Showing 21001 words to 24000 words out of 33918 words

Chapter 8 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

442

bai shirya aure ba a wancan lokacin aka aura masa ita, amma ba kinta yake ba. Bai taba kinta ba. Ta amshi soyayyar sa da hannu bibbiyu, ta maida martani iyakar iyawar ta, suka dunkule suka zama abu daya a wannan dare mai dumbin tarihi a cikin rayuwar su. Ba su suka samu suka runtsa ba sai misalin karfe uku na sulusin dare.
Goshin asubahi, a lokacin masallatai sun fara kiran sallah, Prince Turaki, ya muskuta manne da Kulsum a jikin sa, amma sai ya ji wani sururun sanyi na shigar sa ta kasan sa. Ya sake gyara kwanciya har zuwa yanzu bai raba Kulsum da barin jikin sa ba don kada ya tashe ta daga barcin hutun da ta samu. Jin sa ya yi male-male a cikin damshi, tun daga samansa har kasan sa a jike yake yarab! Daga shi har Kulsumun.
Cikin tsananin tu ajjibi da mamaki har ma da tsoro ya raba Kulsum da jikin sa ya mike zaune. Wannan ruwa daga ina haka? Motsin sa ne ya tada Kulsum, juyawar ta da zaman ta suka ankarar da ita abin da ke faruwa.

 Ta yi fitsarin kwance!

 Innalillahi wa inna ilaihi raji un .

Kulsum ta ambata cikin tsananin tashin hankali. Kafin ta sunkuya ta fashe da kuka, gigitaccen kuka mai nuna zurfin tashin hankalin da ta samu kan ta. Ta dauka ya tafi, ta dauka sun yi sallama, ashe jira yake ta yi aure ya dawo ya sake raba ta da farin ciki a rayuwar ta???
Shi dai Turaki har zuwa lokacin ya kasa gane komai. Kukan ta ne ya kidima shi, ya kamata, ta yi sauri ta janye jiki a hankali daga gare shi, ta koma can karshen gado ta ci gaba da kukan ta.
Ta san rabuwarta da Turaki ta zo, a lokacin da ta gama samun duk wani contentment na rayuwa. Babu wani namijin da zai jure rayuwar aure da mai lalurar fitsarin kwance, balle babban likita mai matsayin consultant, kuma dan Sarki kwaya daya tal irin TURAKI.
Kukan ta ya tsananta, ya kara gigita Turaki, gabadaya ya rasa gane me ke faruwa? Sai a lokacin kwakwalwar sa ta ankarar da shi. Shekarun baya ya tuna da hirar da ya ji tsakanin ta da Laraba, ashe ba ta warke ba din har zuwa yanzu, har tsayin zaman ta a hannun marikan ta? Fuskar sa expressionless (bata nuna komai ba) ya bar dakin jagab da pajamas din shi sai yarari yake.
A toilet din dakin sa ya cire kayan, ya sakar wa kanshi shower. Ruwan na sauka a jikin sa yana tunanin ta yadda zai taimaki matar sa Kulsum. Tausayin ta ya bi ko ina na jikin sa, ko kadan bai ji kyama ba, sai ma wata sabuwar soyayya da ta kara manne masa a zuci da ruhi, wadda tausayi ke assassawa. Yana iya hasaso how embarrasing ta ke jin kanta, shi ya sa ta ke wannan kukan tamkar na fitar rai. Ya sa a ran sa da taimakon Allah sai ya zama silar da Kulsum za ta samu lafiya, idan kuma wannan ita ce kaddarar ta, wato dauwama cikin lalurar fitsarin kwance, zai ci gaba da zama da ita cikin so da kauna, hakan ba zai raunata komai na daga soyayyar da yake yi mata ba.
Zai saya musuwater mattress, washing machine da zannuwan gado masu yawa, zai taimaka mata ta dinga tsaftace kanta, a duk lokacin da lalurar ta same ta.

Kulsum bayan ta ci kukan ta ta koshi, ta yi tunanin kiran Dr. Sakeenah don ta sanar da ita, ita ma ta san da laifin ta, likita bai ce ta daina shan magungunan ta ba ta daina, tunda ta ga cewa ta samu lafiya. Ba za ta iya tuna lokaci na karshe da ta sha maganin ba, sai dai kuma ta baro wayar ta ne a Lagos tun gigicewar ganin Turaki.
Ta je ta yi wanka, hawaye na bulbula, fitowar ta ke da wuya ta sa mukulli ta kulle kanta, ba za ta iya kara hada ido da Turaki ba. What an embarassment (wannan abun kunya har ina). Sai daga baya ta yi tunanin to wa zai gyara masa gadon idan ba ta je ba? Gara dai ta boye kanta ta ji da gundumemiyar kunyar ta da tozartar ta.
(Wannan ne halin da mata masu lalurar Enuresis ke fuskanta tsakanin su da mazajen su, ga wasu mazajen wannan shi ne dalilin wulakanci a gare su. Ya jama a mu sani cewa, babu wanda yake sama da lalura duk matsayin sa duk ilmin sa, masu lalura soyayya da tausayi suke bukata, musamman daga mazajen su, domin kaddara ba ta wuce kan kowa ba. Allah ka kara mana lafiya da zama lafiya, amin- Takori).

Turaki da kansa ya yaye zanin gadon, ya je ya sa shi a famfo ya zuba Ariel da hypo ya wanke. Ya rasa yadda zai yi da katifar dakin sa, sai ya kada omo a bokiti ya zo ya sa tawul ya dinga gogewa. Da ya tabbatar ya fita, sai ya daga ta ya shimfide a tsakar dakin ya sakar mata fanka da A.C.
A gurguje ya shirya don Maimartaba yana jiran sa, ya fito zuwa dakin Kulsum.
Murdawa ya yi ya ji ta rufe da mukulli, ya kira sunan ta a tausashe,
 Ummu Kulsum bude min kofa .
Yana jiyo shesshekar kukan ta da ke tashi a hankali. Zuciyar sa ta kara raunana, ya ce,  Kulsum& please& .. .
Cikin kuka ta ce,  I cannot face you&  .
Murmushi ya yi ya ce,  Na ji to, zan rufe idona yadda ba zan gan ki ba .
Ta ce,  Ka yi alkawari?
Ya ce,  It s a promise&  .

Ta zo ta bude kofar tana rakubewa a bayan kofar. Ya janyo ta ya hada da jikin sa,  Duk wannan kukan na fitsarin ne? Idan ya sanya miki zazzabi fa? Haka kawai ina cikin amarci na a cuce ni?
Duk halin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, murya abin tausayi ta ce,
 Wane amarci ga mai fitsarin kwance?
Ya kara matse ta a jikin sa sosai, sassanyan kamshin jikin sa na ratsa ta, yana haifar mata da wata irin nutsuwa da kwanciyar hankalin da ta rasa.
Ya ce,  Kulsum ki sa a ranki, ba fitsarin kwance ba, ko yoyon fitsari ki ke yi, I m at the extent of loving you, intending to stay with you, and vowing to help you& we will fight this problem together (ina kan kololuwar sonki, dauke da aniyar ci gaba da zama da ke, da kuma alkawarin taimaka miki. Za mu yaki wannan matsalar tare) insha Allahu. Just relax and pray. Yanzu zan je in ga Maimartaba akwai inda za mu je sai dare zan dawo. Me ki ke so in taho miki da shi?"
Hawayen farin ciki suka zubo daga idanun Ummu Kulsum. Ba ta taba tsammanin martanin da za ta samu daga Turaki ke nan ba. Ta kara gamsuwa da cewa....this is not the previous Turaki& wannan wani sabon Turaki ne, mai dauke da kauna ta ban mamaki a gare ta.
"Ba abin da nake so sai kai Prince dina . Ta fada tana kwantar da kai a kirjin sa. Kaso tamanin cikin dari na tashin hankalin ta ya kau. Ya dan bubbugi bayan ta, ya ce,
 In dai Turaki ne kin samu, I m only yours. Zan kawo miki waya sabida su Goggo, amma ban yafe ba in ki ka yi magana da Taufeeq .
Ta lumshe ido tana murmushi, ta ce,  Ko ka yafe ba zan yi ba. Bana neman komai daga sauran maza, you are more than enough to me. Allah ya bar mu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi .
Sosai Turaki yake kissing din kowacce halitta ta fuskar Kulsumu, ido, hanci, goshi, da baki sai da suka karbi rabon su na sassanyar passionate kiss daga Yarima Abubakar Turaki. Sannan da kyar ya janye ya gyara zaman hular sa ya fice da gudu-gudu sauri-sauri ganin sunan Maimartaba a kan fuskar wayar sa. Kulsum ta bi shi da lallausar murmushi. Ji ta ke kamar su dauwama cikin wannan yanayin da ba ta taba samun kanta a mai dadi da sanya nutsuwar sa ba.
Ko da ya dawo a ranar kin zuwa dakin sa ta yi, har yanzu kunyar ba ta sake ta ba. Ta yi shirin kwanciya ke nan sai ga shi ya shigo, tun daga bakin kofa ya jefa mata harara.
 Me ki ke nufi da ni ne matar nan? Ina ta jiran ki ki zo mu cike wasu takardu, kin barni ni kadai? Shirin kwanciya ma ki ke yi abun ki alhalin ga turakar mijin ki?
Kulsum ta langabar da kai abin tausayi, ta ce kasa-kasa.
 Ina tsoron kada ya kara zuwa ne .
Ya sa hannu ya dago habar ta, murmushi ya sakar mata wanda ya ratsa har cikin ruhin ta. Sannan ya sumbaci bakin ta ya ce,  To sai me? Har na sayo mana injin wanki da katon din hypo da na omo (Ariel). In mun yi sai mu wanke. Watarana sai labari& ..! .
Da karfi Kulsum ta kankame shi tana wani irin kuka. Gabadaya ya daga ta suka fice daga dakin. Cike takardu bai yiwu ba a wannan dare, domin ya kasance daren rahma ga ma auratan, sun raya shi har yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Amma a karshe Kulsum ta ki yarda barci ya dauke ta, tana kallon Turaki yana barcin sa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali irin wanda miji ke samu idan ya samu kyakkyawar gamsuwa daga matar sa.
Sai zarya ta ke daga gadon zuwa toilet tana kakalo fitsari. Ba ita ta kwanta ba sai da suka yi sallar asubahi, Turaki ya dube ta tana lazimi idanun ta sun yi luhu-luhu. Ya daure fuska sosai ya ce,  Look, hau gado ki kwanta sai karfe goma na yarda ki tashi daga barci. Wannan daura wa kai wahala har ina? Ina ce katifa dai tawa ce ko? Zanin gadon ma nawa ne ba naki ba?
Ta sunkuyar da kai tana murmushin maganar sa, soyayyarsa na karuwa a zuciyar ta.
 Oya! Hau ki kwanta tun ban canza manufa ta ba .
Ta gane me yake nufi, don haka ta ja jiki zuwa gadon ta kwanta a dofane, ya jaquilt ya rufe ta da kansa. Tare da sunkuyawa ya sumbaci goshin ta.
Ta yi barci kuwa sosai, domin kuwa shi ba'a cin bashin sa. Sai dai kuma ta tashi ne again cikin yanayin da ya fi na jiya. Turaki yana dining yana karyawa da abincin da Laraba ta tanadar musu. Sai da ya gama ya dawo dakin, ya shiga toilet ya yi wanka ya fito yana zaben kayan da zai sa ba tare da ya san halin da Kulsum ke ciki ba. Ta sanya kanta karkashin filo tana kuka, wanda da hawaye kawai ta ke yin sa babu sauti. Ba ta so yau ma ya yi aikin fitsari shi ya sa ta sa hannu ta toshe bakin ta.
Sai da ya gama tsaf! Ya fesa turarensa one man show, sannan ya iso gabanta don ya duba ko ta tashi. Filon da ta danne kanta da shi ya dauke,  Kina so ki danne numfashin ki ne?
Gani ya yi wajen ya jike sharkab da hawaye. Nan ya gane halin da ta ke ciki. Fuskar sa ta nuna damuwa ya ce,  For God s sake Kulsum, wannan kukan ne zai yi maganin lalurar? Duk abin da na gaya miki bai shiga kunnen ki ba. In dai a kaina ne ki ke shiga wannan halin ni kam kina zaluntata! Damuwar ki da fitar hawayen ki sune manyan damuwa ta ba fitsari ba. Idan  depression ya kama ki ba zan yafe miki ba .
Da kyar ta mike cikin tsananin jin kunya, ya taimaka mata ta hanyar kama hannun ta ta mike ta shige toilet. Ya yaye zanin gadon, amma wannan katifar in ba ta sha rana ba yau akwai matsala, domin ko an goge da omo sai ta yi warin damshi.
Tana fitowa ta same shi ya balle links din hannun rigar shi ya kwance botir din wuyansa ya zage yana goge katifar. Kifa kai ta yi a jikin bango tana hawaye.
Turaki ya yi kwafa ya ce,  Ki yi abin da ki ke ganin shi zai fishsshe ki .
Duk runtsi ba zai fidda katifar nan waje ba sabida  yan aikin su, balle Laraba da yake da masaniyar ta san Kulsum na da lalurar. Ya rasa yadda za su yi da katifar, ya dai sakar mata fanka ta sama da ta kasa. Ya canza kayan jikin sa ya je ya shigowa da Kulsum abin da za ta ci. Da kyar ya samu ta iya cusa dankali biyu a bakin ta. A ran ta ta yanke ba za ta kara kwana dakin Turaki ba duk abinda zai ce mata gara ta je ta yi ta kazantar ta ita kadai a dakin ta.
 Tea din nan sai kin shanye shi, in har kina son zaman lafiya Kulsum".
 Ka yi hakuri Prince, ba ni da appetite, wallahi na tsani kaina! .
Turaki ya tsura mata ido, kalaman rarrashi sun kare masa. A irin wannan stage din ne mata da yawa ke haduwa da depression wanda zai iya yin sanadin suicidal thought.
Ya ajiye kofin shayin ya matsa gare ta ya rungume ta. Ta kwantar da kai a kan kirjinsa tana ta sharbar kuka.
Ya ce,  Is o.k Kulsum, na san abin da ki ke ji. Amma don Allah ki kwantar da hankalin ki, wannan lalura ba kanki farau ba, mata da yawa suna fama da ita, wani lokacin ma har maza. Tun jiya na yi magana da kwararren nephrologist din da zai duba ki Dr. Ibraheem Mansur Takai (Rayuwar Rayhana). Za mu hadu da shi a U.K, zai zo asibitin da nake daga Illinoise (Chicago) kan wani aiki da za mu yi tare. So relax please, stop these waste of tears, ni ko ba ki warke ba ina sonki haka! Zan kuma ci gaba da zama da ke cikin kowanne hali, to the very end .
Kulsum ta shafe hawayen idanun ta, har yanzu kanta na bisa kirjin Turaki, ta ce,  Watarana za ka gaza& watarana za ka auro wata& in ta gane zan wulakanta& zan tozarta&  .
Hannu ya sa ya toshe mata baki.
 Ban yi miki alkawarin har abada ba zan kara aure ba, tunda Ba-sarake ne ni. Amma Kulsum ko aure ya kama ni sai na tabbata kin warke. Ba dai in yi aure saboda lalurar ki ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki .
Kara shigewa jikin sa ta yi tana jin kanta tamkar a kan gajimare. Turaki ya gama yi mata komai a rayuwa, Allah ya sa ya tabbata a hakan.
 Now, gaya min treatments din da ki ka taba karba a asibiti, in cike a wadannan takardun zan tura wa Dr. Ibraheem&  .
Tiryan-tiryan ta soma gaya masa tun zuwanta Lagos gidan Aunty Sakeenah, treatments din da ta karba; pharmacological and non-pharmacological. Result din da treatments din suka bayar. Kwayoyin maganin da aka dora ta a kai, wato tricyclic antidepressants, tofranil (imipremine) da kuma (desmopressin acetate) da ta jima tana sha. Ta kuma daina sha ba tare da likita ya dakatar da ita ba, sai don a tsammanin ta ya tafi ke nan.
Duka Turaki ya shigar da bayanan, sannan ya tura wa Dr. Ibrahim ta email din sa. Ba jimawa response din sa ya shigo, inda ya ce ya amince zai ga Kulsum a U.K sati uku masu zuwa.
Turaki yake gaya mata da ma hutun da ya dauka na aure na wata daya ne, don haka za su koma a daidai lokacin da Dr. Takai ya diba musu. A nan ta ke ji ya zo Lagos ne ziyarar aiki ba'a can yake ba dindindin. Yana aiki ne da asibitin koyarwa na jami ar Reading wato Royal Berkshire Hospital wanda reshe ne na NHS Foundation.
A nan ne ta san abubuwa da yawa game da Turaki wadanda a baya ba ta sani ba. Har haduwar su a jami ar Reading shi da Abdul Ahad da irin abotar da ke tsakanin su, da rawar da ya taka wajen taimaka mishi ya same ta. Ya dube ta ya yi murmushi,
 Shi ya sa na dame ki sosai kan ki karbi bakuncin su, they are your real supporters .
Yana kwance rigingine da laptop a kan kirjinsa yayin da kansa ke bisa cinyoyin ta suke hirar, a lokaci guda yana processing visa dinta ta shiga U.K as his spouse. In ka gan su sai sun ba ka sha awa, yatsun ta cikin sumar kansa wai kitso ta ke mishi cikin tarin kwantacciyar sumar sa duk ta duddunkule mishi gashi, ko kofar gida yau bai fita ba, duk don kada ya fita Kulsum ta koma cikin damuwar ta.
Da magriba ne ya je ya yi sallah ya dawo, ya ce ta shirya su je ta gaida Umma da sauran mutanen gida.
Sosai ta yi shiga ta alfarma sai kamshi suke daga ita har shi. Tsakanin gidan su da masarautar Gaya ba tafiya ce mai yawa ba, a kafa ma za a iya zuwa. Amma mota suka hau, lokacin da suka isa Umma fada ta hau yi kan don me zai fiddo Kulsum ko wata guda ba ta rufa ba, in gaisuwa ce ai tana aiko mata kullum. Shi dai hakuri yake ba ta, bai gaya mata ba ya so ya fito ya baro Kulsum cikin damuwa ba ne.
Umma ta tambaye ta,  In ce ko babu matsala Kulsum?
Kanta a kasa ta ce,  Babu Umma, muna godiya da dukkan dawainiyar ku. Allah ya kara girma, Allah ya kara yawan rai .
Umma ta ce,  Ko kina bukatar karin ma aikata? An ce gidan naku da girma sosai .
Kulsum ta ce,  Umma har sun yi yawa, Baba Laraba akwai zafin nama kamar ba tsohuwa ba".
Umma ta yi murmushi, ta ce,  Ga iya girki kuma. Sannan tana son ki sosai .
Kulsum ta ce,  Yaya labarin mutanen kaduna? Tun bayan biki babu labarin su .
 To ke din ce ai babu waya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login