Showing 9001 words to 12000 words out of 34734 words

Chapter 4 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

518

amince masa ba ne, kawai bai taba sharing al’amuran rayuwarsa da kowa ba, sannan ya sani shi mai laifi ne ga iyaye abin tinkahon kowanne dan Adam, watakila har wajen Ubangijinsa! Ba ya so Abdul’Ahad ya bar ganin mutuncin sa.
“Okey, tunda hakan ka zaba wa kanka, da yardar Allah ba zan sake tambayarka komai a kan rayuwarka ba. Abin da nake so kawai shi ne, ka kula da lafiyarka, ka kare ta daga cututtukan zamani wadanda ba mu da maganinsu. Aboki, me ce ce rayuwa? Komai da ke cikinta mai wucewa ne, idan har mun dauke shi da sauki”.
Daidai lokacin likita Andrew ya shigo dakin. Ruwan ya cire masa, ya ce suna iya tafiya yanzu, amma yana kara jan hankalin Dr. Aboubacar da babbar murya ya raba kansa da damuwa da tunani.

Abdul’Ahad ke tuka su cikin motar Aboubakar Turaki kirar Acura. Suna tafe a kan titin da zai sada su da gidan Abubakar-Turaki da ke cikin jerin gidajen malaman jami’ar 'Reading'. Turaki ya rasa me ya sa yau zuciyarsa ke neman wanda za ta raba dimbin damuwar nan da ke nukurkusarshi da shi ko da kadan ne? At least ya samu sassaucin damuwar nan in yayi voicing dinta ga wani, someone caring like Abdul Ahad. Yana gefen Abdul’ahad yayin da Abdul’Ahad din ke tuki cikin nutsuwa, bakinsa ya motsa kadan ya fadi abin da bai ta furtawa ba tsayin shekarun da suka yi tare.

“I am married Aboki”.

Ya fada daga can kasan makoshin sa.

“What?" Maikano ya tambaya kamar bai ji daidai ba.
“Aure ka ce ko me?”
“Aure aboki, I’ve a wife at home (inada mata a gida), ina cikin tasku, domin na yi wa iyayena laifi, na kasa zuwa in ba su hakuri don ban san da kalamin da zan wanke kaina ba.
Na yi musu babban laifi, na kin waiwayar su all these while a kan bana son auren da suka yi min. Tun bayan na taho kuma tunanin yarinyar ya kasa barina, sabida ita ma na yi mata wani babban laifi. I lack the courage na fuskantarsu su duka ukun, in ce su yafe min”.
A wannan lokacin ya kwashe labarin sa kaf ya gayawa Abdul Ahad, garin su, inda ya fito da matsayin mahaifin sa.
Cikin mamaki Abdul’Ahad ya ce, “Kana nufin tun tahowar ka ba ka kara waiwayar gida ba?”
Cikin jin nauyin abin da ya aikata ya ce, “Duk halin da suke ciki na sani. Wani abokina a garin mu yana gaya min, na san lafiyar su kalau. Ina bibiyar lafiyar su. Da farko ina kira, daga baya ne na daina, ba don komai ba sai don kada su takura min in dawo wajen matar da suka aura min. I thought I don’t like her anymore Aboki, saboda tana da lalura... I thought I escaped, auren da bana son, amma tunaninta ya hana ni sakat a duka shekarun nan, something like infatuation… emotional disturbance.... I just..... cannot express…, kawai ji nake zan iya zama da ita da lalurar tata against all odds”.
Abdul’Ahad ya yi wani mischevous murmushi ya ce, “Man, ka dawo hanya kawai, tell me you love your wife right now (kana son matar ka yanzu), shawarar da zan baka itace ka koma gida ka taho da ita, ka kuma nemi afuwar iyayenka bisa kaurace musun da kayi alhalin su da alheri suke nufin ka, in ba haka ba, ba za ka taba zama lafiya ba na gaya maka, kuma ba za ka ga albarka cikin rayuwar ka ba. Babu iyayen da suka san ciwon kansu da zasu so dan su ya tafi Turai ba aure. Da ka kwantar da hankalin ka da ka fahimci manufarsu tuntuni. Ba sun yi ne don su takura maka ba. Shawarar da zan baka ke nan, ka je gida, ka karbi duk wani punishment daga gare su, sannan ka dauko matarka!”.
“Kana ganin za su yafe min Aboki? UmmuKulsum za ta kara kallona da kima bayan duka laifuffukan da na yi mata? Ban taba kallon ta da matsayin mata ba! Aboki har raping dinta na yi don kawai in nuna rashin kaunata gare ta. This is the worst moment da nake tunawa a kanta, kuma abin da ya canza zuciyata zuwa alkhairi bakidaya a kanta.
Ba ta cancanci duk abubuwan nuna rashin kauna da na yi mata ba tunda ba ita ta zo ta ce tana sona ba, iyayena ne suka je suka nemo min aurenta har gaban iyayenta kamar yadda ake neman auren kowacce diya ta mutunci. Ban kyauta ba Aboki, watakila Ubangiji ke hukunta ni da feelings a kan UmmuKulsum, wadanda ke kassara ni a yanzu, suka kuma hana ni jin dadin kowacce nasara da ta same ni”.
Abdul’Ahad ya ce cikin tausayawa, “Don’t ever say you raped her again, tunda igiyar aure ta hada ku. Matarka ce. Sai dai ka ce, ...not in a nice way...! Mace kuma mai rauni ce a halittar ta, ban hakuri, kulawa da nuna soyayya tareda nuna ka amshi laifin ka kadai zai wanke laifinka komai girman sa.
Iyaye kuwa tsakaninmu da su akwai afuwa, yafiya da jin kai, wanda Ubangiji Subhana ya sanya a tsakaninmu da su.
Ka je gida ka kwantar da kai, ka amshi kowanne laifinka. Ka karbi punishement komai tsaurin sa. Sannan ka ba su hakuri, ka dauko matarka kusa da kai ina tabbatar maka hakan kawai za ka yi ka wanke kanka a wajensu, kuma ka samu nutsuwa da zaman lafiyar cigaba da gudanar da al'amuran rayuwar ka”.
Turaki ya yi na’am da shawarar amininsa, cikin satin gabadaya ya maida hankali wajen shirin dawowa kasar haihuwarsa, soyayyar da bai san cewa ita ce ke nukurkusar sa ba tana kara masa azama ga son dawowa gida, da burin ya dora ido a kan KULSUMU.

*** *** ***

GAYA
Batulu na markada abarba cikin blander a kicin din Umma, yayin da Umma ke turara alkubus a kan wuta, ga dukkan alama ita ce da turakar Maimartaba yau. Don girkinshi matansa ne kadai ke yi mishi da hannunsu. Suka jiyo hayaniya daga tsakar gida, wani suna yana tashi daga bakin jama’ar gida, kamar TURAKI!
Umma tayi sak! Daga abinda take yi, ba ta gaskata kunnuwanta ba don haka ta mike ta leka tsakar gidan ta tagar kicin. Ba ta yi nasarar hango wanda jama’ar gidan suka yanyame ba, amma tabbas ta ji suna fadin, "Turaki", komawa ta yi ta zauna ta ci gaba da turara alkubus dinta, amma hankalinta ya rabu biyu. Batulu ta kashe blander ta ce, “Umma kina jin me ake fadi kuwa? Kamar Yaya Turaki na ji suna cewa…”.
Kafin Batulu ra rufe bakin ta Umma kuma ta samu zarafin amsa mata, kamshin turaren Turaki (one man show) ya ziyarci hancin su, daga nan kuma sai sallamarsa, cikin muryar nan tasa mai cike da haiba da ginshiran sarauta, kafin ingarma kuma kyakkyawa Abubakar (Turaki) ya sako kai ta hanyar rage tsawon sa a kofar kitchen din Umman sa.
Sanye yake da kaftan na wata lallausar farar shadda (filtex), hular kansa ruwan kasa ce mai haske, haka fatar agogon hannunsa samfurin RADO itama ruwan kasar ce, a kafarsa budadden takalmin fata ne dan kasar Italy. Kallo daya Umma ta yi masa ta dauke kanta, amma sai da zuciyarta ta buga sosai da sßganinsa.
Ban da uwa-uwa ce da ba za ta yarda Turaki ne ba, domin gabadaya ya canza ya zama wani gogaggen matashi, wheather din kasar England ya amshe shi ba kadan ba. Ya kara kyau da ilhama, ga wani lallausan saje da ya tara a gefen fuskarsa wanda a da ba shi da shi. Batulu ta hangame baki sannan ta sheka da gudu ta rungume shi tana fadin.

“Yaya Turaki kai ne? Ashe za mu sake ganinka?”

Shi ma ya rike ta a jikinsa yana fadin, “Autar Umma kin kara girma, me Umma ke ba ki hakan?”
Dariya ta yi tare da riko hannuwansa duk biyu kamar ta hadiye shi don farin ciki, sai fargawa suka yi babu Umma a kicin din babu alamarta.
Shi da Batulu suka bi bayanta zuwa dakinta, zaune suka same ta a gefen gadonta ta kifa fuska cikin tafukanta tana share hawaye. Jikin Turaki ya kara yin la’asar, fiye da wanda yazo a cikin sa, a kan gwiwoyinsa ya tsugunna a gabanta.
“Umma na san ni Abubakar Turaki mai laifi ne, mai tarin laifuffuka a gare ku, Umma duk laifin da ku ke zargina da shi na karba, kuma na san na yi. Amma don Allah Umma ku ba ni dama in gyara kuskurena. Don Allah Ummah. Ajizanci ne irin na dan adam.
Umma cikin tarin alfarmomin ki na uwa, wadanda ba za su taba karewa a gare mu ba nake rokon ki da ki yafe mini, na tabbata na yi muku laifi wanda in ba ku yafe min ba ba zan taba zama cikin kwanciyar hankali ba. Na kwashe shekaru ban zo na gan ku ba, ban nemeku a waya ba, ban ji lafiyar matar da kuka zaba min ba wanda ba akan haka muka rabu ni da ku ba. Mun rabu ne akan duk shekara zan zo, kuma zan dinga kiran waya.
Ummah a yau gani a gaban ku, durkushe akan gwiwoyi na, na zo in tabbatar muku na karbi zabin da ku ka yi min da hannu bibbiyu. Ki taya ni ba ta hakuri. Ba zan kara maimaita kuskure na ba”.

Umma dai ba ta ce komai ba, amma kalamansa sun shigeta, yana ta magiyar sa, ita kuma tana aikin share hawaye.
Wuni guda ya yi cur yana bin Umma da neman gafarar ta, amma uffan ta ki ce masa komai, Batulu kadai ke kula da al’amarinsa. Ita ma in ta tuna babu Kulsumu a gidan duk sai ta ji wani irin haushin sa ya rufe ta. A haka dai ta yi masa girki mai kyau, ta kuma shigar masa da kayansa sashen sa. Bayan ta sa an share an goge ko'ina.
Yana so ya tambayi Batulu Kulsumu, ya rasa ta ina zai fara. Sabida yadda take sha masa kamshi. Kwarai hankalinsa ya dugunzuma ya tashi da ya fahimci babu ita a sashen nasa, babu komai nata, kai da alama ma an dade ba a yi amfani da sashen nasu ba. Amma ya kasa tambaya. Saboda fargabar abinda za'a gaya masa.

Bai samu ganin Maimartaba ba sai washegari da safe yana kalaci. Mai girki wato Hajiya Saratu ta yi masa iso turakar mahaifinsa.
Maimartaba ya amsa gaisuwar sa kadaran-kadahan, amma daga gaisuwar bai kara ce masa komai ba. Hankalinsa ya kara yin kololuwar tashi. Ya gurfana gaban Maimartaba yana ba shi hakuri tare da jaddada cewa ya amince ya karbi dukkan laifuffukansa. Ya karbi zabin su da hannu bibbiyu.
An dauki lokaci kafin Maimartaba Sarki ya ce da shi.

“Mu kam ai mu za mu ba ka hakuri Turaki, tunda mun takura rayuwarka ba da sanin mu ba. Har dalilin hakan ka zabi ka kaurace mana a wannan lokaci na tsufa da muka fi bukatar kulawarku da komai.
Ka kwantar da hankalinka, kuma ka daina gudun mu in dai a kan yarinya Kulsumu ne, tuni mun maida wa iyayenta ‘yar su, bayan mun sa Alkali ya raba auren bisa doron shari’ah”.

Wani gumi ne ya keto wa Turaki tun daga tsakar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Ya san Maimartaba ba ya zolaya, kuma ba ya fadin abin da bai aikata ba. Idan mafarki yake yana rokon Allah ya farkar da shi, Maimartaba ya janye abin da ya gaya masa yanzun nan.
Maimartaba ya ci gaba da cewa, “Muna fatan yanzu za ka daina gudun mu, tunda mun bi ra’ayinka, mun yi maka yadda ka ke so? Wato zama babu aure?”
Hawaye suka zubo daga idon Turaki, ya rasa da bakin da zai yi wa mahaifinsa bayanin cewa; gabadaya shekarun da ya yi, ya yi su ne cikin son Kulsumu, da nadamar abin da ya yi musu. Sannan ganin girman laifin sa ne ya hana shi dawowa har sai da Abdul’Ahad ya karfafe shi. Ba fitsarin kwance ba, ko kashin kwance ta ke yi a yanzu kam ya daura dammarar zama da ita cikin so da kauna. Sannan as a medical doctor zai nema mata magani iyakar iyawarsa, idan ma ba ta samu lafiya ba ya alkawarta wa ransa ci gaba da zama da ita da lalurar da Allah ya dora mata. Har bincike na musamman ya yi a kan lalurar ‘Eneuresis’ kasancewar ba fanninsa ba ne, ya kuma samu kwarin gwiwar cewa, da ya dawo zai kai ta inda za ta samu magani.
A wannan halin Umma ta shigo ta same su. Dukkan su babu wanda zuciyarsa ba ta motsa ba ganin Turaki yana kuka. Daga yarintar sa zuwa yanzu za su iya kididdige sau nawa ya yi kuka a rayuwarsa. Amma ba su yi saurin nuna karayar su ga laifin da ya yi musu ba tukunna, domin ya jawo sun cutar da yarinyar mutane, sannan ya nuna wa duniya ba su isa da shi ba. Wannan shi ne babban abin da ke kara fushinsu a kan dan nasu.
***
Washegarin ranar Kiru ya tafi wajen Yayarsa Hadiza. Hadiza ta karbe shi kadaran-kadahan don ita ma ya bata mata rai ba dan kadan ba. Allah ya gani tana son Kulsumu! A zaman shekaru hudu da suka yi da yarinyar ba za su taba cewa ga aibunta ba. Ta shiga ran su sosai sabida kyawawan halayenta. Amma yadda Turaki ya kwantar da kai yana ba ta hakuri tare da rokonta ta shige masa gaba ya shawo kan iyayensu su dawo masa da matarsa su kuma yafe masa laifin sa, dole ta tausaya masa. An ce naka sai naka, don duk cikin kannenta Turaki ne favourite dinta, tana sonshi sosai a matsayin sa na namiji daya tal a cikinsu. Dole ta hakura ta karbi uzurinsa ta ce ya tafi gobe za ta zo gidan insha Allahu za su shawo kansu, amma tana mai kara gaya masa bai kyauta musu ba, kuma ya yi babban kuskure. Kulsumu duk da kasancewar ta tashin kauye, mace ce cikin dubu ba zai samu kamar ta da sauki ba. Turaki ba ya ja, akan ko me aka ce ya yi, ya karbi laifinsa, shi mai baiwa kowa hakuri ne da dukkan iyawarsa.
Washegari Hadiza ta zo Gaya, Umma ta yi mamakin ganinta ko waya ba ta yi ta ce za ta zo ba.
Bayan sun gaisa ta ce, “Umma wajenku na zo ke da Maimartaba, kuma a tare nake son ganinku”.
Ko kusa Umma ba ta kawo zancen Turaki ba ne, don ba ta san jiya ya je Kiru ba, ta ce, Maimartaba yana da baki, in sun tafi sai mu je. Allah ya sa dai lafiya”.
Hadiza ta ce, “Lafiya kalau, sai alheri Umma”.
Bayan tafiyar bakin Maimartaba suka je suka same shi a falon da yake ganawa da iyalinsa. Ya dubi Hadiza ya yi murmushi, ya ce,
“Fulanin Kiru ku ne tafe?”
Hadiza ta zube ta gaida mahaifinta yana tambayarta ‘yan jikokinsa, ta ce, duk a gida ta baro su, ita kadai ta zo. Sannan ba ta bata lokaci ba ta dora da abin da ya kawo ta, wato nema wa Turaki afuwa daga gare su, ta ce ba komai ya hana shi dawowa ba illa iyaka yana hango girman laifin da ya yi muku ne, yana jin nauyi har sai da abokinsa ya ba shi shawararar ya ture hakan ya fuskance ku, ya karbi laifinsa komai girman sa.
Don Allah Umma ku yi hakuri ku maida masa matarsa tunda shi da kanshi yanzu ya zo ya ce yana son ta, na kuma fahimci wallahi da gaske yake, kuma wannan shi ne karo na farko da ya taba saba wa umarnin ku. Sannan karo na farko da Turaki ya taba bude baki duk kawaicin sa ya ce yana son mace. Ni na tabbatar su Goggon Kulsumu ba za su ki dawo da ita dakinta ba tunda dama ba su suka nemi a mayar musu da ita ba, daga gare mu ne”.
Maimartaba ya ce da Hadiza shi ai tun jiya ya yafe wa Turaki, amma ba zai zama karamin mutum a idon talakawansa ba, ba zai yi masa bikon Kulsumu ba, ya je da kansa in iyayenta sun gamsu da nadamar sa su sake bashi aurenta, kada kunyarsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login