Showing 12001 words to 15000 words out of 33918 words

Chapter 5 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

446

biyar na yamma  yan daukar amarya suka zo, Dr. Sakeenah ta zabo mata wani sabon lace din ta don Kulsumu ba ta zo da kaya ba, sannan ba wasu kayan aure da aka kawo mata, Baffa ya sa an maida sauran ya ce, sadaki kawai zai karba kamar wancan karon. Wadanda suka zo daukan amaryar dattijai ne su uku, cikin wata kosasshiyar mota ta Maimartaba. Daya kanwarsa ce Goggo Hanna, daya yayar Umma ce da ta zo daga Gombe, dayar kuwa matar Galadiman Gaya ce Hajiya Rabi.
A karo na biyu yau ma sai da Lami ta goya Kulsumu sannan suka iya tafiya da ita. Ko nasiha Goggo ba ta samu ta yi mata ba sabida tsananin tausayin da Kulsumun ta ba ta, ga ta cikin matsanancin kuka kamar na fitar rai. Abubuwa da yawa ne suka damu Kulsumu, zuwa yanzu ba ta damu da sai ta san ko wane ne mijin da iyayen ta suka zaba mata ba, domin ta sa a ranta wannan auren za ta je bautar Allah ne kawai albarkacin ba za ta iya tozarta Baffa ba. Ba ruwan ta da ko waye mijin. Tausayin Nasara da  ya yanta shi ne babban abin da ya fi damun ta.
Ta yi nadamar kin Taufeeq da ta yi, domin an ce ko a lahira wani kan ci albarkacin wani, amma ba ta duba hakan ba ta yi abin da zuciyar ta ta fi kwanciya da shi, ga shi sakamakon hakan ya jawo mata auren wanda ba ta sani ba, ba ta san shi kuma mene ne nashi nakasun ba.
Kugin da motar ta yi na karshe a kofar gidan Dr. Turaki ne, kyakkyawan gidan da duk garin Gaya babu mai kyau da tsarin sa. Asali Maimartaba ya gina gidan ne don hutawar sa ba da sunan Turaki ba, amma da ya ji kowa Turaki zai aura, ya tabbatar Turaki da gaske yake ya karbi zabin da suka yi masa da hannu bibbiyu, kuma ya yi damarar zaman aure ne yanzu da Kulsum, sannan kaunar sa ga yarinya UmmuKulsum wadda ba ya wa Turaki sha awar kowacce mace sai ita, sabida sun zauna da ita, sun san halayen ta. Sannan sun amince da dattakon iyayen ta, da soyayyar da ta ke yi wa Turaki. Da wannan zazzafan darasin da iyayenta suka koyar da shi, su suka hadu suka faranta ransa har ya yi wa Turaki kyautar wannan dankareren gida.
Abin da ya janyo kishi karara daga sauran matan sa, amma ba su da ta cewa tunda ba su da Da namijin da zai kara da Turaki, duk  ya yan su mata ne a gidan aure.
Su Batulu ai tun safe ana gidan amarya, da ita aka yi jere/kafi da komai. Ba ta damu da ta ga Kulsumu ba tana cikin sabga sosai. Yaya Hadiza ce ta taro su lokacin da suka iso, ta yi musu jagora zuwa dakin Kulsumun, wadda ke rufe ruf cikin yalwataccen mayafin da Dr. Sakeenah ta lullube ta da shi. Hajiya Nasara ce rike da ita, a kofar dakin ta gaya mata ta shiga da kafar dama, sannan da addu ar da za ta karanta. Batulu ba ta gidan, Umma ta kira ta don ta je su hada kayan sallamar masu kafi da kawo amarya. Daga Yaya Hadiza sai Aunty Ramla da sauran sisters din Turaki da suke uba daya.
Ko da wasa Kulsumu ba ta bude lullubin ta ba wai don ta ga inda aka kawo ta. Kukanta ta ke bilhakki duk ta jika mayafin ta da hawaye. Lokacin da ta ji su Hajiya Nasara na haramar tafiya sai ta rirrike ta, cikin kuka ta ce.

 Mum ki yafe mini, kin yi min komai a rayuwa, amma ni na ki Yaya Taufeeq a kan ajizancin da babu wanda ya wuce shi. Mum daga baya na so in gyara kuskurena baffa bai ba ni dama ba, wallahi Mum da wannan damuwar zan rayu har karshen rayuwa ta&  . Ta fada jikin ta tana kuka mai nuna nadamarta.
Hajiya Nasara ta riko ta sosai a jikin ta, ta ce,  Kulsum kada in kara jin wannan maganar a bakin ki, ke  yata ce kamar yadda Taufeeq yake dana. Ba Taufeeq ne ya hada mu ba zumuncin Allah ne wanda Ubangiji ya yi mana umarni dole mu yi shi. Da kin auri da na da ba ki aure shi ba, matsayin ki na  ya a gare ni ba zai taba canzawa ba. Ba ki da wadda ta fi ni ke da Goggo, kamar yadda ba ni wadanda suka fi ku. Ki sa a ranki Allah ne bai kaddara aure tsakaninki da Yayanki Taufeeq ba, ki taya ni addu a Allah ya yaye masa halin da ya jefa kansa ya samu mata nutsattsiya kamar ki ya aura .
Kulsum ta kara rungume Hajiya Nasara tana sakin wani sabon kukan, ta ce,
 Na gode, na gode Mum .
Ta ce,  Ba kin gode ba, be happy with your marriage, ki yi wa mijin ki biyayyah, shi din mai son ki ne. Ina da tabbacin wannan karon sai kin fi kowa farin ciki da zaman aure. Daina kukan nan in mun tafi ki dauro alwalla ki yi nafila raka a hudu ki roki Ubangiji Ya dorar da farin ciki a rayuwar auren ki .
Tana ji tana gani duk suka shige motoci suka tafi babu wanda ya rage a gidan. Hatta masu aiki Umma ta ce sai bayan kwana bakwai za a kai mata.
Ta yi kukanta ma ishi, a karshe ta yanke bin shawarar Hajiya Nasara, wato ta yi sallahr nafila. Mikewa ta yi ta warware mayafin da ke jikinta ta ajiye, idanun ta suka hango mata kyakkyawan dakin nata, wanda ya ji rantsattsun furnitures tafiyayyu tun daga China. Ta san wannan aikin Hajiya Nasara ne, ta yi mata tanadin rayuwa da danta, amma a karshe gidan wani suka shigo. Ta girgiza kai a hankali, ta doshi kofar da ta tabbatar toilet ne.
Tana murda kofar toilet don fitowa, Turaki na turo kofar dakin don shigowa. Sanye yake da wani irin tattausan yadin filtex fari sol, dinkin tazarce. Kansa babu hula, sumar nan baka wuluk da ya tara a U.K ta kwanta luf a kansa, sai sheki ta ke yi, hade da lallausar sajen fuskar sa wanda a lokacin samartakar sa bashi da shi.
A hankali ta daga idanu ta dube shi. It was a sudden shock irin wanda zai iya haifar da bugun zuciya a l???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?okaci guda. Fuskar ta kuma ba ta boye halin shock na ba-zata da ta shiga ba, sai ta tsaya standstill rike da hannun kofa. Ta rasa mafarki ta ke yi ko idonta biyu? Ya fi kama da mafarki, wanda kusan kullum ba ta rabo da yin irin sa,. Seeing Turaki a matsayin mijin ta!!!
Wani tattausan murmushi ya yi, wanda ya nuna fahimtar sa ga halin firgicin da ta samu kan ta, ya kuma gane ba ta san kan shi Baffa ya maida auren ba. Wannan abu ya kara yi masa dadi ba kadan ba. Takowa ya yi a hankali zuwa gaban ta. Ya mika hannu da nufin ya kamo hannunta. Da wani mugun zafin nama ta ja da baya, sannan ta daddage ta fasa wani firgitaccen kuka tare da durkushewa a kasa tana ta gunza shi kamar za ta fasa dakin.
Wannan abu ya matukar bai wa Turaki dariya, waje ya samu gefen gadon ta ya zauna, ya zuba mata ido, daga baya sai ya kishingide ya dauko wayar shi ya shiga danne-danne, ba da sanin ta ba vedio yake yi mata.
Cikin gunjin kuka ta ke fadin,
 Na shiga uku na lalace ni Kulsum, abin da Baffa ya yi min ke nan???
Wannan karon dariyar Turaki ta kasa boyuwa. Ya ce,  Ummukulsumun Turaki, this is the best decision ever, ki gode wa Baffa saboda ya taimake ki. Ya dawo da ke inda kike so ake son ki. Ina amfanin badi ba rai? Ina amfanin ki je gidan Taufeeq alhalin kina da mijin ki a gefe? To ki je ki kai masa me? Bayan Turaki ya kwashe komai tun Kulsum na kwailar ta? Ai da muguwar rawa gwanda kin tashi . Ya karasa da wani mischievous smile (murmushin keta) a siririyar fatar bakin sa.
Kulsum ta yi sak! Daga kukan fitar ran da ta ke yi tana nazarin kalaman sa, kafin wani dan lokaci ta gane me yake nufi. Wata zuciyar na cewa ta rufe shi da duka ko ta ji dadi, wata na cewa ta fice ta bar masa dakin. Ta je ta yi jinyar abin da ya same ta ita kadai.
Kamar Turaki ya san tunanin da ta ke yi, ya mike kamar zai fita, kawai sai ya murza wa dakin key, ya tako ya iso har gaban ta ya durkusa. For the first time a rayuwar sa da ya samu kansa durkushe gaban mace, sannan da niyyar lallashin ta. Kulsumu ta yi wuf za ta mike, ya riko ta da kyakkyawan rikon da ba za ta iya kubucewa ba. Sannan a hankali ya mike shi ma suka fuskanci juna, kirjin ta na heaving faster and faster tamkar mai ciwon asthma, yayin da zuciyar Turaki ke wani irin circulating tana haifar masa da abubuwan da bai taba ji a rayuwar sa ba akan diya mace. Kulsum ba ta gama tantance halin da ta ke ciki ba ta ji Turaki ya rungume ta da wata irin kyakkyawar runguma (tight hug) yadda jikin sa ya ratsa ko'ina na jikin ta. Bugun zuciyar ta ya karu, kamar yadda nasa ke yi, suka koma bugawa a tare, kamar zuciyar su za ta ballo allon kirazan su ta fito.
Kokari yake ya lalubo bakin ta, amma Kulsum ta ki ba shi damar hakan. Sai faman cusa kai yake a masangalin wuyan ta yana sunsunar ta yana kissing iya abinda zai iya samu. Zamewa ta yi ta kasan hannayen sa ta koma toilet da gudu ta banko kofa ta murza key. Ta koma ta jingina da kofar bandakin tana sauke ajiyar zuciya. Gara ta kwana a toilet da ta kwana tana ganin Turaki a gaban ta, kuma wai a matsayin mijin ta na sunna a karo na biyu.
Tana jin shi yana mata magana a daidai kofar bandakin,  It s okey, ni ba bakon zafi ba ne. Na bar miki dakin ki, ki kwana cikin aminci UmmuKulsumun Turaki. And dreamt of our twin babies masu zuwa nan da watanni tara .
Ya yi murmushin da har ta ji tashin sautin sa, ya sake cewa  Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwar sa. Mutumin da ya yi hakurin shekara takwas ai ba zai gaza yin na dare daya ba .
Ita dai ba ta ce komai ba. Ya sake cewa,
 Na barki lafiya Princess .
Tana jin fitar sa da rufo kofar sa, amma ba ta fito ba sai da ta tabbatar ya fita din. Tana fitowa ta murza wa dakin makulli. Kasa tada sallar ta yi, sai ta zauna a bakin gado tana tunanin rayuwar ta mai abun mamaki. Turaki as her husband for the second time, tare da wasu mabambanta halaye da suka barranta da nasa.
Ba ta da zuciyar da za ta kara yarda da Turaki, kamar yadda ba ta taba shirya wa ranta sake rayuwa da shi ba. Zai sha mamaki kuwa, idan har yana zaton wannan karon ma zai ci galaba a kan ta, kamar yadda ya ci a baya, idan zaton sa karamar yarinya Kulsumun da, ita ce a cikin gidan sa yanzu.
Sai yanzu ta gane maganganun da Baban ta Malam Hadi ke yi a kan gidan Sarkin Gaya, ashe-ashe nufin sa can za ta sake komawa. To me ya sa Baffa ya boye mata? Ba shakka don ya san ba za ta amince ba ne.
Hawaye suka zubo mata, how could she forget his wickedness (ta ya ya za ta manta muguntar sa?) Shi ne yanzu ya zo yana  yar murya don ta tashi daga Kulsumu  yar kauye, mai fitsarin kwance? Ta koma yadda yake son ganin mace? Ko ta rasa miji me za ta dawo ta dauka a gidan Turaki? Gara masa ya maida ita inda ya dauko ta ko ya shirya zama cikin bakin ciki da tashin hankali, ba za ta taba zaman lafiya da shi ba har karshen rayuwar ta.
A wannan daren, duk iya sata irin na barci da kyar ya iya sace UmmuKulsumu, tana kitsawa tana warwarewa, amma ta kasa gano hanyar da za ta bi ta tserar da kanta daga auren Turaki. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Ta yi kuka, ta yi kuka har ta gode Allah. A rayuwa Baffa bai taba bakanta mata irin wannan lokacin ba, shin ko sun manta wane ne Turaki ne?
Turakin da ya bula musu kasa a ido, ta koma sunan karamar Bazawara a dalilin sa, har ta yi zaman gidan sa ta kare ba ta taba ganin murmushin sa ba, kalma ta arziki bata taba hada su ba, bai taba daga ido ya kalle ta ba, sabida a baya bai dauke ta mutum ba, yanzu ne ta ke mutum, sabida ba ta fitsarin kwance, kuma ta yi ilmi ta goge?
Zai sha mamaki kuwa, don ba don shi ta dage ta canza rayuwar ta ba. Ta canza ne don amfanin kan ta. Tabbas za ta aro rigar rashin mutunci wanda ba halin ta ba ne ta saka a zama da Turaki, sai ya maida ita inda ya dauko ta yana so ko ba ya so. Da wannan tunanin barci ya samu nasarar sace ta goshin asubahi.
Turaki a nasa dakin bayan ya rage kayan jikin sa zuwa na barci, komawa ya yi falo ya yi waya da Abdul Ahad, yana bukatar raba farin cikin da yake ciki tare da aminin nasa.
Ya ce,  Aboki, ga ni ga Kulsum a cikin gida na, matsayin matata for the second time, wace irin godiya ya kamata na yi wa Ubangiji?
Abdul Ahad ya ce,  ka yi sadaka ga mabukata, ka ziyarci marassa lafiya a asibiti, ka yi musu ihsani. Sannan ka yi damarar rike matar ka tsakani da Allah, don ba dabararmu ce ta sa Ubangiji ya dube mu Ya yaye mana damuwar mu ba. Rahamarsa ce da Gafarar sa gare mu .
Turaki ya gamsu da maganganun Abdul Ahad, ya yi niyyar bin duk abin da ya ce da zuciya daya. Nan ya ce,  Amma wani hanzari ba gudu ba, Kulsum matukar fushi ta ke da ni Aboki, don ba ta ma san da ni aka daura mata aure ba. Fushin da ban san yadda zan yi in rarrashe ta ba .
Murmushi Abdul Ahad ya yi, ya ce,  Turaki kada ka bada maza mana, ai kawai rikidewa za ka yi daga likitan ido ka koma Romeo, ka yi hakuri da duk abin da za ta yi, za ta gaji ta bari ne tunda bakin alkalami ya bushe .
Turaki ya kyabe baki, ya ce,  ni fa ba zan yi abin da zai jawo min raini ba Malam, idan ta kawo ni bango dauke ta zan yi mu bar garin, mu tafi inda ba mu da kowa, in yaso ta tsire ni ta huta .
Dariya Abdul Ahad ya yi, ya ce,  Sanda za ka zama Romeo din ai ba gaya min za ka yi ba. Ina nan isowa jibi insha Allahu, da ni za a yi kilisa .
A yau ya san ya yi barci irin wanda tsawon shekaru takwas da doriya rabon sa da yin irin sa. Duk wani tension ya kau. Duk wani migraine ya tabbata daga yau babu shi; Kulsum cikin gidan sa, matsayin matar sa ta sunnah! Babu wani kwanciyar hankali da contentment din da ya fi wannan a gare shi.
Da asubahi ya so ya je ya buga mata kofa, sai kuma ya yi tunanin ya kyale ta, a sanin da ya yi mata sallar asubah ba ta wuce ta ba tare da wani ya tashe ta ba. Domin lokacin ne ta ke aikin wankin kayan fitsarin ta.
Ta dade da tashi kuwa kamar yadda ya yi hasashe, ta yi wanka, amma babu kayan da za ta canza. Tana cikin gyaran gado ta ga wata jakar bacco a gefe, da ta bude sai ta tarar da kayan sawa ne na Dr. Sakeenah, ta santa da kayan a jikin ta, ta gane ajiye mata ta yi don ta yi amfani da su kafin a tattaro kayan ta daga Abuja a kawo mata. Kaunar Sakeenah da ganin girman ta suka kara cika ranta. Ta zabi wata shudiyar super holland riga da zani da dankwalin su ta sanya, ta lullube jikin ta da mayafin kayan kamar mai shirin fita unguwa, lotion kawai ta shafa, ko hoda ta ki shafawa kada Turaki ya dauka kwalliya ta yi masa.
Tunanin sa kawai ya janyo mata wani irin bacin rai. Daidai lokacin da ta ji ana buga kofar ta. Dole ta je ta bude don rana har ta soma fitowa.
Wa za ta gani? Batulu!
Wani irin rungume juna suka yi, Batulu na fadin,  Kulsumu na, ashe zan sake ganin ki?
Ta ce,  Batulu kudurar Allah ai ta fi gaban haka .
Tare suka wuce zuwa tangamemen falon wanda ya sha tsari da tsadaddun kaya kamar a Turai. Batulu ta ce,  In na ce wa Yaya Turaki ya kwantar da hankalin sa, idan Kulsumu matar sa ce babu makawa sai ya same ta, sai ya ga kamar na fada masa karya, yau Allah cikin hikimar sa ga Kulsumun mu ta dawo mana cikin yardar Ubangiji .
Nan suka fara labarin bayan rabo, Kulsum ta ce, ina yaran ta? Ta ce suna wajen Ummah.
Suna zaune kamar sa hadiye juna don kauna da aminci, kowacce na labarta wa  yar uwarta yadda rayuwa ta kasance mata bayan rabuwar su, Batulu na ba ta labarin irin bilinbituwar da suka sha ita da Turaki wajen neman komen auren ta. A cikin ran ta ta yi mamaki sosai, mamaki ba dan kadan ba, in ta ce mamaki tana nufin mamaki, sai dai wannan bai ishe ta ta yarda yanzu Turaki na matukar son ta ba ne, yana dai da hujjar sa, watakila don ya samu cikar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login