Showing 6001 words to 9000 words out of 33918 words

Chapter 3 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

445

mata& amma ban da fasa aure!
Washegari tun asubah suka kamo hanyar Kano a cikin babbar (Land Cruiser) din Daddy, Taufeeq ke jan motar, Daddy na gefensa, Hajiya Nasara da Goggo suna baya, Nasmah ba ta biyo su ba sabida ba za ta iya jure tafiyar mota ba, za ta jira su har su dawo tare da amarya in an dauro aure. Mujaheed sai goben zai bi su ya samu daurin aure.
Karfe goma sha daya na safe suna cikin Kano, daga nan suka dauki hanyar Gaya. Wajen karfe daya na rana Taufeeq ya kashe mota a kofar gidan Malam Jibo.

(Daga can nesa da su, wani gajeren saurayi ya fiddo waya jikin sa har rawa yake, ya lalubo lamba ya kara a kunnen sa).

*** *** ***
Daga inda ta ke kwance a kan gadon karfen Goggo tana jiyo sallamar su daya bayan daya. A hankali ta runtse ido tare da kiran sunan Allah. Goggo ce ta fara shigowa dakin ta haska ta da tocilan kasancewar dakin ba haske. Kwafa ta yi tare da cewa,
 Kin kyauta abin da ki ka yi. Shin Kulsumu ke karamar yarinya ce, ko ko goyon ki ake yi? Kin bi kin daga wa bayin Allah hankali babu gaira babu sabar. Yanzu ga shi kin taso su bagatatan, wai kina cikin hankalin ki kuwa?
Kulsumu ta gyara kwanciyar ta ba ta ce wa Goggo komai ba. Ta yi bambamin fadan ta har ta gaji, Kulsumu ba ta tanka mata ba. Hajiya Nasara ce ta shigo ta bude tagogin dakin da Kulsumu ta rurrufe, haske ya wadaci dakin.
Ta ce,  Fadan nan ya isa haka Goggo, ki bari su Daddy su dawo sallah sai mu zauna da ita mu ji damuwar ta. Na san Kulsumu ba za ta yi abubuwan da ta ke yi haka kawai ba . Sannan ne Kulsumu ta samu lafiya daga sababin Goggo, ta sauko ta yi wa Hajiya Nasara barka da zuwa, tare da tambayar Nasmah.
Hajiya Nasara kallon ta kawai ta ke tana mamakin yadda ta zabge cikin kwana biyu kacal. Ta ce,  Nasmahn da ki ka kusa sa wa nakuda lokacin ta bai yi ba. Ki ka jefa su a tashin hankali, ai ba ki da guts na tambayar ta. Amma Kulsum ko ma mene ne ki tsallake ni ki taho tun daga La??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????gos har Gaya ke kadai? Gaskiya ban ji dadi ba. Na dauka ni ce mutum ta farko da za ki fara dosa da kowacce damuwar ki?
Kulsum ta yi kasa da kai, ta ce,  Ki yi hakuri, ba zan sake ba Mum . Iya abin da ta fada ke nan. Don bata da kalaman kare kan ta.
Bayan kowa ya yi sallah mazan sun dawo daga masallaci, Baffa ya yi musu shimfida a falon sa. Tunda suka shigo Taufeeq ke raba idon ganin Kulsumu amma ko inuwar ta bai gani ba. Har sai da Baffa ya yi wa Goggo umarnin a kirawo Kulsumu.
Daddy na zaune kusa da Baffa, Taufeeq a kusa da shi, sai Hajiya da Goggo daga kusa da kofar dakin. Kulsumu ta yi sallama ta shigo kanta a kasa, ta ja mayafi ta rufe fuskar ta. Daga kusa da Hajiya ta zauna ta ki yarda ta kalli bangaren da Taufeeq yake, wanda ke cikin dukkan damuwar duniyar nan, ya rasa abin da ke damun ta. Ya bi ta da kallo har ta nemi wuri ta zauna.
Baffa ne ya bude taron da addu a, sannan ya ce,  Na ji dadi da ku ka zo bakidayan ku, domin na yi-na yi da Kulsumu ta fada min abin da ya taso da ita haka afujajan tun daga Lagos har Gaya ita kadai, ta ki gaya min. Ta ce sai Taufeeq yana zaune .
Ya gaya musu a halin da ta zo masa jiya na jigata da fita hayyaci, sannan ya dube ta, ya ce,  To Kulsumu, ga Taufeeq ga iyayen sa, ga kuma mu kakannin ki wadanda ba ki da wanda ya fi su, muna so ki gaya mana abin da ke damun ki, ko hankalin wadannan bayin Allah ya kwanta a ci gaba da shirin daurin aure .
Kulsumu ta muskuta, ta ga cewa wannan ita ce damar ta ta karshe, idan ta yi shiru Baffa ya fusata da ita, ko ta zo daga baya ta fada ba zai saurare ta ba. A cikin ranta kuma sai ta ji tausayin Taufeeq ya darsu mata, don ita ta san irin masifaffen son da yake mata. Amma dole ta fadi abubuwan da idanun ta suka gane mata, ko da a ce zai musanta hakan. In ba haka ba hankalin ta ba zai taba kwanciya da shi ba.
 Ke muke saurare Kulsumu, duka wajen nan babu bare, kamar yadda babu abokin wasan ki, idan ba ki da damuwa ki fada mana mu kama abubuwan da ke gaban mu . In ji Goggo.
A hankali muryar Kulsumu ta fito, ta ratsa kunnuwan su.
 Baffa, na fasa auren Taufeeq, ku yi hakuri .
Goggo ta yi shiru tana mamakin karfin halin Kulsumu, shi kuwa Taufeeq dagowa ya yi a firgice ya dube ta. Duk da bai yi sa ar ganin fuskar ta ba. Daddy ya hadiyi miyau da kyar, Hajiya Nasara kuwa a ranta cewa ta yi, ta san za a rina, don tuntuni ta yi zargin Taufeeq shi ne matsalar Kulsumu.
Baffa ya ce,  Ko za ki fadi dalilin ki, tunda Allah ya hana hukuncin da babu hujja?
Kulsumu ta yi shiru, Daddy ya ce,  Kulsumu feel free to talk, we are all here for you. Idan mun amince da hujjojin ki ba za a daura auren nan ba .
Tausayin iyayen Taufeeq ya kama Kulsumu, amma haka ta rufe ido ta fadi abubuwan da ta gani a cikin firij din sa. Ta kare da cewa,  Ina tsoron auren ko da mashayin wiwi ne, balle giya. Ina tsoron halin da zan fada a gaba, da kuma ranar da  ya yanmu za su gane dabi'ar mahaifin su, su zarge ni da zaba musu mai wannan dabi a. Amma in Yaya Taufeeq ya ce na yi masa karya, yana iya rantsewa ba haka ba ne .
Tsit! Ka ke ji a falon, yayin da Taufeeq ya sunkuyar da kai yana hada zufa. Bai taba tozarta a rayuwar sa irin yau ba. Bai taba zato watarana asirin sa zai tonu ga iyayen sa ba, bai taba zaton abin da Kulsumu ta gani kenan ba ya hargitsa ta haka. Tun farko shi me ya kai shi kiran ta zuwa gidansa ya kasa hakurin a daura musu aure? Yau ga abin da ya janyo wa kansa.
Hajiya da Daddy ne suka tsura masa ido, Daddy ya yi karfin halin cewa.
 Da gaske ne Taufeeq?
Ya kara yin kasa da kansa kamar ya roki kasar ta tsage ya shige.
Hajiya Nasara ta ce,  Da gaske ta ke ko sharri ta yi maka?
Cikin tsananin nadama Taufeeq ya ce,  Ba ta yi min sharri ba. Tabbas ta gani din. Amma Mum don Allah ku yi min afuwa, wallahi ban dade da fara sha ba& a komawa ta Lagos ne don in samu in rage tunanin ta, a lokacin da ki ka ce sai na jira ta for some years& na ga cewa ba zan iya jiran ba, shi ne na nemi abin da zai yi assisting dina, amma wallahi daga yau Mum na bari, na bari har abada, ba zan sake ba. Tsautsayi ne .
Goggo ta kawar da kai, jin hawaye na son zubo mata. Tausayin Nasara ya yi bala in kama ta ganin halin tashin hankalin da ta fada lokaci daya. Daddyn Taufeeq kuwa kada ka so ka ga fuskar sa a lokacin sabida tsananin fushin da ke cikin ta.
Ya ce,  Taufeeq, sabida mace ka zabi ka sha GIYA, ka saba wa Ubangijin ka? Duk tarbiyyar da uwarka ta yi maka? Ba ka sha giya a Turai ba sai a Nigeria Muhammad Taufeeq?
Hawaye Taufeeq ya soma, ya ce,  Daddy na yi kuskure, na yi nadama, zan yi istigfari, amma don Allah kada ku hana ni auren Kulsum, wallahi daga yau na bar giya har abada! .
Hajiya Nasara ta mike hawaye fal idon ta, ta ce,  Maganar aure tsakanin ka da Kulsumu babu ita, na soke ta har abada. This is your punishment, ka je ka yi karatun-ta-nutsu. Don mai shan giya bai iya rikon aure sai dukan mata. Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi .
Goggo ta ce,  Ku yi masa afuwa mana, don Allah ke Kulsumu ba kya afuwa? Da Allah ba ya afuwa gare mu da tuni bai kifar da duniyar ba? Dukkan mu masu kuskure ne, sai ake so in muka gane kuskuren mu a karbi hanzarin mu. Ki yi hakuri tunda ya ce ya bari .
Kulsumu ta girgiza kai tana hawaye.
 Ba zan iya ba Goggo, tunda Hajiya ta ce a yi hakuri, to a yi. Zan taya Yaya Taufeeq addu a Allah ya ba shi wadda ta fi ni .
Daddy ya ce,  Goggo a bar maganar nan, Taufeeq has to be punished don gobe ya gane ba duk abin da ka ke so sai ka same shi dole ba, a kuma lokacin da kake so. Ya je ya yi karatun-ta-nutsu, ranar da ya tabbatar ya zama mutumin kirki ya dawo ya auri Kulsumu, amma aure gobe babu shi .
Ya mike shi ma ya fice.
Hawayen idon Taufeeq suka gangaro, ya ce,  Don Allah Baffa ku ba su hakuri, ina son Kulsum ba zan iya hakura da rashin ta ba& 
Baffa ya ce, "Taufeeq yanzu sun dauki zafi, ka bari su huce. Ba za su saurare mu ba. Ku tashi ku je, Allah ya yi muku albarka .
Duk yadda Taufeeq ya yi don ya kebe da Kulsumu ya samu ya lallashe ta ta ki fitowa daga dakin Goggo, har Daddy ya yi kiransa domin su tafi cikin Kano su kama hotel su kwana, gobe su biyo su dauki Hajiya Nasara su wuce, don lokacin magriba ta kusa ba za su iya kama hanya ba.
Haka Taufeeq ya bi bayan Daddy, yana mai jin karshen duniyar sa ya zo. Yana mai hasaso yadda rayuwa za ta koma masa babu Kulsumu. Ya yi nadama sau ba adadi, nadamar da ya tabbatar iyayen sa ba za su karbe ta a wannan lokacin da suke cikin tsananin fushi da shi ba.
Sun idar da sallar isha, Hajiya Nasara na kwance a dakin Goggo, zazzabi ya rufe ta, Goggon sai ba ta baki ta ke, tana cewa, ta dauki abin nan da sauki kada ciwon zamani ya shige ta, yaran yanzu ai kowanne da matsalar sa, kuma Taufeeq ya yi nadama tana da tabbacin in ya auri Kulsumu ba zai sake ba.
Daga kwancen da ta ke Hajiya Nasara ta ce,  Allah ya kiyaye in hada Kulsumu da mai shan giya, kuma tunda sai ya samu Kulsumu ne zai bari ya je ya yi ta sha, Kulsumu ta riga ta tsere masa .
Sallamar yaro suka jiyo daga tsakar gida, Goggo ce ta fito tana amsawa.
Ya ce,  Wai ana sallama da Baffa .
Goggo ta ce,  Tunda ya tafi sallah bai dawo ba&  .
Ba ta rufe bakin ta ba sai ga Baffan na shigowa, fadi yake,  Kai din bako ne da za ka tsaya a waje kana sallama? Da can haka ka ke yi ba sallama ka ke yi kan ka tsaye ka shigo ba?
Ya shigo, bakon na biye bayan sa. Hasken farin wata ya haska wa Goggo fuskar Yarima Turaki, gabadaya tsakar gidan su ya dauki kamshin sassanyan turaren sa, a idanun Goggo har tsayi da girma ya kara, fatar sa sai sheki ta ke a cikin hasken farin wata, ga wata shadda mai maiko da ya zuba sai walainiya ta ke (Excelcior), ya dora hula wadda ta dace da shaddar jikin sa ruwan toka, hannayen sa biyu zube cikin aljihu kamar yadda ya saba. Sai faman sunkuyar da kai yake, yana murmushin da da ka gani ka san na rashin nutsuwa ne.
Dazun nan da safe yaron nan Sadi makwabcin su Kulsumu da ya sa ya dinga yi masa dakon zuwan ta Gaya ya fada masa ta zo har da marikan nata, kuma ya ji kishin-kishin gobe ne za a daura auren ta.
Duk abubuwan da ke gabansa haka ya zubar da su ya taho Gaya, bai samu jirgi da wuri ba shi ya sa isowar sa Gaya ke nan ko gidan su bai shiga ba ya zarto nan, don ya ga ko da abin da zuwan sa zai amfana masa.
Har gobe jikin shi yana ba shi zai samu Kulsum, zai dawo da ita cikin rayuwar sa komai daren dadewa. Ganin ta da ya yi a Lagos ya kara tabbatar masa Ubangiji na nufin wani babban al amari a tsakanin su.
Goggo ta ce,  A ah! Turaki ne tafe?
Yayin da Baffa ya shimfida masa darduma ya zauna, Goggo ta shigo ta zauna a gefe suna gaisawa. Baffa ya dube shi ya yi murmushi, ya ce,  To alhamdulillahi, da ma yanzun nan da ka gan ni na dawo, gidan ku za ni wajen Maimartaba, in gaya masa in har yanzu kana bisa ra ayinka na neman komen Kulsumu, gobe ka kawo sadaki a mayar maka da matar ka .
Turaki ji ya yi tamkar zuciyar sa ta yi tsalle ta fito daga kirjin sa, sannan ta kuma yin wani tsallen ta koma muhallin ta. Ya ji shi tamkar yana yawo a kan gajimare, duk da haka bai gaskata kunnuwan sa ba, domin wani abu ne da ya zo masa bagatatan tamkar saukar aradu, ya bugi zuciya da kwakwalwarsa a lokaci daya.
 Na am Baffa& me ka ce? Ya tambayi Baffa don dai ya samu wannan karon zuciyar sa ta karbi tabbacin maganar.
Baffa ya sake maimaita masa, ya ce,  A da, gobe za a daura auren ta da dan uwanta, to amma an samu matsalar da ta sa aka fasa, sabida haka in har yanzu kana kan ra ayin komen, ni a gobe zan yi wa Kulsumu aure, da ko ma waye, jama ar da na tara ba ni da bakin sallamar su .
Baffa bai yi aune ba sai ganin Turaki ya yi ya fuskanci gabas ya yi sujjadah. Murmushi Baffa ya yi don ya fi kowa sanin wahalar da yaron ke yi a kan neman komen Kulsumu, ko sati daya ba a yi ba ya zo, amma bai gaya masa ta kusa aure ba, don ba ya so ya karya masa zuciya. Ya yi musu hidima mai yawa ta kayan abinci kamar yadda ya saba, Allah ya sani! Tun farko ya fi so Kulsumu ta koma wa Turaki, kunyar Hajiya Nasara ce ta sa ya amince da zancen Taufeeq.
Bayan ya dago daga sujjadar Baffa gani ya yi hatta kyawun fuskarsa ya karu.
Ya ce,  Baffa "na gode" ta yi kadan ta bayyana godiya ta. Na gode Baffa, Allah ya yi muku duk abin da ku ke so a duniya da lahira. Ya jikan mahaifa, ya ja kwanan ku. Yanzun nan zan je na fada wa Maimartaba da Umma, kuma a daren nan ba sai gobe ba za a kawo sadaki .
Mikewa ya yi zai fita, jikinsa har rawa yake.
Baffa ya ce,  Bari a kirawo Kulsumun mana ko gaisawa ne ku yi .
Turaki ya juyo daga bakin kofa gaban sa na faduwa, ya ce,  A ah Baffa, kyale ta za mu gaisa gobe. Yanzu dare ya yi . A
zuciyarsa kuwa ya fadi hakan ne gudun rigimar Kulsumu kada ta ruguje wannan maganar, amma kwarai zai so ya sake ganin ta. Bayan ganin da ya yi mata a Lagos, wanda ya hana shi ko da runtsawa tsayin kwanaki biyun nan gabadaya.
A hankali yake tukin motar hawaye na sauka a kan kundukukin sa. Hawayen farin ciki irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Kai tsaye cikin gida ya wuce da sassarfa, bangaren Umma ya nufa. Har dakin barcin ta ya duba ba ta nan, sai ga Laraba za ta gifta ya tambaye ta Umma, ta ce tana turakar Maimartaba, ita ce mai girki. Bai tsaya ya gama jin me ta ke cewa ba ya wuce bangaren mahaifin nasa.
Sallama ya yi cikin kokarin daidaita nutsuwar sa, duk suka amsa mishi, Umma na serving Maimartaba abinci. Murmushi ya yi lokacin da Turaki ya gurfana a gaban sa yana gaisuwa. Ya amsa, sannan ya ce,  Yanzu da ma na ce Umman ka ta kira min kai a waya, kwana biyu idanun nan nawa sun matsa min da kaikayi, ga wani hawaye da ke yawan fitowa .
Turaki ya yi kasa da kansa, ya ce,  Allah ya kara ma yawan rai, zan kawo maganin da za a dinga digawa . Sannan ba tare da ya jira amsar Maimartaba ba ya dora abin da ke cin sa a zucci.
 Baffan Kulsumu ne ya aiko ni Allah ya kara maka lafiya, ya ce, in har yanzu ina son komen Kulsumu in aika sadaki gobe a mayar da auren ta da zaa daura a kaina .
Umma ta saki cokalin da ke hannun ta, ta ce,  Kai Turaki bana son hauka, ko dai soyayya ta sa ka fara kuncewa ne? Ya ya za su daura wa  yar su aure da dan uwanta ka ce wai wani an ce da kai za a daura?
Murmushi ya yi, ya ce,  Wallahi Umma babu shirme cikin magana ta, na je ne in gaishe su kamar yadda na saba, sai yake cewa an samu matsala da wancan an fasa, in zo a daura da ni .
Maimartaba ya ce,  to ban da abinki rabon kwado yana hawa sama ne?
Umma ta yi hamdala a fili, ta ce,  Ina ruwan Allah, abinda nake gaya maka kullum ke nan Turaki, cewa ka fauwala wa Allah komai, idan da rabon sauran zama a tsakanin ku Allah zai ba ka wannan damar . Sai ga hawaye a idon ta. Ta kai hannu ta goge ta sake cewa,  Allah na gode maKa da Ka nufi Kulsumu da dawowa gare mu .
Maimartaba kuwa cewa ya yi, ya kirawo masa Galadima a waya. Nan da nan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login