Showing 18001 words to 21000 words out of 33918 words

Chapter 7 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

441

Yanzu-yanzu idanun ta zasu bada ita. Sai dai ta sa a ranta ba za ta yi abin da zai bata ran shi ba, don ta lura kwarai yake ji da bakin nan nasa.
Sosai Sajeedah ta ke kallon Kulsum, ta yaba da nutsuwa da kamalar ta. Kyau kam akwai shi, amma ba na tada hankali ba. Irin dai na fulanin Gaya. Farat daya ta ji Kulsum ta shiga ran ta. Duk yadda Turaki ke son su hada ido ta ki yarda. Ta kai kayan Sajeedah har bedroom din ta, ta dawo ta zauna a kusa da ita, sannan ta yi musu tayin cin abinci.
Gabadayan su suka hau tebir ta yi serving kowa, making sure ta fara serving Turaki first. Wannan abu ya yi masa dadi, har ya samu karfin gwiwar yi mata magana.
 Sajeedah ta ce a wajen ki za ta sauka .
Ta yi fara a sosai tana duban Sajeedah,  You are most welcome Aunty Sajeedah, na gode sosai da wannan karramawa . Ta fada da harshen Turanci, kasancewar ta gane Sajeedah ba ta jin hausa.
Sajeedah ta ce,  Da fatan ba zan takura wa amarya da ango ba. ina so mu saba ne, mu fahimci juna. Wannan ne karona na farko na zuwa kasar Nigeria. I m Eritrean .
Dr. Abdul Ahad ya ce,  To fadi ba a tambaye ki ba .
Kulsum ta yi  yar dariya, tana son mutane irin Sajeedah, haka suke open minded, sannan ba sa bakunta a duk inda suka samu kan su.
Mazan suka koma tsakiyar falo suna hirar da ta shafe su. Ta ja Sajeedah suka yi dakin ta. Sajeedah ta ce,  Ni fa na sanki ba tun yau ba, labarin ki iri-iri babu wanda ban sani ba .
Mamaki ya kama Kulsum, ta ce,  ke kuwa a ina ki ka san labari na?
Duk cikin harshen turanci suke magana. Sajeedah ta ce,  Duk wanda ya san Dr. Abubakar farin sani ya san ki Kulsum, ki gode wa Allah ba karamin so mijin ki ke miki ba. Har ya yi rayuwar dalibtaka zuwa ta aiki a jami ar Reading Dr. Abubakar ba shi da budurwa. You are his only love tun daga sanda ya rabu da ke har zuwa yau da ya kara samun ki.
Na san za ki yi mamakin dalilin da ya sa na nace sai na sauka a wurin ki. To babban dalilin shi ne, don in labarta miki yadda Turaki ya kwashe shekara da shekaru a cikin soyayyar ki, da neman inda zai gan ki. Babban burin kowace diya mace shi ne ta auri mijin da ke son ta, fiye da son da ta ke yi masa. In haka ne kuwa ke kam Kulsum kin dace, sai in ce ki kara rike mijin ki da daraja, soyayya da kauna don ki kara nesanta zuciyar sa daga sauran mata".
Idanun Kulsumu suka cicciko da kwallah, ta ce,  Sajeedah, Turaki ya yi min laifi da yawa, laifin da zuciya ta ta kasa yafe masa& . . Ta labarta mata komai, na rayuwar su ta farko, amma ban da zancen fitsarin kwancen ta. Da haduwar su a Lagos, da yadda ta gan shi a matsayin mijin ta na biyu. Ta share hawayen ta, ta ce,
 In ke ce za ki yarda yanzun da gaske yake son ki? A lokacin da na so ya so ni, zuciya ta ta ke matukar son sa duk bai so ni ba, sai lokacin da na yi yaki da ita na fidda shi da komai nasa a rai na?
Sajeedah ta dafa kafadun ta biyu, ta ce,  Na fahimta Kulsum, shi da ma aure na hadin iyaye ai haka yake, soyayya ba ta zuwa farat daya, tana zuwa ne gradually along the way a cikin rayuwar aure. So ki bude zuciyar ki ki karbi soyayyar mijin ki a wannan karon, ku mori rayuwar ku tare. Ki manta da duk abin da ya faru a baya, tabbas Turaki bai kyauta ba, amma ki dauki hakan as a system of understanding one another ke da Turaki. Ki daina waiwayen abin da ya riga ya faru, just the present.
Ubangijin da ya halicce mu ma yana mana afuwa a bisa kurakuran mu in mun yi nadama, mun yi alkawarin ba za mu sake aikata wannan laifin ba .
Kulsum ta turo baki cikin shagwaba irin tata ta ce,  Aunty Sajeedah, Turaki ba ya lallashi na, komai cikin gadara da sarautar sa yake yin shi&  .
Dariya Sajeedah ta yi, ta ce,  Ke kuma so ki ke ya kwantar da kai ya lallashe ki ko?
Kulsum ta kai hannu ta rufe fuskar ta kunyar duniya ta lullube ta. Sajeedah ta yi dariya, ta ce,  To ai wannan aikin ki ne Kulsum, shi naturally haka yake ko magana wahala ta ke masa. Amma a matsayin ki na mace za ki iya shaping behaviour din sa zuwa duk irin yadda ki ke so ya koma. Don Allah ki manta da komai Kulsum, Turaki needs your love, ki rungume mijin ki, ya sha wahala a kan ki yadda ba kya zato, yanzu ne lokacin da ya dace ya samu hutu da farin ciki a rayuwar sa .
Kulsumu ba ta ce komai ba, amma tabbas maganganun Sajeedah sun yi tasiri sosai a gare ta, ta yadda za ta fara gina kyakkyawar mu amala tsakanin ta da Turaki ne ba ta sani ba. Akwai kunya sosai ta sauko da wuri haka. Sajeedah ba ta kyale ta ba ta ci gaba da tausar zuciyar ta, da kalamai masu dadi da karfafa gwiwa, sannan ta ce,
 na zo miki da abin da zai kara mallaka miki Turaki, sirrin mu ne na matan Eritrea .
Ta dauko jakar ta ta dinga fiddo mata su, ta kuma takura mata ta sha a gaban ta.
Sai wajen goma na dare Abdul Ahad ya koma masaukin sa bayan sun yi sallama shi da Sajeedah. Ta yi shirin bacci ta ga Kulsum na gyara daya barin ita ma za ta kwanta.
Ta ce,  A ah Kulsum ya ya haka? Duk abubuwan da na fada miki ba ki dauki ko daya ba ke nan? Ai sai Turaki ya gan ni Yayar banza, na zo na makale masa mata a daki. Maza dauki duk abin da za ki dauka ki tafi turakar mijin ki .
Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta da wannan umarni na Aunty Sajeedah. Ta kai kan ta turakar Turaki? To ta ce masa me? Me ya kawo ta?
Girgiza kai ta yi, za ta yi magana Sajeedah ta tare ta,  Kulsum, mazan da ki ka sani a da, ba daya suke da na yanzu ba. Dole ki mike ki nemo aljannar ki, ba ruwan Allah da fushin da ki ke da Turaki, auren Turaki da ke wuyan ki shi ne abin da Ubangiji zai yi la akari da shi ranar gobe kiyama. Don haka ki sa a ranki kin yafe wa Turaki dukkan laifukan sa, kin yi damarar kyakkyawan zama da shi daga daren yau, ki roki Ubangiji ya ba ki karfin gwiwa don na lura kina da riko .
Murmushi ta yi, sai dai ga dukkan alamu maganganun Sajeedah sun shige ta. Hatta ruwan da za ta yi wanka Sajeedah ce ta hada mata, ta zuba turaren su na mutanen Eritrea a cikin ruwan wankan. Ko da ta fito ita ta zabar mata rigar barcin da za ta saka. Ta ce,
 Na fasa kwana a gidan nan, masaukin mu zan koma, har na kira Turaki na fada masa, yanzun nan zai maida ni .
Ta dafa kafadun Kulsum da idanunta suka yi rau-rau.
 Enjoy the blessings of your marriage my dear. Sai da safen mu .
A nan ta bar jakarta, sai handbag dinta kawai ta dauka.
Bayan fitar ta Kulsum kasa bin shawarar ta ta yi, ta yi kwanciyar ta a dakin ta, a ranta tana fadin,  Mu Hausa/Fulani ne Sajeedah, ba kabilar mu daya ba, da kunya da kamun kai aka haife mu .
Tana jin dawowar Turaki daga maida Sajeedah wajen mijin ta, ya kashe fitilun falo da kayan wuta ya wuce dakin sa.
Mikewa ta yi ta kashe wutar dakin. Ta yi addu a ta kwanta. Rana ta farko da ba ta sanya key a kofar ba. Amma har barci ya dauke ta babu Turaki babu ko inuwar sa.
Wai kuma sai ta ji duk ta damu, ko dai shawarar Sajeedah za ta bi ne? Yau ta yarda ba ta taba daina son Turaki ba, daidai da dakika daya, fushi da bacin ran abin da ya yi mata a zaman su na baya shi ne ya danne soyayyar. A yanzu sai bankado kanta ta ke tana bude sababbin rassa tana zuba sabuwar yabanya. Musamman da ta ji labarin nan daga bakin Sajeedah na yadda Turaki ya sha wahalar dawainiyar soyayyar ta.
Sai dai duk kokarin ta na ta iya kai kanta turakar Turaki ta kasa. Haka ta kwana tana juyi a gado, ga ciwon mara sabida magungunan da Sajeedah ta dankara mata masu karfi ne. Amma ta daure komai don tsira da jan ajin ta.
A dakin Turaki kuma yana bisa na ura mai kwakwalwa ne yana yin wani research a kan wani aikin ido da zai yi wa Sarkin Gombe mai fama da lalurar glaucoma sati mai zuwa. Aikin da ya kai shi har karfe biyu na dare. Da ya gama ya yi shirin kwanciya bai leka Kulsum ba, ba ya son ya yi abin da zai tunzurata ta fasa kula masa da bakin sa. Saidai kwarai yake son ganin ta ko dan fadan ne su yi kafin ya kwanta. Amma ya taushi zuciyar sa ya kyale ta, sai dai fa tun dazu da ya yi kissing Kulsum komai ya kwance masa, cikin karfin hali yake komai, amma al amarin ya tado masa da tunanin can baya. Watarana guda daya da ba zai taba mantawa ba tsakanin sa da Kulsum, ranar da ta canza rayuwar sa da zuciyar sa akan ta, ranar da Kulsum ta shige sukuf cikin ransa.
Washegari ba su hadu ba sai wajen karfe goma na safe, ita ta fito tana kara kintsa falon kamin isowar bakin su, shi kuma ya fito cikin shirin fita. Yadin filtex ne ruwan makuba mai shara-shara a jikinsa. Ta lura Turaki na son yadikan filtex marassa nauyi, masu taushi haka. Ba ta juyo daga abin da ta ke yi ba, wato karkade center table da duster duk da babu wata kura a jikin sa. Turaki ya iso gare ta, ta bayanta ya rungume ta ya sanya kansa a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta, wani irin qamshi ya ji da ya gigita shi (turaren Sajeedah). Ya juyo da ita bakidayanta suka fuskanci juna, da azama ya kara rungume ta ya s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????oma kissing idanun ta, hancin ta da bakinta very softly. Ta yi kokarin janyewa, amma bai ba ta damar hakan ba. Bugun da ake yi wa kofar shigowa ya sa dole ya janye daga gare ta ya je ya bude kofar. Abincin karin kumallon su ne da na bakin su Umma ta aiko a kawo.
Hanya ya bai wa matan suka wuce zuwa ciki, shi kuma ya koma inda ya baro Kulsum, ta gagara ci gaba da aikin da ta ke yi ta zauna a cikin kujera tana regaining consciousness din ta.
Ya ce,  Good morning Ma'am, za mu je gaida Baffa ni da Abdul Ahad, ko kina da sako wajen Goggo? Sajeedah za'a rako ta yanzu, ba za ku gan mu ba sai dare, don yau ne za mu yi kilisa .
Ciki-ciki ta amsa,  Ba ni da sako, a gaida Goggo da Baffa". Amma har cikin ranta ta ji dadi, tana son mijin auren ta ya zamo mai yawan gaida iyayen ta, ko da ba zai ba su komai ba.
Laraba ce ta rako Sajeedah tare da faggon kayan ta tare da wata yarinya budurwa, in kun tuna Laraba tsohuwar mai aikin Kulsum, Umma ta cika alkawari da ma ta ce sai bayan sati daya za ta turo wa Kulsum masu aiki, don daga yau an daina aiko musu da abinci daga can gida. Kulsum ta rungume Sajeedah tana mata barka da zuwa. Da kyar ta gane Laraba sabida ta kara tsufa. Zo ki ga murna wajen Kulsum ta rungume tsohuwar wadda ta ke hawayen farin cikin dawowar Kulsum. Sun yi zama na kauna da amana.
Laraba ta gaya mata yarinyar jikar ta ce, sunanta Ladidi, su za su dinga yi mata duk wasu aikace-aikace, in tana da aike wajen Umma ta aika Ladidi. Kulsum ta raka su dakin da za su zauna, sannan ita da Sajeedah suka wuce nata.
Wuni guda Sajeedah tana kara wayarwa da Kulsum kai a kan yadda za ta zauna da Turaki ta mallake zuciyar sa ita kadai, don ta fahimci Kulsum din har yau tana da raunin wayewar kai. Tare suka yi girkin rana da na dare suka adana na su Turaki wadanda ke can suna hawan angonci. Ba su shigo gidan ba sai bayan isha, Sajeedah ta dubi mijin ta cikin kayan sarauta abin ya yi matukar burge ta, Kulsum kuwa makalewa ta yi daga bayan labule tana leken Turaki cikin Royal Attire din sa, kayan da ba ta taba ganin shi da su ba. Ya yi mata kyau da kwarjini har yadda ba za ta iya kwatantawa ba. Ya fidda tuntumemen rawanin kansa ya dubi Sajeedah da ta rungume Abdul Ahad a gaban sa, ya ce,
 Ina Ummu Kulsum?
Sajeedah ta hau waige-waige, don dai ita dai ta san tare suke a falon, ba ta san yaushe ta shige ba.
 Ai kuwa muna tare, ban san ina ta yi ba .
Turaki ne ya ga motsi a bayan labule, ya tafi kansa tsaye ya janyo ta suka shige daki.
 Sai kin gaya min dalilin leke na, na yi kama da wannan raggon saurayin naki dan Abuja ne?
Kulsum ta yi kicin-kicin da fuska, ita a dole ba shi ta ke leke ba, hadi da zumburo baki. Bakin da ta zumburo ya sa yatsansa ibham ya dalle shi da karfi. Ta kai hannu ta dafe bakin ta hawaye suka ciko idon ta don zafi. Sai kuma ta ba shi tausayi, ya tarairayo ta ya rungume yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi.
 Kulsum ko wane irin laifi na yi miki ya kamata a ce zuwa yanzu kin hakura kin yafe min, tunda na kawo kaina a matsayin mai neman afuwa. No one is above mistake, Kulsum don Allah ki yafe mini mu shimfida rayuwar mu haka. Ko me ki ke so zan miki in dai za ki daina fushin nan da ni. Amma don Allah kada ki ce za ki sake bari na a karo na biyu&  .
Saura kalaman suka makale a makoshin sa sakamakon jin hannayen Kulsum sun zagayo ta bayan sa sun rungume shi. Wani abu da bai taba zata ba a wannan lokacin, don haka fadin halin da Turaki ya samu kansa unimaginable ne. It was kind of gentle romance da biro na ba zai iya rubutawa ba. Yayin da Kulsum duk da ba ta cikin hayyacin ta sabida yadda Turaki ke gigitata da nau'ikan soyayyar sa ba ta manta da bakin su da ke falo ba.
A hankali ta zame da kyar ta tura Turaki baya, ya fada bisa gado da baya da baya, dariya ta bashi ganin yadda duk ta sukurkuce, just daga kissing, ficewa ta yi tana cewa,  Kai da Abdul Ahad babu ruwana .
Sanda ta fito Abdul Ahad din da Sajeedah suna bisa dining suna cin abinci. Sajeedah ta jefo mata kallon ko ke fa? Kulsum ta yi murmushi, ta ja kujerar kusa da Turaki ta zauna, shi ta fara serving sanan ta zuba wa kanta. Shi da Abdul Ahad suke maganganun da suka shafe su. A ranar suka yi sallama da su don gobe za su wuce Abuja su kwana, su bi British Airzuwa U.K.
Sosai Kulsum ta ke kewar Sajeedah, tunda Turaki ya fita tare da su bai dawo ba sai sha dayan dare. Kulsum ta yi wanka ta fito tana shafa mai a kan stool gaban madubin ta, Turaki ya murda kofar dakin ya shigo sanye da fararen Pajamas.
Tunda Kulsum ta kalle shi sau daya ta dukar da kai, ba ta kara iya hada ido da shi ba. Turaki ya kara kunna fitila mai haske a dakin yana ta kallon Kulsum sosai, ganin komai yake tamkar a mafarki. Tamkar idan ya rufe ido kafin ya bude za ta sake kufce masa. Rayuwa ta koya masa darussa sosai. Ya kara fahimtar ka rike abin da ka ke da shi da daraja, ranar da ya kubuce daga hannun ka za ka sha wuya kafin ka same shi, idan ma ka yi sa'a ka same shin ke nan!
Sannan ya fahimci soyayya ta gaskiya ba ta faruwa a lokaci daya& ita wata irin aba ce da ba ruwan ta da lokaci, ko lafiya da dangogin su. Abu ce wadda ke faruwa a duk sanda ta so, ta gudanar da Tunani ta sarrafa gangar jiki (ALHERI-TAKORI). In haka ne, ke nan shi a ra ayinsa bai yarda da abin da bature ya kira love at first sight ba, wannan infatuation ne.
Ya karaso a hankali gaban Kulsum wadda ko shafa man da ta ke yi ta kasa ci gaba sakamakon idanun nan na Turaki masu kama da magnetism da hasken fitila da ya wadaci dakin. Gaban ta ya iso tamkar mai counting steps dinsa (kirga takun sawun sa).
A hankali ya tsugunna a gaban ta ya dora hannun damansa a kan tafin kafar ta, ya jima tsugunne kanshi bisa cinyoyin ta, kafin ya dauke ta gaba daya su fice dakin zuwa turakar sa.
Komai ya faru ne ba yadda ta zata ba, komai ya faru ne cikin kauna da soyayyah. Gently, softly, romantically, emotionally. Dare ne da al amuran da suka faru cikin sa suka shige cikin kundin tarihin rayuwar Ummu Kulsumu. Ta amince da soyayyar mijin ta Turaki, ta yarda shi din ba wanda ta sani a baya ba ne, wani sabon Turaki ne wannan. Loving and romantic. Sannan fassarori da yawa da ta yi masa abin ba haka yake ba, shi dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login