Showing 30001 words to 33000 words out of 34734 words
ta ce, “Rike goronka tunda ka gwale ni”.
Engnr. Farouq ya shigo falon, ya mike ya ba shi hannu, ita kuma Kulsum ta wuce dakinsu.
Nasma da ke taje dogon gashin kanta ta ce, “Kamar muryar Yaya Taufeeq nake ji a falo?”
Ta amsa mata da, “Shi ne”.
Nasmah ta ce, “To fa shi ke nan yanzu ba sauki, ga shi muna da wajen zuwa, gidan su wata course mate dina za mu je”.
Ya karaso har kofar dakin nasu, ya ce, “Kulsum, abin ma haka ne ko? Za ki zo amma jiya ba ki gaya min ba?”
Tana kawar da kai daga gare shi, ta ce, “Ni ma ban san da tafiyar da wuri ba, don da Aunty Nasmah ita kadai za ta zo”.
Nasmah ta ce, “Ba wani nan, ko sanda ku ke waya jiya ai kin dade da kulle jakar kayanki”.
Ya jinjina kai, ya ce, “Na gode Kulsum, na kwana da sanin ba ki damu da ni ba ai. Ni kadai nake bilinbituwa ta…”.
“Yanzu dai Ya Taufeeq ka dauke mu ka kai mu Lekki gidan su kawata Iftihal, sai ku yi soyayyar a hanya kada ku shiga lokaci na”. In ji Nasmah.
“O.K, ku fito ina jiranku”.
Bakar Abaya ta fiddo za ta dora a kan kayan jikinta, wadanda english wears ne ba masu kama jiki ba, cikin tsarabar da Nasmah ta kawo mata, amma sai Nasmah ta karbe. Wata dakakkiyar shadda dark pink wadda aka yi wa dinki Senegalese ta fiddo mata cikin dinkunan da Sakeenah ta yi mata, tana faman mitar, “Ban san yaushe za ki shigo gari ba Kulsum, kullum ana fiddo ki kina nokewa”.
Kwalliya sosai ta yi mata, sannan suka tadda Taufeeq a mota bayan sun yi wa Dr. Sakeenah sallama.
Suna tafiya zuwa Lekki, Taufeeq na tsokanarta.
“Ka ga amaryar Taufeeq M. Bello ta kashe kala”.
Ta sha kunu sosai sannan a shagwabe ta ce, “Wallahi Aunty Nasmah ce ta takura min na yi kwalliya”.
Ya ce, “Tana so ki burge Yayanta ne, kuma kin burge shin. Duk kin dusashe hasken sauran mata daga idanun sa”.
Ya daga wayarsa ya kashe ta da hoto. Ta yi narai-narai da ido sai hoton ya bada wata irin kala mai kyau.
Tarba ta musamman Iftihal kawar Nasmah ta yi musu. Ba su dade sosai ba sabida Taufeeq da ke damun Nasmah da waya. Sai da ta gwammace ba ta sa shi ya kawo su ba. Ta san arzikin Kulsum ta ci da har ya yarda ya kawo su din.
A hanyarsu ta komawa gida, shopping sosai ya tsaya ya yi wa Kulsum, Nasmah na taya shi zabe.
A kwanaki bakwai da suka yi a Lagos, kullum sai Taufeeq ya zo wajen Kulsum in ya taso daga aiki, a gidan yake cin abincin dare. Kullum kokarinsa Kulsum ta sake da shi, ta yarda za ta ba shi martanin soyayyar da yake yi mata, amma kullum jiya-i-yau, Turaki ya yi wa zuciyar Kulsum babbar illah, duk da ta cire shi a ranta, ba ta da hope a kansa, amma ba ta jin bayan shi za ta iya kara sanya wani Da namiji a zuciyar ta.
Sai dai tana martaba Taufeeq sabida mahaifiyarsa da ‘yan uwansa da ke rikonta bilhakki.
Ta dawo gida ranar lahadi, litinin ta koma makaranta. A can ta baro Nasmah wadda za ta kwana biyu kafin ta dawo.
*** *** ***
BAYAN SHEKARA HUDU
Kamar kiftawar ido, haka shekarun suka zo suka mirgina, abubuwa da yawa sun faru a cikinsu. A shekaru hudun Ummu Kulsum Abdulhadi Yalleman ta fiddo da HND in Nursing. An yi bikin Batulu shekaru biyu a baya, tana garin Kaduna tare da mijinta Abdulkadir ma’aikacin GT Bank, yaranta biyu mace da namiji twins.
Wannan ne lokacin da Hajiya Nasara ta deba wa Taufeeq na jiran Kulsumu, don haka zuwa yanzu kusan kowa nata ya san da zaman Taufeeq, ya je har Gaya da 'Yalleman ya gabatar da kansa. Yanzu burin kakanninta shi ne kawai ta yi aure. Amma Kulsumu kullum tausarsu ta ke yi kan su barta ta yi hidimar kasa, ta fara specialization dinta.
Daddyn su Taufeeq ne ya sa hannu aka barta yin hidimar kasa a Abuja, inda bayan camping suka tura ta National Hospital.
Shekara daya baya suka sha bikin Nasma da masoyinta Mujaheed dan abokin Daddynsu, Mujaheed ma’aikacin Shell Company ne, suna zaune garin Port-Hearcourt.
Kulsum Abdulhadi, cikakkiyar ma’aikaciyar jinya mai shekaru ashirin da hudu, a wannan lokacin komai nata ya kai ya kawo. Ta samu wayewar kai irin wadda zurfin ilimin boko ke sabbabawa mai shi. Wayewa mai tafe da rikon addini. Ta canza gabadaya daga Kulsumun Goggo zuwa Kulsum din Nasara. Ba abin da Goggo Shatu da mijinta za su ce wa Hajiya Nasara sai addu’ar alheri, domin ta zama bayan da ya goya marainiya Kulsum ta tsaya da kafafunta, ta cika burinta na zamowa mai amfani ga al’umma.
Zuwa wannan lokacin ko ta ki ko ta so, ta tsayar da Taufeeq a matsayin mijin da za ta aura, sabida dalilai masu yawa da ba za su kidayu ba. Muhimmi shi ne mahaifiyarsa, sannan ‘yan uwansa mata da suka ba ta kaunar ‘yan uwantaka irin ta 'yan uwa na ciki daya wadda ba ta taba samu a rayuwarta ba. Ta manta ita din marainiya ce. Turaki ya zama wani rufaffen kundi (littafi) wanda ba a bukatar a bude shi. Ya zama past, wani irin past da ba ta ko son tunawa, domin babu wanda ya taba barin tabo a zuciyar ta kamar sa. Ba ta taba hasaso future dinta da shi ba. He is her past and Taufeeq her present.
*** *** ***
Tana kammala hidimar kasa su Goggo ba su biye mata ba, suka saka ranar aurenta da Taufeeq watanni uku masu zuwa, in don ta ita ne a barta ta je Yola ta yi shekara daya don zama cikakkiyar Perioperative Nurse.
Zumudi a wajen Taufeeq abin ba a cewa komai. Zuwa yanzu ya daina damuwa da son martanin soyayya daga Kulsum, mu’amalarta da shi saffa-saffa. Ba ta zafafa a ciki ba, shi ma kuma ya ja girmansa bai cika takura mata ba. Amma daga lokacin da aka sanya musu ranar aure gabadaya ya canza, soyayya yake nuna mata a sarari kamar ya cinye ta. Ita kuma in ta tuna cewa ba a budurwa zai aure ta ba duk zumudin nan da yake nunawa a kanta, sai jikinta ya kara yin sanyi. Ita bazawara, shi saurayi, wannan abu yana damunta a rai. Amma shi ko a jikinsa. Ta lura ba karamin shiri yake yi wa aurensu ba. Gidan da za su zauna a Lagos ya gama gyara shi, ya wadata shi da komai na rayuwa.
Biki saura sati biyu, Goggo Shatu ta ga ya kamata ta je ta sanar da Umma auren Kulsum, amma nauyi ya hana ta. Ta ga cewa kuma in ba ta sanar da ita ba, hakika ba ta kyauta ba, alakar da ke tsakaninsu ba Turaki da Kulsumu ne suka hada ta ba, don haka bai dace a ce su za su raba ba. Ta san ta yi musu babban laifi, amma ba ta da yadda za ta yi ne, ta kuma ji dadi da har gobe Umma ko Maimartaba babu wanda ya taba saka baki a kan komen Kulsumu, wannan ne ya ba ta karfin gwiwar amincewa da maganar Dan Nasara.
Shekaru biyun baya Abubakar Turaki ya zo tare da abokinsa, ban hakuri na duniya babu irin wanda ba su yi ba, amma ta yi abin da har gobe yake damunta; kafewa kan bata san inda Kulsumu take ba, wanda sanadin hakan ne ya sa watakila Turaki bai sake takowa kofar gidansu ba.
Ta hanga ta duba ta ga ba mafita, dole Umma ta san da auren Kulsumu, don haka ta kwashi kunyarta a tafin kafarta ta tafi gidan Sarki.
Umma na lale marhabin da zuwan Goggo kamar yadda ta saba, kuma ta cika gabanta da kayan makulashe. Sun dade suna gaisawa, sannan suka barke da hira, inda Umma ke sanar da Goggo nan da sati biyu za a yi bikin Nana babbar ‘yar Yaya Hadiza a garin Kiru, ko Goggon za ta samu zuwa?
Goggo ta yi dan jim! Kafin ta ce, “To ai ni ma gayyatar bikin ce ta kawo ni, auren Kulsumu ne ya tashi da dan marikiyarta, shi ne na zo in gaya miki”.
Wani irin rikicewa Umma ta yi, amma ta yi kokarin rike kanta a gaban Goggo ba ta nuna dukan da maganar auren ta yi mata ba. In suna da matsala a yanzu kan ‘ya’yansu, to matsalar Turaki ce, ya ki aure har gobe yana jiran dawowar Kulsum rayuwarsa, Turaki ya dangana da neman Kulsumu ne ba don ya hakura ba, sai don fahimta da ya yi cewa, iyayenta ba sa bukatar sauran alaka a tsakanin su. Har gobe ba ta fidda rai da dawowar Kulsum cikin iyalinta ba, domin Allah ta ke son yarinyar ba kuma ta yi wa Turaki sha’awar kowacce mace bayan Kulsum. Ashe babu rabon sake shigowar ta cikin rayuwar su?
Wani guntun hawayen tausayin Turaki ne ya zubo mata, ta yi kokarin dauke shi da dan yatsanta, ba ta bari Goggo ta gani ba don kada ta karya mata zuciya. Ta ce,
“Masha Allahu, Kulsumu aure ya zo! Allah ya sanya alkhairi Ya bada zaman lafiya da zuri’a mai albarka”.
Goggo a zuciyar ta ta ce, “Amin”. Ta kasa amsawa a fili, saboda ganewa da ta yi Hajiya Rakiya hawaye ta ke yi.
Ba ta jima ba suka yi sallama, kowa jiki a sanyaye.
A daren Umma ta samu Maimartaba ta gaya masa maganar auren Kulsum. Ba ta fahimci komai a tare da shi ba.
Washegari da ta shigo kawo masa karin kumallo ya ce, “Na bada umarni a yi wa yarinyar nan kayan daki kamar yadda na alkawarta a baya. Sai ki samu wadanda za su je su kai wa iyayenta. Allah ya sanya alkhairi”.
Umma don takaicin sa tashi ta yi ta fita ba tare da ta ce komai ba.
Saura sati daya biki Nasma ta zo Abuja tana tura tsohon cikinta. Aunty Sakeenah ta roki Hajiya Nasara amarya ta je Lagos a can za ta sa a yi mata gyaran jiki. Kuma a can za a yi dinner din ango da abokansa wadda Nigerian Navy suka shirya masa kafin daurin aure. Hajiya ba da son ranta ba ta yarda ita da Nasma da mijin Nasma Mujaheed suka tafi Lagos.
Mai gyaran jikin da Sakeenah ta dauko ‘yar Sudan ce mazauna Lagos, tun washegarin zuwansu ta fara aikinta a kan Kulsum. Sakeenah ta hana Taufeeq ganin amaryarsa ko da wasa, ya zo gidan ya fi a kirga ta hana shi ganinta. Shi kuma ya hada baki da Mujaheed mijin Nasma kan ya san yadda zai yi Nasma ta kawo masa Kulsum, shi dai ya ganta ko na minti biyu ne. Mujaheed ya tausaya masa, ya dau waya ya kira Nasma.
“Sweety har yanzu ba a gama muku gyaran jikin ba ne?”
Nasma ta ce, “An gama na yau, saura na gobe. Wani abu?”
Ya ce, “Ba wani abu, Yayanki ke son amaryarsa ta zo su je wajen telan da zai dinka kayansu na dinner, telan ya ce dole sai ta zo da kanta kayan za su fi fitting dinta. Amma don Allah kada Sakeenah ta san kun fito, ba za ta bari ba”.
Nasma ta ce, “Ba wani abu, we will be there in 25 minutes, Aunty Sakeenah sun fita da Engnr, amma ba za mu dade ba ko?”
“Ko minti talatin ba za ku yi ba insha Allahu”.
Nasma ba ta gaya wa Kulsum inda za su ba, har ta yi parking a kofar gidan Taufeeq. Wani kyakkyawan mansion mai kyau da tsari a Lekki. Har suka shiga falon farko inda ta ci karo da hotonta window size. Ba a dade da yi mata dilka da halawa ba, sai sheki ta ke yi, ga wani sihirtaccen kamshi da ke tashi daga jikinta.
Tana juyawa daya barin ta tadda the same window size na hoton Taufeeq, nan ta gane inda suka zo. Suna ta sallama shiru, sai Nasma ta ja hannunta suka kutsa har bedroom din Taufeeq, amma ba ya nan, kuma babu Mujaheed, ta ce da ita ta zauna ta duba su a backyard, ta kira wayar Mujaheed bai dauka ba.
Nan Kulsum ta samu wuri ta zauna a kan sofa kwaya daya da ke dakin.
Wata irin kishirwa ce ta dameta tun kafin su taho. Tana juyawa ta yi arba da bedside fridge din Taufeeq. Mikewa ta yi a hankali ta isa ga dan karamin firjin ta rage tsawon ta tana addu’ar Allah ya sa ta samu Maltina. Best drink dinta kenan. Sai dai me? Kwalaben da ta gani a jere a ciki ba ta taba ganin irin su ba, wasu dogaye da su masu fadi daga kasa.
Da sauri ta zaro kwalba daya, ta bi rubutun jikin su da kallo "whisky" baro-baro. Wato “GIYA" ga su nan kala-kala na zamani, masu karshen tsada.
Jin takunsu ta yi ana nufo dakin, da sauri ta mayar da kwalaben yadda ta gansu, ta koma bisa sofa ta zauna, kirjinta na wani irin bugawa da sauri da sauri. Numafshin ta na neman daukewa. La-shakka da tana da asthma da hawan jini ba abinda zai hana su tashi a wannan lokacin.
Wannan duhun da ya kan mamayi idanunta ya zo ya lullube idonta. Allah ya so ta a zaune ta ke, da babu shakka faduwa za ta yi. Daidai lokacin da Taufeeq da Nasmah suka shigo dakin.
Runtse idanunta ta yi tana tasbihi ga Allah, ba ta ko son bude su don kada ta ga fuskar Taufeeq. Kujerar da ta ke zaune ya zo ya zauna dab da ita. Kamshin sassanyan turarensa ya bugi hancinta, ta kara runtse idonta, ta ki yarda ta bude.
Ya sa hannu zai taba ta, ko me ya tuna kuma ya fasa. Da ganinsa ka ga wanda ke cikin madaukakin farin ciki, shaddar jikinsa fara kal, sai maiko ta ke yi tana nuna tsadarta. Ya yi wani irin fresh da shi, da ganinsa ka ga sabon ango wanda ya gama samun duk wani farin cikin rayuwarsa.
Tunda ya zauna yake tsokanar ta. Sai a lokacin ya lura Kulsum hawaye ta ke yi, hawayen da bai san dalilin zubarsu ba. Hankalin sa yayi mummunan tashi, bai san sanda ya dora hannunsa a kan nata ba ya kira sunanta muryarsa na sarkewa.
Har yanzu ba ta bude idonta ba, don bata son ganin sa, amma hawaye ne ke zuba ta gefen idonta. Da ya dora hannunsa a kan nata ji ta yi tamkar ya dala mata garwashin wuta. Ta soma kokarin janye hannunta, amma ya hana ta damar hakan.
Yau mashayin giya Allah ya nufe ta da aure, ita Kulsumu jikar Goggo? Astagfirullah! Ita ko wane laifi ta yi wa Ubangiji ya hada ta da wannan kaddarar? Tayi saurin yin istigfari ga kalamanta.
Mikewa ta yi da niyyar barin dakin, amma Taufeeq bai saki hannunta ba. Wata zuciyar ta gargade ta da cewa, kada ta yi wani action wanda zai sa ya fahimci ta ga sirrinsa. Don haka ta bude idanunta a jigace, ta zube su a kanshi, kana iya hango zurfin kololuwar tashin hankalin data ke shimfide cikin idanunta, ta ce,
“Yaya Taufeeq ka sake ni gida zan tafi”.
Yana kokarin kallon tsakiyar idanunta data sake runtsewa ya ce, “Laifin me na yi miki haka Kulsum?”
Da sauri ta ce, “Ba ka yi min laifin komai ba, na ga bai dace in zo nan ba ne, kuma bana jin dadi”.
Ya ce, “Na biya sadaki, fatiha kawai ya rage a shafa, shi ne ki ke cewa bai dace ba don kin zo gidanki?”
Wasu hawayen suka shimfido mata, ta ce, “Wallahi bana jin dadi, don Allah ka bar ni in je in kwanta”.
With concern ya ce, “Ban ji komai a jikin ki ba na alamun zazzabi, ina yake miki ciwo?”
Da sauri ta ce, “Ido na”. Don dai ta samu ya kyaleta.
Ya ce, “Then let us go ki ga ophthalmologist”.
Ta katse shi da hanzari,
“Ba fa ciwon yau ba ne, tunda na taso da shi na taso”.
“Kuma ba ki taba ganin likita a kai ba? this is silly, ki wuce mu je kawai”.
Za ta yi musu ya dora yatsansa a kan labbansa, tare da jan hannunta suka bar dakin. A haka suka tadda Nasmah da Mujaheed a falo, wadanda ke zaune suna shan coffee. Su duka biyun suka dago ido suna kallonsu, Nasmah ta ce,
“Lafiya?”