Showing 9001 words to 12000 words out of 33918 words

Chapter 4 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

444

kira ya hada su. Yana ji Maimartaba na bada umarnin a hada dukiyar aure da sadaki na alfarma su je shi da Chiroma su karba wa Turaki auren matar sa ta baya.
Tuni Umma ta fice zuwa dakin ta. Batulu ta fara kira, sannan Yaya Hadiza da Ramla ta ce, su yi kokari dukkan su su zo gobe, amma ba ta gaya musu makasudin kiran nasu ba.
Nan kuma ta hada barorin ta da masu girkin bangaren ta ta soma bada umarnin girke-girken da za a yi gobe, da abubuwan da ta ke so a tanada, Laraba kawai ta gaya wa ko me ke nan, sai ga tsohuwar tana rawa tana juyawa.
A waya Baffa ya kira Daddyn Taufeeq wanda ke cikin Kano tare da Taufeeq din, ya gaya masa hukuncin da ya yanke na maida Kulsumu ga mijinta don ba zai iya kyale ta ta sake kwana a gabansa babu aure ba. Duk da Daddy ya ji ba dadi, don shi ya yi hukuncin ne don in an kwana biyu Taufeeq ya sake nutsuwa a dawo da maganar auren. Amma sai ya kasa fadin kudurin zuciyar tasa kada Baffa ya ga ya yi son kai, ya bi bayan nasa. Ya sa albarka tare da cewa, insha Allahu da su za a daura auren Kulsumu gobe kafin su wuce.
Bai gaya wa Taufeeq ba, don a lokacin ma yana gaban sa yana masa magiya da hawaye, da zai amsa wayar Baffa sai ya kauce daga gaban sa don bai san me wayar karfe goma na dare ta kunsa ba.
Karfe goma sha dayan dare Galadiman Gaya kanin Maimartaba da Chiroma da limamin masallacin fadar Maimartaba Sarkin Gaya suka iso gidan Malam Jibo. Babu wanda za su aika don haka Chiroma ne ya yi sallama da kansa. Baffa da ke yi wa Goggo da Hajiya bayanin hukuncin da ya yanke a lokacin, ya fito don ganin masu sallama. Nan ya ga manyan bakin dake tafe cikin dare daga fadar maimartaba Sarki. Komawa ya yi ya sanar da su Goggo suka koma dakin Goggo ita da Hajiya Nasara, suna ta kakabin al amarin a zukatan su. Hajiya Nasara ba ta yi mamaki can-can ba, don ta san su Baffa har gobe suna son Turaki.
Baffa ya shigo da bakin sa har dakinsa, nan aka yi magana ta gemu-da-gemu. Ya ce, sadakin da suka kawo ya yi yawa, don Kulsumu ba yau za ta fara zuwa gidan su ba, Galadima ya ce ai ba su da hurumin maida ko sisi ga maimartaba. Nan aka sa lokacin daurin aure karfe goma sha daya na safe. Kuma a daren ranar duk wanda ya kamata ya san zancen auren Turaki a masarautar Gaya sai da ya sani. Mata ne kawai ba su da labari, su ma zuwa wayewar gari duk Laraba ta gama fesawa kowa labarin dawowar uwardakin ta UmmuKulsumu. Nan aka fara hidimar girki wanda za a raba wa jama a bayan daurin aure. Daga nan kuma mata za su zarce da biki ne.
Kulsumu na kwance uwardakin Goggo a daren ranar, ba ta san wainar da ake toyawa ba. Haka kawai ta ke fama da guilty conscience? Ta ke tuhumar kanta, anya hukuncin da ta yanke a kan Taufeeq ta yi daidai? Me ya sa ba ta yi hakuri ta aure shi haka ba? Ko don albarkacin iyayensa da  yan uwan sa, ta san son da Taufeeq ke mata idan ta ce ya bar abu komai tsaurin sa za bari, in har za ta yi farin ciki. Yanzu ga shi ta jefa iyayen sa cikin damuwa, ta hada su da dan su, anya hukuncin ta bai yi tsauri ba, kuma bai yi kama da butulci ba?
Da wannan guilty conscience din ta kwana, tana jin kamar ta je ta samu Baffa ta gaya masa ta janye hukuncinta. Amma lokacin karfe biyu ne na dare, Hajiya na falon Goggo tana sallah, ta san shiriya ta ke roka wa Taufeeq a wurin Ubangiji. Ta san halin Hajiya Nasara, duk wata matsala idan ta tunkaro ta, to ta daina barci ke nan har sai ta ga karshen ta da karfin addu a. Ta kara jin nadama ta lullube ta, ta sa a ranta gobe in Allah ya tashe su lafiya the first thing in the morning (abu na farko da zata yi da safe) shi ne gaya wa Baffa, Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, za ta auri dan uwanta Taufeeq cikin kowanne hali, ta taimaka masa ya yi yaki da kowanne irin sabon Allah.
Da safe bayan sun idar da sallar asubahi duk su ukun ba ta tashi a wajen ba sai da ta bude baki ta gaya wa Hajiya da Goggo ta janye hukuncin ta, a ci gaba da shirin daurin aure. Ba su ce mata komai ba sai ido da suka bi ta da shi suna tunanin ko dai ta samu depression ne?
Baffa na shigowa daga masallaci, shi ma ta je ta gaya masa. Murmushi ya yi ya janyo wata jaka ya tura mata gaban ta.
 Dauki wannan, sadakin ki ne. Amma ba da Taufeeq ba, da wanda Allah ya tsaga da rabon sa .
Kulsumu ta bi Baffa da kallo kamar za ta yi kuka.
 Baffa, sadakata ka bayar?
Wani murmushin ya sake yi, ya ce,  Wace irin sadaka bayan ga sadaki irin wanda duk garin nan babu  yar wanda ta taba samun rabin sa? Ni ba sadakar ki na bayar ba, aure ne na na-gani-ina-so. Ba ki kara kwana daya gaba na sai da igiyar aure a kanki, domin kin gama zaman Abuja .
Hankali tashe Kulsumu ta bar gaban Baffa ta koma daki ta soma rusa kuka. Daga Goggo har Hajiya babu wanda ya rarrashe ta. Gari na wayewa suka shiga hidimar da ke gaban su kada jama ar da suka gayyata su fara isowa ba su shirya komai ba.
Karfe goma sha daya na safe, dumbin jama ar garin Gaya da wajenta suka sake shaida daurin auren UMMUKULSUM ABDULHADI  YALLEMAN da YARIMA ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI a kan sadaki lakadan ba ajalan ba.  Yan  Yalleman sai ana gab da daurin aure suka iso. Daga nan ne kowanne bangare (gidan su amarya da gidan su ango) ya zarce da wunin biki. Turaki dai ko ganin sa ba a yi saboda yawan jama a, kai ka ce an yi sati guda ana gayyatar su. Kodayake su su Goggo sun yi gayyatar haka duk wadanda su Hajiya Nasara suka gayyato daga Abuja domin halartar auren dan su, sune suka halarci daurin auren Kulsumu da Turaki a karo na biyu. Cikin mahalarta daurin auren har da TAUFEEQ MUHAMMAD BELLO (tears).
Boye kansa ya yi bayan daurin aure a cikin sassan shi da ke cikin gidan, ya gabatar da alwala ya sallaci walha (dhuha), sannan ya dora da sallar nafila raka a biyu ya yi godiya ga Allah da Ya cika masa buri na karshe a rayuwar sa. Duk wasu burikansa Ubangiji ya cika masa su daya bayan daya, wanda yake gani a matsayin mafi wahala (wato samun Kulsumu), yau ga shi Ubangiji ya cika mishi ba tare da kokari, dabara ko iyawar sa ba.
Lallai ne shi Allah fa a alun lima yuridu ne (wato mai aikata abin da ya so) a kuma lokacin da Ya ga dama.
Wayar sa ya lalubo daga cajin da ya sanyata tun jiya, mutum na farko da ya kira shi ne, Dr. Abdul Ahad Aminu Maikano, ya ce,
"Aboki, kana ina?
Ya ce,  Ina Manchester, amma gobe insha Allah zan koma Reading .
Ya ce,  To kunnen ka nawa?
Murmushi ya yi mai sauti ta cikin wayar, ya san albishir din ba zai wuce a kan Kulsumu ba, the only obstacle of Turaki. To ko dai ya samo ta ne? Ya ce,  Kunne na goma sha biyu, plus na Turaki in an hada da nawa sun zama sha hudu kenan .
Dariya ya yi, ya ce,  To kai komai sai ka sa wasa a ciki? I called to inform you yau na zama angon UmmuKulsum for the very second time, cikin yardar Ubangiji da amincewar sa .
Dr. Abdul Ahad ya ce,  Idan wasa ka ke min, to bana so mu yi magana ta gaskiya .
Turaki ya ce,  Na taba yi maka irin wannan wasan? Well, ba ni da lokacin ka yanzu. Zan so ka zo Gaya, akwai hawan angonci na musamman da zan shirya next week wanda ba a taba irinsa a Gaya ba. It''s a promise da na yi da dadewa cewa duk ranar da zan yi auren soyayyah zan yi hawan angonci. Your Horse is reserved for you (an ajiye maka Dokin ka)."
Zuwa yanzu Abdul Ahad ya yarda Turaki da gaske yake. At last ya samu Kulsumu, kowa zai samu lafiya. Ya ce cikin murmushi,

 Dole ne ma in zo, ko don in ga Kulsum, in ga shin me ta taka haka da ta sukurkuta min aboki shekara da shekarusaura kadan yayi asarar likatancin sa a kanta? .
Murmushi Turaki ya yi, ya kashe wayar sa ba tare da ya ba shi amsa ba. Shi kansa in za'a tsare shi ba zai iya fadar abu guda daya da yake son Kulsumu sabida shi ba, ita din bakidayan ta yake so, the whole her. (Dukkanta).

*** *** ***
Umma ta aiko an gaya wa Goggo gobe lahadi da yamma za su dauki amarya, don haka duk wani shirye-shiryen su daga yau zuwa gobe gare su. Hajiya Nasara ta sa Sakeenah ta hado duka kayan dakin Kulsum da suka tanada ta taho da su Gaya a gobe-goben nan. Ba ta gaya mata ko me ke nan ba, ta dai ce ta yi kokari ta zo tare da kayan, kuma kada ta gaya wa Nasmah komai kada ta dage sai ta biyo ta ta zo tana haihuwa a kan hanya.
Washegarin ranar Sakeenah ta iso da motocin kaya, Baffa ya bude dakin da ya ajiye wadanda Maimartaba ya aiko wa Kulsumu tun ma kafin auren ya juye kan dansa. Aka hada da wadanda su Hajiya Nasara suka yi wa Kulsum aka wuce da su gidan Sarkin Gaya inda za a yi wa Kulsumu kafi. Amma sai Maimartaba ya ce, Turaki ba zai zauna cikin gidan ba wannan karon, sassan ya yi musu kadan kuma ya tsufa, ya mallaka masa sabon gidan sa da ya gama ginawa a bayan gari, don haka can aka wuce da kayan, aka kuma yi wa su Hajiya Nasara da za su yi kafi jagora zuwa can.
Lokacin da su Batulu suka iso, Umma ta gaya musu kome ke nan. Batulu hawaye ta dinga yi, farin ciki ya kai mata ya kawo. Ta ce a lokacin za ta tafi gidan su Kulsumu, Ummah ta ce ba ta yarda ta je ta cikata da dumi ba, ta bari sai gobe su je su dauko ta gabadaya.
Dr. Sakeenah ta ji abin da ya faru, ta yi bakin ciki sosai a kan Taufeeq, ta yi fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi, Ya yi wa Taufeeq sauyin alheri.
Sun je sun yi kafi, suka dawo suna ta yaba tsaruwar gidan, Lami matar Malam Hadi ta rangada wa Kulsumu guda aka ta ce,
 Allah ya sa kannen ki a damshin ki Kulsumu, gida kam na duniya kin yi shi, Allah ya sa na lahira ya fi shi .
Kulsumu wadda tun wayewar garin yau ta ke risgar kuka, damuwar ta shi ne, wannan aure da Baffa ya yi mata mai kama da auren sadaka da mijin da ba ta san ko waye ba. Duk maganganun da mutane ke yi a kan gidan wanda suka je kafi suka dawo ko daya bai burge ta ba. za ta fi so a ce Baffa ya yi hakuri ya kara mata lokaci ta kawo masa wani mijin, tunda ba su karbi nadamar ta a kan Taufeeq ba.
To shi wannan din an san nasa halin? Kada dai ta yi gudun gara ta tadda zago. Kada garin neman gira ta rasa ido. Allah ya sa dai Baffa ba kudi ya gani ba, tunda yana ikirarin sadakin ta duk Gaya ba  yar wanda ta samu kamar sa. Su kuma ga su sun zo suna santin gida. Amma da ta tuna ko wane ne Baffan nata, ta san hakan ba za ta taba faruwa da shi ba.
Ba ta samu kebewa da Babanta Malam Hadi ba sai da ya zo tafiya bayan daurin aure, kasancewar shi ba zai kwana ba, amma su Lami duk suna nan sai sun raka Kulsumu dakin ta.
A zauren farko suka tsaya sabida yadda gidan ke cike da jama a. Ya dubi Kulsumu wadda idon ta ya yi kozai-kozai don kuka, babu wata kwalliya ta amare a tare da ita. Haushin kowa ta ke ji, musamman Baffa. Ko da Aunty Sakeenah ta yi mata magana kan ta canza kayan jikin ta ko hoda ce ta shafa kuka ta fasa mata. Kukan da ya sa dole ta kyale ta, don ita Sakeenah ba ta son kuka a rayuwar ta.
Malam Hadi ya ce,  Kulsumu komai ki ka ga ya faru da bawa, da ma rubutacce ne a lauhul mahfuz, wani ba ya auren matar wani kamar yadda wata ba ta auren mijin wata. Ki sa a ranki duk mijin da Allah ya zaba miki shi ne alherin ki. Na ji an fasa aure da shi wannan yaron dan wajen marikiyar ki sabida wasu matsaloli da suka taso.
To dama ni tun farko na amsa ne sabida karamcin iyayen sa gare ki, amma Kulsumu na fi so ki koma gidan tsohon mijin ki. Hausawa suka ce da sabon gini gwanda yabe, su kam ai sun sanki ciki-da-bai din ki, babu wani abu naki da zai zame musu sabo, ke ma kuma in kin nutsu kin kwantar da hankalin ki sai kin fi jin dadin gidan Sarkin Gaya.
A hankali Kulsumu ke daga kumburarrun idanun ta tana bude su a kan Baban ta. Wai me yake nufi ne da wannan zancen nasa? Ita ko alifun ba ta fahimta ba, ban da sunan gidan SARKIN GAYA.
Har ya yi mata sallama ya sanya mata albarka tare da yi mata addu o I masu yawa ya tafi, Kulsumu ba ta koma daidai daga razanar da ya sanya ta a ciki ba. Maganar gidan Sarkin Gaya da ba ta fahimci musabbabin ta ba. Ga shi har ya wuce ya tafi ba ta nemi karin bayani daga gare shi ba. Harshen ta kamar an daure mata shi, haka ta ja jiki ta koma cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Gadon Goggo ta hau ta kwanta, ta lumshe idanun ta tana sauke ajiyar zuciya. Cikin dare ta kasa barci sai juyi a kan gadon karfen Goggo, ta tabbata ita din yanzu matar aure ce, matar wanda ba ta sani ba, ta yi sallama da Taufeeq daga cikin rayuwarta. Kwata-kwata kwakwalwar Kulsumu ta ki yarda ta karbi zancen gidan Sarkin Gaya da malam Hadi ya yi mata, sabida tsabar ba ta kawo hakan a ranta ba. Ta fi sa wa a ranta ya fada mata ra ayin sa ne kawai na gidan da ya fi so ta yi zaman aure.
Ko mecece kaddarar ta tunda ita ta ki karbar Taufeeq ita ta ja wa kanta, dole ta karbe ta da hannu bibbiyu. Amma ba ta taba lissafo wa da Turaki cikin kaddarorin da ka iya samunta ba. Duk da haduwar su a Lagos ya bankado shafuka da yawa daga karkashin zuciyar ta da ta dade da binnewa na ciwon abin da ya yi mata.
Wai "matarsa da ya rasa bai sake ta ba". Ta tuna statement din sa. Ita ta san wannan ba Turaki ba ne, Turakin gaske bai taba son ta ba! Turakin da ta sani daban yake da wanda ta gani, tunda ta aure shi har Allah ya raba su ba ta taba ganin murmushi a fatar bakin sa ba. Amma haduwar su a Lagos Turaki har rungumar ta ya yi, ya sumbace ta passionately, duk da ce masa da ta yi tana da aure, sannan ta ga murmushin sa ya kai sau nawa, wanda ya kusa tafiya da sauran numfashin ta.
Tana wannan tunanin har aka yi kiran assalatu a kan kunnen ta. Har aka tada sallah ta kasa motsawa, sai da Goggo ta bubbuge ta. Ko da ta yi sallah kasa komawa barci ta yi, idon ta ya soye, zuciyar ta ma ta soye kamar soyayyar gyada marau-marau, da tunanin yau ne rana ta biyu da za ta sake barin gaban iyayen ta zuwa gidan aure. Akwai fargaba mai yawa a tattare da ita, wadda ta cika ruhin ta sakamakon tunanin shi kuma wannan auren me za ta je ta tarar a cikin sa?
Idan lalurarta ta dawo fa? Tunda har gobe likita bai ba ta tabbacin warkewa gabadaya ba? Babban abin da ya sa ta ke gudun aure ke nan, ba ta so ta kuma yinsa a sake sako ta. Sannan ba ta son terere da bankada a kan lalurar da Allah ya dora mata. Duk da jikin ta yana ba ta ta gama warkewa, Dr. Sakeenah ma na da tabbacin hakan.
A haka barci mai nauyi ya dauke ta, a karshe ta bingire a kan sallayar tana yin sa bilhakki, babu wanda ya tashe ta don sun lura kwanan ido biyu ta yi.
Washegari gidan aka tashi da hidimar tafiya kai amarya wanda za'ayi da yamma, Dr. sakeenah ta ja hannunta suka shige dakin Baffa kasancewar ba ya nan ya fita. Wani fulas ta jawo ta aje mata a gaban ta ta ce, ta cinye kazar ciki tas! Ta ba ta kasusuwan, sannan ta ba ta wasu kwayoyin magani ta ce in ta gama ta hadiye su. Ta dube ta cikin ido, ta ce,
 Na san Kulsumu ba za ki ki bin umarni na ba, na san kina girmama ni! .
Bayan fitar Sakeenah ta dade kafin ta fara ci. Kasancewar da yunwa ta kwana, sai naman ya yi mata dadi ta bude ciki ta ci sosai, ta hada mata kasusuwan kamar yadda ta umarce ta. Ta kuma hadiye magungunan da ba ta san na mene ne ba.
Karfe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login