Showing 27001 words to 30000 words out of 33918 words

Chapter 10 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

439

sannan suka fito don tafiya (Brains&Hammers) wato gidan Hajiya Nasara.
Hajiya Nasara kadai suka samu a gidan, karshen farin ciki ta yi shi da ganin su. Ta sa Serah ta shirya musu abinci. Turaki duk ya kasa sakewa saboda surukuta, amma haka ta matsa musu kan sai sun ci abinci. A dakin ta da Kulsum ta shiga domin su gaisa sosai Hajiya Nasara ta kasa boye farin cikin ta, ta ce,
 Na ji dadin yanayin da na ganki ciki Kulsum, na kuma tabbata Turaki na kula da ke yadda ya kamata. Madallah .
Nan Kulsum ta ke gaya mata sallama ta zo ta yi mata za su wuce U.K can inda Turaki ya ke zaune, ba ta san lokacin da za su dawo ba. Farin cikin Hajiya Nasara ya karu, ta ce,  Ai kuwa zama bai gan ni ba, bari in tattara miki kayan girki, don a can ba za ki samu irin su ba .
A waya Hajiya Nasara ta kira Dr. Sakeenah da Nasmah duk ta gaya musu tafiyar Kulsum. Nasma ta shiga EDD dinta, Taufeeq na Lagos, kayan amfani masu yawa Hajiya Nasara ta hada mata. Ko da wasa Kulsumu ba ta yi zancen fitsarin ta ba, ba ta so ta kara daga wa kowa hankali, wahalar da suka sha a baya Allah ne kadai zai biya su da mafificin alherin sa.
Sai karfe goma suka bar gidan, domin hira ce sosai ta shiga tsakanin Turaki da Hajiya Nasara, kasancewar su duka mazauna Birnin Sarauniya.
Hajiya ta ce, ta taba zuwa Reading Berkshire, kuma insha Allah ba da jimawa ba in sun shigo London za su zo har Reading su gan su ita da Daddy.
Ko da suka koma hotel gajiya ba ta bar su sun tsinana komai ba. Amma Kulsum ta ki yarda ta kwanta don kada ta yi fitsari. Ta hau kujera kwalli daya da ke dakin ta kishingida tana faman daddanna wayar ta. Turaki ya kwace wayar, ya kuma kashe fitila mai haske ya ce,
 Malama ki kwanta please, gobe asubanci za mu yi, is good ki samu barci ko yaya ne .
Ta bi umarnin sa ne kawai don ta san ko me za ta ce ba zai kyale ta ba. Suka kwanta Kulsum kalmashe cikin jikin sa. Amma ko na sekon daya ba ta bari barci ya dauke ta ba. Ta lafe a jikin Turaki tana sauraron yadda yake sauke numfashi a hankali, ita ina ta ga wannan kwanciyar hankalin? Ta lura Turaki na jin dadin barcin sa, don haka ba ta nuna wata alama da za ta nuna idanunta biyu ba, har lokacin sallar asubahi ya yi.
Karfe shidda wanda zai kai su filin jirgi ya kuma tafi da motar Turaki ya zo, wani abokin sa ne Dr. Habib mazaunin Abuja. Sun bata lokaci wajen screening da zaman jiran jirgi ya daidaita. Karfe goma sha daya na safe jirgin su ya tashi zuwa United Kingdom.

*** *** ***
A cikin jirgi ne Kulsum ta samu ta yi barci sosai a jikin Turaki. Tafiyar awanni takwas a cikin jirgin British Air ta sauke su a birnin London. Inda daga nan suka dauki taxi ta kai su tashar jirgin kasa, suka bi train zuwa garin Reading, Berkshire.
Nisan da ke tsakanin babban birni (London) da garin Reading (37 miles) ne, wato tafiyar mintuna arba in da biyu a cikin jirgin kasa. Reading babban gari ne mai tsohon tarihi a kan kasuwanci a yankin Berkshire (South-East England).
Gidan Turaki na cikin jerin gidajen malaman jami ar Reading. Mai taxi din da ya dauko su har kofar gidan ya sauke su. Gajiyar da ke tare da Kulsum ta sa ba ta gane komai da ke cikin gidan ba sai washegari. Gida ne a cikin Estate duka gidajen iri daya ne, masu dakuna ciki-biyu da falo, kowanne daki da toilet manne a cikin sa, sai kicin wanda kofar sa ke cikin falon, sai garden daga wajen kitchen din, mai shimfide da korran ciyayi daga sama har kasa sun yi wa gidan rumfa ruf, gidan karami ne sosai kamar sauran gidajen Estate din, sai dai ya ishi dan Adam duk wasu bukatu na rayuwar sa.
Kwanan su uku ba su je ko ina ba suna ta fama da fitsarin Kulsumu. Fitsarin da kamar jira yake su sauka a Reading ya kara ta azzara. Hutawar da suka yi niyya duk ba su same ta ba, soyayya an jingine ta a gefe saboda Kulsumun kwata-kwata ba ta cikin hayyacin ta saboda damuwa da tashin hankali.
Ita babbar damuwarta shi ne Turaki zai tsane ta. Yayin da shi kuma damuwar sa ita ce damuwar da ta ke jefa kanta a ciki, wadda yake tsananin tsoron kada ta taba brain dinta, ta jawo wata matsala wadda ta fi ta fitsarin kwance.
Ya kira Dr. Ibrahim Takai kan appointment din su na ganin sa, ya ce za su hadu a asibitin nasu Turaki, wato Royal Berkshire Hospital ya zo ziyarar aiki ne daga Illinoise teaching hospital na watanni uku a asibitin koyarwa na garin Reading.

Kulsum ta yi tsai da idanun ta tana kallon Dr. I.M Takai, ta dauka za ta ga mutum wanda ya manyan ta kamar likitan ta na Lagos, sai ta ga sardidin mijin na Rayhanah Baban Asma u matashi tamkar nata mijin. Sun dade suna magana shi da Turaki, da turancin su mai accent wanda ba duka ta ke fahimta ba. Ya yi mata tambayoyi masu yawa tana ba shi amsa. Ta kuma gaya masa sunayen magungunan da ta ke sha a baya, da dukkan treatment din da ta karba daga hannun likitan ta na Lagos.
Dr. Ibrahim ya dube ta sosai, sannan ya ce,  Ina tsammanin kina da karamar mafitsara ko blocked urethra (mafitsara tosasshiya), zan yi miki test har guda hudu; na farkourinalysis, inda za mu dauki sample na fitsarinki mu duba infection acikin sa ko sauran urinary tract infections. Test na biyu da za mu yi shi ne urine culture, inda za mu tura sample na fitsarin ki zuwa lab don duba ko akwai bacteria ko yeast a cikin fitsarin ki. Sai test na uku shi ne uroflowmetry, inda za ki yi fitsari a cikin special funnel da za mu ba ki, mu auna yawan fitsarin da ki ke yi and how quickly it flows out. Sai test na karshepost-void residual urine measurement; wannan test din zai nuna yawan fitsarin da yake ragewa a mafitsarar ki ba tare da ya fito ba duk lokacin da ki ka yi fitsari. Idan muka yi duk wadannan gwaje-gwaje, za mu gane what are the possible causes na nocturnal enuresis din ki. Za mu gane blocked urethra ne ko pelvic organ prolapse, ko kuma matsalar daga structure din mafitsarar ki ta ke (wanda na fi tsammani), ko enlarge prostate ne ko urinarytract stones ko infection na mafitsara.
Ki ci gaba da non-pharmacological treatment irin na baya, sannan inaso ki gaya min abubuwa guda hudu.
Karfe nawa ki ke bed -wetting?
Yawan fitsarin da ki ke yi (kadan ne ko mai yawa)?
Yawan abin da ki ke sha kafin kwanciya barci?
Sauran alamomin da ke nuna za ki yi fitsari?
Kulsum ta fada masa duk abin da ya tambaye ta iya sanin ta. Doctor Takai ya ce,
 To yanzu za ki shiga toilet ki ba mu fitsarin ki, mu auna mu gani, sannan akai lab, gobe sai ku dawo mu ga me result ya nuna .

Washegari karfe goma na safe suna gaban Dr. Takai, nan ya gaya musu result din gwaje-gwajensu ya nuna Kulsum na da karamar mafitsara. Za ta sha magunguna masu karfi ba irin na baya ba na tsawon sati biyu, derifenacin (enablex), oxybutynin (ditropan), tolterodine (detrol) da kuma trospium chloride. Idan ba ta daina fitsari tsayin wata guda ba za su dawo. Dole sai an yi surgery. Sunan surgery din da za'a yi  Bladder augmentation .
Dr. Takai ya ce,  It s an operation that makes your bladder larger, which raises the amount of urine it can hold (aiki ne da ake yi wanda zai kara girman mafitsarar ki, ya kara yawan fitsarin da za ta iya rikewa) .
Da wannan suka baro gaban likita Takai bayan Turaki ya sayo duka magungunan da aka rubuta musu.
Haka kawai Kulsum ke jin wata irin gamsuwa wannan karon da treatment din gawurtaccen nephrologist Ibrahim Takai, domin kwata-kwata bai yi kusa da wanda ta samu a Lagos ba. Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Magungunan sun fi na baya karfi nesa ba kusa ba. Sai da ta yi sati daya ba ta yi fitsari ba ko sau daya da ta fara shan su. Murna wurin Kulsum abin ba'a cewa komai, amma Turaki kallon ta kawai yake. As a medical doctor jikin sa yana ba shi karshen ta dole sai an yi surgery din nan.
Ya koma aikin sa tuni, don haka ita kadai ta ke wuni a gidan, Sajeedah da Abdul Ahad sun bar Reading sun koma Manchester inda aka yi wa Abdul Ahad transfer. Turaki ya mata alkawarin in hankalin su ya kwanta sun gama da asibiti za su je musu har Manchester wajen su.
Ilai kuwa bayan kwana goma sai ga shi ta sake yin fitsari, wanda alama ce da ke nuna cewa, karshen ta surgery zai tabbata. Turaki bai gaza ba wajen karfafa mata gwiwa kan cewa yana tare da ita cikin kowanne hali, yana son ta a duk yadda ta ke.
Sati hudu suka cika suka koma gaban likita, ko a ranar ma sai da ta yi fitsari, don haka Dr. Ibrahim Mansur Takai ya sa musu ranar surgery kwanaki biyar masu zuwa.

*****
Ana i gobe surgery din Kulsumu kasa barci ta yi, gani ta ke in ta shiga dakin tiyata ba za ta fito da sauran numfashi ba. Turakin ta zai zama mallakin wata a bayan ran ta. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta ji babu dadi.
Ko da Turaki ya dawo aiki a ranar ya fahimci ta ci kuka ta gode Allah. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen wanke damuwar ta da nau ikan soyayyar sa masu tsayawa a zuci. Da ya fita sai ga shi ya dawo da sinkin adult diaper (pampers din manya) don su huta da wankin zanin gado, duk da yanzu ba ya taba katifar su sabida water mattress ce. Dr. Takai ne ya ba shi wannan shawarar ya ce, hakan zai fi musu sauki, after intercourse din su ta sanya diaper idan non-pharmacological treatment ya ki aiki a jikin ta.
Kulsum ba ta taba jin madaukakiyar kunya a duniya irin ta yau ba. Wane embarrassment ne ya wuce miji ya sanya maka diaper? Ta jinjina wa Turaki a zuciyar ta, ta amince samun kamar sa cikin maza dubu sai an tona. She is indeed among the luckiest women on earth (tana daga cikin mata masu sa'a a duniya), amma shi din ko a jikin sa, gaya mata ma yake,
 Ba shi ke nan mun huta da wankin bedsheets ba?
Ita dai kunya ba ta barta ta ce komai ba. Da idanun sa yake lalubo idon ta wanda ya cika taf da hawayen tausayin Turaki. Ta fi tausayin shi akan yadda ta ke tausayawa kanta. Ita ke fitsari, amma shi ke cin wahalar sa. Da suka hada ido ya daga mata gira, a hankali ta ce,
 Na gode Prince .
Sai ta fashe da kukan tausayin kanta. Turaki ya janyo ta barin jikin sa yana fadin.
 In dai diaper ce ta sa min mata kuka, sai a bar ta, babu dole .
Kulsum ta shafe hawayen ta, a hankali ta ce, "Ba kukan diaper nake ba, kuka nake don tausayin ka, ka auri wahala... Ka auri kazanta. Yet ba ka taba nuna min gazawar ka ba. Ba ka taba nuna kyama a gare ni ba. Don Allah Prince ka kara aure... Wallahi na amince, in ba haka ba sai alhakinka ya hana ni warkewa".
Murmushi Turaki ya yi, ya ce, "Well, mu bari after surgery in ba ki warke din ba sai ki zabo min mata na aura. Amma ni ba ni da idon kallon mata. Mai fitsarin kwancen kawai ido na yake iya hangowa".
Za ta iya cewa ba ta taba jin kalmar da ta yi mata dadi a rayuwar ta irin wannan ba. Ko da kuwa Turaki ya fada ne don ya faranta mata kadai ba don haka abin yake a zuciyar sa ba.
*****

Washegari aka shiga da Kulsum dakin tiyata. Bayan sun yi wata irin sallama da mijin ta Turaki 'very emotional'. Ya sumbace ta a goshi da hanci. Ya ce, "Insha Allah lafiya za ki tashi Kulsum, kuma da yardar Allah wannan shi ne karshen wahalar ki".

*** *** ***
A rayuwar Dr. Ibrahim Takai, bai taba yin 'surgery' ko 'kidney transplant' an samu kuskure ba, to haka ma a wannan karon yana kyautata zaton samun nasara a aikin da ya yi wa Ummu Kulsum. Amma ba za a gane hakan ba sai nan da wata daya. Kulsum za ta ci gaba da zama a gadon asibiti.
A wannan lokaci jinyar duk wata kulawa da soyayyah Kulsum ta same su daga mijin ta Turaki. 'The one in million husband', wanda ta ke fatan har a lahira Allah ya tashe su tare matsayin abokan rayuwar juna.
Bayan 'surgery' da jinyar wata guda, sun ci gaba da zuwa 'check up' a asibitin 'Royal Berkshire' hannun likitan da Dr. Ibrahim Takai ya yi 'referring' din su, wato Dr. Kennedy baturen Worcaster, shi din 'kidney and bladder specialist' ne da ake ji da shi a asibitin nasu. Yayin da Ibrahim Takai ya koma Illinoise wajen Rayhanar sa,bayan ya gama aikin da ya kawo shi Reading.
A duk sanda suka zo 'check up' Dr. Kennedy na fada musu aiki ya yi kyau. Akwai ci gaba sosai, da taimakon Ubangiji wannan karon Kulsum ta rabu da lalurar 'Nocturnal Enuresis'. Ranar 'check up' din su na karshe likitan ya yi murmushi ya dube su.
"Congratulations Mr. and Mrs. Abubakar Turaki Abdullahi, your wife is finally saved from bed-wetting". (Matar ka ta kubuta daga lalurar fitsarin kwance).
Ya kara murmusawa ya ce yana bai wa Dr. Abubakar shawarar ya dauki hutu domin ya murmure daga jinyar nan da ya sha, su je garin Chelsea su huta.
Dariya Turaki ya yi ya dubi Kulsum, wadda ta sadda kai kasa, hawayen farin ciki na zuba daga idanun ta. A haka Turaki ya kama hannunta suka bar gaban likita bayan ya yi masa godiya sosai.

*** *** ***
"Shi ke nan yanzu kuma sai mu fara shirin zuwan amarya tunda uwargida ta warke?" Turaki ya fada a lokacin da ya zura mukulli yana bude kofar 'apartment' dinsu.
Kulsum ta yi gumm! Kamar ba ta ji shi ba.
Ya sake maimaita abin da ya fada, ta dauke kai ta shige dakin ta. Wanka ta yi, ta yi kwalliya irin wadda tun zuwansu U.K ba ta taba yi ba saboda rashin kwanciyar hankali. Ta yi alkawarin ingantawa Turaki daren yau da dukkan iyawar ta, domin nuna masa godiyar ta ga dumbin lkhairin sa da soyayyarsa gare ta.
Wata irin doguwar riga ta saka mai bin jiki da aka yi da yadin 'velvet', ta bi fatar jikin ta ta kwanta lambam. An tsaga ta tun daga idon sawu har zuwa gwiwa ta yadda santala-santalan kafafunta suka fito 'freely' in tana tafiya. Ta feshe jikinta da turaren nan na mata mai dadin kamshi COOL WATER (Davidoff). Gashin kanta da ba wani yawa ne da shi ba sai salki da cika irin na fulanin Gaya ta raba biyu ta tufke shi gefe-da-gefe. Ba ta taba shafa 'lip-stick' ba tun auren ta da Turaki sai yau. Ta shafa shi kalar 'light pink' samfurin avon. Ta taje gassun idon ta da girar idon ta da 'mascara' nan da nan fuskar ta ta zama 'cute' ta yi kyan da ba ta taba yi ba.
A hankali Kulsum ta ke taku kamar a filin fashion-parade tana ta faman shige da fice a gaban Turaki, wanda ya baza takardu a falo yana ta aiki cikin 'macbook' din sa.
A hankali ya cira kai ya dube ta za ta wuce rike da robar 'ice-cream' a hannun ta. Ya dan kara girman idanun sa yana kallonta sosai. Bai san sanda ya ce,
"...Come here baby...".
Ta rangwadar da kai, "Ba aiki ka ke ba Prince?"
Ya ture 'macbook' din gefe, ya ce,
"Na ce ki zo koh?"
Ta tako a hankali tana shan 'ice-cream' din ta debo kadan ta nufo bakin sa, yayin da shi ba ta wannan yake ba, kokari yake don ganin ya zuge zib din rigarta gabadaya, yana fadin.
"A duniya akwai mai hakuri iri na? Quite three months ba tare da mata ta ba...".
Kulsum ta sakar masa komai, tare da inganta masa daren yadda ya kamata. Ita kanta wani abun bata san ina ta koyo shi ba. Ta dai sa wa ran ta ne za ta yi komai don ta faranta wa Turaki. Rayuwar ta kacokam fansa ce ga farin cikin sa.
Daren ya kasance musu tamkar a ranar suka taba kusantar juna, ya shige cikin darare masu dumbin tarihi da suke adanawa a kundin rayuwar su.
Washegari suka shirya suka tafi Chelsea, kwanan su uku a 'hotel' din 'The Chelsea Harbour Hotel' suna gwangwaje soyayyah zallah, ko wayoyin su kashewa suka yi. Sai lahadi da daddare suka bi 'train' suka koma Reading.

Rayuwar auren Kulsum da Turaki kenan, rayuwa ce wadda aka gina bisa soyayyah, kauna ta fisabilillahi da yarda zallah, wadda biro ya yi kadan ya bayyanata. Sun gina rayuwar auren su ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login