Showing 18001 words to 21000 words out of 34734 words

Chapter 7 - Kulsum Book 2 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

516

amsa ko bai amsa ba ita ba ta sani ba. Sai da suka ajiye su Waleed a makarantarsu suna fadin, “Aunty Kulsum yau in mun dawo tuwo za ki yi mana irin na rannan”.
Ta juya ta share idonta ta yi musu murmushi, sannan ta ce, “Toh insha Allahu Waleed. Ka yi karatu mai yawa, ka zama Doctor irin Mummy”.
Suna waving dinta, ita ma tana waving dinsu, Engnr. Farouq ya ja motar suka bar filin makarantar yaran zuwa filin jirgi.
Sun yi sa’a akwai jirgin da zai tashi zuwa Abuja nan da awa daya, Taufeeq ya yankar musu tiket guda biyu, Sakeenah da Farouq suka yi musu sallama suka tafi don duk wajen aiki za su. Suka zauna a waiting lounge ba mai ce da dan uwansa komai. Taufeeq wayar hannunsa yake daddannawa, da alama he is addicted to that, ita ma wayar ce a hannunta, amma game ta ke yi. Daga baya ta bude jakarta ta jefa ta. Ta dauko dan karamin littafin Alma’asurat tana karantawa.
Ba jimawa aka kira su kowa ya tashi, wayar Taufeeq ta zame daga aljihunsa ta fadi kasa ta tarwatse. A tare ita da shi suka sunkuya suna tsincewa. Ta dago tana mika masa battery din wayar ne suka hada ido. Kallo kai tsaye cikin idanunsu. Taufeeq ya rasa me ya hana shi janye idonsa daga na Kulsum, samun kansa ya yi da ci gaba da kallonta. Ita ta fara dauke idonta ganin kowa ya fita daga lounge din sai su biyu. Ya daga kafa ya bi bayanta yana tambayar kansa,
“What’s wrong with me? Wannan kallo haka!”
A kujerun da ke daura da juna suka zauna, tana daga jikin taga yana gefenta, tana zama tasa ear-piece a jikin wayarta tana sauraron kira’a. Ana ta fadin a daura belt Kulsum ba ta san ana yi ba, sai bude ido ta yi ta ga hannayen Taufeeq zagaye da ita yana fastening mata belt din. Kamshin turarensa ya sa tsigar jikinta tashi ta yi catching breadth dinta sharply. Har jirgin ya bar kasa ba ta yi regaining mood dinta ba. Ji ta yi duk jikinta ya saki. Ba ta taba zama so close da namiji ba irin haka. A take wani tunani ya fado mata a rai, "TURAKI" da abin da ya faru tsakaninsu… that fateful day...... Sosai ta matsa jikin taga ta takure jikinta, ta runtse idanunta. Ta kara sa wa a ranta ba ita ba MAZA! Dukkansu mugaye ne. Amma hakan bai hana wani sako na zuciyarta lakewa a gefe ya yi tunanin Turaki ba lokaci-lokaci.
Zamanta daura da Taufeeq a cikin jirgi, duk memories din Turaki ya kawo mata. Ganinsa ta yi ma yana rikidewa yana komawa Turakin. Ta rasa wane irin masifaffen so zuciyarta ke ma Turaki. Ta tabbata zuwa yanzu shi ya mance da ita, amma ita ta kasa manta shi, ko ta yi kokarin hakan ba ta cin nasara.
Idan maza sun yi dubu a duniya Turaki ne kadai karbabbe ga zuciyarta. Duk tarin laifuffukansa zuciyarta uzuri ta ke masa a lokuta da dama. Sai dai ta san ko a lahira suka sake haduwa ba za ta sake bari ya shigo cikin rayuwarta ba. Ya yi mata laifin da ba za ta iya yafe masa ba, wanda sai yanzu da hankali ya kara shigar ta ta gane hakan. Ta gane ya kwanta da ita ne out of hatred. Sannan bisa dole. Ya raba ta da tinkahonta na diya mace, sannan ya tsallake ya barta cikin wani hali na neman agaji, amma bai tausaya mata ba, sannan bai agaza mata ba, still tunda ya tafi bai kara waiwayarta ba. Duk da haka zuciyarta mara mafadi is craving for him… ai ko shi ya saura Da namiji a duniya za ta yi yaki da ita wajen ganin ta fidda shi daga cikinta.
Har suka sauka a Abuja tunanin da ta ke ta yi kenan. Yusha'u Hajiya ta turo ya dauke su zuwa gida.
Taufeeq na lura da mood dinta, tunda suka taho ba ta walwala, kamar ta fi son ta zauna a Lagos din ne ko mene ne? Bai sani ba shi.

*** *** ***
ABUJA
Tarba ta musamma Kulsumu ta samu daga Hajiya, har ta fi murna da dawowarta a kan ta Taufeeq. Abinci kala-kala ta sa Serah ta shirya musu a dining. Hajiya ta aika Serah dakinta ta ce ta kirata ta ci abinci in ta huta. A lokacin ta fito wanka tana shafa mai Serah ta iske ta da sakon Hajiya. Doguwar riga kawai ta saka ta yafa veil din rigar ta bi bayan serah.
Ta zauna kenan ta fara zuba fried rice a faranti, Taufeeq ya shigo falon. Kai tsaye dining din ya nufo ya ja kujera mai fuskantarta ya zauna. Shi ma ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa T/Shirt DKNY ruwan goro da bakin wando chinose. Da ka ganshi ka ga Alhaji Muhammad Bello, wanda asalinsa bafullatanin Adamawa ne, kuruciya kawai ya fi shi, kwata-kwata ba ya kama da su Nasmah, ya fi su dogon hanci da kwantacciyar suma, su kuma sun fi shi haske.
Tunda ya zauna sai ta samu kanta da kasa cin abincin da ta zuba, sai juya cokali ta ke cikin shinkafa, tana kallonshi yana ta loda vegetables a kan 'yar shinkafar da ya zuba. Ya gama ya fara ci, yana satar kallonta.
"Yanayin yarinyar mai sanya tausayi ne," Taufeeq ya fada a ransa, sam ba ta da rawar kai irin wanda 'yammata tsararrakin ta ke da shi, sannan akwai tarin nutsuwa tattare da ita da wata irin kamala da bai taba gani tare da mace ba. Yana kallo ta dauke farantin abincin ta ta nufi dakin ta. Wannan na nufin; ba za ta iya cin abinci a gaban shi ba. Wanda ya nuna ita din mai kamun kai ce.
Ya ji yana son yi wa mahaifiyarsa tambayoyi a kanta, yana son sanin komai na rayuwar ta.
Shi da Hajiya ne a uwar dakin Hajiyar a daren ranar suna hirar abubuwan da suka baro a UK, Hajiya ta ce, “Don me za ka ajiye aikinka Taufeeq? Idan ka zo nan ka zauna me za ka yi mana? Ga Daddy shi ma tunda ya yi ritaya ba wani abu yake yi ba da pension dinsa kawai yake amfani”.
Taufeeq ya ce, “Mum I cannot endure the loneliness (ba zan iya jure kadaicin ba). Baban wani abokina ya sa an yi min transfer zuwa NIGERIAN NAVY, ina jiran su kira ni”.
Hajiya Nasara ta ce, “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi”.
Taufeeq ya ce, “Amin Mum… ita wannan yarinyar da na dauko daga gidan Sakeenah wace ce dinki? Ko ita ce yarinyar da Nasmah ta ba ni waya in kawo mata?”
Hajiya Nasara ta ce, “Kulsum ba, ita ce. Jika ta ke ga kanwar mahaifiyata ta Gaya, ai ka san Goggo Aishatu da nake ba ku labari? An yi mata aure ne da Dan Sarkin Gaya, auren bai je ko’ina ba, shi ne na dauko ta don ta ci gaba da karatu nan a gabana. Gobe da safe za ka kaita ta sayo form din school of Nursing, Gwagwalada”.
Taufeeq ya ce, “Kamar ya ya auren bai je ko’ina ba? Mijin ya sake ta ne?”
Hajiya ta girgiza kai, “Bai sake ta ba, iyayensa ne suka raba auren. Ya tafi karatu Turai ya ki dawowa”.
Taufeeq bai kara magana akai ba, wani zancen daban ya koma yi. Amma cikin zuciyarsa sai ya ji yana tausaya wa Kulsumun, karamar yarinya da ita an maida ita bazawara. Matsalar 'ya'yan sarautar nan kenan.
Washegari da safe Kulsumu na yi wa Hajiya Nasara gyaran daki, ta ce da ita ta shirya Taufeeq zai kai ta sayen form. Haka nan dai ita ba ta son hada hanya da Taufeeq dinnan, kallon idanunsa na sa wa ta ji wani iri a ranta. Za ta so a ce ba shi zai kai ta ba, Hajiyar ce da kanta ko direba ko Serah ta raka ta, amma ba za ta iya yi wa Hajiya musu ba. Dole ta shirya cikin daya daga kayan da Sakeenah ta bata ta nemi hijab cikin kayan da ta zo da su daga Gaya ta dora a kai. Ta je ta ce da Hajiya ta shirya, ita kuma ta kira Taufeeq a waya, ya ce ta same shi a cikin mota yana waje.
Suna tafe cikin motar Daddy (Honda 2015 model) babu mai cewa komai tun bayan da ta gaishe shi ya amsa. Sai da suka iso makarantar ya yi tambaya aka nuna musu inda za su je. A mota ya ce ta jira shi, ya je ya sayo ya dawo ya dora mata a cinya. A hanyarsu ta dawowa ya tsaya ya sayi abu a supermarket, sannan suka karaso gida.
Ta bude kofar motar za ta fita, ya kira sunanta. Da dumbin mamaki ta juyo don ba ta san ya san sunan ta ba. Wani dan karamin farin kwali ya miko mata.
Cikin taushin murya ya ce,
“A message from Nasmah (sako daga Nasmah)”.
Hannu biyu ta sa ta amsa, ta yi masa godiya ta shige cikin gida. Ya bi bayanta da kallo. Wani irin kallo da ya tabbata bai taba yiwa kowacce diya mace ba.
A falo ta tadda Hajiya, ta ce, “Har an dawo?”
“Mun dawo Hajiya, kin ga sakon da Nasmah ta aiko min”.
Ta zauna gefen Hajiyar tana kokarin bude kwalin wayar. Murna fal kumatunta, Hajiya ta ce, “An gode wa Nasmah”.
Ta fiddo wayar mai kyau da ita. Ta ce, “Hajiya ki aika wa Baban ‘Yalleman, ni sai in ci gaba da amfani da ta wajen Aunty Sakeenah”.
Hajiya Nasra ta ce, “Ba za a yi haka ba, tunda ta saya da sunanki ki hada duka ki yi amfani da su, insha Allah zan bai wa Yusha'u wata ya kai masa har Gaya, sai Goggo ta ba shi”.
Kulsum ta ji dadi sosai, wai ita ce mallakin wayar hannu har guda biyu rus! Na nunawa sa'a.
Taufeeq Hajiya ta sa ya taimaka mata ta cike form din ta online. Babu jimawa admission ya fito, an dauke ta a FCT Nursing School. Duka wani shige da fice da Taufeeq suka yi shi, har ta fara shiga aji.
Malam Yusha'u direban Hajiya ya ci gaba da kaita yana dauko ta, sabida shi ma Taufeeq din aikinsa ya fito ya yi joining Nigerian Navy, ya tattara ya tafi Lagos inda suka ajiye shi.
Sai dai kuma ya tafi ne da Kulsum manne cikin ransa. Wani al’amari da bai taba faruwa da shi ba a kan diya mace. Tun daga ranar da Hajiya ta hada su zuwa sayen form ya kasa mallakar kansa a kan Kulsum. Sosai ta zauna cikin zuciyarsa, da ya ji labarinta kuma da yadda mijin ta ya tafi ya barta sai feelings dinsa a kanta ya karu. Da ma kuma tausayi yana taimakawa wajen kimsa so. Ya bar wa ransa komai don ya san yadda Hajiyarsa ta sa wa ranta son Kulsum ta yi karatu ba za ta taba aminta ba.
Amma ko da ya kama aikinsa a Lagos sai nutsuwa ta gagare shi. A duk abin da yake yi Kulsum na gilma masa, tunaninta ya hana shi sakat, yana mamakin wane ne ya auri Kulsum ya kuma sake ta cikin hankalinsa? Wannan shi ake kira sauta ga wawa.
Hajiya ba ta fito fili ta gaya wa Taufeeq lalurar da Kulsum ta yi fama a baya ba, kuma ba ta kafa hujja da ita a kan dalilin rabuwar aurenta ba, tunda su Goggo kansu ba su da tabbas a kan hakan. Ta barshi a yadda su ma suka barshi, wato ya tafi karatu ya ki dawowa, iyayensa suka raba auren.

A rayuwar Taufeeq Muhammad Bello, bai taba haduwa da abin da ya tsaya masa a rai irin Kulsumu ba. Kulsumun da ba ta san yana yi ba, karatunta ta dumfara with much enthusiasm. Karatun kadai ta sa a gaba, shi ne goal dinta, ko ta so ta yi tunanin Turaki tana yakice shi ne da dukkan karfinta.
Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta daukar wa Kulsum, ta aika wa Malam Hadi waya, don haka Kulsum ta zamo ba ta da damuwa, kullum tana tare da iyayenta da kakanninta a waya, in ta dawo gida. Ga Nasmah da Aunty Sakeenah su ma suna kiranta akai-akai.
Sati uku da tafiyar Taufeeq sai ga shi ya dawo ba zato ba tsammani. Hajiya ta ganshi at a smart pace (afujajan), gabadaya ya zama tamkar ba shi ba. Duk ya birkice ba nutsuwa sam a tare da shi. Da Hajiya ta nemi ba’asin dawowarshi ba lokacin da ya kamata ya dawo ba, sai ya ce lafiya kalau. Ba ta kara maida hankalinta ta kanshi ba, sai ta sa Serah ta shirya masa vegetarian meal dinsa, lokacin Kulsum na makaranta.
Taufeeq ya samu Daddy dinsa a falonsa yana shan gahwah, ya shigo falon ya samu wuri gefen Daddyn ya zauna, Alhaji Muhammad Bello ya dubi dan nasa cike da kulawa ya ce, “Ya aka yi ne Taufeeq? Na ganka ba'a yadda na saba ganinka ba, is anything wrong a wajen aikin?”
Taufeeq ya sunkuyar da kansa yana tauna kalaman da zai furta wa mahaifinsa. Daddy bai katse hanzarinsa ba har sai da ya mula don kansa ya yi magana.
“Daddy aure nake so!”
Daddy ya hadiye mamakinsa ta hanyar murmushi, kafin ya ce, “Ka samu matar ne?”
Taufeeq ya kara yin kasa da kai, ya ce, “Daddy, Kulsum nake so, ka roka min Hajiya ta ba ni aurenta. Na yi alkawarin zan barta ta ci gaba da karatu har sai ta ce ya ishe ta, aurena ba zai zama barrier ga neman iliminta ba, insha Allahu.
Ka yi min alfarma Daddy ka roka min Hajiya, in ni na yi mata magana ba za ta amince ba”.
Daddy ya gyada kai, ya ce, “Wai yarinyar nan da ta dauko a Gaya?”
Taufeeq ya ce, “Ita Daddy”.
Alhaji Muhammad Bello ya ce, “Da kyau, na yaba da hankalin yarinyar, ga ta ‘yar uwarka. Ka bar komai a hannuna in dai yarinyar ta amince Hajiyarku za ta fi kowa son al’amarin”.
Amma ko da Daddyn ya furta zancen ga Hajiya Nasara, budar bakinta sai cewa ta yi.
“Ba zai yiwu ba. Na dauko Kulsum don ta yi karatu ne ba don in aura wa dan cikina ita ba. In auren yake so ya nemo wata, amma ban da Kulsum, iyayenta sai su zarge ni da son kai. Don yanzu haka tsohon mijinta ma na ta bilinbituwar nemanta da kome, ni na ce kada a gaya masa inda ta ke, don dai mu samu ta yi karatun nan. Sai kawai yanzu in je in ce musu Dana zai aure ta ko shekarar farko ba ta rufa a karatunta ba?”
Daddy ya dan tsura wa matar tasa ido, kafin cikin sanyin murya ya ce.
“Can we wait for her?”
Murmushi ta yi sabida yadda ya yi maganar cikin lallashi.
Ta ce, “Za ku iya jira har ta kare Nursing School sai ku shiga jerin manema, in Allah ya sa ku ne da rabo sai ku samu, in kuma mijin ta ke da nasara sai kuyi hakuri”.
Murmushi mai sauti Alhaji Muhammad Bello ya yi, kafin ya ce, “Alright. Insha Allah mu ne da rabon. Zan lallashi Taufeeq ko zai fahimce ki, don a yadda na fahimta soyayya mai zafi ce ta kama shi. Ki duba kunya da kawaici irin na Taufeeq, amma ya fito fili ya ce min aure yake so. Ta nan za ki fahimci ba da wasa yake ba. Amma muna neman alfarmar ki barsu su fara fahimtar juna kafin ta gama karatun ko don ya samu nutsuwa”.
A nan ma Hajiya Nasara ta ce ba ta yarda ba, zai kasa wa Kulsum hankali, karatu za ta yi ko soyayya? Ya kyale ta kawai ta yi abin da ke gabanta ya nemo wata ya aura.
Daddy ya ce, “Nasara ki fahimta, Taufeeq ba aure yake so ba, yarinyar wajenki yake so. Ki zama mai tausayi mana? Kuma zan ja masa kunne ba ko yaushe zai dameta ba. Don Allah ki yi mana alfarma”.
Hajiya Nasara ta san yadda Alhaji Muhammad Bello ke son Taufeeq fiye da kowa cikin ‘ya’yansa ba lallashin da ba zai mata ba. Sai ta ce a ranta za ta gwada Taufeeq don ta fahimci ko wane irin so yake yi wa Kulsum. Ta ce da Daddy za ta yi magana da Taufeq din kafin ta amince ya soma kula Kulsum.
Da daddare bayan sun gama cin abincin dare su uku, ita, daddy da Taufeeq, Kulsum na daki ta ki fitowa. Hajiya ta lura tun zuwan Taufeeq ta koma daddawar daka, ko falo ba ta zama. Ita Kulsum a kan-karan-kanta ta rasa me ya sa ta ke jin nauyin Taufeeq? Idanuwansa ne manyan (magnet) din da ke takura zuciyar ta. Yana da wasu irin idanuwa tamkar maganadisu masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login