Showing 24001 words to 27000 words out of 34734 words

Chapter 9 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

524

ba?”
Ya sauke hannayensa bisa tebirin tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ya ce, “Abdul’Ahad na rasa Kulsum, sakaci na ya jawo min babban da na sani. Maimartaba ya raba auren da kansa, sun maida UmmuKulsum ga iyayenta, su kuma sun bar garin da ita. Na tashi a tutar babu, ma’abocin da na sani. Hakika bijirewa iyaye babu inda zai kai mu sai ga rashin albarka da rashin kwanciyar hankali. Ina ma na karbi auren Kulsum da kyakkyawar manufa da ban kasance cikin kuncin da nake a yanzu ba”.
Maikano ya tausaya wa abokinsa, ya san irin wannan nadamar, ita ake kira ‘NADAMA MARA AMFANI’, ya ce, “Amma tsakaninka da su fa? Ina nufin iyayen ka?”
Ya ce, “Sun yafe min da kyar da sidin ludayi, sannan Maimartaba ya ba ni shekaru uku in kammala duk abin da nake yi a nan in koma gida, su kuma kakannin Kulsum sun ce ko sunan kasar da aka tafi da ita ba su rike ba, mun dai rabu a kan in sun zo end of the year za su karba min lambar wayar marikan nata. Su kuma su Maimartaba sun ce, in mun daidaita tsakanin ni da ita shi ke nan za su amince mu koma auren mu”.
Abdul’Ahad ya ce, “Ni kuma ka san wani abu? Ban yarda kakannin Kulsum ba su san inda aka tafi da ita ba. they just want to teach you a lesson or something else… in za ka koma next year zan raka ka mu je tare, kuma insha Allahu ba za mu dawo ba sai tare da Kulsum. Game din yanzu tsakanin kai da Kulsum ne babu interference na iyaye. Idan ka maida kanka dan soyayya Aboki ka samu Kulsum ka gama”.
Murmushin gefen baki Turaki ya yi, murmushin kasaitar sa da ginshirar sa da ya saba. Wannan kuma wani abu ne da bai san ya yake ba (lallashin mace da soyayya), ya saba shi ake cewa ana so har a yi ta husumar kishi a kansa. Yau Abdul’Ahad na fadin shi zai koma neman soyayya. A yadda yake jin son Kulsum ta dawo cikin rayuwarsa yana jin ba abin da ba zai iya ba, in dai zai same tan.

Ya fara tuna rayuwarsa, bayan shigowarsa UK, ya fara karatun medicine a jami’ar Reading Berkshire, ya kammala da kwali mai daraja inda kai tsaye ya tafi specializing a Ophthalmology wato fannin likitancin ido.
A dukka wadannan shekarun yana rayuwa ne with the guilt na laifin da ya san ya aikata wa Kulsum, yana kuma cike da taraddadin komawa ga iyayensa don ya san cewa ya yi musu laifi. Sannan tsaurin karatu irin na medicine ya hana shi samun lokacin komawa gida. Daga ranar da abun ya faru (ranar da ya karbe wa Kulsum alfarmarta) kamar an sa igiya an zarge zuciyarsa da soyayyarta. Everything happens like a magic, kuma kamar an tsara shi ya tafi a hakan. Abin da bai sani ba shi ne, Maimartaba ya tsara din, kuma komai ya tafi a yadda ya tsaran. (Kulsumu ta zauna a zuciyarsa koda ya tafi, idan ya san ya tafi ne ya barta a cikakkiyar matar sa).
Ganin girman laifin da ya aikata wa Kulsum a ranar da zai taho ya san Umma ta dau zafi da shi, shi ya sa ya ki kiran waya, kullum kokari yake ya kammala abin da ke gabansa ya koma gida bakidaya ya fuskanci kowanne irin hukunci daga iyayensa. Da wannan damuwar ya rayu a dukkan shekarun da ya kwashe yana karatu. Yana gama karatunsa kuma university din ta rike shi ya yi mata aikin koyarwa temporary sabida kyawun takardunsa.
Tun a shekararsa ta farko ya hadu da Abdul’Ahad Aminu Maikano. Babansa diplomat ne, ‘yan asalin jihar Katsina. Abotarsu mai ban sha’awa ce, sai dai Abdul’Ahad bai san komai a kan Turaki ba sabida zurfin ciki da rashin son magana irin nasa. Sai fa lokacin da ya rasa yadda zai yi da damuwarsa har ta soma sabbaba masa rashin lafiyar ciwon kai mai fitar da shi hayyacin sa da Abdul’Ahad din ya samu ya bayyana masa komai nasa.
Kuma bisa shawarar Abdul’Ahad din ne ya zo gida har abubuwa suka kwana yadda suka wakana. Madallah da aboki irin Abdul’Ahad mai fitar da abokinsa daga damuwa. Ya ji dadin shawarar sa, don haka ne yanzu ba ya boye masa komai da ya shafe shi. Tunda ga shi ya samu ya shirya da iyayensa.
Tunda ya dawo duk bayan kwana uku sai ya kira gida, secretly kuma suna waya da Batulu tana gaya masa har yanzu ba bayani, ta je wurin Goggo sau ba adadi ko za ta ci karo da wani abu a kan Kulsum din, amma sai dai su yi hira ta taho, kullum zancen Goggo daya ne, ita ba ta san sunan kasar da aka tafi da Kulsum ba. Baffa kuwa ba abokin zancenta ba ne da ma. Ga Kulsumun babu kawa balle aminiya, ita ce da ma kawar tata. Kuma aminiyar ta. She is very anti-social. Amma tunda Goggon ta ce za su zo karshen shekara ita kuma ta yi masa alkawarin kawo masa labarin Kulsum idan ta zo gari, sannan Goggo ta yi alkawarin bada lambarsu.

*** *** ***


Tana kwance da daddare a tsakiyar gadonta washegarin komawar Taufeeq Lagos. Wani textbook ta ke nazari NURSING ETHICS IN EVERYDAY PRACTICE (Connie M. Ulrich). Wayarta da ke karkashin filo ta yi kara. Ko da ta daga babu suna, bakuwar lamba ce a wayarta. Da ma contacts din nata ba su fi shidda ba, Goggo, Hajiya, Aunty Sakeena da Baban Yalleman sai Nasma da wata abokiyar karatun ta Grace. Don haka da sallama ta amsa cikin siririyar muryarta.
Daga daya bangaren Taufeeq ya kira sunanta, “Ko ki bugo ki ji yaya abokin ki ya isa Lagos?”.
Murmushi ta yi, don ta gane mai magana.
Ya ce, “Na kira kawai in miki sai da safe. Kada ki manta da ni cikin wadanda za ki yi mafarki. Also put me in your Du’as, ina da bukata muhimmiya wurin Ubangiji. Wadda nake so ba ta so na”.
“Kamar ni da Turaki”. Zancen zucinta ya fito fili ba tare da ta sani ba.
Taufeeq ya runtse idonsa.
“Ya Allah! Kulsum me ki ka ce?”
Da sauri ta ce, “Ban ce komai ba Ya Taufeeq, zance ne irin na zuci”.
Ya yi murmushi cikin jin tausayin kansa, ya ce, “Ko?”
“Eh, amma me ya sa ba ta sonka Ya Taufeeq?”
“Watakila ban yi mata ba ne”.
“Kai din? Ita kuwa wane irin miji ta ke so bayan kai?”
Murmushi mai sauti Taufeeq ya yi, ya ce, “Kin san an ce shan koko daukar rai”.
Ta jinjina zancensa, sannan ta ce, “Yanzu yaushe za ka zo gida?”
Ya ce, “Kina so ki gan ni ne Kulsum? I thought bayan Turaki ba kya son ganin kowa?”
Ta kai tafin hannunta ta rufe idonta kamar yana ganinta.
“Ya Taufeeq na yarda da abin da ka ce… do away with him… amma ji nake har abada ba zan iya kara aure ba…”.
“Sabida kin rasa autan maza?” Ya katse ta.
Ta lumshe idanunta, ta ce, “Ba haka ba ne. Ban gane komai a cikin auren ba, sai bacin rai. Bana so a maimaita”.
Taufeeq ya yi ajiyar zuciya, ya ce, “Kulsum ko ni ne?”
Wayar ta cire daga kunnenta na ‘yan sakanni, kirjinta na bugawa sabida dukan da kalamansa suka yi mata. Cikin kasa da murya ya ce, “Ina son ki Kulsum, na ba ki lokaci ki yi tunani, tunanin abin da ya dace da ni, da ke. Ki karbe ni a matsayin miji ko a'ah. Duk matsayin da ki ka ba ni Kulsum zan karba da godiya. Sai dai idan ki ka sake ambaton Turaki a kunnena..... zuciyata za ta buga Kulsum!”.
Bai kara cewa komai ba ya katse wayar.
A wannan daren Kulsumu kwana ta yi tunani, mamakin mutum kamar Taufeeq dan gata gaba da baya ya ce yana sonta. Ba ta taba kawo hakan a ranta ba ko da wasa. Ta rasa a matsayin da zuciyarta ta amshi batun nan.
Shi kuma Taufeeq tun daga ranar bai barta haka ba. Text din safe daban, na dare daban mai jaddada kaunar shi gare ta. Ba ta da abin da zata ce mishi, ta tattara komai ta mika wa Ubangiji.
A karshen wannan watan Nasma ta kare karatunta, Hajiya da Daddy za su je graduation dinta a garin Nottingham din kasar Ingila. Kwarai Hajiya ta so su tafi tare da Kulsum, amma tana da jarabawar karshen zangon karatunta na farko. Don haka Kulsum da Serah kawai aka bari a gidan sai maigadi da ke bakin get. Yusha'u da ke kai ta makaranta sai da safe yake zuwa ya kai ta, in ta tashi ya koma ya dauko ta. Sai ta yi amfani da kadaicin wajen yin karatu yadda ya kamata. In abu ya shige mata duhu sai ta kira Aunty Sakeenah a waya ta warware mata.
Ana saura kwana biyu su Hajiya za su dawo, dawowarta daga makaranta ke nan ta zauna a dining tana shan ruwan sanyi sabida gajiya da kishin da ta kwaso. Aka danna kararrawar shigowa falon gidan. Ta tashi a hankali ta je ta bude, ba ta tsammaci ganinsa a wannan lokacin ba, don haka ta dan bude baki cikin mamaki, wanda ke hade da murmushi.
Taufeeq ne cikin fararen uniform dinsa na Nigerian Navy. Ya yi kyau har ya gaji. Ya daga mata gira ya ce, “Hello, Nurse”.
Ta rufe baki tana dariya, ta ce, “Ya Taufeeq kana hanya, amma ba ka gaya min ba in shirya maka better?”
Ya sa kafa ya karasa shigowa cikin dakin, ya ce, “Ai ke ce bettern. Ni ba ni hanya in wuce. Ya ya na ji gidan shiru haka?”
Ta ja da baya tare da karbe masa jakar da ya goyo a bayansa suka isa ga kujerun falon suka zauna.
Ta ce, “Hajiya da Daddy ai ba sa nan, sun je graduation din Nasma, sai jibi za su dawo”.
Ya ce, “Oh, yes Daddy ya gaya min na manta ne. How are you managing ke kadai toh?”
Ta ce, “Ba ni kadai ba ce, Serah tana nan. And my textbooks also”.
Ya yi murmushinsa mai aji, “To me zan samu express yunwa nake ji Aunty Nurse”.
Ta mike da azama ta nufi kicin tana fadin, “Ka ba ni minti sha biyar in ga abinda za'a samu".
Murmushi ya sake yi, ya bi ta da kallo admiringly har ta shige kicin din.
Cikin mintuna sha biyar din da ta ce kuwa ta hado masa vegetarian meal dinsa. Har gabansa ta kawo ta ja karamin tebur ta dora.
Taufeeq ya dube ta da murmushi, ya ce, “Thank you”. Sannan ya kara da, “I’m here just to see you, Kulsum kin hana ni sakat, kin hana zuciyata sukuni. Don Allah ki tallafe ni ko na samu sa’idah”.
Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi.
Ya ce, “Kulsum?”
Yadda ya fadi sunan a hankali kamar mai rada sai da Kulsum ta ji shi har ranta. Ta dago ba tare da ta shirya wa hakan ba, ta kai dubanta gare shi, kwayar idanunsu ya sarke ta yadda ba za ta iya janyewa ba in ba shi ya ba ta damar hakan ba.
“Kin amince in gabatar da ke ga su Daddy a matsayin matar aurena? Zan barki ki yi karatun ki har sai kin ce ya ishe ki. Zan mantar da ke tsohon mijin ki har sai kin yarda shi din ba autan maza ba ne. Zan ba ki soyayya da kauna har sai kin amince cikin matan duniya ke ta musamman ce. Ki ba ni dama Kulsum, Kulsum don Allah!”.
A hankali ta kai tafukanta ta rufe fuskarta, kawai ji ta yi ta yarda da Taufeeq, ta amince da kowacce kalma ta bakinsa. Ba ta san sanda wadannan kalaman suka fito daga bakinta ba.
“Yaya Taufeeq ina da lalura wadda ta sa na cire aure daga zuciya ta. Tunda aka haife ni nake fitsarin kwance har girma. A yanzu haka ba ni da tabbacin na daina ko ban daina ba. Ka yi hakuri ka nemi mai lafiya kamar ka ka aura, bana so in zame maka lalura. Har yanzu magani nake sha”.
Taufeeq yana da kima a idanunta, ba ta so ta fito kiri-kiri ta ce da shi, Turaki kawai ta ke so a duniya. Hakan zai zama cin fuska kuma zai gane cewa, duk abin da ya fada mata, iyayenta ma suka fada mata na ta manta da Turaki ta bayan kunnenta yake bi. Turaki bai shig rayuwarta don ya fita a sanda ta ke so ba.
Amma ga mamakin ta budar bakinsa, sai cewa ya yi.
“Kulsum, ina son ki da dukkan lalurar duniya da ke tare da ke. Zan kuma zauna da ke a haka. Kin amince in gabatar da zancen mu ga manya?”
A wannan matakin, ba ta da wani tunanin yi, ta yi duba ga wane ne Taufeeq da gatan da yake ciki, ta kwatanta da nata gatan, amma ga shi ya nace yana binta da kokon barar soyayya. Duk da lalurarta abar kyama data sanar da shi. Ta tuno tarin alkhairin mahaifiyarsa da ‘yan uwansa gare ta. Ko ita butulu ce ya kamata ta duba halacci. Don haka ta samu kanta da daga masa kai alamar ta amince.
Da yana da dama a wannan lokacin rungume ta zai yi don ya nuna mata iyakar farin cikin sa. Da ba shi da damar hakan sai ya rausayar da kai tare da lumshe idanun sa ya ce.
“Na gode Kulsum, kuma insha Allahu ba za ki taba yin nadamar zamantowa ta mahadin rayuwar ki ba!”.
A kwana biyun bakidaya yana like da ita, tana musu girki yana taimaka mata, ko ya zauna ya yi ta mata hira. Sosai suka shaku ta kuma fahimci Taufeeq mai matukar saukin kai ne ba kamar yadda ta dauke shi a baya ba. Idan yana son abu yana mishi so ne da dukkan zuciyarsa, haka idan yana kinsa ba ya iya boyewa. Shi ya je ya dauko su Hajiya ranar da za su dawo lokacin ita tana makaranta.
Sai dawowa ta yi ta tadda Nasma a gida, dakin Hajiya ta fara zuwa ta yi mata sannu da zuwa. Hajiya ta ce, “Sannu da gida Kulsum, da fatan mun same ku lafiya, ya ya jarrabawar?”
Ta ce, “Alhamdu lillah, gobe insha Allah za mu gama, za mu samu dan hutu, ina son zuwa wajen su Goggo”.
Hajiya ta yi dan shiru sannan ta ce, “Zuwan ki Gaya ba yanzu ba Kulsum, ki bari sai can gaba. In dai Goggon ki ke son gani kawai zan sa Yusha'u ya dauko ta ta kwana mana biyu”.
Kulsum har da dan tsallenta don murna, ta ce kuma a dakinta za ta sauki Goggon. Ta fice cike da murna ta samu Nasma a falo ta dora kafa daya kan daya tana kallon talabijin tana shan ice-cream, ta ce, “Kulsum me Mum ta ke ba ki ne? Kin yi girma kin kara fari sai wani glowing ki ke yi idanunki na sparkling?”
Dariya ta yi ta zauna kusa da ita ta ce, “Ai dai ban kai ki ba Aunty Nasmah”.
Ta ce, “To ya karatun? Ina fatan ba ki da matsala?”
“Alhamdu lillahi ko da matsala Aunty Sakeenah na kokari a kai”.
Nasma ta ce, “To masha Allah, have some ice-cream”.
Ta debo a cokali ta nufo bakinta.
Dariya ta yi ta bude bakin kenan za ta karba suka yi ido hudu da Taufeeq da ke shigowa, ba shiri ta rufe bakin sai kuma ta kware ta soma tari.
Nasma ta juya don ganin abin da ya kwarar da ita, ta ga Taufeeq ne. Ya zuba hannayensa biyu a aljihunsa yadda ya saba ya zuba mata lumsassun idanunsa.
Ta sake juyawa ta dubi Kulsum nan da nan ta fahimci akwai wani abu.
“Ya Taufeeq, ice-cream zan ba ta fah, ta ganka ta kware”.
“To me ye wani za ki ba ta ice-cream, ita jaririya ce?”
Ya samu kujerar da ke kallon ta Kulsum ya zauna. Ai da sauri ta tashi ta yi daki, ya ce, “Tafi a hankali kada ki yi tuntube mana”.
Nasmah ta ce, “Ai kawai ka goyata ka kai ta dakin”.
Ta bi bayan Kulsum da gudu kada ya make ta.
A washegari da zai koma Lagos ya samu Hajiya a daki ya gaya mata sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login