Showing 30001 words to 30491 words out of 30491 words

Chapter 11 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel

ta
Rungumesa  tace "  Yaya inasu SONA Baku dawo tare dasu bane?"
Kokarin cireta daga jikinsa yake domin bazai iya jure rungumeshi da tayi ba, ita kuma kara shiga jikinsa take, da k'yar ya rabata da jikinsa yace " suna asibiti tama warke, kallonsa tay da dan murmushi a fuskar ta tace
"Da gaske Yaya?"
Eh na taba miki karya ne"
Toh mesa basu dawoba?" Ba'a sallamesu ba sai gobe acan zasu kwana"
Rike masa hannu tayi ta shugub'e Fuska tace " don Allah nima ka kaini mu kwana tare wlh hankalina bazai iya kwanciya ba ni kadai, don Allah Yaya"
Zuba mata idanu yayi yana kallon yanda take mgn a hankali kamar bata son yin maganar,
Yayaaaaaaa! ta sake kiran sunan sa tana lungub'e masa fuska tace " ba don niba ka kai ni don Allah"
Hada fuska yay yace " dare yayi ki bari sai gobe na kai ki"
D'iddire kafafunta ta farayi tana kukan shugub'a"
Tsayawa yay yana kallonta, a ransa yace " daman haka yarinyar nan take"
Murmushi yayi yace " toh naji zan kaiki sai ki daina kukan ko"
Wani gunguma ta masa tanà dariya tace " ngd sosai bari na dauko hijab dina mu tafi,
Haurawa sama tayi ta barshi tsaye yana kallonta, tana shigewa bedroom yaja numfashi tare da zama kan kujera"
Bata wuce 5 minutes ba ta fito hannunta dauke da wani karamin bags a hannunta tace " muje ko"
Kallonta yay daga sama har kasa kayan baccin ne ajikinta sai hijab din datasa iya guiwa"
Fuska d'aure yace "ba inda zanje in dai haka zaki tafi asibitin"
Kallon kanta tay tace " me kuma nayi?"
Je ki canja kayan nan idan zakije idan kuma bazaki tafi ba nayi tafiya ta"
Shugub'e Fuska tay tace " na canja me kuma?"
Mikewa yayi zai tafi da sauri ta taresa tace " don Allah ka zauna bari na canja mu tafi"
Bece komai ya koma ya zauna, da sauri ta koma bedroom din ta canja ta fito, tace " toh yanzu fa?" Kansa ya daga kan wayar sa da yake lasawa ya kalleta doguwar riga ce wanda ta k'arbi jikinta sosai, sai gelen kayan data yafa, bece komai ya ci gaba ta lasar wayar sa kafin yace " jeki dauko hijab dinki"
Cikin jin haushin sa ta koma dakin ta sanya hijab ta fito, tace " sai ka duba ai"
Kallonta yayi yaga ta wani hada rai murmushi yayi yace " idan baki saki fuskar kiba sai na fasa zuwan, murmushi ta sakar masa tace " kayi hakuri mu tafi don Allah"
Bece komai ba ya fita ta bishi a baya"
Parking space suka wuce, bude motar yayi ya shiga itama ta shiga suka bar gidan"
A hanya ya tsaya ya musu shopping suka wuce asibitin,
Suna isa direct dakin da aka kwantar da SONA suka shiga, Momy na kallonsu tace " dawowa kukayi?" Yace " eh itace ta masamin sai na kawota, murmushi kawai Momy tayi Fatu tace " ya jinkin?"
Alhamdulillah my daughter"
Murmushi ta zauna gefin SONA tana kallonta"
Sallama Saif ya musu ya wuce gida"

   Washe gari...!

Share fisabilliah Habibaty 🥰





Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login