Showing 15001 words to 18000 words out of 33918 words

Chapter 6 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

440

wani burin nasa ne. Sai dai ba ta ce da Batulu komai ba, ganin yadda ta ke jaddada mata kaunar Yayan ta gare ta.
To da ma ita soyayyar kan shiga farat daya ne bayan kiyayyah? Don dai ita a gabadaya sanin da ta yi wa Turaki kiyayya yake mata ba soyayya ba, don haka ba za ta yarda da wannan campaign din na Batulu ba, a dai yi sha ani kawai wai kaza ta so tsegumi.
Gyaran muryar Turaki ya sa Batulu ta nutsu, ya shigo dakin cikin shirin fita, kamshin sassanyan turaren sa one man show ya mamaye su. Ya dubi Batulu ya ce,
 Ke kuma haka ake zuwa gidan mutane da sassafe? Mutanen ma amare sabon aure?
Dariya ta yi, ta ce,  wadannan ai tsofaffin amare ne. Yaya Turaki na kasa hakurin yamma ta yi ban ga Kulsumu ba. Ka san tun tafiyar ta ba mu sake haduwa ba .
 I can relate . In ji Turaki.
Ya maida duban sa ga Kulsum,  Ummukulsum zan fita, ko kina da sako wajen su Baffa?
Dauke kanta ta yi gefe ba ta amsa ba.
Sai da Turaki ya yi da na sanin kula ta, ga shi ta dizga shi a gaban kanwar sa da ke matukar ganin girman sa.
Yana fita Batulu ta ce,  Wai fushi ki ke da Yaya Turaki Kulsumu? Ki yi wa Allah ki yi wa Yaya Turaki adalci mana, ya sha wahala a kan ki, ya sha matukar wuya kafin ya same ki. Ya yi nadama! .
Murmushi kawai ta yi, ai Yayan ta ne da ta ke so, uwar su daya uban su daya, ba abin da ba za ta ce ba don kafa gwamnatin sa. Ita kuma ta sha wahalar soyayya idan shi wahalar neman ta ya sha, shekara da shekaru tana dawainiya da soyayyar sa, wadda ba ta ga ranar da ta yi mata ba.
Batulu ta bar zancen don ta san ba hurumin ta ba ne. Ta ce su je su zagaya ta ga gidan nata sosai. Ba inda ba su shiga ba, har ran ta ta yaba da gidan, sai dai farin cikin ta ragagge ne duk da kasancewar ta mallakin sa, tunda da Turaki za ta yi rayuwa a cikin sa, wanda ba shi da gurbi ko kankani a zuciyar ta yanzu. Ko son ganin sa ba ta yi.
Umma ta aiko musu da abincin karin kumallo a manyan warmers, suka zauna suka ci ita da Batulu. A lokacin ne baki suka soma zuwa  yan ganin daki da  yan ganin kwaf!  Yan uwan Turaki da  ya yan zuri ar su duk sun zo. Wadanda ta saba da su a baya, da wadanda sai yanzu ta san su. Har dare suna hidimar baki ita da Batulu, sai da aka zo daukan Yayar su Magajiya  yar wajen Hajiya Saratu, sannan Batulu ta bi su suka tafi da alkawarin gobe kafin ta koma Kaduna za ta biyo su yi sallama, ta kawo mata Nurain da Zunnurain  ya yanta ta gan su.

*** *** ***
Turaki bai shigo gidan ba sai karfe tara na dare. A matukar gajiye yake, a kan dining ya samu abinci cikin warmers, ya debi wanda zai iya ci, ya koma kujerar tsakiyar falo ya yi zaman sa, ya kunna talabijin ya kamo tashar da yake so, wato CNN, ya koma cikin kujera yana cin abinci yana sauraron labarai.
Bai damu da ya je inda ta ke ba, amma zuciyar sa da idanun sa so suke su gan ta, ko da kuwa rikici za su yi, ba zai iya kwana bai san halin da ta ke ciki ba.
Mikewa ya yi zuwa dakin nata. Ya murda kofar ya ji ta a rufe. A hankali ya ce,
 Ummukulsum, bude min kofa .
Banza ta yi da shi ta ci gaba da shimfidar gadon da ta ke yi. A ran ta ta ce,  Yadda ka aure ni ba da sani da amincewa ta ba, haka za ka gaji da ni ka maida ni inda ka dauko ni".
Ya sake tausasa murya,  Kulsum kada ki yi abin da zai fusata ni, idan na shigo dakin nan...&  .
Sauri ta yi ta je ta maida mukullin jikin kofar, yadda ko ya zira nasa ba zai budu ba, wato ya doke ta sannan ya hana ta kuka saboda zalunci? A lokacin da ta ke neman jin kan sa, kulawar sa da soyayyar sa bata samu ba sai yanzu da ta daina bukata?
Hakan kuwa ya yi, domin dakin sa ya koma ya dauko bunch of keys na gidan gabadaya, ya zo ya yi ta gwadawa, amma ya ki shiga. Nan ya gane makullin ta bari a jiki. Ya yi kwafa. Ya ce.
 Ni da gidana a ke rufe min kofa? Ki yi kina sani, ranar da zan rama tana nan zuwa .
Kulsum ta yi murmushi ta san ta shaka masa. A zuciyar ta ta ce, "da na ce gidana ne? Dadin abin ba daga bola ka tsinto ni ba .

Turaki kwana ya yi da wannan bacin ran, washegari ba ta fito ba sai da Batulu ta zo yi mata sallama tare da yaran ta. Suka yi sallama cike da begen juna. Kuma a ranar ne Malam Yusha u ya kawo mata dukkan kayan ta na sawa da na amfani, da takardun makaranta daga Abuja.
A daren ranar Turaki bai neme ta ba, ya sa a ran sa ya fita sabgar ta, don shi duk wata hanya da za ta kawo raini tsakanin sa da kowa bai son ta. Balle iyalin sa. Duk da hudubar da Abdul Ahad ke ta yi masa na cewar, kwantar da kai zai yi, girman kai ba nasa ba ne a halin yanzu, ya aje sarautar sa da mulkin sa a gefe ya lallashi Kulsum, laifi har ba iyaka ya san ya yi mata, amma ya san shi ba zai iya ba, yana tattalin girman sa sosai.
A tunanin sa in har zai samu su kebe cikin nutsuwa ya san ta duk hanyar da zai bi ya wanke laifin sa a aikace, amma ba ta irin hanyar da Abdul Ahad ke so ba. Shi Ba-sarake ne, wanda ya gaji sarauta gaba-da-baya ba haye ya yi ba. Kulsum ta je ta yi ta yi, ranar da ta gaji za ta bari ne. Domin wannan karon auren su na har gaban abada ne, don haka tun ranar bai kara zuwa ya buga mata kofa ba, ita kuma ba ta fasa shigewa tun yamma ta kulle kan ta ba. Da ma ita in ta ci abinci karfe shida na yamma shi ke nan kuma ba ta kara ci sai breakfast din washegari.
A haka suka zauna ba mai shiga harkar dan uwan sa har tsayin kwana biyar, ya kama washegari ne hawan angoncin da Turaki ya shirya da abokan sa da  yan uwansa maza. Kuma a ranar ne Abdul Ahad ya iso, abin mamaki tare da Sajeedah. Bai gaya masa ba don ta ce surprise ta ke son yi musu. Ba za ta iya hakuri ta zauna ba ta zo ta ga Kulsum din Dr. Abubakar ba. Ta zama kawar ta ta farko daga bangaren matan abokan su.
Turaki da kansa ya raka su wajen Umma da wajen Maimartaba suka kwashi gaisuwa, Umma ta dade tana jin labarin Abdul Ahad a wajen Turaki. Ba karamar tarba tasa aka yi musu ba, aka kai su guest house din Maimartaba, amma sai Sajeedah ta ce ita Allahnbur wajen Kulsum za ta sauka. Abdul Ahad ya harare ta, ya ce,
 kin taba jin inda aka yi masauki a dakin amaryar da ko sati ba ta rufa ba?
Ta ce,  Dear, ni ba zan hana su amarci ba, akwai sakonnin da zan bata ne. And I want to be her first friend from Reading .
Turaki ya ce da Abdul Ahad ya kyale ta, in sun yi wanka sun huta zai zo ya dauke ta zuwa wajen Kulsum din, amma a can karkashin zuciyar sa cike yake da zullumi da taraddadin tarbar da za ta samu daga Kulsum din, shi kansa a me yake gare ta balle wani nasa? Gabadaya ta canza daga Kulsum din da ya santa, saliha mai sanyin hali, ta rikide zuwa wata halittar daban. Kamar ba ta san girman hakkin aure a kan ta ba.
Laifi ya san ya yi mata, amma ta ba shi da ma mana ya wanke kansa?, Ya ba ta hakuri kamar yadda Abdul Ahad ya ce, su fahimci juna su manta baya? Babu dan Adam din da ba ya kuskure a rayuwar sa. Sai dai shi zaman nan da yake tare da Kulsum cikin gidan sa, duk da babu wata alaka mai dadi a tsakanin su, ya fiye masa gabadaya lokutan rayuwar sa a Reading dadi, sanin cewa ita din mallakin sa ce, kuma tana cikin dakin auren sa, shi ne babban kwanciyar hankalin sa.
Bai aure ta don biyan bukatar gangar jiki ba, sai don ita din bakidayan ta yake so. Fatan sa Allah ya nuna masa ranar da zai sake mallakar Kulsum a shimfidar sa, ya wanke gabadaya laifukan sa na baya ta hanyar da shi kadai ya san ta, ta hanyar da shi kansa ya san unexpressable ce. Shi ne kuma kadai maganin taurin kan Kulsum.
Da wannan tunanin ya iso gida, ya adana motar a inda ya saba adana ta. Cikin rashin karsashi ya nufi dakin Kulsum. Cikin sa a ba ta kai ga rufewa ba kamar yadda ta saba, don a lokacin ta ke sallar la asar ma. Yana shiga ya rufe dakin da makullin da ke jiki ya zare shi, ya rufe toilet shi ma ya zare. Ya hada su duka ya zuba a aljihun rigar sa.
Kulsum na sallah tana jin duk abin da yake yi. Gaban ta ya yi mummunar faduwa da ba ta san dalili ba. Turaki ya kishingida a gefen gadon ta yana kallonta with lingering emotion a zuciya da idanun sa. Rabon da ya sanya ta a idanun sa yau kwana hudu ke nan. Haka kawai ta hana musu morar amarcin su da kuruciyar su, sabida wani fushin ta wanda bai karewa.
Kin sallamewa ta yi, in ta sallame sai ta tada wata, bayan kuma ya san bayan la asar ne ba lokacin nafila ba ne. Wato dai wadannan sallolin don shi aka kirkire su, ba don Allah ba. Murmushi ya yi ya mike ya saki labulayen dakin gabadaya, ya kashe kwan lantar ki ya kunna A.C. Dakin ya bada wani irin dim, sanyi mai dadi ya fara ratsawa a jikkunan su. Rigar voile din da ke jikin sa ya cire ya saura daga shi sai singileti da wandon jikin sa, ya yi kwanciyar sa a gadon Kulsum, yana fadin,
 Yau daga ni sai ke, sai Ubangijin da ya sanya min soyayyar ki. Ki kashe ni ki huta Kulsum, ya fiye min wannan silent killer punishment din naki .
Ya dau filo ya rungume, ya yi kwanciyar sa.
Kulsum ta rasa inda za ta sa kanta, ta yi sallolin har kafafun ta sun gaza daukar ta, sallolin da ta tabbatar babu lada a cikin su. Ba ta yi aune ba ta dan zauna tana hutawa, sai jin ta ta yi a hannun Abubakar-Turaki. Gabadayan ta ya sure ta ya haye gadon da ita, ya ja duvet mai laushi ya lullube su, bayan ya rungume ta tsam-tsam a cikin kowacce kusurwa ta jikin sa yadda bazata iya kwacewa ba. Kafin ya soma kissing din ta wholeheartedly ma'ana da dukkan zuciyar sa. Ya ja tunga da lips dinsa cikin nata, amma duk da ta soma ficewa a hayyacin ta a dalilin deep kisses din Turaki, ba ta fasa kokarin kwatar kanta ba. Ba abin da ta tuno a lokacin sai ranar su ta farko, ranar da Turaki bai taba tausayin ta ba& ranar da ya tabbatar mata ba ya son ta, ya tara da ita ne a bisa tilas. Nan da nan ta fara protest, wasu hawaye masu zafi na bin gefen fuskar ta. Turaki ya ji dumin su a kan fuskar sa, ya sassauta daga tsattsauran rikon da ya yi mata, ya sake kissing din tausasan labbanta softly. Wadanda a lokacin suka koma kalar light pink.
A hankali ya kira sunan ta, ba ta amsa ba sai hawayen ta da suke kara gudu, sassanyan kamshin jikin sa na sanya ta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta daina kokawar da ta ke yi da shi duk jikin ta ya saki. Abin da yake so ke nan, ta nutsu ta saurare shi.
Ya ce,  Ummu Kulsum ko mene ne a tsakanin mu, komai girman laifi na, ina rokon ki darajar iyayen ki ba don ni ba, ki jingine shi a gefe zuwa kwanaki uku, ki karbi bakuncin babban amini na da matar sa, wadanda suka taso takanas tun daga U.K, saboda su taya mu murnar aure .
Kulsum ta kwace jikinta daga nasa, ta juya masa baya. Har wata murna za a taya a wannan auren na rashin adalci? Turaki ya kwantar da kai a bayan ta, ya shiga magiya da rokon ta yayin da hannayensa ke shafa kwantaccen gashin kanta, abin da bai taba tunanin zai iya ba a rayuwar sa. Amma Abdul Ahad na da babban matsayi a wurin sa, duk da ya san komai ba ya so ya tozarta a idanun Sajeedah kamar yadda ya tozarta a gaban Batulu, domin ya lura da gaske ta ke son Kulsumun, dole ya nemi hadin kanta kafin ya kawo ta.
Kulsumu sai ta sa masa kuka, ta ce,  Ni ina ruwana da abokin ka balle matar sa? Ce musu ka yi auren soyayya ka yi da zan nuna musu ina son auren ka? Ai gara ma ka fada musu gaskiya cewa, yaudara ta ka yi ka dawo da ni gidan ka .
Ajiyar zuciya ya yi, ya ce,  Duk na amince, atleast forget everything sai sun tafi, sai ki ci gaba da gasa ni yadda ki ke so, in ci arzikin su. Ko a lahira wani kan ci albarkacin wani. Kada ki manta bakon ka Annabin ka .

Ba ta ce komai ba, amma reaction din ta ya nuna sassauci, ya mike daga gadon ya kunna fitila jin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba. Ta ja quilt din ta rufe har kanta.
Ya yi kwafa, ya ce,  Lokacin ki ne, ki ci gaba da wulakanta ni son ran ki, ni na jawo da na saka miki ido har zuwa yau. Da na bambanta miki da da yanzu, da ba ki raina ni har haka ba .
Kyabe baki ta yi a cikin quilt din, kamar yana ganin ta.
Ya ce,  Zan dauko su idan na yi sallah, Umma za ta aiko da duk abin da za su ci. Don Allah Kulsum ki taimake ni, irin dan murmushin nan na mata da miji da caring din da mace ke nuna wa mijin ta. Ni kuma na yi alkawarin in sun tafi duk abin da ki ke so zan yi miki .
Da sauri ta ce,  Ba abin da nake so illa ka daina shigo min daki. Ba za ka taba samun yadda ka ke so a tare da ni ba. Me ya hana lokacin da ni ma nake bukatar kulawar ka a baya ka kula da ni ka tausaya mun? Ka kaunace ni? Amma sai ka tsallake ka bar ni? Sai yanzu don na zama mutum? Wallahi ba zan taba mantawa da ko wane ne Turaki ba. The vicious& the selfish& the rapist&  . (Mugu, mai son kai, mai fyade).
Runtse idanun sa ya yi, ya ce,  Ummu Kulsum, ki san abin da ki ke fada min, I m your husband no matter what, ki tuna mala iku suna tare da ke. Ashe da ma akwai rape a cikin aure? Idan na ce miki nima a lokacin ban san yaya ake auratayyar bafa? Abin da zan ce shi ne, ki yi hakuri ki hadiye komai just for three days, ......please". Ya fada cikin roko.
Shiru ta yi tana kara boye kanta cikin quilt, ba ta son kallon wadannan idanun na Turaki, wadanda ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu. Yau ga Turaki ta samu, amma zuciyar ta ta kasa karbar sa.
 In je in taho da su Kulsum kin amince? Please Kulsum just for three days&  .
Ta gaji da magiyar sa, kamar ba Turaki ba, wannan Prince din mai ji da kan sa, ciki-ciki ta ce,
 na amince .
Sosai fuskarsa ta washe ba tare da sanin sa ba, ya yi murmushin nan nasa na gefen baki.
 Inyaso in sun tafi sai a cigaba da gasa ni, ko a yi gunduwa-gunduwa da ni, Allah Sarki ni Abubakar .
Ya fice yana cewa,
 Ki tashi ki shirya yanzu za mu shigo .
Ko amsa ba ta ba shi ba, ya bude mata toilet da kofa da ya rufe ya fice har wata irin sassarfa yake don farin cikin ya fara samun kanta.

Masaukin su Abdul Ahad ya koma ya samu duk sun kimtsa, shi suke jira. Sajeedah ta dauko  yar trolly din da ta zuba kayanta suka tafi.
Tun fitar sa Kulsum ta mike daga gadon, wanka ta sake yi, ta fito ta shirya sosai. Wata shadda Ghanilla ta saka mai babban dinki senegalese ruwan goro, ta sha aiki daga sama har kasa. Ta kawo mayafin da ya dace da kayan ta yafa. Tana fitowa falo ta tarar Umma ta aiko  yan aikin ta sun kawo abincin da bakin za su ci. Ta jera komai a dining ta kunna turaren oud a burner, gidan gabadaya ya dau sanyin kamshi. Tana kokarin kunna talabijin ta ji sallamar su.
Turaki ne a gaba, Abdul Ahad ya biyo bayan sa. Sai wata kyakkyawar mace son kowa, wadda kallo daya ta yi mata ta gane zubinta ba na matan Nigeria ba ne. Ta amsa sallamar su, tare da karasawa ta karbi jakar hannun Sajeedah. Murmushi suka yi wa juna ta yi musu jagora zuwa cikin falon, amma ta kasa hada ido da Turaki, balle ta yi masa abin da yake so, don ita ba ta iya pretending a komai ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login