Showing 9001 words to 12000 words out of 30491 words
Chapter 4 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel
itama a Nigeria zata kwanna tunda akoi yar Uwar ta tana Aure a can ta saki ranta sosai suka more daren su cikin farin ciki...
Washe gari ta riga Iman tashi don haka ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta shirya daukar handbags dinta da key din motar tar ta fice daga gidan...
Inda ake yankar ticket ta wuce ta yanki ticket din tafiya Nigeria" direct gidan su ta wuce tana isah ta danna wa mai gadi hon, da sauri ya tashe kasan cewar sa yasan hon din motar ta, bud'e mata get din yayi ta shigo, tana parking cikin gida ta wuce part din Anty Yusra ta shige tana shiga parlour ta sameta zaune cikin daya daga cikin kaya tantun kujerun parlou tana lasar wayar ta da hannu daya, dayan kuma tana ri'ke da karamin cup tana sha.. ko sallama batayi ba tazo zata shige ta kenan, Anty Yusra tace "ke Rukayya baki san yanda ake sallama bane zaki shigowa mutane kai tsaye haka?" Kallon kin raina min wayo ta mata tare da cewa "keeeee! Matar nan ki fita daga idona na rufe ba ruwanki da shigowa ko nayi sallama ko kar nayi sallama wannan ruwa ne ba naki ba, don haka banason sa ido mutun da gidan Yaya yan sa bazai yi abunda yake so sai an wani taku ra masa,tana fad'ar haka ta shige cikin bedroom dinta"...
Girgiza kanta tayi tace " Allah ya shirye ku yaran zamani sai Addu'a"
Tana shiga direct gaban wrdp dinta ta tsaya budeshi tayi ta dauki akwatin ta fara zuba kayan ta a ciki sanda ta dauki duk abunda zata amfani dashi duka sanda ta gama ta rufe a kwatin ta wuce toilet ta sake yin wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na a tampa sai k'amshi take zubawa fuskar ta dauke da make up mai shegen kyau, daka aganta sai dauka mutumiyar kirki ce wlh..
A kwatin ta ta janyo ta fita dashi parlon, ajiye a kwatin tayi ta wuce dining area ta jawo kujeran ta zauna ta dibi abinci ta fara ci sanda taci mai isar ta kafin ta dawo parlon ta zauna kan kujera tana jiran Yayan ta ya sauko sbd tasan baya fita office da wuri...
Ai kuwa bata dad'e da zama ba ya sauko shida Anty Yusra, kallon a kwatin yayi yace "wanan kuma daga ina?" Ruky dake zaune ne ta hada kafa daya kan daya ne ta mike tare da cewa "ina kwana Yaya" lafiya kalau Rukayya me ya faru kwana biyu baki kwana a gida?" Tace "wlh Yaya aikin ne ya mana yawa a office shiyasa bana samun lokacin da wowa yanzu haka ma Najeria aka turani wani aikin
"Najeria kuma Rukayya?"
Eh Yaya amma a gidan Anty Amina zan sauka"
Okay shekenan yanzu zaki tafi ko sai anjuma?" Eh yanzu karfe 10:00 jirgin zai tashi. Okay zan tura miki kudi ta account dinki wata kila zaki iya bukatar sa, murmushi tayi tace "thank u so much my brother Allah ya kara arziki da girma" shima murmushi yayi yace " Allah ya bada sa'a Allah ya kaiku lafiya, Amin ta amsa masa dashi tana jan a kwatin ta fita daga parlon...
Anty Yusra ce tace "haba sweetheart ya zaka bar yarinya nan ta tafi Najeria ita kadai ba tare da ka tambatar da gaske take ko akasin haka,kana ganin fa yau kwanan ta biyu bata dawo gidan nan ta kwana ba, tana dawowa kuma ta had'a kayan ta tace tafiya zatayi" numfashi yaja yace "kina nufin ba aiki take yi ba kenan wani abun daban take aika tawa kenan?" Tace "a'a ina dai nufin ka dinga sa mata Ido sosai da abunda take" kice zargin ta kike Kawai ba abunda kika iya sai sawa yarinyar nan ido, insha Allah ma ba abunda kike zargin ta dashi bane take" ganin abun zai jawo mgn tsaka nin su ne yasa ta sanja zancen mgn nar da wata..."
Tana fita daga gidan, direct gida Iman ta wuce tana parking ta shige cikin parlon, bata samesa a parlon ba hakan ya sata shigewa bedroom din, tana shiga ta ganshi gaban dressing mirror yana shafar mai, kara tsawa tayi ta karbi mai din ta fara shafa mishi, ta cikin madubin yake kare mata kallo daga tsama har kasa kafin yace "wanan wankan duka ina zakije haka?" Tace "tafiya ce ta kama ni" tafiya kuma a ina?" Najeria kasan akoi yan uwana a can tom akoi wacce ta rasu shine my brother ya turani gai suwar rasuwan, karfe 10:00 jirgin mu zai tashi"
Juyuwa yayi yace "da gaske kike ko dai wasa kike min?" Hmmm sweet kenan ka tab'a ganin na maka mgn nar wasa ne?" Yanzu ma sallama nazo muyi domin tafiya zanyi, dan Jim yayi na wasu mintina kafin yace "okay Allah ya kaiki lafiya, da Amin ta amsa mishe tana shafa mishi mai din tsanda ta gama ya mikewa tare da daukar kayan sa ya shirya sab kafin ya bude wani dorowa ya dibi kudi masu yawan gaske ya sanya mata cikin bags dinta" yana cewa " yaushe zaki dawo?" Uhmmm sai kayi kewata zan dawo"
Murmushi Yayi yace " uhmm ai ni ko yanzu ma banso ki fasa tafiyar ba, muje muyi breakfast sai na rakaki airport din ko" murmushi kawai tayi ya kama hannuta ya manna mata kiss akai suka fito parlon, dining area suka wuce zama sukayi suka fara cin abinci Ruky dai bata ci sosai ba sbd taci dazun, Suna gamawa suka fita daga parlour lokacin har 9:30 yayi direct airport kafin jirginsu ya tashi sanda suka tab'a romance na sallama kafin ta fita ta shiga jirgin har suka tashi kafin yabar wajen da kewar ta domin a iya matan da yake nema ba wance take masa yanda yake so kamar ta shiyasa yake sonta"...
**************************
Tunda suka dauki hanya SONA ce ki hira da Daddy batun kauye tana cewa "ita gaskiya tana son kauye sosai, Daddy kuwa sai murmushi yake yana bata yan da labarin kauye yake...Saif dake Drive yana jinsu ji yake kamar ya make ta wato kara zuga Daddy take don yace so dinga zuwa wanan shegeb k'auyen da ko hanyar kirki bata dashi"
Shi dai bai ce musu komai ba har suka isa k'auyen WANGARA k'auyen dake gefe da garin kano.. kwatan ce Daddy yayi ta masa har suka isah kofar gidan, ai kuwa suna tsayawa yara suka fara taruwa suna kallon su wayen ne zasu fito daga cikin motar, Daddy da SONA ne suka fara fita daga matar suka shiga cikin gida, Baffa dake zaune a zaure ne ya tare su cikin murna da farin ciki, cikin gidan suka shiga Inna dake zaune kan tabur ma tana tunanin ina Fatu ta shiga tun da ta aiketa da safe bata dawo ba gashi har rana tayi sosai... Tunanin ta tsayawa yayi lokacin da taji sallamar su Daddy, da sauri ta d'ago da kanta tana cewa "kamar muryar AMINU na nakeji Ko?" Dariya gaba dayan su sukayi Daddy yace "eh Inna ni dinne... Ai farin ciki gun Inna ba'a mgn dauko ta burma a cikin daki tayi ta shinfida musu suka zauna, SONA dake tsaye ta turu baki gaba tace "wato ma Inna baki kalleni ba sai Daddy" Inna tace "haba dai kawas ai ke na fara gani kafin kowa zoki zauna kusa dani, murmushi tayi ta karaso itama ta zauna a tabur mar da Inna take zaune akai"...
"Saif kuwa Sanda ya gera parking din motar kafin ya fito, shima ya shiga cikin gidan"
Shiga cikin gidan yayi da sallama abakin sa, amsa masa sallamar sukayi Inna wa nake gani kamar mijina ,Murmushi kawai yay ya kara so ya zauna a kan tabur mar gefen Baffa, kafin yace "eh nidin ne yar tsohuwa ai na zata idanun naki sun dai gani ashe dai da lafiyar su har yanzu" washe baki tayi tace "kaji ja'irin yaro idona ai yafi naka lafiya wlh, gaishe ta yayi ta amsa masa cikin farin ciki da wasa irin nasu na kakan ni, gaishe da Baffa ma yayi ya amsa masa, Inna ta kawo musu ruwa da abinci harda da men miyar fura Mai kyau ta ajiye musu a gaban su, Daddy da Baffa kam bayan sun gaisa suka wuce zaune gidan a can SONA ta kai musu abinci da ruwa da furan duka.."
Fatu da tunda ta fita ta kai aike gidan su Saude zama tayi suka fara ta wasan da Saude sanda taji cikin ta na qugen yunwa ne tace "gaskiya yunwa nake ji wlh kamar naci babu yanzu tashi mu tafi gida nasan Inna ta gama abinci sai muci"
Tom Saude ta amsa tashi suka fita daga gidan a hanyar su na zuwane suka hadura da Garba, Garba yace "Fatu wlh yanzu nan naga wasu mutane sun zu gurin Baffa kin gansu kuwa da wani katon Mota suka zo dashi, Fatu tace "da gaske kake ko kuma karya kake min?" Wlh da gaske nake idan kin koma zaki gani yana fad'an haka ya wuce a'bunsa"
Saude tace "kai da gaske ne fa, muyi sauri kar ayi bamu Fatu ta fad'a, ai kuwa run tumar na kare suka sai gida, suna isa kofar gida suka ga wata dalleliyar mota na tsaye, Fatu tace "ashe da gaske yake"
Shiga cikin gidan sukayi ko sallama babu Fatu na cewa "Inna yau kuwa su wayen suka zo naga mota a waje?" Domin bata kula ma da SONA dake zaune tana kallonta ba, Inna tace "baki mukayi baki gansu bane?"juyawa tayi ta Kalli SONA data kura mata ido tana kallonta, kallon tay daga sama har kasa tace "yan birni sannun ku da zuwa" murmushi SONA tayi tace "yaewa yar Kanwar mu, kara sawa kusa da Saif tayi dake zaune yana lasar wayar sa bai ma san ta kara sa kusa dashi ba, tace "Kai Malam bakajin ina muku sannu da zuwa ne ko dai kurma be Inna?" Jin wani irin tsami da doyi da yake jine ya tsashi daga da kansa ganin meke wari haka hada ido sukayi da Fatu tsaye gaban sa tana kare masa kallo, a hankali yace "me yake wari hakane matar naji gidan ta dauki wani kalan wari da tsami haka?" Daman haka kuke fama da wari a k'auyen nan?" Inna dai dariyar k'asa k'asa tayi domin tasan bai waci matsowar da Fatu tayi kusa da shine yaji tsamin jikinta" Fatu tace" kan uban can ni.....!
👯♀️🔥Toh fa ga Fatu ga Saif koya zasu kare, ko dai ko biyoni da ruwan comments❤️
Comments and share fisabilillah
👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
by Fatima Zahra (Maman Khalid)
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
*ALHAMDULILLAH ALLAH YAYI DAWOWA NA LAFIYA, INA GODIYA GA MASOYA NA, SOSAI DA SOSAI MASU KIRA DA WAEN DA SUKA KIRA BAN SAMU DAMAR DAUKA BA INA KARA GDY DA SOYAYYAR DA KUKA NUNAMIN,I LOVE U SO MUCH MY FAN'S*
(Not edited)
Page7
___ Fatu tace" kan uban can ni dinne nake wari?" Jin abunda ta fada ne ya sashe dago da kansa yana kallon tsabar rashin kunyan dake da mum kwanyar ta"
Inna ce tace "haba Fatu baki ga baki ne ba?" Bana son sakarci maza wuce ki bani waje" Turu baki gaba Fatu Tay bata ce komai ta wuce dakin su Saude ta mara mata baya, suna shiga dakin ta zauna bakin gadon ta tana kunkuni wai yau har ita wani zai zaga akan wanka ai abunda bazai yuba kenan, tashi tay ta fara zagaye dakin, Saude dake zaune itama abakin gadon ta kalleta tace "tab! Lailai wlh wannan mutumin yayi mugun rai na miki wayu wlh, tab nikan kinji abunda ya fada miki kuwa?" Hmmm kawai Fatu ta furta taci gaba da zagayen dakin tana tunanin wani irin abune zata mishi wanda zai tsata ta huce akan abunda ya mata.ta dade tana tsafa da marwa kafin tayi wata muguwar murmushi ta zauna kafin tace "dauko mana abincin nan muci kar yunwa ta illa tani"
Tashi Saude tayi ta kawo musu abincin suka fara ci,sanda suka gaba kafin suka fito waje, suna fita basu tsameshi ba sai Inna da SONA da suke zaune suna hiran su ta kaka da jika"kallon Fatu SONA tayi tace "Fatu ba mgn ne?" Murmushi kawai tay ta zauna a gefin su amma bata ce komai ba, Inna ce tace "haba Fatu na miyen ne ya tsame ki naga sai had'a min fuska kike?" Turu da karamin bakin ta gaba tayi tace"fushe nake dake tunda dai kina jin wanan mutumin yana zagina ke kuma harda goya meshi baya, sbd kinga sun kawo miki Madarar ta birni, sai washe mishi baki kike" da kuwa Inna ta mata yare da cewa" shidin Yaya n kine ai kuma madaran ai kema za kisha,
Dariya SONA tayi tace"Fatu da Inna akoi drama"
Saif kuwa bayan Fatu ta shiga daki ne ya dubi Inna yace "wace mara kunyan ce wannan?"yarinya ne ba hankali kamar shedaniya"
Had'a fuska Inna tayi tace "idan ita shedaniya ce kai ma shedanin ne kenan domin ita din kanwar kace" kanwata fa kike ce fa Inna?"eh da mai k'a dauka?" Nifa bana son iskancin banza dana wofi daga zuwan ka kafara tsokanar ta ahakan har ku iya zaman inuwa daya don haka daga yau karta kara shigar tsapgar ta ehee" cike da mamaki yake kallon Inna kafin ya yace"Allah baki hkr matar"sai lokacin Inna tadan Yi murmushi tace" kamar ka damu da matar taka yaushe rabon ka da garin nan tun kana zanin goye, sai kuma lokacin da uwar ka AISHA tazo kuka kwana, lokacin gaka da kukan tsiya abu kadan kuka sai shar ban majinan da kake"ai kuwa dariya SONA ta kyalkele dashi tace" da gaske Inna don Allah bani labarin Yaya ya akayi"
Inna tace "kai 'yarnan ai baki sani ba lokacin da yake yaro a 'koi shi da kashin banza banza wlh abu kad'an ya tsake miki zawo ajiki, tsuliyar sa baya hutawa kamar famfo,dariya SONA ta fashe dashi har tace"da gaske Inna?" Hmm! ke dai bari kawai 'yar nan ai in fad'a miki....ai Saif bai bari ta kai gayin mgn ba ya mikewa tare da cewa"haba Inna yaushe nazo gunki da har kike bata wani lbr n sherme,kudai tsonfi ba abunda kuka iya sai bada lbr shirben banza dana wufe yana fadar haka ya fice daga wurin da haushen SONA ma data ce ta bata lbr n"
Inna kuwa lbr taci gaba da bawa SONA har lokacin da su Fatu suka fito daga dakin suka ci gaba da hira"....
Da d'an dare bayan sunyi Sallah i'sha Fatu da SONA sukaci abinci tare domin har sun fara tsabawa,suna gamawa Fatu ta mike tare daukar babban bokiti ta cika shi da ruwa da k'yar ta dauke she zuwa ta ajiye ta dawo da kinsu ta dauki tsoson wankan ta wanda ta boyeshi tun randa Inna ta tsaya mata, a cewar ta bazata iya goge jikinta dashi ba salon jikinta ya dinga mata zafi, dauka tayi ta tana fad'an har mu za'a gwadawa tsafta ta wuce ban dakin dashi.ta jima tana goge jikinta da tsoson sanda taji jikinta ya fara mata zafi kafin ta bari ta zuba ruwa ta fito, ji tay jikinta ko ta ina iska na shigar ta har wani lumshe idanu take domin wani irin bacci daya zo mata,sai dai kuwa yau baza tayi bacci ba domin da abunda ta gudurta a ranta, shiga dakin su tayi ta shirya cikin wata doguwar riga faran TAs ta fito ta sami su Inna na zaune a tsakiyan gidan suna hira harda su Daddy da Saif domin sun shigo cikin gidan, tunda ta zaune take bin Saif dake lasar wayar shi da kallon, suna hada ido ya wasa mata wani muguwar harara,sai murmushi kawai tay, da haka sukaci gaba da hira kafin kowa ya shige dakinsa in da Daddy zai kwana da Baffa Saif kuwa a wani dakin, Inna da SONA da Fatu kuwa daki daya suka kwanta"
Saif na shiga dakin tsanda ya karewa dakin kallon, karamin daki ne ba komai acikin sa sai kapet da kati far dake kwance an shinfida masa zanin gado Akai sai kuma fitillar da aka kunna masa adakin" karewa dakin kallo sab tare da tabe bakin sa a ransa ya cewa" gaskiya Daddy bai k'yauta mana ba yanzu a wanan dakin zai kwanta tsaki yaja kafin ya ciri kayan jikinsa yay yana son yin wanka gashi ban dakin ba cikin dakin yake ba sai ka fita dakin gashe kuma sanyi na busawa awojen ba zai iya yin wanka ba,haka dai ya shirya cikin kayan baccin sa ya kwanta a saman kati far dake dakin, Ba'a jima bacci yay gaba dashi domin gajiyar da ya debo"
Chan cikin dare tsanda kowa na gidan yayi bacci Fatu ta lallabo ta tashi ta dauki wani wani katon hijab din Inna fari ta sanya tare da barin dakin ahankali,bata tsaya ko ina ba sai kofar dakin da Saif yake ciki ta tsaya hade da baza dogon gashin kanta akan fuskar ta, tare da tura kofar dakin ahankali daman Ba'a kolle yake ba, Hango sa tay a 'kwance yana baccin sa hankali kwance, murmushi tayi ta karasa bakin kati far ta wani irin bugashi da karfi, ai kuwa a firgice ya bud'e idanunsa da suka masa nauyi, masifa zai fara abunda idanunsa ya ganine ya sashi furta innalillahi!" Lkc daya yaji gumu ya mugun k'etomar daga tsama har k'asa kar dai ace yau gamo yayi, domin Gani da yay yarinya a tsaye a gaban sa da fararen k'aya daga tsama har k'asa gashi baya kallon komai a jikinta harta fuskar ma a rufe yake da dogon gashi baki kirin'
Lokaci gud'a jikinshi ya dauki rawa domin ya rasa gane mutun ne ko Aljan"
Fatu kuwa ma 'kwalkule murya tayi ta dawor dashi na babban mutun tace" k'ai yaro! Mai ya kawoka cikin dakin nan?"
Saif d'aya gama rudewa domin a rayuwar sa tsoron Aljanu yake ko labarin su baya son ji" daka mata tsaya tay tace "me ya kawoka cikin tsansa ninmu?" Tsautsayi wlh nima kawoni dakin akayi wlh dan Allah dan Annabi kuyi hakuri wlh zan fita in bako waje"
Hahahahaha! Ai duk wanda tsautsayi ya kawo shi gunmu baya tab'a fita, sai dai muyi ferfesu da kai