Showing 3001 words to 6000 words out of 33918 words

Chapter 2 - Kulsum Book 3 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

447

fili ban da kukan bakin cikin Turaki, ba abin da ta ke da rinannun idanun ta.
Suna sanyo motar cikin get din gidan Aunty Sakeenah gabadaya jama'ar gidan suka nufo su har Engnr. Farouq. Shi ya bude side din da Kulsumu ke zaune, yayin da Taufeeq ya bude wa Turaki. Tana fitowa Nasmah da Aunty Sakeenah suka yi kanta suna kiran sunanta don tabbatar da lafiyar ta. Ba ta tsaya ba, wuce su ta yi dukkan su ta yi cikin gida da gudu, Aunty Sakeenah ta bi bayanta hankali a tashe.
Taufeeq na bude masa kofar ya fito, inda Taufeeq din ya ba shi hannu, sannan suka yi musabaha, Taufeeq na ta yi masa godiya, ya ce,  Amma anya Doctor do you think she is okey?
Murmushi Turaki ya yi, wanda ya fi kama da na rainin hankali, ya ce,  Lafiyar ta kalau, na fi kyautata zaton akwai abinda ta gani ne wanda ya hargitsa ta. Amma tunda kai mijin ta ne ai za ta gaya maka .
Da haka suka yi sallama, Engnr. Farouq ma na ta yi masa godiya.
Gabadaya suka rufu zuwa cikin gidan, Mujaheed ya ja Nasmah gefe suna magana. Tsayawa suka yi bakidaya a kanta, kowa da tambayar da yake jefo mata.
 Kulsumu lafiyar ki kalau? Sakeenah ta fada.
 Ya ya za ki yi min haka Kulsumu? In kai ki asibiti mu shiga ofishin likita, kawai sai in juyo in neme ki in rasa? Kin daga min hankali yadda ba kya zato, kadan ya rage jini na ya hau, to ina ki ka shiga cikin asibitin da muka neme ki muka rasa? In ji Taufeeq.
 Ku yi mata a hankali, ba kwa ganin kuka ta ke ne? Duk mu kyale ta zuwa ta samu nutsuwa, please, na tabbata ko mene ne za ta gaya muku . Cewar Engnr. Farouq.
Da wannan duk suka watse suka bar ta da Taufeeq, ya zauna kusa da ita, ya kira sunan ta a tausashe,
 Kulsum .
Ba ta amsa ba, kamar yadda ba ta dago ta kalle shi ba.
Ya dora hannun sa bisa nata, ai da mugun sauri ta janye hannun ta. Abubuwan sun mata yawa, har suna son fin karfin kwakwalwar ta.
 Wai me ke damunki ne? Are you okey?
Maimakon ta ba shi amsa, sai ta mike ta nufi toilet, ta shige tare da rufe kofar da mukulli, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Ya dade a zaune inda ta bar shi cikin matsananciyar damuwar da ya kasa gano ta inda zai bullo mata.
 Ko dai Kulsum ta yi gamo da aljannu ne? Wani bangare na zuciyar sa ya tambaya, a karshe ya ga shawarar Engnr. ita ce abar bi, wato su ba ta lokaci ko zuwa gobe ne. Yana so ya kira Hajiya Nasara ya gaya mata, amma bai san me zai ce mata ba, tunda bai san abin da ke damun Kulsum din ba. Don haka ya tashi jikin sa a sanyaye ya bar dakin zuwa falo, suka hadu dukkan su suna ta tattaunawa a kan al amarin, kowa da abin da yake fadi. Sakeenah ta dubi Nasmah kamar ta mare ta, ta ce,
 Tun farko da izinin wa ki ka dauke ta ku ka fita? Ba ki san amarya taka tsan-tsan ake da ita lokacin auren ta ba? Yanzu in gamo ta yi me ki ke so na gaya wa Mum? Da ma ba da son ranta ta yarda ta barta ta zo ba, ta fi so ko mene ne a yi shi a can Abuja da Gaya .
Nasmah ta yi narai-narai da ido,  Wallahi Aunty Sakeenah ba ni da laifi, kin gansu nan, su ne suka kira mu . Ta fada tana nuna Taufeeq da Mujaheed.
Taufeeq ya dalla mata harara, ya tashi ya bar wurin.
Sakeenah ta ci gaba da yi wa Nasmah fada, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, kan don me za ta biye musu? Tunda ta san gyaran jiki ake mata kuma ba a barin ango ya ga amarya har sai bayan daurin aure.
Nasmah dai ta karbi laifin ta, Mujaheed shi ne mai bada hakuri, don ya ce shi Taufeeq tausayi ya ba shi, ya damu ya gan ta sosai, amma su kwantar da hankalin su insha Allahu babu aljannu a tare da ita, kamar dai yadda likitan da ya kawo ta ya ce ne, wani abin ta gani ya hargitsa ta.
Cikin dare Nasmah na barci, Kulsum ta tashi ta zauna dungurgur! Ya zama dole ta nema wa kanta mafita. Mafita daga auren mashayi wanda ba za ta iya ba, ko ita ta fi kowa halarci a duniya, da kuma kubucewa daga inda Turaki zai sake samun ta. Turaki daga dukkan alamu bai zo gidan su don ya kawo ta kawai ba, sai don ya ga inda ta ke. A yayin da ita kuma ba ta ga dalilin hakan ba. Duniyar sa ta riga ta kare a tata duniyar, ba ta fatan wata mu amala ta sake hada su ko da ta gaisuwa ce.
Ya riga ya gama playing duk wani game din sa cikin rayuwar ta. Ba ta jin a yanzu za ta iya sake daukar wani komai kankantar sa. Allah da ya hada Ya riga ya raba, don hakan ya zama alkhairi a gare ta. Alkhairin da ta ke zaton Taufeeq ne, ashe shi ma nashi kalubalen har ya fi na Turaki. Shawara ta karshe da ta yanke wa zuciyar ta shi ne, ta yi nisa da dukkan su, ta tanadi kalaman da Hajiya Nasara za ta fahimce ta ranar da duk Allah ya sake hada su.
Mikewa ta yi ta dauko handbag din ta, ta duba return ticket din ta ta tabbatar yana nan. Tana da kudi wajen dubu ashirin a jakar ta, ta tabbata za su ishe ta har ma su yi canji. Allah-Allah ta ke a kira sallar asubahi, daidai lokacin da ta san maigadin gidan Sakeenah na tafiya zuwa masallacin kusa da su.
Yadda Kulsum ta ga rana yau haka ta ga dare. A kan idonta da kunnen ta aka tada sallar asubahi, ko kayan ta ba ta dauka ba ban da handbag, waya da hijabin sallarta dogo har kasa. Sadaf! Sadaf! Ta fice daga dakin ta bar Nasmah na ta kirba minshari. A zuciyar ta tana fadin,  Sai watarana Nasmah! Zan yi kewar ki ba  yar kadan ba . Ta kai bayan hannunta ta shafe hawayen idanun ta ta fice daga dakin.
Kofar falon wadda za ta fidda kai waje jam-lock aka saka mata ta ciki. A hakali ta bude ta fice ta rufo kofar silently. Kanta tsaye ta doshi get inda cikin sa a ta tadda maigadi ya shiga masallaci kamar yadda ya saba. Sakatar kofar wucewar mutum daya ta zare ta fice a hankali tare da rufo kofar.
Sauri ta ke ta yi kamar za ta tashi sama, sai da ta kai bakin titi ba ta ga mota ko babur ba. Ta dan jima tsaye a titi tana waigen bayanta ko an biyo ta. Cikin ikon Allah sai ga wani okada-rider ya zo zai gifta gabanta. Da saurin ta ta tare shi, ta ce da shi cikin harshen Turanci ya kai ta airport na garin Lagos ko nawa yake so za ta ba shi.
Mai okada har cikin airport ya shiga da ita, naira dubu biyu ya ce ta ba shi. Ba musu ta kirgo ta ba shi, sannan ta karasa. Ba yau ta fara hawa jirgi daga Abuja zuwa Lagos ba, don haka ba ta sha wahalar samun jirgin Abuja ba, amma sai karfe takwas na safe zai tashi, lokacin bakwai ta kusa. Don haka ta soma neman inda za ta buya, ta yadda ko su Taufeeq sun biyo bayan ta ba za su ganta ba. Cikin fasinjoji ta kutsa ta shige, masu jiran lokacin tashin jirgi, ta ja hijabin ta ta rufe fuskar ta.
Karfe bakwai jirginsu ya tashi daga Lagos zuwa Abuja. Tana sauka a Abuja ta nemi taxi ta ce a kai ta Jabi Motor Park. Tana zuwa ta tambayi inda ake lodin Kano, aka nuna mata. Ta biya kudin mota, cikin sa a motar saura mutum daya ta cika, tana shiga direban ya tada mota suka durfafi Kanon Dabo.
Sai wannan lokacin Kulsumu ta samu ta sauke ajiyar zuciya, at least she escaped daga Taufeeq har Turaki. Ta san Baffa da Goggo za su fahimce ta, sannan ba za su taba bari rayuwar ta ta tozarta da auren mashayin giya ba. Kamar yadda ba za su kara bari azzalumi, mugu, mai son kansa, makiyin ta Turaki ya sake dawowa cikin rayuwar ta ba. Ta sa a ranta ta gama zaman Abuja, ta gama zaman gidan Hajiya Nasara, ta dawo gaban kakannin ta kenan har abada! Da ma karatu ta je yi, kuma cikin yardar Allah ta yi ta gama. Za ta koma mahaifar ta ta gina sabuwar rayuwa, ba za ta yarda ta wargaza rayuwar ta da sunan halarci ba don ko Ubangiji bai yarda da wannan ba. Haka ba za ta yarda a karo na biyu Turaki ya sake zamowa barrier ga farin cikin rayuwar ta ba.
Tafiyar awanni biyar ta kawo su Kanon-Dabo, inda daga nan ta hawo bus mai zuwa garin GAYA. Bakin ta dauke da addu o i masu yawa na Allah ya sa Goggo da Baffa su fahimce ta, su fahimci ta yi hakan ne ba don butulci ga Hajiya Nasara ba, sai don ta gina wa kanta kyakkyawan future. Ba ta ji dadin auren kuruciya ba, ba ta fatan ya kasance shi ma auren da ta yi cikin cikakken hankalin ta ya zo ya samu nakasu, tunda kuwa zuciyar ta ba za ta iya juriyar zama da mashayin barasa ba.

*** *** ***
Baffa Jibo na gyare-gyare cikin dakin da yake jibge amfanin gonar sa, kafin ya kai su kasuwa. Ya jiyo wata siririyar sallama kamar ta Kulsumu. Kwana biyu ke nan da tafiyar Goggo Abuja, shi kadai ne a gidan, shi bai je ba don nan Gaya za a taho daurin aure ranar asabar. Duk wanda ya kamata su gayyata sun gayyata, mutanen 'Yalleman gobe za su wuce Abuja, inda za su kwana biyu daga can za su taho bakidaya ranar juma a zuwa Gaya tare da Hajiya Nasara da jama arsu, a yi daurin aure asabar, su juya da amarya ranar lahadi.
To sai ga wata makalalliyar sallama yana ji kamar muryar Kulsumun. A cikin muryar akwai jigata da alamun gajiya. Da sauri Baffa ya fito, ya kalle ta sanye da zumbulelen hijabin ta har kasa idanuwan ta duk sun fada, ta yi zuru-zuru saboda wahala da yunwa. Baffa ya bude baki ya ce,
 Kulsumu, ke ce? Ko kuwa mai kama da ke ce?
Ai tana ganin Baffa, hawaye ya kece mata. Ta karasa da azama ta rike shi cikin kuka, ta ce,  Ni ce Baffa .
 Lafiya na gan ki yanzu? Ke da waye?
 Ni kadai ce, tun daga Lagos na taho .
Baffa ya yi salati, ya sallamewa Ubangiji, amma sai ya kama hannun ta suka shiga dakin Goggo, sai da ya tabbatar ta kwanta a gadon Goggo ya juya yana fadin,  Jira ni ina zuwa .
Baffa bai fi minti goma sha biyar ba ya dawo rike da bakar leda guda biyu, gasasshen balangu ne mai yawa da damammiyar fura a ciki, ya samu har zuwa lokacin kuka ta ke yi kasa-kasa. Babban tashin hankalin ta shi ne, kada Baffa da Goggo su kasa fahimtar ta sabida kunyar Hajiya Nasara. Ba ta da nufin tozarta Hajiya Nasara ko shi Taufeeq din kansa, amma wannan aure ba za ta yi shi ba, domin ba ta son ta kara yin aure ta sake fitowa, auren mashayi kuwa babu kwanciyar hankali a cikin sa, sannan  ya yan da za ta haifa watarana sai sun tuhume ta da zaba musu uba mashayin giya tunda dai Allah da ya nufe ta da gani gabanin auren, ya nufe ta ne da rahamar sa.
Ko da ma can ita ba damuwa ta yi da ta yi aure ba, sannan Taufeeq ba wai tana masa mugun so ba ne, abubuwa ne da yawa suka taru suka yi dalilin amincewar ta da auren sa.
Muhimmi shi ne, mahaifiyar sa da  yan uwan sa, sai kuma takurawar su Goggo a kan ta yi auren. Amma ita tun daga kan auren Turaki ba ta kara marmarin aure a rayuwar ta ba. Har yanzu ba ta daina tsoron maza ba. Ba ta daina tunanin dukkansu halin su daya ne ba. Halin selfishness da heartlessness irin na TURAKI. Wadanda ba su dauki mace a bakin komai ba.
Baffa ya ce,  Tashi maza ki ci wannan, ko kin samu karfin yin sallah .
A halin da ta ke ciki ta manta da wani abu wai shi abinci. Duk wani kyakkyawan tunanin ta ya ta allaka ne a kan yadda za ta samar wa kanta mafita daga auren Taufeeq, auren da sauran kwanaki uku a daura shi. Amma ta san in ba ta ci abincin nan ba, ba za ta samu nutsuwar yi wa Baffa bayanin da zai fahimce ta ba. Don haka ta sauko kafafun ta daga gadon karfen Goggo, ta karbi ledojin da Baffa ke mika mata. Ya juya ya fita yana fadin,
 Ki ci ki yi wanka da sallah, sannan mu zauna in ji me ya faru kin ji Kulsumu? Ki kwantar da hankalin ki, da raina da lafiya ta babu abin da zan kasa yi miki .
Wadannan kalaman na Baffa su suka sanyaya mata zuciya. Har ta samu karfin gwiwar cin naman sosai. Da ma tsakanin ta da balangu akwai kyakkyawan aminci. Ta shanye furar gabadaya wadda ba'a cika mata sukari ba, sannan ta tashi ta je ta yi wanka ta dauro alwala. Sai da ta rama duka sallolin da ke kanta, sannan ta ji nutsuwa ta soma shigar ta.
Sai da Baffa ya dawo sallar isha sannan ya kira Kulsumu a dakin sa. Ta shigo sanye da hijabi ta zauna ta rakube abin tausayi. Baffa ya ce,  Kulsumu?
Ta ce,  Na am Baffa .
 Ina so ba tare da kin boye min komai ba, ki gaya min duk abin da ya faru. Mene ne dalilin tahowar ki daga wajen marikan ki kwanaki uku kafin daurin auren ki ke kadai tun daga Lagos?
Kulsumu ta share hawaye, ta ce,  Baffa auren ne na fasa .
Baffa ya hadiye fushin sa da razanar sa, ya ce,  A wane dalili, ko ko don ki wulakanta dattakon mu, ki saka hairan da sharran?
Hawaye suka zubo wa Kulsumu, ta ce,  ko daya Baffa, sai don in tserar da kaina daga sake zawarci a shekarun girmana, bayan wanda na yi a shekarun kuruciya ta, in zaba wa  ya yana uba na gari, in kuma yi jihadin ceton tarbiyyar  ya ya na a can gaba .
Baffa ya kasa fahimtar ta, sai ya ce,  kai tsaye ki gaya min, me ya faru?
Kulsumu ta sunkuyar da kai.
 Baffa zan fi so a ce yana zaune zan fada, don kada ya samu damar cewa na yi masa sharri. Sannan Hajiya da Daddy kada su zarge ni da munafuntar su .
Baffa bai ce komai ba, sai ya yi shiru yana nazarin kalaman ta, amma hankalin sa ya tashi sosai, don ya kasa cankar inda zancen ta ya sa gaba.
Kira ne ya shigo wayar Baffa a lokacin. Yana dagawa ya ce,  ga Nasaran nan ma . Ya amsa suka gaisa a mutunce yadda suka saba, sai dai ya ji muryar ta ba yadda ya saba jin ta ba.
Ta ce,  Baffa, Kulsumu Gaya ta taho?
Baffa ya dubi Kulsumu, sannan ya ce,  ga ta nan a gabana .
Wata irin ajiyar zuciya Hajiya Nasara ta saki a fili, ta jero alhamdulillahi sau uku. Ta juya ta ce da su Goggo,
 Kun ji Kulsumu na Gaya .
Goggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce,  Idona idon Kulsumu& wannan yarinya ta dauki alhakin mu, ni Taufeeq na fi tausayawa, dubi yadda ya fita hayyacin sa sabida neman ta, wannan sakarci da me ya yi kama? Ki kamo hanya tun daga Legas ba tare da sanin kowa ba?
Hajiya ta nisa, ta ce  Ku daina fadan nan Goggo, ni na tabbata Kulsum cikin hankalin ta ta ke, akwai muhimmin abin da ke damun ta da ya sa ta aikata hakan. Da ma gobe za mu tafi Gaya dukkan mu ko mene ne za mu hadu a yi maganin sa, Daddy sai ranar daurin aure ya yi niyyar tafiya, amma gobe zan sa shi a gaba mu tafi tare gabadaya har Taufeeq din .
Hajiya Nasara ta kira Malam Hadi ta ce da shi, mutanen  Yalleman kada su zo Abuja, su zarce Gaya su ma gobe can za su tafi, an fasa yin kamu da wunin a Abuja. Taufeeq na shigowa ta gaya masa Kulsum na Gaya,. Zama ya yi jabar! A kan kujera ya rasa abin da ke masa dadi. Me ke damun yarinyar nan ne tamkar mai motsuwar kwakwalwa?
Hajiya Nasara ta dube shi ta kasan idanu kafin ta yi magana cikin bacin rai.
 In ma wani abun ne ka yi mata wanda har ta zabi ta koma wajen iyayen ta, kada ka yi tunanin za ka yi amfani da ni ka cuce ta, ita din marainiya ce kuma amana a hannuna. Zan yi adalci ne na gaskiya a tsakanin ku .
A jigace Taufeeq ya dago ya dube ta, he is looking helpless tun tafiyar Kulsum, tun jiya yake cikin tashin hankali da wahalar da Kulsum ta sabbaba masa. Shi kuwa me zai yi wa Kulsum da har za ta zabi barin su? Babu komai cikin zuciyar sa a kanta sai tsananin so da kaunar ta. Iyakar tunanin sa ya san bai yi mata komai ba. Ko dai Kulsum ta fasa auren sa ne shi ya sa ta ke tsiro da wadannan bakin halayen? Wani abu da shi kuma ba zai taba lamunta ba, ya yi saken da Kulsum za ta kubuce masa. Shi kadai ya san wahalar da ya sha kafin ya samu kanta, ko me ta ke so zai yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login