Showing 15001 words to 18000 words out of 34734 words
suke so ta yi, ta auri miji mai sonta tsakani da Allah. Yau da mun saka baki da mun shiga hakkinsu, kunyarmu tasa su dawo da ita ya zo ya sake ba mu kunya, ya sake tafiya ya barta, don ya ce min ashe aiki ya samu a can din amma bayan shekaru uku zai dawo gida gabadaya.
Rakiya raba kanki da sha’anin Turaki, in ya damu ya je ya nemo ta a inda iyayenta suka boye ta. Ya karbi aurenta a hannunsu da kansa, in sun amince mu sai mu bi su da addu’a, amma kada ki sake sa baki a sha’anin Turaki, wanda muka yi a baya ya bula mana kasa a ido, Allah ya ba mu lada”.
Umma ta ce, “Ai na cire hannun nawa ranka ya dade, na dai kasa cire yarinyar a raina ne. Ni na san na yi asarar surukar kwarai mai son Turaki da zuciya daya. Zan bi su da addu’a Allah ya yi musu zabin alkhairi dukkanninsu. Allah ya sa watarana Kulsumu za ta dawo min”.
Murmushi Maimartaba Sarkin Gaya ya yi, ya ce, “Mata kuna son kanku da yawa, sannan kuna saurin manta girman laifin ‘ya’yan ku. Ni kuma na fi yi mata addu’ar Allah ya ba ta miji mai sonta ba Turaki ba, har yanzu ban gasgata wannan sabuwar soyayyar tasa ta dare daya ba, ya ce tunda ya tafi ya soma sonta, me ya hana ya dawo ya gyara laifinsa a lokacin da ya dace?”
Umma ta ce, “Haka Allah ya rubuta masa ranka ya dade, ko mun yi niyyar yin abu sai Allah ya nufa, ko ni ka shammace ni ban taba zaton za ka raba auren nan ba komai dadewar da Turaki zai yi. Sabida jikina na ba ni komai daren dadewa Turaki zai so Kulsumu, domin na mika lamarin su ga Ubangiji, kuma na tabbatar da ya karbi budurcin ta ranar da zai tafi. Kuma Alhamdulillah inada yaqinin wannan ne ya zama silar canzawar zuciyar sa a kanta”.
Maimartaba ya tsura mata ido, bai ce komai ba, amma can a karkashin zuciyarsa ya fara nadamar tsatstsauran hukuncin nasa, da ta yi masa wannan bayanin tun farko da ya yi wani hukuncin da bai kai raba su tsauri ba. Bai san cewa Turaki ya bi umarninsa ba ya tabbatar da auren sa kafin ya tafi. Ya soma zargin kansa da yin zalunci ga karamar yarinyar da ya mayar bazawara a kananan shekarunta. Amma da ya tuna ya yi ne bisa kyakkyawar niyya ta adalci ga talakawansa sai ya rage zargin kan nasa.
***
Watanni biyu Turaki ya kwashe cikin iyayensa da ‘yan uwansa. Duk wata ‘yar uwarsa da ke gidan aure sai da ya kai mata ziyara. Wajen aikinsa na ta nemansa, don haka ya kara neman izinin iyayensa kan ya koma U.K, ya kammala consultant ya baro aiki da su ya dawo gida bakidaya. A kan wannan alkawarin suka amince masa ya koma. Batulu har kuka ta yi sosai da zai tafi.
Bai tafi ba sai da ya je ya yi wa Goggo sallama ita da Baffa, yana kara yi musu tunin lambar waya idan su Kulsumu sun zo, ya yi alkawarin ko a wacce kasa suke zai bi Kulsumu. Baffa dai sai da ya ji kamar ya ba shi lambar, amma ya tuna rokon da Nasara ta yi ta yi masa a waya kan kada ya bayar din. Ya sani ita mai nufin alkhairi ga Kulsumu ne. Ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa ba don ta hana ta zaman aure ba.
Ranar da ya tafi ne kuma aka sauke musu buhunhuna da katon-katon na kayan abinci. Sai da aka cika dakin da Baffa ke ajiye shirginsa. Sako ne daga Turaki, da kudi masu yawa cikin ambulan.
Baffa ya ce da ‘yan aiken su mayar masa da kudin ba zai karba ba, inda suke gaya amsa ai Turaki ya riga ya bar garin Gaya zuwa inda ya fito. Haka ya wuni da jimamin abin. Goggo ta ce za ta je ta yi wa Hajiya Rakiya godiya, Baffa ya yi hakuri kawai ya karba don bai kamata su mayar wa Hajiya Rakiya ba.
Ko da ta je yi wa Umma godiyar cewa ta yi, “Haba Hajiya Shatu, Turaki ai dan ku ne, don ya yi muku alheri ba sai na sani ba. Don Allah kada irin haka ta sake faruwa ki ce za ki yi min godiya, tsakaninku ne da Dan ku, ni babu ruwana”.
*** *** ***
LAGOS
Saukarsa ke nan a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke garin Lagos. Wankan tarwada ne makimanci ga kyau. Ma’abocin yalwar murmushi, irin mutanen nan ne masu jovial personality. Babu ta yadda za a yi daga kallo na farko ka sanya shi a jerin kyawawa, amma annurin fuskarsa da cikar zati ya isa misali. Sanan yanayin fatar jikinsa abin so ne ga duk namijin da Allah ya baiwa. Alamun yawaitar murmushi, wani personality ne da ba kasafai ake samun maza da shi ba. Navy Officer TAWFEEQ MUHAMMAD BELLO yana saukowa daga matattakalar jirgin yana kokarin roaming layinsa domin ya samu ya kira ‘yar uwarsa da shi. Ya sanar da ita saukar sa.
Waje ya samu ya zauna a reception na filin jirgin yana ci gaba da danne-danne a wayarsa. Sanye yake da grey suit da jan neck-tie a wuyansa. da kyar ya samu ya yi roaming layin. Ya dannawa ‘yar uwarsa Sakeenah kira.
“Kin shanya ni, and you know na tsani jira, ban da Hajiya da ta ce in tsaya in tafi mata da sako a wajenki ko kyalli na ba za ki gani ba, kin sani”.
Cike da damuwa Dr. Sakeenah ta ce, “I’m so sorry Yaya Taufeeq wallahi I’m on call. Amma yanzu Baban Waleed zai zo ya tafi da kai, na gaya masa kuma ya taho”.
Ya ce, “Ni ba zan kwana a gidanku ba, ki gaya masa hotel zai kai ni, bana son jayayya da wannan kafaffen mijin naki”.
Murmushi ta yi cikin lallashi, don ta saba da rigimar Yayan nata, ta ce, “Amma at least ka shigo gidan nawa ka ci abinci ka huta. Na shirya maka better, my king brother, my very own Bachelor Brother”.
Dole tasa shi yin murmushi. Sakeenah is his favourite sister. An san sako da sako da rigima da juna, amma shi Sakeenah kullum lallaba shi ta ke, duk abin da ta san yana so shi ta ke masa, ko ya yi fushi da ita fushin ba ya zuwa ko’ina. To yau ma hakan, ta kare zancenta da cewa.
“Zan iso gida kafin awa daya, kuma gidan akwai mutane. Na sa Kulsum ta shirya maka table. Please smile at me (ka yi min murmushi). I assure you zan hango shi daga nan inda nake a dakin haihuwa”.
Murmushin ya yi ba don ya shirya yinsa ba, ya ce, “O.K, see you then”.
Ya kashe wayar da ya hango Engnr. Farouq na karasowa. Mikewa ya yi ya tadda shi suka kama hannun juna cikin musabiha. Farouk ya dauki jakarsa wadda ba ta cika nauyi ba suka nufi motar da ya zo da ita suna kara gaisawa da tambayar lafiyar su Waleed.
Kararrarwar shiga falo Farouq ya danna, daga ciki ta amsa da siririyar muryarta.
“Ana zuwa”.
Cikin nutsuwa ta murda mukullin tare da yi wa Baban Waleed barka da zuwa, ba ta lura cewa ba shi kadai ba ne.
Ya ce, “Ina ‘ya’yan naki na ganki ke kadai?”
Dan murmushi ta yi, ta ce, “Muna homework da su duk suka yi bacci”.
Sai a lokacin ta ankara da bakon da ke bayansa. Ta kara nutsuwa tare da ja da baya ta ba shi hanya tare da cewa,
“Barka da zuwa”.
Taufeeq ya kalle ta sau daya ya dauke kai, ya sako kafa cikin falon. Ko kadan ba ta ji dadin yadda ya yi mata ba. Ba ta san cewa shi naturally haka yake ba, ba ya sakar wa mata fuska. Sannan baya yi musu kallo na biyu. Daga uwarsa sai kannensa biyu. Duk yawan murmushinsa ya san a inda yake yinsa.
Wucewa ta yi dinning tana kara gyara musu komai kafin ta wuce daki. Amma tana shiga Engnr. Faruoq ya kwala mata kira,
“Kulsum!”
Ta amsa tare da fitowa a tsanake tana sanye da doguwar riga ta atamfa (Hitarget) mai ruwan jinin kare, ya ce, “Zo nan”.
Ta matso har inda ya kira ta ya nuna mata farfesun naman Sa da taliya da miya da ta aje musu, ya ce, “Taufeeq vegetarian ne, ba ya cin nama, ki hada masa salad da orange juice kada ki sa sukari. Kwashe wadannan din ki tafi da su”.
Gabanta har faduwa yake sabida wani kallo da Taufeeq din ke mata shi ba na raini ba, shi ba na mutunci ba. Tana shiga kitchen din ta debo lemon zaki (orange) guda shidda manya ta yanka ta soma matsewa a juicer kamar yadda Sakeenah ta koya mata. Nan da nan ta gama. Allah ya so ta iya hada salad din, nan ta yanka shi manya-manya ta yanka cocumber, tomatoe, cabbage da karas ta yi masa hadi yadda Sakeenah ke yi, tana so ta saka mayonnaise tana tsoron kada ta yi ba daidai ba, ga shi ba za ta iya tambayarsa ba, don yadda ta ga wannan Taufeeq din ba sauki kuma ba wargi ba kamar Baban Waleed ba.
Haka ta dauko salad din da mayonnaise din daban ba ta zuba a kai ba ta kawo musu. Ta koma ta dauko juice din cikin jug din da ta juye shi ta jefa kananan kankara a ciki ta kawo ta aje, Taufeeq na dannan wayarsa bai kalleta ba har ta gama, ta tambayi Baban Waleed ko suna bukatar wani abu? Ya ce babu, ta je sun gode, Allah yai mata albarka. Ta wuce daki tana amsawa a zuciyarta.
Suna fara ci Sakeenah ta shigo, kai tsaye Taufeeq ta dosa tana ta zuba murmushi. "My king brother Ya Taufeeq, ina fatan ka zo lafiya, kayi hakuri bai kamata in je ofis ba yau tunda na san za ka zo, believe me.... emergency call ne" (ka yarda da ni kiran gaggawa ne).
Bai ce mata komai ba sai shan lemonsa yake yi. Ta narke fuska.
“Ya Taufeeq, please smile at me, saboda kai fa na baro aikina na taho”.
A nan ne ya daga ido ya dube ta.
“Kin ce kin shirya min better, wannan ne bettern? Kin sa ‘yar aikinki ta kawo min nama, juice an zuba kankara bayan kin san ni ne zan ci”.
Sakeenah ta zaro ido, “Ya Taufeeq ba ‘yar aiki ba ce, niece dinmu ce, ina sauri an kira ni on emergency (kiran gaggawa) na bar mata girkin, and she don’t know your problem (bata san matsalar ka ba), don Allah ka yi hakuri”.
Haka dai ta samu ta lallaba shi. A ranta tana fadin, “Rigimamme”.
Har dare suna falon suna ta hira, Kulsumu na kicin tana musu girkin dare, lokaci-lokaci Sakeenah na zuwa ta duba aikin nata. Sosai ta ke jinjinawa kwazon Kulsumu don duk abin da ta koya mata sau daya ta dauke shi ke nan.
Wayar Hajiya biyu tana jaddadawa Sakeenah kafar Taufeeq kafar Kulsum zuwa Abuja, ta hado su su taho tare. An fara sayar da form na School of Nursing Kulsumun za ta cike nata (FCT School of Nursing, Gwagwalada).
“Ka tashi ka kai ni Hotel in samu in huta, gobe asubanci zan yi. Na matsu in gan ni gaban uwata”. In ji Taufeeq yana kallon Engnr. Farouq.
Farouq din ya ce, “Babu fa inda zan kai ka, alhalin ina da dakin baki”.
“Sai in zauna kuna ba ni abincin ‘yar aiki?”
Sakeenah ta dube shi cikin takaici.
“Na fa gaya maka ba ‘yar aiki ba ce Ya Taufeeq, jikar kanwar Babar Hajiya ce da Hajiya ta dauko a Gaya. Don Allah kar ka sake fadi, in ta ji ranta ba zai yi dadi ba. Tunda ka zo ba ta zauna ba tana ta hidima da kai, amma kana kiranta ‘yar aiki. Haba! Haba Ya Taufeeq ban sanka da wulakanta mutane ba”.
Jikin sa ne ya yi sanyi, duk da bai fada ba, ya ce, “Dauko min sakon Hajiya in wuce, Allah ba zan kwana gidanku ba. Haba suruki ne ni fa!”.
Dariya Farouq ya yi, ya ce, “A inda babu surukai ko?”
Sakeenah kuma ta ce, “Ai Kulsum din ita ce sakon da za ka daukan”.
“Ban gane ba?” Ya fada yana hararar ta.
Ta yi murmushin mugunta don ta san halinsa ba ya hada hanya da mata.
Ta ce, “I mean Hajiya cewa ta yi ka tafi mata da 'yar ta Kulsum Abuja, kafarka-kafarta”.
“Da tare muka zo?”
“Sai ka tambayi Hajiya, in ba za ka dauka ba sai in gaya mata”.
Mikewa ya yi tare da daukar wayarsa bai ce komai ba. Amma har zuciyarsa ransa ya baci. Da ya san sakon kenan da ba zai tsaya gidan Sakeenah ba.
Farouq tashi ya yi don ya kai shi inda yake so, ya san sarai ba zai yarda ya kwanan ba tunda an bata masa rai.
Dr. Sakeenah ta shigo daki ta samu Kulsumu na hada kayanta, tun safe Hajiya ta gaya mata yau za ta koma Abuja, an fara saida form din makarantar da za ta shiga. In ta ce ba za ta yi kewar Sakeenah da iyalinta ba ta yi karya, musamman Waleed da Waleeda. Sun yi zama na mutunta juna da amana ita da Dr. Sakeenah, kuma Sakeenah ta yi mata gata da taimakon da har abada ba za ta manta ba.
Ita ce silar samun saukin ta daga lalurar fitsarin kwance, lalurar da ta yi ta fama da ita tun haihuwar ta, ta hana ta jin dadin rayuwar aure. Don haka ba za ta taba mantawa da wannan taimako da iyalin Hajiya Nasara suka yi mata ba. Sakeenah ba ta tsaya a taimako ga lafiyarta kadai ba, har ga sauran fannonin rayuwar diya mace ta taka rawar gani wajen inganta mata. Girki, tsaftar jiki da ta muhalli, kwalliya da duk abin da zai amfani mace Sakeenah ta koya mata.
“Wato Kulsumu farin ciki ki ke za ki bar mu shi ya sa ki ke ta faman tattare inaki-inaki”. In ji Dr. Sakeenah tana mai zama a gefenta.
Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai, sai ga hawaye sun zubo. Ta kama hannun Sakeenah ta rike cikin tafukanta, ta ce, “Doctor, na gode. Na gode, wallahi bana farin ciki, zan yi kewarku sosai. Musamman su Waleed”.
Sakeenah na dariya ta ke share mata hawaye ta ce, “Ni ma na gode Kulsum, Allah ya ba ki ilmi mai amfani ya kuma ba ki abokin rayuwa na gari. Na ji dadin zama da ke. Insha Allahu duk sanda ku ka samu hutu zan roki Hajiya ta ba ni ke, mu ma in mun samu sararin aiki za ki gan mu a Abuja insha Allah”.
Ta je dakinta ta shigo da akwati shake da kaya, ta ce, “Ga kaya na sa an dinka miki kala goma ne, za su yi miki amfani, saboda zuwa makaranta, kowanne da gyalensa, ga takalma da jaka set biyar ki yi amfani da su”.
Duk sai ta rasa da bakin da za ta gode. Aunty Sakeenah ba ta da abin da za ta gode mata da shi sai addu’ar alkhairi gare ta da zuri’arta.
Washegari Baban Waleed ya je ya dauko Taufeeq don ya yi kalaci, sannan su kai su airport. Kafin su gama Kulsumu ta kimtsa komai nata. Da ma tun bakwai na safe ta yi wanka. Daya daga cikin swiss laces din da Sakeenah ta dinka mata ta saka mai ruwan zuma da ratsin coffe. Lokacin da ta fito falo jaye da katuwar jakarta.
Taufeeq ya daga kai ya kalle ta, sai ya ga jiya ashe kallon tsoro ya yi mata. Duk inda ake neman kyakkyawar mace ta kai, iyakaci a ce ba ta da wayewa irin ta matan birni. Baban Waleed ya karbi akwatin daga hannunta bayan sun gaisa. Tana so ta gaida Taufeeq babu fuska. Dr. Sakeenah ta ce, “Kulsum ba ki gaida brothernki ba”.
A sanyaye ta ce, “Barka da safiya”.
Irin gaisuwarsu ta gidan Sarkin Gaya. Ta riga ta saba ba ta iya gaisuwar ina wuni ko ina kwana ba, sai dai ta ce barka da asubah, barka da yamma, ko barka da rana. Ko ya