Showing 33001 words to 34734 words out of 34734 words

Chapter 12 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

521

Ya ce, “Mujaheed ya maida ke gida, zan kai Kulsum ta ga likitan ido”.
Ta ce, “Haka ake zuwa ganin likitan afujajan ba shiri ba appointment?” Ni dai gaskiya kada ka hada ni da Aunty Sakeenah".
Ya harare ta yace, “European Hospital zan kai ta, sabon asibitin ido ne, na hadin gwiwar European Union (EU), ko yaushe ka je za ka ga likita”.
Kulsum wadda duk rawar jikin da yake a kanta ya daina burge ta, kwarjininsa ya zube daga idanunta, ta ce, “Don Allah Ya Taufeeq ka barmu mu tafi gida, ma je asibitin daga baya, idan Aunty Sakeenah ta dawo ta ga ba ma nan za ta yi mana fada”.
Ya ce, “To hell with Aunty Sakeenah, kina zaune da ciwon ido shekara da shekaru ba ki taba ganin likita a kai ba ki ce wata Sakeenah? Wuce mu je kada ki bata min rai”.
Nasmah ta ce, “Ni dai ka san yadda za ka yi ka fidda ni wajen Aunty, sai kun dawo”.
Har ya tada motar suka hau titi Kulsum hawaye ta ke yi, hawayen da ya danganta da ciwon idon nata, ko on fadan da yayi mata. Da kuma rakin ta, haka ta ke da raki kamar kankanuwar yarinya, abin kuka ba ya mata wuya.
Kulsum ta daga kai ta dubi tankareren asibitin da Taufeeq ya kawo ta. European Specialist Eye Hospital. Ya samu wuri ya yi parking ya bude mata kofa. Tare da cewa,
“Mu je ciki, ko sai na dauke ki ne?”
Ba ta ce masa komai ba, don yanzu komai nasa ya daina burgeta, ta sa kafa ta fito.
Tana zaune ya je ya yanki kati ya yi komai ya dawo. Aka nuna musu ofishin da za su ga likita. Mutum biyu ne a gabansu, daya na ciki bai fito ba, daya na kan layi daga waje. Suka zauna, Taufeeq ya ce da ita, “Ba sa bata lokaci su, kana zuwa za'a duba ka, sunada kwararrun likitocin ido, duk Nigeria babu kamarsu a fannin ido, don haka ne tsadarsa ba ta dada ni da kasa ba”.
Ita dai jinsa kawai ta ke yana kara sire mata. Abun ba kama! Wai Taufeeq mashayin giya. Allah Sarki Hajiya! Ko ya ya za ta ji duk ranar da ta samu wannan bakin labarin? Tana alfahari da ‘ya’yanta, tana bugun kirji da tarbiyyar da ta ba su. Kullum burinta shi ne su zame mata ‘ya’ya na gari. Musamman Taufeeq da yake namiji tilo shi kadai da Allah ya ba su.
Daddy na son Taufeeq yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba! Ya ya za su ji idan ta zo gabansu ta ce ta fasa auren Taufeeq, saboda giya yake sha, ana saura kwana hudu daurin aurensu? In kuma suka karyata ta fa? Suka ce sharri ta yi wa dan su?
Anya za ta iya yi wa Hajiya Nasara wannan sakayyar ta fasa auren Taufeeq kwanaki kadan gabanin aurensu? Duk wani shiri na duniya sun gama shi, har kayan aure su suka yi mata, da wane bakin za ta zo ta ce ta fasa auren Taufeeq a yarda da hujjar ta?
To amma haka za ta bari tana ji tana gani a aura mata mashayin giya ya zama uban ‘ya’yanta?
Tana wannan tunanin mai matukar soya zuciya mutumin da suka tarar ya fito daga ofishin likita, Taufeeq ya wuce gaba ta bi shi a baya. A jikin kofar ofishin an rubuta (Consultant Ophthalmology), ta bi bayan Taufeeq cikin mutuwar jiki da ta zuciya suka shiga.
Sanyin Iya kwandishan ne ya fara bugun jikkunan su. Kulsum ta kai dubanta ga mamallakin ofishin wanda ke zaune cikin kujerar sa mai juyawa dama zuwa hagu, ya baiwa kofar shigowa baya, idon sa na kan file din ta. Sanye cikin grey-black Italian suit. Gabadaya ya juyo da kujerar sa ya fuskance su, amma idon sa na kan file din gaban sa. Ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane TURAKI ba, Turakin ta .... Her Ex-Turaki, kowanne irin canjin rayuwa ya samu kuwa, sai dai ya tara suma a kansa wadda a baya ba shi da ita, ta kwanta luf a kansa sai sheki ta ke ta fulanin Gaya.
A jikin dan karfen da ke kan teburin sa cikakken sunan sa ne cikin ruwan gold, DR. ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI GAYA..... ta wani irin zuki numfashi ta fesar. A hankali ta soma maida kafafunta baya don barin ofishin. Cikin tsananin taka-tsan-tsan na kada takunta ya bada sauti. Abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun ta.... Alaqar da ke tsakaninsu, wata irin alaqa ce ba mai kankaruwa daga zuciya ba!!!
Saura taku biyu ya rage mata ta fice ya dago kansa gaba-gadi don ganin masu shigowa… Bayyanannen canjin da ta samu cikin shekaru takwas da doriyar watanni bai hana shi gane ta farat daya ba, kamar yadda itama nashi canjin da nauyin shekarun da suka hau kansa, suka bashi suffar cikakken mutum wanda ke cikin ganiyar cin ilmin sa, ya kuma san ciwon kansa a halin yanzu, bai hanata gane shi ba.
Ya kafe ta da idanunsa ta cikin farin gilashin da ke manne a idon sa,... idanun nan na Turaki da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu... A lokacin da ita kuma ta bude kofa ta fice da dan banzan sauri… har tana tuntube, saura kadan ta fadi!

Mu karasa a littafi na uku. Kuma na karshe insha Allahu. Kulsum 3 zai biyo bayan sa bada jimawa ba. Nayi muku alkawarin cigaban bazai jima ba. Gundarin labarin Kulsum yana cikin littafi na uku.
Taku har abada:- SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI.
JANUARY, 2021.

Ga masu bukatar tsofaffin littafaina zaku iya mallakar su a softcopy ko hardcopy (based on order idan hardcopy ne), a tuntube ni a whtsp ta wannan lamba 07030137870.

DANDANO DAGA KULSUM 3
"Malam lafiya?"
Tayi tambayar tana dojewa kallon idanunsa. "Na zo fita, ka sa securities din ku sun tare ni, na ci bashin ku ban biya ne?"
Bata yi aune ba ta ji hannun ta cikin na Turaki, kafin ta tantance meke faruwa ya jata tana tirjewa ya bude motarshi ya sanya ta, tare da rufe kofar da key din hannunsa. Ya zagaya ya shiga mazaunin sa ya tashi motar. Masu gadin suka wangale masa kofar ya fice suna daga masa hannu cikin girmamawa.

Tafiya kawai yake bisa shimfidaddun titunan garin Lagos ba tareda Kulsumu ta san inda aka nufa ba. "Malam sace ni zaka yi? Malam ina ruwan ka da ni ne? Malam ni matar aure ce ko baka ganni tare da mijina ba!" Idan sitiyarin motar ya bata amsa, to mai tukin motar ma ya bata. Inda take wannan bai kalla ba, tukin sa kawai yake cikin nishadi, sai sharara gudu yake amma murmushin dake kan tattausar fatar bakin sa ya kasa bacewa.
Kulsumu ta soma bugun gilashin motar da duka hannayen ta, fatan ta gilashin ya fashe koda zai yanke ta ne, tayi ihun da mutane zasu ji su kawo mata dauki. Amma ta lura gilashin motar ko sound baya badawa kuma ko zata shekara tana bugun sa bazai fashe ba.
Kawai sai ta fashe da kuka tana kiran Goggonta da Baffanta. Abinda yayi matukar baiwa Turaki dariya, ya dubeta ta gefen idanunsa,
"saura Batulu da Ummah".
Idanun cike da kuka amma hararar shi take yi. Har suka shiga unguwar Ikoyi Kulsumu bata bar kuka ba, don ta gane in ma sata ce Turaki ya gama sace ta. Sun wuce gidaje kamar guda biyar kafin su shiga wani kyakkyawan 'lodge' mai hawa daya. Mai gadi ya zo ya bude, Turaki ya zura hancin motar sa cikin gidan.
Yayi parking a rumfar adana motoci wadda ke dauke da wasu motocin guda biyu, ya kashe motar tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya. Ya dubi Kulsumu wadda ta ki dagowa daga cinyoyinta, balle ta san inda ya kawo ta. Sautin kukanta kadai kake ji a motar, kamar wadda aka fadawa sakon mutuwar iyayen ta.
Kirjinsa ne kawai yake dagawa yana sauka da sauri da sauri. Ya yarda wani lokacin 'excitement' zai iya haifar da bugun zuciya. To hakan ce ta faru ga Turaki. Wanda ke ganin komai dake faruwa dashi yau kamar a mafarki..... wai shine da Kulsumu a gabansa!
Idan mafarki yake yana rokon Allah kada ya farkar dashi daga wannan mafarkin, har sai ya ga karshen sa. Har sai ya gan shi tare da Kulsumu matsayin ma'aurata a karo na biyu. Ashe duk mahaukacin neman nan da yake wa Kulsumu tana cikin kasar Nigeria, a Najeriyar ma a garin da yake rayuwa!. Allah shine shaida kan babu abinda ya wahalar dashi a duniya irin neman da yayi wa Kulsumu, shekaru dai-dai har guda hudu. Shi Allah da yake Gafurun-Rahimu ne, yau gashi ya tankado keyar Kulsumu ya kawo mishi ita har cikin ofishinsa. Shin shi wane irin wawa ne da zai yi saken da zata sake kufce masa?
"If u are done the cry (idan kin gama kukan) ki wuce mu karasa ciki".
A matukar fusace ta dago ta dubeshi....

"Nima bansan meye hadin nawa dake ba.... I just want to confirm ko Kulsumu na ce wannan. I just want to confirm....idan matata dana rasa nake nema ce. I just want to confirm....idan reaction din ta sabida ganina a inda bata yi tsammani ba yana da alaqa da ta gane ni ne itama, ko kuwa wani abu ne daban ya firgitata take neman mafaka.....".

Kulsum 3. Kada ku bari a baku labari. Akwai Dambarwa ba 'yar kadan ba.
-Takori

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login