Showing 21001 words to 24000 words out of 30491 words

Chapter 8 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel

" okay ba laifi Amma for the last wining bana son haka, murmushi tayi tace " insha Allah bud'e Booth shi ya bud'e tare da bata shopping din d'aya mata" karb'a tayi bata godiya tace " tafiya zakayi?" Ehh sauri nake daman sbd cemin da kikayi..saurin daka tar tashi tayi tace " okay thank you so much naji dad'in ganin ka sosai, idan ka tafi kuma sai yaushe?"
Kallonta yayi yace " No Ruky bazan miki karya ba ki fitar da soyayya ta acikin zuciyar ki domin ba soyayya bane a gabana, yana faɗ'an haka ya shiga Motan shi yabar gidan, da kallo ta bishi kafin tace " ai kuwa dole sai ka Soni in kuwa baka Soni ba bawata ya mace da zan bari ka sota, tana fad'ar haka ta shige cikin gidah"

************** Direct gida ya nufa yana isah hon yyi mai gad'i ya bud'e mishi get ya shigo, parking yayi ya shige cikin gida a parlor yayi sallama ba kowa sai Fatu dake zaune saman kujera tana kallo, amsawa tayi domin bata san shine ba , suna had'a ido dashi da  sauri ta mike da niyar  guduwa da zauri yayi charaf ya d'anko ta da karfi, sanda tayi yar kara, yace " wa na kama?"
Ko karin kwace k'anta take  tace "ni ka tsake kar ka jamin masifa da tsakiyar ranan nan"
kara matseta a jikinshi yayi yace " idan naki fa me zakiyi sarkin rashin kunya?"  Waro idonta tayi tace "
Don Allah ka rufa min asiri ka tsakeni kar Momy ko SONA su gan mu haka ace iskanci mukeyi" daman Inna tace min duk wanda  na miji  ya tab'ata  to fa iskanci ne"  k'a tsakeni bana son yin iskanci yanzu sai na girma"
Baganar tanma dariya taso bashi amma sai ya basar ya murtuk'e fuska yace " sai kin girma ko?" D'aga masa kai tayi, yace " kice kedin yar iskace kenan ban sani ba?"
Ya fad'a tare da murde mata baki da karfi, don Allah k'a barni karka kashe ni, tun banyi iskancin ba,  naji ana cewa iskace nada dad'i sosai, kaga ni kuma ina son  abu mai dad'i wlh"
Wani bakin ciki ne ya k'amashi d'aya tsaya yana mgn da mara hankali" cikin haushi ya kara burde bakin ta yace " yanzu kuwa zaki ga iskanci mara kunya k'awai" janta ya farayi har suka isah part dinsa, yana jinta tana cewa" bafa yanzu nace ma zanyi iskanci ba, ance yara basayi sai manya"
Bai kolata ba ya shiga da ita parlor shi yayi wurgi da ita sanda ta buge akanta da kujera" da gowa tayi tace " wanan ne iskanci indai haka ne wlh na gomma ce na mutu banyi shiba"
Harara ya watsa mata yace " dan gidan ku wama zai yi iskanci dake kazama irinki"
Tace " toh yanzu idan za'a fara iskancin ta yay ake farashi kaga nima yaba in kwaya ko"
B'ulalan d'aya dauko ne ya zuba mata a bayan ta, wani Ihu ta tsala tana cewa wayyo Allah Inna zai kashe ni d'aga cewar k'awai ya kwatan  ta min yanda ake iskanci"
Rufe min baki mara kunya banza kinga ida kika bata nan duka sai kin gyara shi sab wlh"
bin ko ina na parlor tayi da kallo, kallonshi tayi tace " wlh bazan iya ba k'asa a share maka mana kaga ni yarinya ne bazan iya wanan aikin ba sai manya"
Fuska murtuk'e yace "ba kece.....!

Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰

Mrs Ahfat ✍️

👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Msr Ahfat

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 14

____________ Murtuk'e fuska tayi yace "ba kece kikace kina son kwayun iskanci ba?"
Ai duk wacce ta iya mgn haka dole kuma ta iya shara, dan gidan ku d'auki tsinsiyan nan ko na Karya ki gida biyu mara hankali k'awai"
Ya tsina fuska tayi tare zunburu baki tace" Allah bazan iya shara nan ba ka tausaya min ka barni na huta, wlh wand'a nayi dazun ma sai k'aji yanda jikina yyi tsami, jikina duka ciwo yake min"
Da K'auye nake d'a yanzu Saude tanamin tausa wlh"
K'o  zaka min tausan ne kona samu saukin jikina, ta fad'a tare da rike gugunta tace 'washhh Allah na gaji sosai, k'amar bacci² ma nakeji wlh"
Ka mgn yayi sai binta da kallo yake zuciyarsa banda ta fasa babu abinda take, haushi da bakin ciki duk ya cika shi,
Kallonshi tayi tace" tausan zaka minne naga sai wani bina da kallo kake ka k'amar sabon maye"
Murmushi mugunta yayi Yace "tausa k'awai kike so?"
Yace"Sosai zaka minne?" Wlh da kuwa taimaka min sosai k'aga ma sai na babban ce tausan  K'auye d'ana birni wanne yafi dad'i"
Yace " okay"
Ai  kuwa batayi auni ba taji Saukar b'ulala ajikinta, k'urma uban ihu tayi tace" tausa fa nace kamin bawai ka kashe niba"
Yace " No tausa zan miki sai ki tattance ko?"
Yaci gaba da zabga mata b'ulala,
Gani da gaske yake sai ya kasheta anan  ba wanda ya sanine, zagaye parlor ta fara yi tana k'urma ihu wayyo Allah, taimako jama'a za'ayi kisan a gidan nan, taimako² b'acin rai ne ya k'ara kamashi yaci gaba da zabga mata b'ulalan, yana cewa ba tausa kike so ba?" Yau sai naga me kwace ki ai"
Cikin kuka tace" don Allah kayi hakuri tsubur baki ne, yasa ni cewar kamin tausa"
Be kulata ba yaci gaba da zabga mata b'ulalan suna zagaye parlor"
Momy da SONA ne suka k'araso cikin parlor da gudu, domin ihun da Fatu take ya karad'e gidan gaba d'aya"
Tsawa Momy ta d'aka mishi tace " baka da hankali ne Saif?"  Ko kasheta zakayi?"
Cak ya tsaya
Yace "No Momy ki d'uba ko ina na parlor nan kiga yanda ta batashi, bama nan kad'ai ba har cikin bedroom bata bari ba sanda ta b'ata, gashi sai fad'amin   wani banzan maganganu take"
Sai a lkcn ne Momy ta lura da inda parlor  ya koma duk a hargitse K'ota ina"
Fatu d'ake boye b'ayan SONA tanà shenshekan kuka tace "Karya yake Momy d'aga k'awai nace masa yamin tausa, shine fa mai makon naji tausa sai naji saukar b'ulali ajikina"
dariya SONA tayi tace" haba bro's d'aga tausa sai ka tausas'a mata jiki da duka"
Kusan dry abin yaba Momy tace" Ashe duk abunda ya miki ke kika wayowa kanki"
Turu baki gaba tayi batace komai ba"
Kallon Saif Momy tayi tace " last warning ka sake dukar yarinyar nan sai ranka ya b'aci"
tana fad'ar haka ta fice d'aga parlor ta barsu tsaye"
dariyar ta SONA ta had'eye ganin Yaya nata yanda ya murtuk'e fuska, jan Fatu tayi sukabi b'ayan Momy, kafin su fita sanda ta masa Gwalo tare da burgud'a masa baki"
Ta kaici da b'acen rai, da bakin ciki ne ya k'amashi, ji yake k'amar ya mutu,
  ficewa yyi d'aga parlor direct parking space ya wuce shigewa Motan sa yayi yabar gidan"
*******************A parlor suka tsami Momy zaune saman kujera, kara sawa sukayi suka zauna, kallo Fatu Momy tayi tace" yata na nimi wani Alfarma a wajen ki zakimin?"
Sunkuyar da k'anta tayi tace" ki fad'i kome zan miki ba sai kin nemi wata Alfarma ba"
Murmushi tayi tace" ina son ki fita d'aga harkan my son, idan ya saki wani abu ki masa idan kuma ya tsaki abunda bazaki iya ba ki fad'amin"
Kuma d'aga yau karki sake ce babba yayi k'arya kinji ko?"

Fatu tace " insha Allah Momy zanyi duk abunda kika ce"
Murmushi jin dad'i tayi tace" ki shirya d'aga gobe zaki ringa tafiya islamiya SONA, kafin ki shiga school, ina son ki mai da hankali sosai kinji diyata"
Murmushi tayi tace" insha Allah ngd sosai Allah ya kara girma, Amen ta amsa dashi tace " toh idan kun huta SONA kuje da ita ku gyara masa part dinsan, tunda baya son mai aiki suna shigar masa part"
Okay Momy SONA ta amsa mata dashi, mikewa tayi ta haura sama"
Kallon Fatu SONA tayi sai kuma ta fashe da dariya tace" gaskiya Yaya ya iya tattausa jiki fa"
Shugub'e Fuska tayi k'amar zatayi kuka tace" Allah bana son mgn d'ake"
Ohhh! Sorry dear tashi mu tafi mu gyra barnan da kikayi, mikewa tayi suna tafiya tana k'ukbure²"

Direct gidan su Hafiz ya wuce, hon yayi a bakin get, lekawa me gad'i yayi ganin Motan Saif ne ya sashi bud'ewa da sauri ya shigo, parking yayi ya fito suka gaisa da Baba me gad'i, ya wuce part din Hafiz, a bakin parlor yay knocking, bai jira amsa ba ya shigo ciki, b'akin shi dauke da sallama, ciki² iya lips dinshi ya tsaya, idan ba kunnen maciji ne da kai ba bazaka jiba"
Hafiz dake zaune saman kujera ya d'aura kafa d'aya kan d'aya yana lasar wayar sa, d'ago da idanunshi yayi ya kallesa tare da tsakin murmushi yace "wata sabon gani, yau kai kaine agidan namu?" 
Banza yayi dashi bai ce masa komai ba,ya zauna a'kan kujera"
Murmushi yayi tare da mikewa ya d'auko mishi drink da ruwa me sanyi da cup ya ajiye masa a gaban, daukan goran ruwan yyi ya kafa a bakin shi sanda ya kusa shan rabi kafin ya sauke yana sauke ajiyar zuciya"
Murmushi Hafiz yayi yace " ya akayi a minina yau kuma waya bata maka rai ne haka?"
Numfashi ya tsauke yace " wlh yarinyar nan sai na k'arai rayata, zannu na mata ita din k'aramar mara kunya ce"
Dariya Hafiz yayi yace " wace yarinya ce ta b'ata ma rai yau kuma?"
Hmmm bari k'awai wata village girl ne ta ba....!

Kuyi hakuri wlh nayi typing sai ya goge shiyasa kuka samu guntun page

07061204735

Msr Ahfat ✍️
[1/21, 8:32 PM] +234 706 120 4735: 👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Msr Ahfat

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 15

______________  Wata village girl ne take bata min rai wlh sai ta gane kuskuren ta, zata san dani take zancen, Ya fad'a Yana me  fuszar iska d'aga cikin bakinsa"
Hafiz dake zaune ya zuba masa ido yana kallonsa ne yace" come down my Man! Yanzu dai a ina ka hadu da yarinyar da har ta maka rashin k'unya?"
K'uma rashin k'unyan me taimaka har haka?"  Ya dauki 5 second kafin ya bude idanunsa d'aya lumshe su yace " she is my wife" Zaro ido Hafiz yay yace" What k'asan me kake fad'a  kuwa?" Matar k'afa kace?"
Yaushe kayi Aure ban sani ba?"
a lkcn d'aya ya jira masa tambayan"
Dan cije lips dinsa na k'asa yayi Yace " yes" dawowa na d'aga America kenan Dad ya samu zuwa 'Kauye toh a nan ne aka haduni da ita,
Labarin kumai ya fada mishi har abunda Fatu ta masa ya bar gidan"
Dariya Hafiz ya fashe dashi har yana rike ciki, yace " are u series Man?"
Wani banzan kallo ya wurga mishi yace " au dariya ma na baka?" Toh ba d'uleba yarinya tace ma tanà bukatar ka mata tausa, ka tsaya kana kallonta haba gaskiya baka kweita Mata ba" tsaki Saif yayi Yace "  Allah ya tsare ni da tab'a yarinyar da bata kai ko 15 yrs ba,  me zanyi da ita ai wanan ko kwaila bata kai ba, zaka wani ce na mata tausa da alama k'ai ma kanka ba daya ba, ya k'arasa mgnr da jan dogon tsaki"
Waro ido Hafiz yay yace " kana nufin bata kai ko 15yrs ba, take wanan mgnr gaskiya wanan shi ake kiran MIJIN YARINYA wlh, gaskiya abokina dole sai kayi hakuri sosai k'a kai zuciya nesa wlh"
ya fad'a yana danne dariyar dake cinsa domin yanda yaga abokin nasa ya had'a fuska tamau"
Wata uwar harara Saif ya watsa mishi yace " dole kayi dariya ai, tunda ba kai akama hakan ba,  wlh idan kayi sai nasa Mami tama Auren dole kaima kaji yanda akeji,
Rufamin asiri kar Baby na tajika" harara ya gaila mishi yace " wlh nifa ko kallon yarinyar Nan nayi sai naji raina ya baci"

Dariya Hafiz yayi yace "  duka a cikin sone,
ni dai shawar da zan  baka shine kayi hakuri  kabi a sannu wlh kar wata ran kazo kana d'ana tsani"
Ka rungume kaddara my Man!, kuma ka rage wannan girman kai da miskilancin naka" kayi wa iyayenka biyayya,wata ran zakayi alfari da hakan, lkcn da kuke shan love dinku"
Allah ya tsauwake naso wanan k'azami yar  K'auyen har nayi love da ita, Mata masu aji ma basa gabana  balle dak'ik'iyar kauye"
Hmmm Malam abi dai a sannu kar wata ran azo ana neman taimako, wlh nima lkcn ina fama da nawa Baby bazan saurare kaba nima ina ta kaina"
Banza yayi dashi ya lumshe idanunsa,yana sauke ajiyar zuciya k'amar wanda yayi wasan tsere, sun dad'e a zaune kafin Saif yace " nidai zan wuce bari na shiga na gaida Mami na wuce ya fad'a yana kokarin ficewa d'aga parlor, da sauri Hafiz ya tashi yace " au fushe zakayi dan na fad'a maka gaskiya, toh Allah huci zuciyar ka,nidai fad'a maka gaskiya nake kabi asannu, Please ka bar zancen nan ya ishene haka"
Murmushi k'awai Hafiz yay suka wuce part din Mami, a zaune suka tsameta a parlor tana hakince Saman kujera, tanà kallonsu tace " ah ah sannu da zuwa mutanen America, yaushe a gari?"
Murmushi yay yace " ina kwana Mami, Lafiya k'alau son ya gida?" Alhamdulillah, masha Allah hira sukayi kad'an suka sallame ta suka fito, har parking space Hafiz ya rakashi, shigar Motar sa yayi Hafiz yace " ka gaida min da Amarya sai nazo gaisheta ka gaida min  dasu Momy"
Tabe baki yayi yaja motar sa ya fice d'aga gidan"
**************** Bangaren Ruky kuwa cikin gida ta koma, tanà shiga parlor ta sami Antyn ta zaune Fuska d'aure, tanà ganinta a fusace tace " ke Ruky uban wa ya rasu da zaki k'awumin wani ya gaishe ni?" mesa  baki da hankali da kamun kai ne Ruky?" Kisani fa yanzu kin girma bai kamata kina wasu abubuwan a matsayin ki na mace ba"
Kallonta Ruky tayi sama da k'asa ta tabe baki tace " haba Anty don mutun ya gaisheki k'awai shine kike daga min murya haba Anty, shine fa wanda zai zama tsurkin ki garama ki shirya, tanà fad'ar hka ta haura sama abunta da k'ayan yakin da Saif ya bata" binta da kallo Anty tyi tace " Allah ya shiryeki Ruky ya kawo wanda zaiyi mgnin ki, tana fad'ar haka ta mike ta shige kitchen tanà girgiza kanta"
bedroom dinta ta shige k'ayan dake hannunta ta zubesu kan bed dinta ta zauna gefin bed din, tunani ta shiga yi tayaya zata samu Saif a hannunta, domin ta halin yay sai ta Aure she ta d'andani zumar sa"
Tunuwa da wata kawarta da sauri ta dauki wayarta ta fara d'anne²  number Sumy ta dubu acikin wayarta ta fara,  kiran number, ringin biyu Sumy ta dauki wayar tace " yar duniya kina duniyar nan?"
Murmushi Ruky tayi tace " inanan wlh yanzu dai idan kina gidah gani nan zuwa akoi mgn"
Murmushi Sumy tayi tace " da gaske toh ina jiranki yar duniya"
Kashe wayar tayi tare da mikewa ta dauki key din Motar ta fice d'aga gidan, Anty dake kitchen taji fitar ta girgiza kai tayi tace " gaskiya zan iya zama wanan yarinyar kuwa dole nasan abunyi"
*************bangaren su Fatu kuwa gyara komai sukayi suka share, sukayi mopping ko ina sai kelle yake"
Turaren wuta suka kunta tare da fesa mishi air frishner, ko ina sai k'amshi yake, Fatu tace " gaskiya ko ina yayi k'yau sai k'amshi abun burguwa"
Murmushi SONA tayi tace " kinga ai yanda mukayi d'aga yau idan ance miki ki gyara haka zakiyi"
Murmushi  tare da d'aga kai alamar eh, rufe part din sukayi suka kuma nasu, direct bedroom d'insu suka wuce, wanka SONA tayi hadayen Alwala ta fito, ta tada Sallah"
Fatu kuwa Alwala k'awai tayi² Sallah"

Bayan sun gama sallah shiryawa SONA tayi saf Fatu na kallonta, kallon  Fatu tayi tace " kema tashi kije kiyi wanka,mikewa tayi tana k'unkuni ta wuce toilet, wanka tayi SONA ta gyara mata gashin kanta tayi sosai, ya kuwa fita sosai yayi k'yau sosai, Fatu dai sai murna take don abun ya bala'in burgeta, SONA ma tayi ta yabawa da irin sumar ta, k'ayan da Momy ta bata dazon ne, ta futar mata wando jeans blue da T_sheet pink color sanyawa tayi sosai tayi masifar k'yau bazaka taba tsamanin Fatu bace, domin Fatu akoi ta k'ira mai kyau gata fara sol, duk da cewa bata da shekaru amma fa tana da tsaye, duk abunda tasa k'yau yake mata,
Wayar ta SONA ta dauka ta musu picture masu k'yau"
Suna gamawa suka fito parlor, suna fita  Momy dake kan kujera tanà lasar wayar ta,ta d'ago da k'anta ta kallesu, mamaki tayi ganin Fatu yanda tayi k'yau kamar ba itaba, murmushi tayi tace " wow my daughter gaskiya kinyi k'yau sosai, sunkuyar da kanta k'asa tayi tna murmushi tace "nagode sosai Momy Allah ya Kara arziki da girma"
Murmushi k'awai tayi taci gaba da kallon wayar ta, zama sukayi suka fara hira da suna, inda suna ke kwaya mata wasu abubuwan"
Saif ne ya shigo parlor da sallama, amsa masa sukayi, d'ago idonsa da yayi sukayi ido hudu da Fatu, lumshe idanunsa yayi lkcn da idanunsa suka masa arba da.....✍️

Share fisabilliah Habibaty 🥰
[1/21, 8:32 PM] +234 706 120 4735: 👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Msr Ahfat

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 16

_______________________ Lumshe idanunsa yayi lkcn da idanunsa suka masa arba da wata beautiful girl tanà  tsakin murmushi, d'an ware idanunsa yay don tabbatar da a'bunda yake da gaske ne  kodai gizoce idonsa ke masa"
Ya dauki 5 second yana kare mata kallo,
Ganin da gaske itan ne ba idanunsa bane, ya tsashi jan tsaki, d'aya sa Momy juyuwa tanà kallonsa tace " lafiya kake kuwa?"
Fuska a d'aure yace " ba komai, wucewa part dinsa yayi da mamaki a zuciyar sa na ganin yanda Fatu ta canja  masa lkc daya tayi kyeu k'amar ba itaba, wani zuciyar yace masa yarinyar da ko kwaila ma bata kai ba kake wani tunani akanta,tsaki yaja a fili ya furta Allah tsare ni, yana isah ya bud'e part dinsa wani k'amshi ne ya bugi hancinsa, Lumshe idanunsa yayi tare da bud'esu yana bin ko ina da kallo murmushi k'awai yayi ya wuce bedroom dinsa, k'ayan jikinsa ya rage ya d'aura towel ya shige toilet, 30 minutes ya dauka a toilet din ya fito d'aure da towel, gaban dressing mirror ya tsaya gyara suman kansa yayi ya dauki body lotion dinsa ya shafa a jikinsa tare da feshe jikinsa da body spray sai k'amshi yake, wardrobe dinsa ya bud'e three Quarter da T_shirt ya fitar ya sanya a jikinsa wanda yay mugun amsar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login