Showing 21001 words to 24000 words out of 34734 words
jan zuciyar diya mace, tamkar jan wutar lantarki. They makes her feel unease, shi ya sa ta zabi kebe kanta muddin yana wuri.
Hajiya ta dube shi bayan Daddy ya tashi ya koma tsakiyar kujerun kayataccen falon ya murdo tashar CNN ya kure sautin yana sauraron labarai. Ta dago ido ta dubi dan ta Taufeeq, a tsanake ta kalle shi na ‘yan sakanni, kafin ta ce.
“Na ji sakon ka wajen mahaifinka, amma ko ka san Kulsum na da lalura? Dalilin da ya sa na dauko ta ma ke nan bayan karatu, za ka iya aurenta a haka?”
Taufeeq ya daga kyawawan idanunsa ya dubi mahaifiyarsa, a tsanake ya ce, “Wace irin lalura ce Mum?”
Hajiya Nasara ta dube shi, tana son fahimtar yanayinsa, ta ce, “Fitsarin kwance ta ke yi, tunda aka haife ta”.
Taufeeq ya zuqi numfashi ya fesar, (a bit confused) ya ce, “Fitsarin kwance as in tana barci ta yi fitsari cikin barci?”
Hajiya ta ce, “Shi fa”.
Ya yi dan jimm! Kafin ya ce, “Mum, ai ni ita kawai nake so, bana jin hakan zai hana ni aurenta, zan kuma nema mata magani har Allah ya sa mu dace. Idan kuma ba ta warke ba zan zauna da ita a haka, to the very end. Ni dai ki yi min alfarma ki ba ni aurenta”.
Jikin Hajiya Nasara ya yi mugun sanyi, domin ba amsar da ta tsammata daga gare shi ba ce. Danta ko cikin ‘yan gayun samari ajin farko ne. Ko cikin masu tashen ilimi shi Navy Officer ne (sojan ruwa). Bai taba ce mata ga yarinyar da yake so ba a tsayin shekarunsa talatin da uku da haihuwa. Ya tsallake duk ‘yammata a UK ya zo ya ce ‘yar qauyen Gaya yake so, kuma mai lalurar fitsarin kwance. And he is willing to stay with her cikin lalurar tata ba tare da ta warke ba. Don haka ta yarda ciki al’amarinsa gaskiya ce ziryan.
Amma ita wane bayani za ta iya yi wa iyayen Kulsum ba tare da sun zarge ta da son kai ba? Ga maganar tsohon mijinta da ke bibiyar nemanta har gobe, kuma ta sani su Goggo na son zancen sa, don dai sun bi abin da ta ce din ne kawai don sun san ta yi ne don amfanin Kulsumu. Yanzu kuma ta je ta ce musu Dan cikinta zai auri Kulsumu ai ba ta da hujjar kare kanta daga zargin su na kasancewa mai son kai.
Kwarai za ta so Kulsumu ta zamo suruka a gare ta domin a dan zaman da ta yi da ita ta gama yarda da kyawawan halayen ta. Sannan ta shiga ranta yadda ba a zato. Abin farin cikinta ne Taufeeq ya aure ta, to amma ba dai yanzu ba!
Ta yi ajiyar zuciya ta daga kai ta dubi Taufeeq din, ta ce, “Ka yi hakuri mu bi lamarin nan a sannu, babu bukatar gaggawa a cikin sa. Ka bai wa Kulsum lokaci. Aure ko soyayya ba nata ba ne yanzu. Ka bar wa Allah lamarin ka yi addu’a. Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku”.
Taufeeq ya ce, “Na ji abin da ki ka ce Mum, sannan na fahinta, amma don Allah ki bar ni in nemi yardar ta a hankali. Na yi alkawarin ba zan hana ta karatu ba”.
Hajiya Nasara ta ce, “To Taufeeq na amince, sannan Kulsum amana ce a hannun mu, na rabo ta da iyayen ta ba don ba su da yadda za su yi da ita ba, ko don sun gaza a kanta, a’ah, sun ba ni ita ne sabida yarda da suka yi da ni. Don haka sai ka san irin mu’amalar da za ta kasance a tsakaninku. Wadda ba za ta zamo ta Allah wadai ba”.
Taufeeq ya kwanta a kan gadonsa a wannan daren, ya lumshe idanunsa yana tunano maganganun da suka yi da mahaifiyar sa a ranar a kan Kulsum. Maimakon abin da ya ji na lalurar fitsarin kwance ya sagar da gwiwarsa a kan Kulsum, sai ya ji his feelings for her heightened.
Da ma har yanzu akwai masu irin wannan lalurar a duniya? Ina ma shi likita ne? Likitan ma wanda ya yi specializing a kan lalurar Kulsum. To ko dalilin da ya sa Mum din sa ta kai ta wajen Sakeenah ke nan? Allah Sarki Kulsum! Ubangijin halitta ya kyautata halittar ta da halayyar ta ta kowanne bangare, amma sai ya jarrabce ta ta wannan bangaren. Fitsarin kwance nakasa ne ba kadan ba, musamman ga diya mace. To ko wannan ne dalilin da ya sa mijin nata ya guje ta? Shi ji ya yi hakan ya kara sanya masa son ta da tausayin ta.
Wahegari Kulsum na kicin tana kwaba wa Hajiya fulawar da za ta yi cincin da ita, Taufeeq ya shigo kicin din, kayan barci ne a jikinsa farare ‘yan gidan Ralph Lauren da alama ko wanka bai yi ba. Da Kulsum ya kwana a zuciyarsa da ita ya wayi gari, ya san kuma kicin shi ne wajen da zai ganta a daidai wannan lokacin.
Ilai kuwa yana shigowa ya yi tozali da ita. Wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki, ya jingina da cabinet din kicin din yana kallon ta. Hankalin ta gabadaya yana kan fulawar da ta ke murzawa da hannunta ba ta ma lura da shigowar sa ba.
Taufeeq ya shagala sosai da kallon ta har bai san adadin mintunan da ya bata a tsaye ba. Daga bisani ya kira sunanta cikin taushin murya.
Da hanzari ta dago dara-daran idanunta ta dube shi.
“Barka da kwana, kana son wani abu ne?”
Don dai ita ba ta taba ganinsa a kicin ba.
Ya ce, “Ba abin da nake so. Na zo ne in taya Kulsum hira”.
Dan murmushi ta yi, a ranta ta ce, da sassafen nan?
“Ga shi kuma ina yi wa Hajiya aiki”. Kulsum ta fada cikin sanyi.
“Ba matsala, sai mu yi tare”. Taufeeq ya ba ta amsa.
Dan murmushin ta sake yi har dimples din suka lotsa ciki sosai.
Taufeeq ya rungume hannayensa a kirji, yana kallon ta keenly, ya ce, “Na zo ne mu kulla abota ni da kanwata Kulsum”.
Murmushin ta sake yi har yanzu ba ta ce komai ba, kuma ba ta dago ba. So ta ke ta ce da shi, ai mace da namiji ba sa abota, amma ba za ta iya doguwar magana da shi ba. Tsoron maza ta ke ji, sannan tana jin nauyin sa sosai fiye da komai, ba ta son kallon kwayar idanunsa.
Ya kara kankan da murya, ya ce, “Kulsum please, can we be friends? Sabida ke na baro aikina na taho. In ban zama abokin Kulsum ba ba zan iya aikin ba”.
Wannan karon da dumbin mamaki ta cira kai ta dube shi. Anya Taufeeq ne Yayan Dr. Sakeenah da ta sani? Mutumin da a farkon zuwansa yake mata kallon kaskanci? To ya yi abota da ita ya samu me a cikin abotar? Ita Kulsumu jikar Goggo ‘yar kauyen Gaya wadda ba ta aje ba, ba ta kuma ba wani ajiya ba?
Taufeeq ya fahimci ba ta da abin cewa, sannan he is not welcome in dai Kulsumu ce. Don haka ya sauya akalar hirar tasu ta koma ta karatu, ai kuwa nan da nan ya samu bakin Kulsum. Shi dai burin sa ta sake da shi, sai ta saki jiki da shi ne zai samu damar bayyana mata manufar sa a hankali. So yake su fahimci juna sosai, ya shiga rayuwarta ta yadda duk ranar da ya bayyana mata manufarsa a fili za ta fahimce shi.
“Me ya sa duk fannonin karatun medicine ki ka tsallake su ki ka zabi zama Nurse Kulsum?”
Zuwa lokacin ta gama kwabin da ta ke yi, tana wanke hannunta a sink. Ba tare da ta dube shi ba, ta ce, “Sabida in taimaka wa ‘yan uwana mata da kananan yara. Bana jin dadin yadda ake treating dinsu a asibitoci, musamman asibitocinmu na karkara, sai na zama Nurse ne zan iya bada gudunmawata fully ga mata da yara. A can gaba ina so in yi specializing as a Professional Perioperative”.
Taufeeq ya jinjina kai, sannan ya ce, “Amman kuma zai hana ki samun cikakken lokacin mijinki, ba karamin mai hakuri ne zai yarda matarsa ta dinga kwana a wajen aiki ba”.
Da sauri ta ce, “Yaya Taufeeq ni ai ba zan yi aure ba!”.
“Sabida me?” Taufeeq ya tambaya curiously.
Dan jim ta yi kafin ta ce, “Saboda na yi ban ji dadin sa ba”.
Taufeeq ya ce, “Me ya hana ki jin dadin nasa, bayan an ce Dan Sarki ne ma mijin naki?”
Kulsum ta kasa dagowa ta dubi Taufeeq, don ba ta san bayanin da za ta yi masa ya gane ba. Turaki bai kasance mai adalci a gare ta ba ta kowanne bangare. Wanda hakan ya sa ta ke alakanta gabadayan maza da halin Turaki, wanda in sun fahimci mace na son su kamar ta mutu sai su yi amfani da hakan su cutar da ita, su barta da karyayyar zuciya, sannan su guje ta. Kada Allah ya maimaita mata aure in dai duk maza irin Turaki ne.
A fili ta ce, “Ba ya sona! Bai taba sona ba!!”
Magana ta yi a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ta ba.
Taufeeq ya tsura mata ido, zuciyarsa na racing ya ce, “Kuma sai aka ce duk mazan duniya ba za su so ki ba, sabida dan Sarkin Gaya ya ki ki?”
Kulsum ta ce, “Daga na gaba ake gane zurfin ruwa! Ina da abin da zai ki ni a kansa. Don haka ban ga laifinsa ba da ya kasa zama da ni”.
Ta rasa abin da ya sa ta ji zuciyar ta ta yarda da Taufeeq har ta ke fallasa masa sirrin zuciyarta. Abin da ba ta taba fada wa kowa akan Turaki ba.
Taufeeq ya fahimci in yana son zama very close to Kulsum sai ya janye zancen soyayya a tsakaninsu. Ba karamar illa Turaki ya yi wa zuciyar ta ba. Kuma duk da hakan har gobe she has some kind of strong feelings for him. Which makes him jealous…..(wanda ya sanya shi kishi).
Ya ce, “Kulsum, ba ni labarin auren ki, ki ba ni labarin Turaki”.
Dan murmushi ta yi, ta ce, “Babu wani abin karaswa a kai. It is a very short marriage, which ended abruptly kamar kiftawar ido… he don’t like me at all…”.
Taufeeq ya cusa hannunsa cikin tarin kwantacciyar sumar kansa yana kokarin boye kishin da ya harzuqo masa, domin ya gane zance in na Turaki ne Kulsum na maraba da shi.
“Ke kuma kina son shi… har ba ki ji dadi ba da ya rabu da ke… har kike alaqanta sauran maza dashi, sabida shi ne autan maza…”.
Bude baki ta yi tana mai dafe bakin da yatsun ta tana dariya, dariyar data sa Tawfeeq shagala cikin kallon ta, ta ce, “ ba haka bane Yaya Taufeeq…”.
Taufeeq ya ce, “Haka ne mana! Tunda ga shi har kina fadin ba za ki yi aure ba tunda ya rabu da ke…”.
Ta yi saurin gyara masa da cewa, “Ba shi ya sake ni ba… Maimartaba ne ya raba auren…”.
Taufeeq ya hadiye wani kullutun kishi da ya sake tokare shi a makoshi… ya yi ta maza in ji mata, ya ce, “Well, idan na fahimce ki Kulsum ba aure ne baki so ba, sauran maza ne ba ki so, amma kina son tsohon mijin ki. Ni kuma sai na ga gara ka auri wanda ke sonka, a kan ka auri wanda ka ke so.
As a brother, (a matsayin dan uwa) shawarar da zan ba ki ita ce, ki bude zuciyar ki ki kaunaci masu kaunar ki. Ni a wurina Turaki ba shi da uzurin da zan karba wanda zai tabbatar min ya na son ki.
Ya tafi shekara da shekaru ba sako ba aike kamar yadda Hajiya ta gaya mini, so do away with him from your life Kulsum kamar yadda iyayen sa da kan su suka hango miki, Turaki ba ya sonki!”
Ta san iyakar gaskiyar ke nan, amma ta rasa me ya sa ta yi mata daci? Ba shi ne mutum na farko da ya fada mata hakan ba zuciyar ta ta sha fada mata, Hajiya Nasara ma ta fada, amma sai ta ji ta Taufeeq ta fi ta kowa yi mata daci. Ta ya za ta yi ta fahimtar da su son da ta ke wa Turaki ba yin kanta ba ne? Wani al’amari ne daga Allah wanda ba ta san musabbabinsa ba?
Hawaye suka ciko idonta, amma ta yi kokarin maida su. She don’t want to shed tears for Turaki… Faduwar za ta yi mata yawa.
Taufeeq ya tako har gabanta ya tsaya, hannayensa biyu zube cikin aljihu, ya ce, “Na ba ki assignment Kulsum, ki je ki yi kokarin da za ki yi ki cire tunanin ba za ki yi aure ba, saboda dan Sarkin Gaya. Rayuwa ba haka ta ke ba, every disappointment is a blessing. In wani ya ki-ka da wuni, wani da kwana zai so ka! Ki ba wa wani daban dama ya shigo rayuwarki bayan Turaki, ki sa a ranki abin da ya sa ki ka baro Gaya ba don ki yi karatu ne kadai ba, har ma da samun sabon abokin rayuwa, wanda zai kaunace ki against all odds. Na barki da wannan. Mu wuni lafiya”.
Wunin ranar zungur ta yi shi ne da tunanin maganganun Taufeeq Mohammed Bello, wadanda ta auna ta ga cewa gaskiya ce zallah ya gaya mata. Ta amince za ta bi shawarar sa, za ta ci gaba da kauda Turaki daga kan hanyar ta. Matsalar ikon hakan ba nata ba ne. Ko ta yi kokarin hakan ba ta cin nasara. Ta amince an halicce ta ne domin ta rayu da soyayyar Turaki, soyayyar wanda bai san tana yi ba.
Washegari Taufeeq ne ya kai ta makaranta da kansa. Ya yi hakan ne domin ya samu damar yin sallama da ita. A gobe zai koma Lagos, kokarin sa na son ta sake da shi ya fara yin nasara.
Suna tafe a hanya ya ce, “Kulsum me zan samu? Gobe zan koma Lagos”.
Dan murmushi ta yi, ta ce, “Me nake da shi da zan ba ka Yaya Taufeeq?”
Ya juya kan motar ya shiga harabar makarantar, sannan ba tare da ya juyo ya dube ta ba, ya ce, “Your phone number”.
Ta fadada murmushin ta tare da cewa, “Don dai wannan ba ni wayarka in sa maka”.
Hannu ya mika ya dauki wayar daga inda ya ajiye ta a aljihun motar ya ba ta. Ta juya kyakkyawar wayar samfurin Iphone a hannunta, sannan ta soma dialing lambobinta a ciki. Ta yi saving da (Sister Kulsum) ta mika masa.
Daidai lokacin da ya yi parking a parking lot (wurin adana motoci) ya kashe motar ya juyo ya dube ta with affection (cike da kauna) cikin kwayar idanunsa.
“I will call you tonight, (zan kira ki da dare) Yusha'u zai zo ya tafi da ke, ni akwai inda zan je. Gobe in na tafi zan yi kewar abokiya ta Kulsum”.
Ta yi ‘yar dariya, abokiyar nan da yake fada yana amusing dinta. Don dai ita ba ta san mace da namiji na wata abota ba.
Ya kwantar da kai a kan sitiyari, murya can kasa ya ce, “Kulsum za ki yi kewata?”
Yadda ya yi maganar loving and romantic kamar ba Taufeeq ba. Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta, ta rasa me ya sa ta ji kunya. Watakila yadda ya yi maganar ne.
Ya bude mata kofar side din ta ta fita tana saba jakarta.
“Yaya Taufeeq na gode”.
Ta juya ta soma tafiya, shi kuma ya bi ta da kallo. Ya rasa irin son da zuciyarsa ke ma Kulsum, mai mamaye zuciya haka farat daya.
Sai da ya daina hango ta, sannan ya yi reverse ya bar makarantar.
******
University Of Reading, UK.
Har ya shigo ofishin ya zauna bai sani ba. Ya dora haba a kan hannayensa yayi zurfi a tunani. Dr. Abdul’Ahad Maikano, ya sa hannu ya kwankwasa tebirin da yake tsakaninsu. A hankali ya dago ya dube shi, idanunsa sun kada sun yi jazir.
Abdul’Ahad ya ce, “Dr. Abubakar ko lafiya tunda ka dawo ban ganka ba? Ban ji feedback na zuwan ka gida