Showing 18001 words to 21000 words out of 30491 words
Chapter 7 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel
yayi ya karasa dining din kujera yaja ya zauna yana murmushi, kallonsa SONA tayi tace" good morning" morning how are u dear" Fyn brother"
Murmushi yayi Daddy da Momy ne suka karaso, gaishsu sukayi, suka amsa cikin tsakin fuska suka zauna, serving d'insu SONA tayi suka fara cin abinci" bayan sun gama cin abinci ne Daddy yyi gyaran murya yace "Babana daman inason zanyi mgn da k'ai"
Saif dake shan coffee ne ya kallesa yace "okay Daddy"
Murmushi Daddy yayi yace " ya kamata ace ka dubamin wani irin school ne yaka mata asaka Fatu, kaga bai kamata ace ta zauna bata fara zuwa school"
Tabe baki Saif yayi yace " wannan ne za'a kaita school ai sai mutun ya bata kudinsa a banza ba abunda zata tsinana aciki"
Haba dai Babana mesa zakace haka cewar Momy, toh ai Momy naga k'amar k'anne bazata dauki komai ba sai rashin kunya"
Dan had'a fuska Daddy yayi yace " bana son iskanci fa cewa nayi ka dubamin wani school ne wanda zaifi dacewa da itah, bawai wani zancen ba, sannan kuma inason k'a karb'a mata from din islamiyan da SONA take ciki shima su ringa zuwa tare"
Murmushi yay yace " am very sorry Dad insha Allah zan d'uba yaci gaba dashan coffee d'inshi"
Mikewa Daddy yayi ya musu sallama ya wuce office"
Fatu dai batace komai ba saima sunkuyar da k'ai tayi tana jinsu, zuciyar ta kuma k'amar ta fashe don bakin cikin Saif, yama rai na mata wayo daiwa har ita zaice mata k'anta bazai iya daukar komai ba hmmm"
Shanye coffee yayi ya kalleta yace " ke tashi muje kimin Shara 😱 kallonshi Momy tayi tace " what yanzu Kai ina Fatu ina shara?" Harara ya wasa mata yace " ai kowa Momy d'aga yau ita zata ringa share min part dina"
Baka da hankali ne Saif ai Fatu bazata iya shara ba, ina Indo take?" Tabe baki tayi tace " ai nuna mata zanyi yanda zatayi"
SONA tace "gaskiya bro's wlh Fatu tayi kankan ta sosai"
Had'a fuska yyi yace " okay sai kizo kinuna min abunda zanyi tunda kinfi ne sanin mezan aika ta nida matata, Zaro ido SONA tayi tace " uhmm su mai Mata manya kayi yanda kake so da matar ka bro's nidai nayi gaba, ta fad'a tana barin wajen fuskan ta dauke da dariya"
Momy ma tabe baki tayi tace " toh masu Mata saura kaci zalinta kaga abunda zanma mara kunyan banza, tana fad'an haka itama ta mike ta haura sama"
Kallonta yyi fuska had'e yace "zaki tashi ko sai jikinki ya fad'a miki, itama had'a fuska tayi tace " ko dai jikinmu ya fad'a mana😂 wani irin fincikuta yyi ya burd'e mata baki sanda ta tsake kara, yace " jikinmu ya fad'a mana ko?" Ummm! Don Allah kayi hakuri ba haka nake nufiba, ina nufin namike"
Murmushi gefin baki yyi ya tsaki bakin, ya kama hannunta yana ja har suka karaso part d'insa, a parlor ya yyi wurgi da ita saman kujera, bin ko ina na parlor da kallo take Aranta tace " wow gaskiya wanan wajen ba dai k'yau ba"
Ba abunda taji sai saukan katon abu taji ajikinta, da sauri ta dago da idonta ta kalleshi ai Zaro ido waje tayi tare da mikewa zunbur tace....!
Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰
Msr Ahfat ✍️
👧🏻MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 12
___________________ Zaro ido waje tayi tare da mikewa zunbur tace" k'anb'ala me idona yake gani haka k'amar b'ulala?"
Daman kawoni nan kayi don kaci zalina?" Wlh Allah idan kad'uke ni sai na rama dan rai nin wayon k'awai ta fad'a tana murgud'a masa baki"
murtuk'e fuska yyi ya Karaso inda take da b'ulalan, masawa baya_baya take yana binta harta zauna K'an kujera"
Yace "Yes dukan ki zanyi ba kince zaki rama ba?"
Had'eye miyau tayi tana girgiza kai tace " sabo da Allah mena maka zaka ci zalina wlh Allah ya isa bazan yafema b...."
Saukan b'ulalan d'aya zuba matane ya hanata k'arasa mgnr da take, saka makon wani irin radad'in d'aya ziyarce ta tun d'aga k'anta har tafin kafarta"
Baki ta bud'e da niyan zand'uma ihu yace " akul dinki kika tsake kika min Ihu anan sai na kara miki"
Rufe bakinta tayi da tafukan hanna yinta tayi tana zazzare ido had'e da girgiza masa kai alamar bama zatayi ba"
murmushin munta yyi yace " good" ki bud'e kunnen ki kije abunda zan fad'a miki, in har kika tsab'a abunda zan fad'amiki wlh sai namiki na jaki mara k'unyan banza"
D'aga kai tayi, yayi murmushi
Yace " daga yau ke zaki dinga sharan part dinnan, ki gyara ko ina ki goge, bedroom, parlor, wanke toilet duk aikin kine d'aga yanzu bana son k'azanta, ki dauki ledan nan akoi k'ayan aiki aciki"
K'ayan aiki kuma k'amar ya ta fad'a tana kallonshi?"
D'aga b'ulalan yayi ai da sauri tace " kayi hakuri karka dukeni dazun daka duke nima ji nake k'amar zan mutu,
Yace " ba kina son in fad'a miki abunda ke cikin ledan ba,
Mikewa tay tace " a'a wlh zan d'uba daman tambaya nayi, daukan ledan tayi ta budeshi, tsinyane ta gani da zauran abubun da zatayi amfani dashi
Yace " oya fara d'aga parlor nan kafin na shirya na fito kin gama sai ki share bedroom din"
Tace " toh Yaya a fitoh lafiya, wucewa yayi itama kuma ta zauna kan kujera tana tabe baki tace " hmmm lallai ma wanan mutumin kayi bala'in rai na min hankali a radu Allah"
Zama tayi abunta tana kalle² da tab'e²sanda ta gaji da ta mike tare da daukan tsinsiyan ta rikeshe a hannunta tace " oh ni Fatu dubi tsinsiyan ma yanda yafi karfin hannuna" shara ta fara yi tana jan Allah ya isah 5 mint ta gama sharan da bai fita ba, nunfarfashi take sauke wa sama² ta zauna akan kujera tace " yau nayi aikin da tunda uwata ta kawoni duniya ban tab'a yin irin shiba wlh, ace kuma kullon sai mutun ya share"
Ta jima zaune Tana jiran fitoh warshi amma shiru bai fito ba, tunani k'awai tayi ta haura bedroom din k'awai wata kilma ya fita bata saniba tana shara,mikewa tayi ta haura bedroom din, shiga tayi ko knocking batayi, wow ta furta lkn d'atayi arba da makeken bed d'inshi dake dauke da White bedsheet a saman sa"
Kara tsowa tayi, a hankali tasa hannunta a saman bed din tace " hmmm wanan shine ake kiran sa da Aljannan duniya wlh, jifa laushi k'amar sabon biredi"
Haurawa saman bed din tayi ta zauna akai tana sama da k'asa da duwawun ta tana ta washe baki,
Kwanciya tayi ta lumshe idanunta tace " ji wani irin k'amshi fa har bacci²nake ji a radu kai nasan da Saude sai tashi go wanga d'akin sai ta suma dan dad'i ni din ma k'awai don na fita jarunta ne, Allah sarki Inna ta gaskiya nayi kewar ki naso ace tare zamu kwanta a d'akin nan wlh"
Lumshe idanunta tayi ta tsake budesu, mikewa tayi tace " hmmm gara na gama aikin nan kafin wanan bakin mugun ya dawo ya tsameni"
Sharan d'akin shima tayi shaf² tayi ta gama, tana mai da numfashi, da gudu kuma ta sauko parlor ta dauki mopa da bokitin ruwa ta dawo d'akin, ruwa ta fara zubawa a k'asa sanda ta gama zubawa ko ina wai da niyar yin mopping"
Gogewa tana cewa" irin wanan wahalan har yaushe"
****************
bangaren Saif kuwa yana shiga bedroom din wayan sa ya fara ringin ganin sunan Ruky ne ya tsashi jan dan k'aramin tsaki yana zama bakin bed yayi answering tare da cewa "Hello"
D'aga can bangaren Ruky ta fashe mishi da kukan shugub'a tace " haba sweetheart wani laifi na maka da kake min irin wanan hukumcin, k'asan yanda nakeji kuwa a cikin zuciya ta kuwa?"
Shiru yayi yana tsauraron ta harta gama mgn narta, kafin yace " am very sorry Ruky ina busy ne shiyasa ban d'aga kiranki"
Cikin shugub'a da salon jan hankali tace " shine yasa bazaka iya answering call dina ba?"
Am sorry dear" murmushi tayi tace " no problem yanzu dai nima gani nan a Najeria nazo gun sister na an mana rasuwa" ohhh sorry Allah ya jikanta da rahma, Amen ya rabbi"
Zaka zone?" Dan jim yyi na wasu minutes kafin yace " yeah" murmushi jin dad'i tayi tace " thank you sweetheart, bari na turuma da address din inda muke din"
Okay yana fad'an haka ya kashe kiran yana mai jan tsaki, mikewa yayi ya rage kayan jikinshi ya fad'a bathroom ya tsakar wa kansa shower ya dan jima kad'an kafin yayi wanka ya kammala ya d'aura towel a k'ugunshi d'aya kuma yasa a saman suman kansa yana gogewa, ya bud'e kofar bathroom din ya fito yana taka kafar a waje wani irin tsansi ne ya d'ebesa shuuuu! Ka k'afan sa yayi tare da fad'uwa k'asa Timmmm! K'ugunshi ya bugu da k'asa wani irin kara ya tsake yna mai furta innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n!!!"
Zaro ido Fatu tayi tace " Yaya daman kana cikin nan?" Sai a lokacin ya dawo d'aga duniyan d'aya lula domin bugun ya shigesa, kallonta yayi da idanunshi da suka fara tsauya kala daga fari zowa ja,
Kome kuma ta tuna oho sai ta tsake mopan dake hanunta ta fara kyalkelewa da dariya harda rike ciki tace " haba Yaya karka nuna ragonta mana, dan wanan zabewan da kayi ka wani zauna agurin ba zakayi saurin mikewa kaman wani SOJA ba"
Tsororo yayi yana binta da mugun kallo bakin cikin, b'acin rai,da kuna, duk ya had'a ya tasu masa, da sauri ya mike da zummar d'an kuta ya mata mugun duka inda take dariyar nan, towel din jikin shine ya kunshe, wani irin ihu Fatu ta tsake lkcn d'ata kelleshi, rinshe idanunta tayi tace " Yaya tsirara kayi a gaba na ko kunya baka ji"
Ai kuwa sauri jan towel din yayi ya fad'a bathroom yana mai jin haushin kanshi mesa ma ya kawo yarinyar nan part d'inshi"
Fatu kuwa tana jin shigan sa toilet ta bud'e ido d'aya ganin baya nanne ya tsata bud'e idonta da sauri ta dauki sandan mopa da bokiti ta fito parlor ta ajiyeshi tabar part d'in domin tasan in ta tsaya ma jikinta ne zai gaya mata tunda har ta ganshi ba k'aya a jikinshi, kome ta tuna kuma oho sai ta dafe kirji ta tace " hmhm Allah tsare ni da tsake yin arba da wanga abu" (Niko nace kome Fatu ta gani ohoo 😂)
Direct d'akinsu ta shiga ko sallama batayi ta kwanta a kan gadon ta, tayi shiru tana maida numfashi"
SONA dake kwance tana kallone tace " me ya faru Fatu na ganki haka ko dai ya dukeki ne?" Hmmm bari k'awai kedai ai indai ta dukane sai dai mu duki juna, amma ta wanan hanyan ai sai na mutu ina tsake arba dashi"
SONA da bata gane zancen ba sai k'awai tayi murmushi tace "wlh kedai Fatu a koi ki da tsakarci wlh"
Saif kuwa ya dad'e a tsaye kafin yayi wanka ya fito a hankali kar ya kuma fad'owa"
Bin d'akin da kallo yayi ko ta ina kafin yace " wanan² yarinyar idan na k'amata sai naci gidan su kuwa, gaban dressing mirror ya tsaya ya gama goge sumar kansa yyi dryer dinsa yayi k'yau kaman balarab'e, bodylotion dinsa ya shafa had'e da feshe jikinshi da turarunruka masu sanyi k'amshi na kwantar da zuciya, dakawa yayi ya bud'e drawer dinsa ya Zaro riga da wando na shanda milk color ya sanya a jikinshi, agogo ruwan gold ya d'aura a hannunshi, ya dauko takalmi shima milk color ya sanya tare da hula color gold ya dauka a kansa wani irin bala'in k'yau ya kara, ga lailaisar sajen dake kwance akan fuskan sa baki kirin' sai shekin da yake,
Kara feshe jikinshi da turarunruka ya tsake Yi, wayoyinsa ya dauka ya fito d'aga d'akin"
Tunda ya fito yake bin ko ta ina na parlor da kallo yake girgiza kai k'awai yayi ya sauko parlor k'asa, bai tsami ko waba hakan ya tsashi fitowa direct parking space ya wuce, wani had'add'en faran MOTA ya shiga yasa mata key, Baba mai gadi ya bud'e masa get ya fita, wayan sa ya dauka ya kalle address din da Ruky ta kai koma sa, domin yana son zai fara zuwa company kafin ya wuce inda ta aiko masa address din"
Bangaren Ruky kuwa suna gama mgn da Saif, ta mike ta sauko parlor k'asa daman tana kwance ne a bedroom dinta"
Antyn ta samu zaune a parlor ita da Aminiyar Asma'u suna hira, ta sallama ta karaso inda suke ta zauna a'kan kujera tare da cewa....!
Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰🥰❤️
Msr Ahfat ce ✍️
👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
I just published "page 13" of my story "MIJIN YARINYA". https://www.wattpad.com/1175817772?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Asfats&wp_originator=T%2B%2B2BRf9PXkrhw%2F5QzEG3TTzTWxeklv8OpBjNT46AAjVvqFd4knQhccIuyoMTtRxfpIgTlNKzvdP%2FbHxRAPTBZx%2BZRlG2xHkiZe1hbYqjPUycMl3M%2B7%2FgSEQjZBR8pq8
https://chat.whatsapp.com/FrxF1JdPpOYFYqFAUQdcvC
Page 13
____________________ Ta karaso inda suke ta zauna a'kan kujera tare da cewa" Anty ina da bakon da zai zo yau"
Kallonta tayi tace " bako kuma?" Eh Anty zai zone ya gaishe ki, murmushi tyi tace " okay Allah ya kawo shi lafiya, Amen ta fad'a tare da mikewa ta haura sama"
Binta da kallo sukayi Hajiya Asma'u tace "wace ce wanan kuma"
K'anwa tace" okay kice surkin kine zaizo kenan"
Hmmm ba wani surki baki san Ruky da samarin banza dana wofi bane shiyasa kika ce haka"
Zai iya yuwa kuma wanan da gaske take baki ganta ba har wani rawan jiki take ba"
Toh shikenan Allah yasa da gasken ne da nafi kowa murnar haka, hiran su sukaci gaba dayi abunsu"
Bedroom dinta ta koma, k'ayan jikinta ta cire ta fad'a bathroom don wankan yau na musan man ne, ta dauki 30 minutes a toilet tana wanka, kafin ta fito d'aure da towel, gaban dressing mirror ta tsaya tana goge jikinta tana kallon fuskar ta cikin mirror bodylotion dinta ta dauka ta fara bin jikinta dashi tana shafawa a hankali, simple make Up tayi a fuskar ta ba laifi tayi k'yau, wani duguwar riga ta dauka na atamfa golden and blu color ta sanya d'inkin d'aga sama har k'asa duk rigar ya matse ta d'aga sama har k'asa, d'aura dan kwalin ta tayi ta feshe jikinta da turarunruka masu k'amshi, kallon fuskar ta tayi cikin mirror din ta tsaki wani k'aya tanciyar murmushi yau dai ranta fes, takalmin ta ta sanya, ta fita d'aga dakin, direct parlor k'asa ta sauka ta zauna a'kan kujera tare da kiran zulai me aiki ta kira tare da bata umarnin ta gyara mata parlor bakin ta kunna turaren wuta"
**************Bangaren Saif kuwa direct company ya fara zuwa office dinsa ya shiga wasu file's ya dauka don zanyi aiki a'kan su domin yana so d'aga gobe ya fara shigowa aiki"
Fita yayi ya shiga motan sa bai tsaya ko ina ba sai wani babban super market ya tsaya, shopping ya shiga yayi sanan ya wuce gidan su Ruky, yana isah bakin get din ya kirata, Ruky dake zaune a parlor duk ta gagu ta ganshi, wayar tane yayi ringin da sauri tyi answering din call din " hello" sweetheart ka iso ne"
Yace " eh ina bakin get"
Okay gani nan zuwa, kashe wayar tayi da sauri ta fito waje, me gadi ta fad'a mishi ya bud'e get din, da sauri ya bud'e mishi get"
shigar da Motan sa yyi tun kafin ya k'arasa yin parking ta kara so wajen, Ya parking ta bud'e mishi kofar tanà tsakar mishi murmushi, da kallo ya bita dashi d'aga sama har k'asa, ko gele bata yafa ba, lumshe idanshi yayi lkcn da idanunshi suka sauka saman kirjinta dake bud'e, bud'esu yayi sai kuma ya tabe baki, murmushi ta tsakar masa, shima murmushin karfin hali ya mata, fitowa d'aga motar yayi Yana fita ta wani rungumeshi tanà sauke ajiyar zuciya"
Tureta yayi d'aga jikinsa cikin b'acin rai yace " baki da hankali ne?"
Murmushi tayi tace " Am very sorry wlh nayi missing dinka ne sosai wlh ta fad'a cikin shugub'e Fuska"
Bece komai ba sai ma had'a fuskan da yayi, ganin ya d'aure fuska ne, ya sata fara bashi hakuri don tasan mgn nan sa, yanzu sai ya fasa shiga cikin ma"
Gaba tayi ya bita abaya suka shiga parlor din da sallama suka shiga ciki, zama yayi kan kujera, zama zatayi a kusa dashi wani kallo ya jefa mata d'aya tsata mikewa ta koma wani kujeran ta zauna" zulai me aiki ne ta shigo parlor ta gaishe shi, tare da jera masa drink da dai sauran abun motsa baki a table din dake gaban shi"
Kallon Ruky yayi yace " kira Anty mu gaisa sauri nake" haba dear yaushe kazo da zakace sauri kake?"
Tsaki ya danyi yace " idan bazaki kirata ni zan tafi ya fad'a tare da mikewa, da sauri tace " please don Allah ka zauna bari na kirata"
Haurawa saman tyi bata jima sosai ba suka fito da Anty, zama Anty tayi tare da masa sannu da zuwa" murmushi yayi ya dan rintsina ya gaishe ta yace " ya mukaji da hakuri kuma Allah ya mishi rahma" bata gane mgnr da yake ba ya sata tambayar sa, wayen kuma ya rasu?" dago da idanunshi ya watsa ma Ruky wani kallo d'ake zaune taka sa cewa komai sai sunkuyar da k'anta da tayi"
Kallon Ruky tyi tace " cewa fa kikayi zai zo ya gaishe ni me kuma ya kawo zancen mutuwa a gaisuwa?"
Saif ne yace " don Allah kiyi hakuri cemin tayi an musu rasuwa shiyasa nazo gai sheki, yana faɗ'an haka ya mike ya fice d'aga parlor, da sauri tabi bayan shi"
cikin b'acin rai ya fita d'aga parlor, direct inda yayi parking dinsa ya nufa bude Motar sa yayi zai shiga tayi saurin kara sawa ta rike morfin Motan tace " don Allah kayi hakuri wlh kaunar kace tasa na maka Karya nasan idan ba haka nayi ba bazan samu ganin kaba, na baru k'asa ta sbd k'ai ai yaka mata ace yanzu ka tabbatar da gaske sonka nake, ka amince dani nasan ni mai laifi ce a wajen ka ina rukun afuwan ka please ta fad'a hawaye nabin kuncin ta"
Cikin kunan rai yake kallonta, yace " a hakan kike cewa kina sona?" Kema kinsan ba abunda na tsana k'amar karya" kara marairai cewa tayi masa, sai kuma yaji tausayin ta, domin a rayuwan shi baya son ganin mace tana zubar da hawaye, balle kuma hawayen a kansa take, yace