Showing 24001 words to 27000 words out of 33918 words

Chapter 9 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

443

Turaki ya ya batun wayar Kulsum ne?
Shi dai yana gefe kan shi a kan wayarsa ba sauraron su yake ba, sai da Umma ta kira sunan shi ya dago, ta sake maimaitawa, ya ce,  Ina sane, ban samu shiga Kano ba ne sai wajen jibi .
Duka dakin matan gidan sai da Kulsum ta je ta gaishe su, inda ta tarar Fulani wato kakar su Turaki tana kwance babu lafiya, likita ne ma a kanta ya daura mata ruwa. Tsohuwar tana jin jikin ta, amma albarka ta ke sa wa Kulsumu, tana rokon ta ta rike Turaki da amana, domin shi dan albarka ne, wanda duk gidan ba wanda ta ke so irin sa.
Ba su koma gida ba sai wajen sha dayan dare. Kulsum ta sa a ranta sai dai Turaki ya yi fushi da ita, amma ba za ta sake kwana daki daya da shi ba, hakan cutarwa ne a gare shi, duk son da yake ikirarin yana yi mata in aka ci gaba da tafiya a haka tana sharkaba masa fitsari a gado, watarana na zuwa da za ya tsane ta, in ma bai hada da duka ba. Don haka ta lallaba ta shige dakin ta ta murza key, ta jingina da kofar tana sakin ajiyar zuciyar tausayin kan ta.
Bugun duniya Turaki ya yi, kiran duniya da lallashin duniya amma Kulsum ta ki budewa, don bacin rai kasa kwana a daki ya yi shikadai ya dawo falo ya sa filo a kasa ya kwanta.
Washegari sabida farin cikin ba ta yi fitsari ba don ta bi system din nan na non-pharmacological treatment, da kanta ta hada wa Turaki abin karin kumallo. Ta koma dakin ta ta yi wanka ta zuba kwalliya mai sanyaya zuciyar maigida. Ta feshe jikin ta da turaren fahrenheit ta doshi dakin Turaki.
Da sallama ta shiga, yana kwance daga shi sai kayan barcin jikin sa yayi filo da hannayen sa yana fuskantar ceiling. Bai amsa sallamar ta a fili ba, amma ya amsa a zuciyar sa. Bai kalle ta ba, balle kwalliyar da aka yi domin shi. Tana iya karanto kwantaccen bacin rai a kan kyakkyawar fuskar sa. Ta karasa a hankali ta zauna a daidai saitin kansa.
 Barka da safiya Prince .
Shiru ya yi mata, ta rasa abin da yake mata dadi.
 Na shirya abinci, don Allah ka fito ka ci .
A lokacin ne ya juyo gaba daya ya fuskance ta.
 Kulsum, yaushe raini ya gifta a tsakanin mu, da har za ki kulle min kofa? Ina miki magana ki ka yi banza da ni kamar ba ki san ina yi ba?"
Hawaye suka zubo daga idon Kulsum, ta ce, "Ban yi don raini ba Prince, na yi ne don gudun cutar da kai. Yau da gobe duk hakurin ka da kaunar ka gare ni, wallahi sai ka tsane ni Prince .
 Abin da ki ka yi min shi ne babbar cutarwa a gare ni. Kin sani ba ni da wata matar bayan ke. Ni idan zan same ki a kullum ba ni da matsala da fitsarin ki. Don dai barin garin za mu yi ne, amma tuni na yi mana odar water mattress har guda biyu daga Amazon za su kai min gida na na Reading. In wadannan sun mutu babu damuwa .
Kulsum couldn t help it ban da ta fada jikin sa ta fashe da kuka, wani irin kuka mai kara soyayyar da ta ke yi wa Turaki.
Ta ce,  Na gode Prince, don Allah ka yafe min bacin ran da na sa ka jiya .
Ya ce yana mai tuje daurin da aka bata lokaci ana kalmasawa.
 Ai hakuri daya ne, ki biya ni bashina na jiyan".
Daga haka ya canza akalar hirar zuwa irin wadda ya fi so su yi.

Tun daga ranar Kulsum ba ta kara rufe wa Turaki kofa ba, ta yarda shi din mai son ta ne, mai yawan kaunar ta da tausayin ta ne. Sai dai kuma ta daina barci, kullum cikin non-pharmacological exercise, wato ta daina shan abu mai ruwa-ruwa da shi ruwan kansa daga karfe shidda na yamma, sannan kafin ta kwanta sai ta tabbatar ta yi fitsari, bayan saduwarta da mijin ta abu na farko da ta ke yi shi ne fitsari, sannan ta saita alarm ta aje a saitin kanta tana tashi sau biyu cikin dare at interval ta je ta yi, daga lokacin da suka yi sallar asubah sai ta koma dakin ta, a can ta ke ramuwar barcin ta ta yi fitsarin ta son ranta, sai dai ta yi wata dabara, spreedsheet na kan dining table wanda leda ce ta dauke ta shimfida a saman katifar ta, ta lulluba zanin gado mara kauri a kai.
Turaki ya kara sayo su da yawa ya jibge mata, tana tashi za ta yaye su har ledar ta wanke ta shanya a bandakinta, ba ta taba fitowa waje ta yi shanya ba. Turaki ba karamin tausaya mata yake ba, sabida irin yadda ta ke wahala wajen tsaftace kan ta da muhallin ta.
Aikin da da hali da ba zai barta ta yi shi da kanta ba, tunda suna da wadatar masu aiki, shi ya sa sau tari yake zuwa ya wanke zannuwan gadon da kansa, idan ta jika su a omo ta shiga wata sabgar. Ta yi ta yi ya bari ya ki, cewa yake.

 We are together in this difficulty (muna tare a cikin wannan wahalar) .

A gefe kuma yana ta shirye-shiryen tafiyar su U.K.
Ya cika alkawari ya kawo mata dalleliyar waya, sai damuwar ta ta ragu. Kullum in ba ya nan tana tare da  yan uwan ta a waya, sannan duk inda ya je Allah-Allah yake ya dawo da wuri don kada kadaici ya jefa ta a damuwa. Ba ya son abin da ta ke yawan fadi na cewa, ta tsani kanta. Ji yake me ya sa ma tun farko bai zama kidney and bladder specialist ko Nephrologist ba? Da tuni ya bai wa Kulsum duk treatment din da ya kamata ba wanda ya ji ba wanda ya gani.. Ganin kwanakin da Dr. Ibrahim ya deba musu yake kamar shekaru uku.
Ya je Gombe ya kwana biyu don gudanar da wani private aiki na Sarkin Gombe, wanda cikin ikon Allah aka yi nasara idanun Sarkin suka washe. A lokacin da ya samu lafiya ne ya kira Turaki, wai ya zo ga  yar shi Siyama ya ba shi kyautar ta ko a mata ta hudu ne, bayan iyayen kudin da ya tura masa wadanda sun ninninka kudin da suka yi za'a biya shi.
Turaki ya yi dariya, ya ce da Maimartaba Sarkin Gombe, ya gode, amma ba zai karba ba, sabida ko wata bai yi da yin aure ba.

Wannan labari Turaki ya zo yana bai wa Kulsum, bayan dawowar sa daga Gombe. Kulsum ta lumshe idanun ta ta ce,  Ai da ka karba Prince, ka ga ni babu tabbas din zan warke gabadaya, ko ba zan warke ba. A baya ne nake tsoron ka yi aure, amma yanzu na yarda da kai dari bisa dari, na amince babu macen da za ta sa ka juya min baya. Roko na gare ka shi ne, kada ka taba bari matar ka ta san ina da lalurar urinary incontinence (bed -wetting) .
Turaki ya harare ta son ran sa, ya ce,
 Wato Kulsum ba kya kishi na ko?
Ta ce,  Kishi ba zai sa in kware ka ba, soyayyar da nake maka ita ce ta sanya nake son ka samu cikakken farin ciki kamar kowanne namiji. Ina farin ciki da jin dadi ga auren mai jika gado? Ai sai dai maneji, manejin ma sai irin miji na (Turaki) masu babbar zuciya ta tausayi da jin kai .
Fushi sosai Turaki ya yi, wai ta gasa magana kuma ba ta kishin sa. Wuni guda ya ki dawowa gidan, da ya dawo din kuma ya ki yi mata magana. Ya zauna a falo yana kallon football. Kulsum ta fito cikin kasaitacciyar kwalliya, ta zagaya ta bayan kujerar da yake zaune ta zagaya hannayen ta a wuyan sa suka sauka a kirjin sa. Ta sanya fuskar ta a masangalin wuyansa ta sumbace shi son ranta, sumba sosai, mai tsayi da zurfi.
 Ina bada hakuri my Prince, ka je ka karata da mai fitsarin kwancen ka, ba zan kara cewa ka yi aure ba .
Duk halin fushin da yake ciki sai da ta ba shi dariya. Ya mika hannu ya zagayo da ita gaban shi ya zaunar ta bisa laps din shi. Bakin ta da ya sha wet-lips ya hau tsotsewa sannan ya dalle mata shi da karfi, sai da ta yi  yar kara.
 Matar tawa ki ke cewa mai fitsarin kwance?
Don zafi sai da hawaye ya tsattsafo mata.
 Ka yi hakuri, na bi Allah na bi ka .
Ya rungume ta sosai yana jin bugun zuciyar ta a kirjin sa. Sun dade a haka yana gaya mata babban abin da ba ya so shi ne ta ce ya yi aure, sabida lalurar ta. Kulsum ta ce a ran ta, tabbas da ta rasa Turaki, kamar yadda ta so yin wannan babbar wauta, hakika da ta yi asara irin wacce ba a mayarwa! Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa ya fito fili ya shiga kunnen sa ba.
 What are you saying? Turaki ya tambaya, don bai ji sosai ba.
 I said I love you .
 And I love you more .
 I can t do without you .
 I can t be happy without you too .
 Na gode Prince, once again, I love you with all my heart&  . Ita ce ta ke fadin soyayyar tata in theory, yayin da shi practically ya soma bayyana mata tasa. Ta gane cewa, tata soyayyar is underestimated. Ga masu soyayya in practice, wadanda ba sa bata yawun bakin su wajen bayyana ta.

*** *** ***
Kwanakin da Turaki zai yi a Gaya suka cika, wato wata daya. Ya kama gobe za su tashi zuwa U.K, visa din Kulsum wadda za ta je a matsayin matar aure ga ma'aikaci ta kammala, don haka yau da yamma suka shiga cikin gida don yi wa Umma da Maimartaba sallama, daga can kuma za su biya gidan su Kulsum.
Maryam  yar Yaya Hadiza da ta dawo hannun Umma tun bayan auren Batulu ce ta sanar da su Umma na wurin Maimartaba, bayan sun gaida kowa sun gaida Fulani da jiki sun yi mata sallama tana mai sa musu albarka, suka karasa bangaren Maimartaba din.
Kulsum da Turaki suka zube suka kwashi gaisuwa. Maimartaba sarkin Gaya kallonsu yake cike da murmushi, shi dai haka nan yake son yarinya Kulsumu kamar  yar cikin sa.
Ya ce,  Ummu Kulsum, ina fatan babu matsala, kina nan kina ta hakuri da mijin ki?
Murmushi ta yi, ta ce,  Ai shi ma yana hakuri da ni .
Haka ya yi ta jan ta da hira kamar ba surukar sa ba.
Ya ce,  Za a tafi kasar Turawa a bar mu ko? Ni dai aikin nan na Turai bana son sa Turaki, ba zan gaji da maimaita maka ba, kasar mu na bukatar likitoci irin ka, sau biyu ke nan kana min alkawarin dawowa gida gabadaya, amma sai ka kalallame ni ka kara komawa. Yanzu kuma Kulsumun ma za ka dauke ta, mu da ganin ku sai Baba-ta gani .
Turaki ya muskuta ya kara dukar da kan sa, ya ce, "Insha Allahu wannan karon zan cika alkawari, shekaru uku za mu yi mu tattaro komai mu dawo gida. Allah ya kara maka yawan rai, na yi alkawarin ni da iyali na ko birnin Kano ba za mu je ba, a nan Gaya za mu kafa rayuwar mu har mutuwa. Ina da burin bude asibiti idan na dawo, ga UmmuKulsum ma ma aikaciyar jinya ce za ta taya ni kula da komai. Fatan mu dai a bi mu da addu a .
Ran Maimartaba Sarkin Gaya ya yi fari tas! Ya ce,  Albarkar mu na tare da ku, albarkar uwa da uba, ba za ku taba tabewa ba .
Umma ma da ke gefe tana ta kallon su sun mata kyau a fuska, sun dace da juna. Turaki ya yi aure wanda ta ke so, kuma hankalin ta ya kwanta da shi, don haka ba ta da sauran damuwa a yanzu.
 Umma, ke ma ki sa mana albarka . In ji Kulsum.
Umma ta yi murmushi,  Ai Maimartaba ya hada har da tawa, kada albarkar tamu ta yi muku yawa .
Kowa sai da ya murmusa.
Ta ce,  ku tashi ku je gidan su Kulsumu ku yi musu sallama kada dare ya yi sosai .
Suka mike a tare suna godiya.

 Goggo tana nan? Jibo na kiran ta a zaure .
Kulsum ta make murya ta fada daga tsakar gida.
Goggo na lazimi ta jiyo ta, ta yi dariya da murmushi duka a tare. Baffa Jibo ne ya fara fitowa daga dakin sa. Ya nunata da dan yatsa.
 Wannan Jibon dai ya fi karfin ki, in ma zawarcin sa ki ka zo .
Ta ce,  Haba! Kayyasa! Wane mutum! Ina da sardidin likita na a gefe, me zan ci da tsoho baki duk goro?
Turaki ya sunkuyar da kai yana dariyar su. Goggo ta fito ta shimfida musu tabarma, farin ciki ya cika ta, yau Kulsum ce tare da Turaki suna masu farin ciki da juna. Ya Allah ya kara mata tsawon rai, ta dauki jikokin su. Addu ar da ta ke yi a zuciyar ta ke nan.
Ko da Kulsumu suka shiga daki da goggo, ba ta gaya mata fitsarin ta ya dawo ba. A wannan gabar ta rayuwar su ta amince suna bukatar kwanciyar hankali. Ta kuma kwana da sanin babban tashin hankalin su a rayuwa fitsarin kwancen ta ne.
Duk wani support da encouragement (karfin gwiwa) ta gama samun shi a mijin ta abin kaunsr ta (Turaki). Ba abinda fada musun zai haifar sai tashin hankali a gare su.
Kulsum ta kira Baban ta ta yi masa sallama, sabida Turaki ya ce gobe kafin su wuce Abuja za su fara zuwa 'Yalleman su yi wa Baban sallama, nan Goggo ta ke gaya mata ya kira ta dazu ya ce ba ya gari, ya je Maiduguri kan wata harka da ya samu.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Tausayin Baban ta ya cika ta, mutum ne shi mai kokarin neman na kansa don rufuwar asirin iyalin sa. Ta roki Allah ya ara mata dama ko yaya ne watarana iyayen ta su huta a karkashin inuwar ta. Duk da cewa ba cikin wahala suke ba.
Ta gaya wa Goggo, Turaki ya ce gobe ta Abuja za su tashi, don haka za ta biya gidan Hajiyar ta.
Ba su bar gidan ba sai karfe sha daya na dare. Tunda suka koma gida suka fara hada kayan su.
Washegari karfe shidda na safe suka dauki hanyar Abuja. Daga Kulsum sai Turaki a motar. Yana tuki tana gefen sa, tana so ta yi barci don barcin ta na jiya ragagge ne, ta kwana tana hada kayan su. Amma tana yaki da barcin don kada tsautsayi ya sa ta fitsare masa mota. Da ma ta yo guzurin lipton din ta, shi ta yi ta sha har da su nescape duk don su hana mata barci.
Turaki na tuki ba tare da ya juyo ba ya ce,  Wai wannan shan shayin na mene ne? Ko dai&  . Ya ki karasawa yana murmushi. Kulsum da bata dago inda ya sa gaba ba ta ce,  Ko dai me? Ni don ya korar min bacci nake shan sa .
Da mamaki ya ce,  To a kan me ba za ki yi barci ba? Ana raba jikin dan Adam da barci ne?
 Uhm . Kawai ta ce, ai it is embarrasing ta gaya masa tana tsoron jika masa mota ne.
Hannun hagun sa ya mika ya kwantar mata da kujerar ta.
 Please sleep baby . Yana iya hango fargabar ta cikin kyawawan idanun ta.
Ya kuma san me ta ke fargaba din.
 To Ummu Kulsum, mece ce mota? Barcin ki ya fi ta muhimmanci a waje na .
Tana lumshe idanu cike da barci ta dube shi cikin shaukin so. Mutum kamar mai gani har hanji? Ya daga mata gira tare da kashe ta da wani kyakkyawan murmushi da ya ratsa har cikin ruhin ta.
 Help me and sleep (taimakeni ki yi barci). Kulsum ta lumshe idanun ta, kafin dan lokaci barci ya dauke ta.
Cikin taimakon Allah ba ta yin ba har suka shiga Abuja. Yana kokarin shiga da su hotel din Rockview ta ce,  Prince, don Allah mu je in gaida Hajiya ta, ban yi mata sallama ba .
Ya ce, shi sai ya yi wanka da sallah ya huta. Kuma sai ta tabbatar saurayin ta ba ya gidan sannan za su je. Ta yi narai-narai da ido.
 Ya ya za a yi in san yana gidan ko ba ya nan? Shi da gidan su?"
Ya yi fuska ya ce,  Ki kira ki tambaya".
Dariya ta yi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska.
 Da ma ka cire shi a ran ka, ni ban taba son sa ba, irin son da ka ke tunani. Ina son sa ne a matsayin sa na dan uwa na na jini, kuma shi ma ya sani, ya sha fada da bakin sa;
 Ki taimake ni kada ki kara ambaton Turaki a gabana, zuciya ta za ta buga Kulsum .
Turaki ya yi wani lallausar murmushi yana murza sitiyarin motar sa cikin gwanin ta.
 Wato har zance na ki ke masa Kulsum? Ashe kina so na duk da laifuka na gare ki? Ya fada cikin sanyin murya.
Kulsum ta kare fuska da mayafin ta,  Hatta Hajiyar mu da Goggo, sun san irin son da nake maka Prince".
Turaki ya mika hannun damansa ya kama nata ya matse shi sosai a cikin hannun sa.
 To say I thank you& is not enough to express the feeling& ..... .

Daidai lokacin da suka adana motar a parking lot. Ya mika hannu ya bude mata kofa, jakar hannun ta kawai ta dauka. Turaki ya wuce gaba ya je ya kama musu daki. Ta lifter suka bi zuwa dakin nasu. Duk abubuwan da ya lissafa sai da ya yi su; wanka, sallah, hutawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login