Showing 30001 words to 33000 words out of 33918 words

Chapter 11 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

438

don kyale-kyale na rayuwa ba. Babu sirrin junan su da ba su sani ba. Yo mijin da ki ke yi wa fitsarin kwance ya wanke ai zance ya kare. Turaki ba ya boye wa Kulsum komai da ya shafe shi, ko da a fannin aikin sa ne. Da hankulan su suka natsa ne ya gane Kulsum na da matsala a ido. Sai lokacin ne ya tuno zuwansu European Eye Hospital a Lagos ita da Taufeeq, ya tsare ta da tambaya kan me ya kai ta ranar? A nan ne ya san matsalar idon Kulsum ta tun haihuwa. Mai abu da abunsa, wani ma ya yi rawa bare dan makadi?
Tuni ya sa ta a gaba da bincike da gwaje-gwaje, a nan ya gano tana dauke da matsalar da suke kira amblyopia (lazy eye), wanda magunguna na digawa (eye drops) kadai zai magance shi ba sai ta saka gilashi ba. Tun daga ranar ya soma diga mataeye drops masu kyau har suka washe.
*******
Ranar ta kasance juma'a, da wuri Turaki yake dawowa gida. Ya shigo a matukar gajiye, Kulsum na zaune ta bararraje tana shan 'ya 'yan 'strawberries' in zai iya tunawa yau wajen sati guda ke nan ba ta da abinci sai 'ya'yan 'strawberries'. Ta kashe shi da murmushi, ya ce, "Kulsum are you alright? Cin wannan abun naki ya yi yawa fa".
Ta yi narai-narai da ido, "In ban ji shi a baki na ba sai in ji saliva (miyau) ya cika min baki".
Murmushi ya yi ya aje jakar hannun sa da falmaran din 'suit' din jikin sa akan kujera.
"Then, you are subject to P-t (pregnancy test)".
Zaro ido ta yi abin dariya, "Haba Prince! 'yar yarinya ta da ni za ka yi min wannan fatan?"
Dariya ya yi, ya iso gare ta ya mikar da ita tsaye. Ya jingina bayanta a jikin sa ya daga rigarta da hannun damansa yana shafa shafaffen cikin ta cikin shauki.
"In mace ce, Batulu ce. In namiji ne Abdul'Ahad ne. Su suka taimaka min na same ki 'for the second time', a lokacin da na riga na sa a raina na rasa ki, ciwon son ki kuma shi ne zai yi ajali na. Sun ba ni 'support' din su dari bisa dari tare da tabbatar min ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. With Almighty Allah everything is possible".
Kulsum ta yi murmushi, ta ce, "Ni dai ban fada maka ina da ciki ba".
Ya ce, "Amma kin iya sa miji a daki kina k......".
Da sauri ta kwace jikin ta daga nasa ta yi daki, tare da sa yatsun ta biyu ta toshe kunnen ta. Turaki bai yi shiru ba sai da ya karasa mata. Ya kuma tabbata zahiri Kulsum na da karamin ciki na watanni biyu, lokacin da Turakin ya gaji da ciye-ciyen ta ya kai ta 'lab' aka auna fitsarin ta.
A wannan satin suka shirya zuwa Manchester wajen su Sajeedah. A 'train' suka tafi zuwa Manchester. Sajeedah da Abdul'Ahad suka shirya musu tarba ta musamman za su yi weekend (hutun karshen mako) tare da su. Amma kasancewar gidajen U.K kanana ba 'spare room' dole sai a 'hotel' suka sauka.
Da safe wanka kawai suka yi suka shirya Abdul'Ahad ya zo ya dauke su zuwa gidan su. A can suka yi 'breakfast', Kulsum da Sajeedah suka wuni hira, Sajeedah na kara wayar mata da kai a kan rayuwar duniya gabadaya. Da yamma suka debe su a motar Abdul'Ahad don su zaga da su cikin Manchester, inda suka ziyarci 'Greater Manchester, Castle Field, National Football Meseum, Man City and Man United' da suke jin labari. A karshe suka dire a 'university of Manchester' jami'a mai tsohon tarihi. Sun rabu kamar kar su rabu, a lokacin cikin Sajeedah watanni bakwai. Burin Sajeedah ya cika ta zama 'best friend' din Kulsum, abin da ba ta taba yi a rayuwar ta ba (kawa) bayan Batulu.
Ba tare da shawara da ita ba Turaki ya cike mata 'application' na neman gurbin karatu. Babu jimawa 'admission' dinta ya fito, ya kawo mata har kan cinyar ta. Kulsum ta daga takardar tana karantawa a hankali. 'Admission letter' ce manne da sunan ta KULSUM ABDULHADI YALLEMAN za ta karanci digiri a fannin aikin jinya (B.Sc Nursing) na tsawon shekaru uku a jami'ar da Turaki yake wa aiki, kuma ya yi nasa karatun, wato 'university of Reading'.
Da Kulsum ta buga wani tsalle sai ga ta makalkale a bayan Turaki. Da sauri ya sa hannu ya riko ta.
"Kina da hankali kuwa? Wani abu ya samu cikin nan wallahi sai an fasa karatun".
"Na tuba na bi Allah na bi ka, Baban Batulu, angon Kulsum. Na rasa ta hanyar da zan nuna godiya ta, ka gama cika min duk wani buri na, ka gama yi min duk wani taimako a rayuwa. A lokacin da na fi bukatar taimako. Ka ba ni dukkan kauna da kulawa ta yadda kullum nake kwana in wuni ina tunanin, ni da me zan saka maka Prince?"
Tafiya ya hau yi dauke da ita a bayan sa zuwa dakin sa. Cewa yake, "Kin fi kowa sanin da me ki ke saka min UmmuKulsum. Fata na ki cika min gida da 'ya'ya shi ne kawai tukwicin da za ki yi min".
Cikin sa'a cikin nata ba mai tsarabe-tsarabe ba ne. Barta dai da ciye-ciye, ci banza ci wofi don haka bai ba ta matsala sosai ba lokacin da ta fara zuwa makaranta. Da farko ta sha wahala sosai kafin ta gane kan karatun nasu, amma da ta likewa Turaki duk sanda yake gida tana gefensa rike da littafin ta, nan da nan komai ya fara zauna mata. Domin koyarwar Turaki wanda ya kasance malamin jami'a, kuma 'consultant' a kiwon lafiya ta sha bamban da ta dukkan malaman ta. Ta yarda Turaki dan baiwa ne ba a fannin soyayyah kadai ba, Ubangiji ya ba shi baiwa a ilmin kiwon lafiya.
Ko da watan haihuwarta ya kama Turaki cewa ya yi ba za ta je gida ba, kasancewar suna tsakiyar karatu. Ta haifi kyakkyawar 'yar ta mace a asibitin 'Royal Berkshire' ranar litinin. Turaki ya rungumi 'yar shi ta farko a duniya yana tsaye a kan mahaifiyar ta da ake gyarawa. Tare da shi aka karbi haihuwar.
A wurin ya yi mata khutbah da sunan da ya tanadar mata tuntuni, wato Fatima-Batulu.
Lokacin da Kulsum ta samu kanta, Turaki ya dauko babyn ya ajiye mata a kan kirjin ta. Murmushi ta ke yi tana kallon yarinyar. Komi na Turaki ta kwashe, har zara-zaran yatsun hannun sa. Ta karanta addu'ar kariya daga zina ta tofa mata a al'aurarta, wato aya ta 11 cikin 'suratul Tahrim'.
(Wa Maryam ibnat Imranal-laty ahsanat farjaha fanafakhna fiihi min ruhina wa sadaqat bikalimati rabbiha wa kutubihi wa kanat minal qaniteen) kafa 41, sannan ta mika wa Turaki ita, wanda ya zauna a kusa da ita yana rada mata kalaman da suka zamo sirri ne a tsakanin su.
Lokacin da Kulsum ta yi wa Batulu albishir da sunan da Turaki ya saka wa baby, Batulu kuka ta saki don farin ciki. Tun ba su bar gadon asibitin ba kowa nasu da ke Gaya ya samu labarin haihuwar, Turaki ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, ta ce da man cikin satin nan za su shigo U.K ita da Daddy za su shigo Reading su ga baby.
Hakan kuwa aka yi, washegarin komawar su gida su Hajiya Nasara suka zo, Sajeedah ma da danta Naufal duk sun zo. Duk da Turaki ya dauki nurse wadda za ta kula da su a gida, Hajiya Nasara ita ta ke wa maijego wanka da tawul, ta kuma wanke baby safe da yamma. Dole Turaki ya debi kayansa ya bar musu gidan don ya yi musu kadan, daki ya je ya kama a 'hotel' na tsawon sati biyu da Hajiya Nasara za ta yi.
Umma ta yi fadan lallai ya dauko Kulsum da baby ya dawo mata da su, amma da ta ji Hajiya Nasara na tare da su sai ta hakura, ta tabbatar za ta ba su kulawa yadda ya kamata.
Jego na sosai Hajiya Nasara ta yi wa Kulsum, Sajeedah ce mai musu girki. Cikin kwana bakwai sun murmure sun yi kyau. Turaki da Abdul'Ahad sai dai su zo su ci abinci su tafi, don Abdul'Ahad din tare da Sajeedah da dan su Naufal suka zo. Ya yi 'weekend' tare da su ya koma Manchester ya bar su Sajeedah ita da Hajiya Nasara suka ci gaba da kula da mai jegon da baby har tsayin sati biyu, inda Hajiya Nasara ta soma shirin koma wa London inda ta baro Daddy, za su kara sati daya sannan su wuce gida.
A bakin Hajiya Kulsumu ta ji labarin Taufeeq ya samu mata, diyar abokin Daddy ce, nan da watanni uku za a yi bikin.
Ta nuna wa Mum farin cikin ta sosai tare da yin fatan alheri. A ranta ta ce, da a ce tana da wata sana'a ko tana da kudi, da ta yi wa Taufeeq gudunmuwar lefe. Kamar Turaki ya san abin da ke ranta, lokacin da Mum za ta koma ya dunkulo kudi masu dama ya ba ta, ya ce ta hada wa kowa da ya dace tsaraba. Don haka ta rubuta wa Sajeedah duk abin da ta ke so ta sayo da kudin. Goggo da Umma atamfofi Sharaton turmi uku kowannen su, Baffa da Malam Hadi bandirin shadda excelcior, Maimartaba turare mai daraja, hatta yaya Hadiza da Batulu ta aika musu 'laces' masu kyau, sannan ta sa Sajeedah ta saya mata takalma da jakunkuna set (24) bayan ta sa Nasmah ta tambayo mata 'size' din kafar Fahima matar Taufeeq, ta shirga su cikin akwati ta bai wa Mum ta ce a bai wa Taufeeq gudunmuwar ta.
Aka ce naka-naka ne, sai dai ka yi kara da kawaici. Hajiya Nasara ta yi farin ciki sosai ba don ba ta da shi ba. Sai don alheri wa naka ko ya ya yake dadi ne da shi.
Washegari ta koma wajen mijin ta suka fara shirin dawowa gida.

Taufeeq ya yi mamakin sakon da Kulsum ta aiko masa. Ya dauka ta yanke alaka da shi kenan tunda ta samu dan Sarkin ta. Ko ba komai hakan ya rage kullacin da ya yi mata. Har da Hajiya ta kira ta ya karbi wayar ya yi mata barka, wannan ya faranta ran Hajiya Nasara sosai.
Su ma su Sajeedah washegarin tafiyar Hajiya Nasara suka koma Manchester.
A daren Turaki ya dawo daga balaguron 'hotel' dinsa, ya tadda iyalinsa cikin koshin lafiya. Aka dora soyayya daga inda aka tsaya, musamman da ya kyalla ido ya ga Kulsum na sallah. Kulsum har da kukanta kan cewa za'a sa ta yin kazamin jego, da gwarne (rurrutsa). Duk sai ta bai wa Turaki dariya, ya ce yana mai tallafo kanta cikin tafukansa, "Rurrutsa na taso na ga ana yi a gidanmu, kuma ban ga kowa ya mutu ba. Mun rayu bi-da-bi cikin koshin lafiya. Ni in za ki haifa min yara duk karshen wata ina so Kulsum, tunda Allah bai hana min yadda zan yi da su ba".
A yanayin da ya yi maganar ya karya zuciyar Kulsum. Ta ji cewa, ba gwarne/rurrutsa ba, ko haihuwar kullum yake so za ta yi masa muddin hakan yake so. Ta shige cikin jikin Turaki a hankali tana mai sallamawa dukkan bukatun sa. Idan ta tsaya tana lissafo gudunmuwar Turaki cikin rayuwar ta, sai ta ga cewa ita ba ta taba yi masa komai a duniya ba. Don haka kamar yadda ya ce din ne, da haihuwar kawai za ta biya shi. Burin sa ya bude ido kullum ya ga 'ya'yan ta sun cika masa gida. Wannan ne kadai martanin soyayyar da yake so daga gare ta.
Kafin Kulsum ta kammala B.Sc din ta 'ya'yan su biyu; Batulu da Iftihal. Zuwa wannan lokacin Turaki ya yi murabus daga aiki a 'United Kingdom' ya tattaro tarin kwalayen sa da experience din sa da iyalin sa sun soma shirin dawowa gida gabadaya. Kulsum Abdulhadi, a matsayin cikakkiyar ma'aikaciyar jinya mai shaidar HND da B.Sc.
*****









MURFI
GAYA
Suka dawo mahaifar su kamar yadda suka barta shekaru uku a baya. Cikin iyayen su, kakannin su da 'yan uwan su. Ba jimawa Turaki ya soma ginin asibitin sa a Gaya, wanda ba ido kawai za a dinga dubawa ba. Don haka ya debo kwararru daga fannonin da Kulsum ke so su bada taimakon su, musamman 'obstetrics and gynaecologists'. Da taimakon Maimartaba Sarkin Gaya III tangamemen asibitin ya kammala cikin dan lokaci kalilan. Wanda Turaki ya sanya wa suna GAYA SPECIALISTS HOSPITAL. Asibiti ne na lalurorin mata da haihuwa da cututtukan kananan yara, sannan da matsalolin da suka shafi ido, wanda ya samu lasisi daga hukumar lafiya ta kasa. A kyauta ake duba marassa lafiya, magunguna kadai za su saya, domin akwai hannun gwamnati a cikin sa.
Kulsum ta hada kudaden ta da ta dade tana tarawa da dan aikin 'part-time' da ta yi a U.K ta biya wa Baban ta Malam Hadi hajji shi da Baffa, sai Turaki ya biya wa Goggo da Umma da yayar sa Hadiza, suka tashi gabadaya zuwa kasa mai tsarki.
A wannan tafiya Kulsum ta sha addu'a daga mahaifin ta da kakannin ta, wadanda dukkan burinsu a duniya bai wuce ingantuwar rayuwar ta ba, da dorewar ta cikin zaman lafiya a gidan auren ta.
Ta yi burin dora 'course' a kan 'perioperative' bayan dawowar su Gaya, amma laulayin ciki na uku ya hana ta. Sannan ba za ta iya tafiya Yola shekara guda ta bar Turaki ba shi ya sa ta tsaya haikan a kan asibitin su a matsayin 'Chief of Nurses'. Sun tarar da rasuwar Fulani kakar su Turaki watanni kadan kafin dawowar su.

Gudunmuwar Dr. Abubakar Turaki Gaya ga kiwon lafiya bai tsaya a garin su Gaya kadai ba, ana daukar sa hayar aiki a fannin sa na 'Ophthalmology' a manyan asibitocin idon nan na 'European Union' da ke Lagos, asibitoci masu zaman kansu da manyan Asibitocin gwamnati. Duk inda Turaki ya je ya yi aiki garin su Gaya yake dawowa cikin iyalinsa bai yi gida a kowanne gari cikin maraya ba.

Kulsum ta zauna ta yi tunanin ya kamata ta fito duniya ta yi 'creating awareness' ga mata 'yan uwan ta masu fama da lalurar fitsarin kwance, domin da yawan wadannan mata, wadanda mostly suna gidajen aure, ko gaban iyayen su sabida zaman aure ya gagare su, a kan su fito su nemi 'medical help' a kan lalurar 'ENURESIS'. Yanzu zamani ya zo da sauyi na ci gaba da babu irin lalurar da ba a magancewa a asibiti, maimakon su zauna cikin bakin cikin rayuwa. Ta kuma yi kira ga maza kan su taimaka su kuma tausaya wa matan su masu lalurar fitsarin kwance. Nuna kyama da wulakanci a gare su ko rabuwa da su babban kalubale ne ga rayuwar su. Hakan zai jefa rayuwarsu cikin 'risk' na kamuwa da depression, self-hatred da inferiority complex, wani lokacin har ya jawo tunanin kashe kai, wato (suicidal thought) ga masu raunin imani.
Ta tattauna da mijin ta uban 'ya'yan ta Dr. Abubakar Turaki kan kudirin ta. Shi kuma ya ba ta goyon baya dari bisa dari. Ta soma gabatar da makalar a media (talabijin da radiyo) a manyan tasoshi da taimakon Turaki. Lakcoci ne ta ke gabatarwa masu taken 'Enuresis in Adults; A way out in the medical profession'(fitsarin kwance ga manya; mafitar sa a fannin kiwon lafiya). A wata makalar kuma ta ce 'Psychological Trauma of Noctural Enuresis; ta kawo bayanin yadda mata da yawa ke fama da shi a gidan aure. Yadda maza ke 'treating' dinsu da kyama, hantara, wulakanci da raini, ta yi kira ga masu fama da wannan lalura kan cewa lokaci ya yi da ya kamata su san cewa fitsarin kwance ba shi ne karshen rayuwar su ba. Su mike su nemi magani, don tsira da martabar su a gidan aure.
Tun daga lokacin da aka fara sakin lakcocin Kulsum a 'social media' ta fara karbar kira daga mata daban-daban inda suke tabbatar mata halin da suke ciki kenan, da yanayin zaman su da mazajen su. Kulsum in ta ji wani abun, ta tuno Turaki da nasa kalar 'treatment' din a gare ta, sai kuka ya kwace mata. Ta kara godewa Ubangijin ta,?????????????????????????
???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ta amince Turaki daya ne cikin dubu, kuma Ubangiji ya so ta da rahma ne da ya nufe ta da dawowa hannun sa.
*****

Baffa ne ba ya jin dadi, ta yi masa girki na musamman ta zuba yaran a mota suka tafi don su duba shi. Goggo da Baffa wadanda tsufa ya dada kama su, amma shar suke cike da koshin lafiya sabida kulawar da suke samu daga Kulsumu da Turaki, suka shiga ina suka saka-ina-suka-aje da tattaba kunnensu masu kiriniya. Iftihal ta yi tsalle ta haye wuyan Baffa tana fadin, "Baffan Goggo ka yi min doki irin wanda Baba na yake mana".
Kulsum ta mako ta a fusace tana fadin, "Sai kin karya min Baffa na? Ki je Baban naki ya yi miki amma wannan Kakana ne".
Iftihal ta bare bakin shagwabar ta tana kuka, Baffa ya jawo ta jikin sa yana rarrashin ta.
"Kyale Mama, ni ma ba Baban ta ba ne, Baban ta yana 'Yalleman".
Goggo kuwa ta hau yi wa Kulsumu fadan saurin duka irin nata, fada ta ke,
"Ke wa ya doke ki? Akwai wanda ya kai ki hawa jikin mutane?"
Kulsum murmushi ta ke tana zubo wa Baffa dafuwar hanta da ganyen alayyahu da ta kawo masa a faranti ta mika masa, ta zuba wa Goggo tana fadin, "Ku ci sosai ku murmure, umarah za ku koma sati mai zuwa, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login