya Nasara ta gyara mata daki.
Goggo ta sha labarin zamanta a Lagos gidan Dr. Sakeenah da hanyoyin da Dr. Sakeenah ta bi ta hana ta fitsarin kwance. Da kaita babban asibiti data yi ta ga kwararren likita. Ta ce tun daga lokacin har yau ban kara yi ba. Idan na ji fitsari ko cikin barci ne sai na ji kamar ana alerting dina har cikin kwakwalwata. Amma har yanzu likita bai dauke ni daga shan magani ba. Idan na tuna wahalar da ku ka yi ta sha ke da Baffa, sai in tausaya muku, ashe lalurar tawa ta asibiti ce”.
Goggo ta ce, “Godiya ta tabbata ga Sarkin halitta, shi magani ai dama dace ne, ciwo kuma warakarsa lokaci ne. Kulsumu Allah ya kawo miji na gari tunda lafiya ta samu”.
Ta rufe fuska da hannayenta tana fadin, “Kai Goggo, ni karatu nake yi. Kuma har yau likita bai ce na warke ba”.
Ba ta gaya wa Goggo Taufeeq ya fito yana sonta ba, haka ita ma Goggo ba ta gaya mata dawowar Turaki ba da komenta da ya ke so. Sun yi shawara ita da Hajiya Nasara su bar zancen a tsakanin su kada a raba mata hankali. Ita kuma Kulsumu kunya ce ta hana ta gaya wa Goggo zancen Taufeeq da kuma kasancewar har yau zuciyarta ba ta bai wa soyayyar Taufeeq kwakkwaran matsugunni ba. Ta fi kallonsa a wanda ya fi karfinta, dan gata, amma mutum mai tsananin kirki.
Washegari Nasma ta ce za su kai Goggo ta ga gari ta mike kafa. Kowaccensu ta sha kwalliya, amma ko daga nesa ka san Nasmah ta fi Kulsum aji nesa ba kusa ba. Yayin da Kulsum ta fi Nasma kyau mai fizgar hankali. Nutsuwarta na kara wa kyawun nata ado, yana bayyana kwarjininta.
Nasmah ce ke tukin motar su shiga nan su fita can cikin garin Abuja, suna ta gaya wa Goggo wurare. Sai goshin magriba suka dawo gida.
Kwanan Goggo Shatu bakwai tare da su ta koma Gaya da tsarabar Abuja rankatakaf!
Nasmah ta yi shirin zuwa Lagos za ta yi sati biyu, Dr. Sakeenah ta roki Hajiya su taho tare da Kulsum tunda suna cikin hutu. Hajiya Nasara ta ce, hutun ai ba shi da yawa, nan da sati daya za su koma. Sakeenah ta ce, ko sati dayan ne a bar mata aron Kulsum.
Sosai ta ke murna da wannan tafiyar. A daren ta shirya kayanta, kuma a daren sun yi waya da Taufeeq amma ba ta gaya masa za ta zo Lagos ba. Washegari jirgin Azman na safe ya daga da su zuwa birnin Ikko.
*** *** ***
READING
Turaki ne tafe cikin kankanuwar motar sa kirar Acura akan shimfidadden titin da zai sada shi da gidan aminin sa Abdul'Ahad Aminu Maikano, misalin karfe biyar da rabi na yammacin ranar Talata bayan ya taso aiki daga jami'ar ta Reading. Kamar kullum sanye yake cikin bakaken suit masu kauri, ya tsuke wuyan sa da ruwan tokar tie fatar shi tayi santsi har wani sheki take yi na musamman. Ta earpiece din dake makale a kunnen sa yake magana da Abdul'Ahad din "i am on my way Aboki....nan da mintuna ashirin zan karaso".
Sati biyu kenan da angwancewar Abdul'Ahad da amaryar sa wata hazikar dalibar sa Dr. Sajidah wadda 'yar kasar Eritrea ce. Iyayenta Refugees ne a United Kingdom. Sanda ya iso gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke daga sama har kasa, har lokacin sallar maghriba ya gabato.
A kofar gidan ya tadda Abdul'Ahad da Sajeedah din suna jiran isowar sa, ya faka motar ya fito Sajeedah na yi masa barka da zuwa, tare suka rankaya su duka zuwa cikin gidan.
Gidan nasu bai cika girma ba amma cike yake da duk wani nau'in kayan alatun jin dadi da saukaka rayuwar dan adam. Abdul'Ahad ya gayyato shi cin abincin dare ne kamar yadda su kanyi lokaci zuwa lokaci. Kuma su tattauna akan matsalar Turakin wadda ba komai bace banda 'UmmuKulsum' kamar yadda Turakin ke kiran ta in full.
Sallah suka fara yi, kafin su idar Sajeedah ta gama shirya musu tebir, bayan sun idar suka nufi dining din Abdul'Ahad na cewa Sajeedah "in ji dai kin cika tukunya da kyau, kinsan gwauraye ba'a sa musu sanwa kadan". Dariya Sajidah tayi tace "shima Dr. Abubakar ya kusa tashi daga gwauro don nayi masa kamun kanwata, Fadwa, jira nake ta samu hutu in dauko ta su ga juna". Turaki na dan murmushi bai ce komi ba. Abdul'Ahad yace "wane Abubakar din? Yana da matar sa a gida fa, Allah ya kashe ya bata, ya gama mutuwa a kanta, ki dai taya shi biko shine za ki yi gwanin ta, Kulsum yake jira ya dawo da abar sa, kuma insha Allah zamu yi nasara".
Cikin mamaki Sajeedah ta tambayi mijin ta cikin harshen turanci "dama yana da mata?" Turaki wanda ke zuba abinci a plate kansa a kasa, cikin kwantaccen sautin sa yace "Sajeedah, rabu da mijin ki kin ji, i am all alone, living alone, ta riga ta kubuce min, bisa sakaci da kuskure na, bansan ina zan nemo ta ba, duk wata hanya da zan samu labarin inda take bani da ita, keep praying for me kin ji, ita kadai nake so!"
Cikin mamakin abinda take ji yau daga bakin Dr. Turaki Sajeedah tace.
"Kun rabu ne?"
"An raba mu dai, don ba ni na saketa ba". Ya bata amsa.
A gajarce Abdul'Ahad ya bata labarin komai. Sajeedah ta rasa abinda zata ce, a karshe tace "hakkin iyaye dana Kulsum ne ya rikide ya koma maka soyayyah Dr. Abubakar. How i wish zan ga Kulthum da na yi kokari na bata hakuri ta dawo". Murmushi Abdul'Ahad yayi cikin zolaya ya ce "to ka karbi wadda ake ma tayi mana ka rage zafi? In ya so in Kulsum ta bayyana sai ka hada biyu? Sanyin garinnan without a wife is terrible".
Hararar Abdul'Ahad yayi, sannan ba tare da ya tofa ba ya mike yana duba agogon swatch blustery dake daure a damtsen hannun daman sa.
"Zan tafi gida, akwai marking din takardun dalibai da zan yi. Sajeedah, you cooks nicely, thank you once again". Sajeedah tace "ai fa ka kore shi, inama zan ga Kulthum dinnan in gaya mata how lucky she is! For winning this precious heart of Turaki. Ta dawo wa mijin ta mai kaunar ta.
Dr. Abubakar duk ranar da Kulsum ta dawo mana zan zama babbar abokiyar ta, ko don in gaya mata irin son da muka wanzu muna yi mata, a lokacin da ta kubuce mana".
Murmushin dai kawai yayi, sai dai bai ce komai ba, tausayin kansa yake ji don gani yake kamar ya rasa Kulsum har abada, wani abu da ya tabbatar zuciyar sa komai juriyar ta bazata karba ba. Gaban sa har wani irin faduwa yake yi idan ya tuna Kulsum zata iya auren wani a halin yanzu. Idan kuma hakan ya tabbata shi da aure sai ranar da Ubangiji ya nufa. Zai kare rayuwar sa a haka. Sannan zai fasa komawa gida.
Duk wani tanadin rayuwar sa ta gaba, ya tsara shi ne tare da Kulsum. Duk abinda yake tarawa don ta ji dadi ne ita da 'ya'yan da zasu haifa. Yayi wa Kulsumu tanadin rayuwa mai gardi, da soyayya irin wadda ko a hikaya babu duk don ya wanke laifukan sa na baya. Ya sa kai ya fita ya nufi motar sa Dr. Abdul'Ahad ya biyo bayan sa.
A jikin motar sa suka tsaya yayin da Sajeedah ta koma gida.
"Any development?" AbdulAhad ya tambaya.
"Aboki ina cikin damuwa mai tsanani, i'm just pretending to look okay. Bana iya barci, ko na yi barci mafarkin ta nake yi tare da wani na, na kira Batulu ko sun samu wani labari ta ce har yanzu babu, har makotan su data sa su gaya mata da zarar sun ga tazo wajen Kakannin nata sun ce har yanzu bata zo ba. Na tabbata su Goggo sun boye UmmuKulsum ne kuma ba don kowa suka boye ta ba sai don ni. Idan ta auri wani ba ni ba na tabbata karshen farin ciki na ya zo Aboki. Su Maimartaba sun ki sanya baki har yanzu. Ina cikin yanayin da nake bukatar aure, in kuma ba ita na samu ta dawo min ba bazan iya auren kowacce mace ba, ka bani shawara, domin kwarai na ji dadin shawararka ta baya, na kuma amfana da ita".
Abdul Ahad ya nisa yace "a yanzu dai bamu da zarafin zuwa gida har sai mun hada abinda ke gabanmu (zama cikakkun consultants), na maka alkawarin ni zan taya ka nemo Kulsum kuma kakannin ta da kan su zasu gaya mana inda take, na san abinda zan ce musu su karbi nadamar mu, ai da ciwo abinda ka yin, it's not easy ka dawo yanzu ka ce kana son ta su yarda da wuri, zasu yi ta tsammanin ka dawo ne don ka samu ka farantawa iyayen ka ba don kana son 'yar su ba, in aka yi la'akari da yadda komai ya wakana".
Sun dade suna tattaunawa Abdul 'Ahad na kwantar masa da hankali, har yana fadin "Turaki believe me..... Kulsum bazata iya auren kowa ba bayan kai, u are her first love, her first husband, duk wanda zata aura da fargaba zata shiga gidan sa tunda ta san ita ba budurwa bace, ko zata yi aure a gaskiya ba yanzu ba, abinda zata fi maida hankali a kai yanzu shine neman ilmi don ta gina rayuwar ta".
*** *** ***
Dr. Sakeenah ta daga waya ta yi kiran lambar Taufeeq, “Yaya Taufeeq guess what?”
Dan tsaki ya yi, “Ke fa haka ki ke, sai mutum yana tsaka da aiki ki ishe shi da shirme, komi ba za ki fada kanki tsaye ba sai kin yi ta kumbiya-kumbiya”.
Sakeenah ta ce, “Tunda ba za ka saurare ni ba ka yi wa kanka, na fasa gaya maka albishir din”.
Ta kashe wayarta.
Ya kira ta ki dagawa, ya sake kira ta kashe wayar gabadaya. Don haka da ya tashi aiki ya dauke kan motarsa ya yi Victoria Island gidan Sakeenah, duk da ya san ba wani abu ba ne mai muhimanci za ta gaya masa.
Amma me? Wadda ta bude kofar a lokacin da ya danna door bell bai yi tsammanin ganinta a garin Lagos ba. Baki ya bude sakaka! Yana kallonta. Murmushi ta yi ta ba shi hanya ya wuce, yana fadin.
“So this is the albishir, sorry Doctor, wannan har goron albishir zan ba ki ai. Kulsum in town, what a surprise!”
Sakeenah