Showing 24001 words to 27000 words out of 30491 words
Chapter 9 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel
jikinsa bakin sajen fuskar san nan a kwance' sai shek'i yake, k'ara feshe jikinsa da turarunruka yay, wayar sa ya dauko number SONA ya kira tanà dagawa yace" had'amin abinci ki kawo min, yana faɗ'an haka ya kashe kiran bejira cewar tab'a"
SONA dake kitchen tanà aiki da Momy"
Kallonta Momy tayi tace "had'a masa komai ki b'a Fatu ta kai masa, domin taji duk abunda ya fad'a k'asan cewar wayar a speak tasa"
Had'a masa komai tayi cikin tiren ta mikawa Fatu d'ake tsaye tanà jiranta zuciyar ta sai uku ²yake,tunawa da dukan da ya mata dazun, karb'a tayi ta fice d'aga kitchen din jiki ba k'wari ta nufi part dinsa"
************ Bangaren Ruky kuwa tanà fita direct gidan su Sumy ta wuce, tanà isa me gad'i ya bud'e mata get ta shiga, parking tay ta tanà fita d'aga Motar cikin gidan ta shige kai tsaye, sallama tay a parlor Sumy d'ake zaune ita kadai ta amsa mata tare da mikiwa da sauri suka rungume junan su suna dariya, Sumy tace " gaskiya nayi missing dinki sosai, murmushi Ruky tayi tace " Nima nayi missing dinku sosai, ina Ammi ko bata nan ne?"
Sumy tace" ba wani wlh yaushe rabon da muyi k'oda call ne, Ammi dai bata nan taje gidan Yaya lameer"
Lameer kuma yayi Aure ne?"
Eh Yayi bakin ki Auren saba ba, ta fada tanà hararan ta batare d'ata sani ba"
Kauda zancen tayi da cewa " yanzu dai mubar wanan zancen, nazone ki taimakamin ina cikin damuwa sosai,tabe baki Sumy tayi tace " wanan wacce irin damuwar ce haka?"
Wlh k'awata na kamu dason wani handsome guy ne, amma shi da alama K'ota² k'amar bai damu dani ba, nikuma gaskiya ina matukar sonshi ba kad'an ba, ina cikin wani halin wlh"
Murmushi mugunta Sumy tayi tace " indai wanan ne karki tsawa kanki damuwa" k'amar yaya karna damu?" B'ayan na fad'a miki shidin ba sona yake ba"
Ai wanan abu mai sauki ne indai kin shirya kina da money toh da kafar sa zaizo ya tsameki har inda kike"
A shirye nake wlh ko me zanyi indai abunda nakeso zan sameshi"
Toh kwantar da hankalin ki Yar uwa akoi wajen wani Bokan da zan kaiki a miki aiki, wlh aikinsa t'amkar yankan wuka ne"
Dan Ya tsina fuska Ruky tayi tace " nifa gaskiya kinsan ban cika son irin wadan nan abubuwan ba, amma idan bukata ta zai biya wannan ba komai bane zan iyayi"
Sumy tace " insha Allah zakiji dad'in aikinsa, kinga ma bari na dauki handbags dina sai muwuce, kafin Ammi ta dawo"okay" mikiwa tayi ta wuce bedroom dinta ta shiga tanà murmushin mugunta, handbags dinta ta dauka da wayoyinta ta sauko"
Mikewa Ruky tayi suka ficewa d'aga parlor tana bata lbrn Bokan, jin yanda take yabon sani ya sata jin karfin guiwa, shigewa Motar ta sukayi suka fice d'aga gidan suka dauki hanyar zuwa wajen Boka"
A hankali ta tura kofar parlor tashiga da sallama,
Yana zaune saman kujera yana aiki cikin laptop dinsa, d'ago da kansa yayi da niyar amsa sallamar sukayi ido biyu da Fatu da itama shi take kallo,
Tsaki yayi ya kauda kansa, ya amsa sallamar a dak'ile, yana ya musa fuska k'amar wanda yaga kashi"
Binshi da kallo take tana mamakin yanda yake ta wani ya musa fuska k'amar kashi yaga ajikinta, tabe baki tayi cikin borin rashin kunya tace " toh idan ka gama yasine ²naka sai ka fad'amin inda zan ajiye maka abincin" Asaman kaina zaki ajiye"
A fusace tace " nifa banson rainin hankalin kan nan ka fad'amin inda zan ajiyema,
Baice mata komai ba yaci gaba da abunda yake, harara ta wasa mishi tare da k'arasawa inda yake zaune ta ajiye tiren a saman table din dake kusa dashi" ta juya da niyar zata fice d'aga parlor, a hankali taji cool voice dinsa yana cewa " waye baki izinin fita ne"
Cak ta tsaya tare da juyuwa tace " ba sai an bani izinin fita ba, kafin na fita"
Fuska d'aure yace " uban wa zai bani abincin"
Yanda yayi mgnr sanda ta tsorata,
Batace komai ta dawo inda yake domin yadan bata tsoro, ganin yanda ya murtuk'e fuska kar ya tsake mata duka k'amar na dazun"
A hankali tace "Toh me zan maka?"
A tsayen zan fad'a miki abunda zakiyi, baki gaba ta turu tare da dan rintsina wa,
Murmushi yay wanda bai wuce saman lips dinsa bane yay idan mutun bai kola sosai ba bazai ce yayi ba,yace " had'amin abincin"
Ahade yake ta bashi amsa,
Okay dauko min ruwa a fridge, mikewa tayi ta dauko mishi ta ajiye masa a gaban sa, ta dawo gefinsa ta zauna tana kallonsa, ture laptop din gefe yayi ya fara cin abincin, bai maci sosai ba ya tura plate din gefi, ruwan ya dauka, yace " da idonki zansha ruwan?"
Mikewa tyi ta dauko masa cup dake zaune saman fridge din ta kawo masa, karba yay yazuba ruwan yasha, yace " dauko min drink wanda bai da sanyi sosai ba"
Tana k'unkuni taje ta dauko masa"
Cup din dake ahanunsa ya mika mata yace " bud'e ki zubamin"
Wani irin bakin cikine ya rufe ta, k'amar ta falle mishi mari haka takeji, cike da b'acin rai ta bud'e marfin goran da karfi, ai kuwa bata zubewa drink din yayi ajikinta har da shima sanda ya zube masa ajiki, saurin mikewa yayi don kar ya bata mishi jiki, Fatu kuwa a tsorace ta kuma baya,ai kuwa taka drink din d'aya zube tayi, baya tayi luuuu! Har zata fad'i kenan taji anyi saurin k......
Share fisabilliah Habibaty 🥰
👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 17
__________________Saurin k'amata yay ta fad'a jikinsa, wani ajiyar zuciya ta sauke, lkcn d'ata jita jikinsa, tsaki yaja had'e da tureta saman kujeran har goshinta ya bugu da kujeran, yace " ki wacce iriyar dak'ik'iya ce?"
Baki ganine da zaki bude burfin da karfi?"
Fatu dake goge goshinta da takejin yana mata radad'i² , a fusace tace "k'ai ma wani irin dak'ik'an cen ne sani zuba maka drink din, gashi yanzu k'asa duk jikina ya b'aci, sabar mugun ta irin naka d'uba yanda ka tureni saman kujeran nan har na fasa goshina, ni wlh bansan a inane ka dauki wannan muguntar ba wlh, anya kuwa a asibiti Ba'a canja wa Momy d'aba kuwa, gaskiya yaka mata mukuma asibitin nan, domin na fara tatta....bata ida mgnr ba saka makon marin d'aya kai mata, cikin b'acin rai yace " you are very stupid!! Ke har kin isa ki gayamin mgn?" Ya fada tare da kara mata wani marin" wani uban ihu tayi tace" wayyo Allah k'umatu na ya cire a tayani nema jama'a zai na k'astani, kuma kaima stupid din"
Tsawa ya d'aka mata yace " ko ki rufe b'akin ki kona miki shigen duka"
Tsit tay Tanà kallonsa daman can borin kunya ce"
daf da ita ya k'araso fuska d'aure tamau yace" har yanzu tattaman kike Mu koma asibitin ko?"
Girgiza k'anta tay tace "ah ah wlh tsubutar baki ne, don Allah kayi hakuri karka tsake dukana, wlh ko a kauye Inna da Baffa basu taba dukana ba sai kai, Allah idan ka sake bazan yafema wanan ba tunda na safe na yafema" sai kuma hawaye sharr!suka gangaro a k'umatun ta"
Zuba mata ido yay yana kallonta sai kuma tausayinta ya k'amashi"
Yace " ko kimin shuru kona miki dukan da gaske"
A hankali ta daina kukan nan tanà sai sauke ajiyar zuciyar da take"
Maza tashi ki goge min inda kika bata nan, ya fada tare zama kan kujeran ya fara danna laptop dinsa, domin drink din bai taba shiba"
Mikewa tay jiki a sanyaye tyi mopping din wurin, duk kewar su Inna da Baffa ya rufeta"
Duk abunda takeyi yana kallonta harta gama gyara komai,
A hankali ta dauki
Plate da cup din daya ci abincin ta hada
cikin tire din ta dauka, zata fice daga parlor, yace" zoki zauna bari na kira miki su Baffa sai ku gaisa ko"
Juyuwa tay Tanà tsakin murmushi tace " da gaske Yaya?"
Ni sa'an wasan kine dazan miki Karya ,sai na fasa kiran idan kika min rashin kunya, yay mgnr fuska a d'aure"
Baki washe tace " ah ah kayi hakuri ta fada tare da zama a gefinsa"
Be kulata ba ya fitar da wayar ya kira Baffa, yana d'aga wa suka gaisa ya mikawa Fatu wayar, karb'a tayi tanà murmushin, gaishe da Baffa tay tace " ina Inna Baffa na murmushi yace " tanà cikin gidah bari ma na kai mata ku gaisa"
Kai ma Inna wayar yayi cikin farin ciki suka gaisa da Inna, Inna tace "akoi abunda Saifun yake mikine ki fad'a min idan akoi masalane karki buyemin, kallon Saif tayi da shima ita yake kallo suna hada ido ya wani dauke kansa, murmushi tyi tace " lah ba komai Inna muna zaune dasu lafiya suna sona sosai sai kinga abubuwan da suke min"
murmushin jin dad'i Inna tay tace " toh Allah ya muku Albarka, da amen ta amsa sukayi hira kad'an ta musu Sallama ta bashi wayar ya karb'a ya ajiye"
Tanà dariya ta mike tace" ngd sosai Yaya sai yau k'asani farin ciki duk dai sanda ka bani na jaki, tanà fad'ar haka ta fice daga parlor zuciyar ta cike da farin ciki"
murmushi yay yace "Allah ya shiryeki, har cikin ransa yaji dad'in ganinta tanà farin ciki, kome ya tuna kuma sai yay tsaki yaci gaba da aikin sa cikin laptop"
Direct kitchen ta shiga ta ajiye tiren kwanukan ta fito parlor, bata ga kowa a parlor ba hakan ya sata wuce ba bedroom sun tasan SONA na can tana aikin lashe lashen waya"
*****************Bangaren su Ruky kuwa tafiya me nisa sukayi, kafin suka shiga wani dajin, shima sanda sukayi tafiya sosai kafin suka isoh, parking sukayi, suna fita Ruky ta fara ganin wani hayaki ² tace" Sumy wannan hayakin fa?"
Sumy tace " kedai biyoni kawai ai hayakin da kike gani d'aga can bokkar Bokan take fitowa"
Tabe baki tayi sukaci gaba da zuwa har suka isah bokkar Boka"
Sumy tace " da baya ²zamu shiga" okay Ruky ta fad'a suka shiga da baya² k'amar yanda ta fad'a"
Suna shiga ta hangi wani b'akin mutun zaune sanda taji k'irjinta ya buga, d'aurewa tayi tana tana kokarin zama, Boka ya d'aka mata tsawa yace " uban wa ya baki izinin zama anan?"
Jikinta har rawake tace " afuwan ranka ya dad'e"
Hahahahaha Boka yayi dariya yace " an miki afuwa da'a lama baki tab'a zuwa nan wajen ba"
Da sauri tace " eh"
Ko Fadi a bunda ya kawoku, sbd zanyi wani aikin yanzu inba don naga zuwan kuba da baku tsame niba, sai dai ku sami Aljanu na"
Hadiye miyau tayi a ranta tace " anya zan iya wanan abun kuwa?" Ina jinku dame kuke tafe"
Ta bata Sumy tay ta mata alamu d'ata sanar masa"
Cikin Faduwar gaba ta gaya masa komai, murmushi yay yace " daman can na san da abunda kuke tafe dashi"
Wani abubuwa ya dauka ya wasa cikin jan wutan dake fita acikin wani kwarya yace " zai dawo garike ya Aure ki, zai miki biyayya t'amkar uwar sa, duk abunda kika ce masa shi zanyi, ba wanda ya isah ya sashi canja abunda kika ce,zaki dawo t'amkar sarauni ya, ya dawo miki bawa, idan kina son aiki zaki fara kawo dubu dari biyu wanda zan tsayawa Aljanu k'ayan aiki dashi"
Idan kuma bazaki iya ba hanya a bude take zaku iya tafiya"
Murmushi Ruky tayi tace " indai wanan ne ba masala, handbags dinta ta bude tare da cire dubu dari biyu ta ajiye masa"
Dariya Boka ya fashe dashi yace " bayan kwana biyu ki dawo ki k'arbi aikin ki, zaku iya tafiya"
Tom sukace, kafin suka fita d'aga bokkar"
Suna fita Sumy tace " dan banza da ka farsa zaizo ya tsameki har inda kike"
Murmushi Ruky tayi tace " gaskiya ngd sosai k'awa Allah ya barmu tare,
Hira sukaci gaba dayi har suka isah wajen Motar su suka shiga sukabar dajin"
Direct gidan ta sauke Sumy ita kuma ta wuce cikin farin ciki, Saif zai dawo hannunta"
Tana wucewa Sumy tayi dariya tace " yarinya baki san wuta ba sai kin taka tana fad'ar haka ta shige cikin gidah"
**********Da d'addare b'ayan anyi Sallah i'shane Fatu tayi wanka ta shirya cikin wani lailaisar k'ayan bacci wanda Momy ta bata, wando da riga pick color mai k'yau sai k'amshi take, fitowa parlor tayi, SONA k'awai ta samu Tanà kallon wani Indian series my sona what kind of love to this" lkcn da ake zuba ruwan love acikin sa, zama tayi akan kujera, kallonta SONA tayi tace " wow kinyi k'yau sosai sister "murmushi tay tace " ngd sosai, shiru sukayi suna kallon films din"
A hankali Saif yake saukowa sanye yake da kananan kaya wanda suka masa masifar k'yau sai k'amshi yake,
Kansa ya d'aga daga kallon da yakewa wayar sa, idanunsa suka sauka a.....!
Share fisabilliah Habibaty 🥰
[1/21, 8:32 PM] +234 706 120 4735: 👧🏻 *MIJIN YARINYA* 👧🏻
*Story and written*
*By*
*Fatima Msr Ahfat*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*📚
*Bismillahir rahmanir Rahim*
*Page 18*
_____________ Idanunsa suka sauka k'an Fatu d'ake zaune saman kujera tama TV k'uri da ido sai murmushi takeyi, Narkakkun idanunsa ya zuba mata, yana binta da wani irin kallo, kallonta yake bako k'iftawa, cikin ransa kuwa yace" wow so beautiful, k'aramar yarinya ce amma komai tay yana burgesa, lips dinta da take dan motsawa yabi da kallo, murmushi yay yace " magana disu sai rashin kunya"
Idanunsa ya maida Saman k'anta yabi sumar kanta da kallo wanda ke kwance lup dashi"
Lips dinsa ya ciza yace " hmmm k'yawunta na banza tunda nidai ba sonta nake ba, tsaki yaja yace " ina ma abun son anan"
Da wanan tunanin da yake a ransa ya sauko parlor, dining area ya nufa yana taku a hankali ² har ya karaso ya zauna, savings din kansa yay ya tsoma ci"
Fatu ma najin k'amshin turaren sa ta lumshe idanunta a ranta tace " gaskiya wanan turaren ba dai k'amshi, daina kallon TV tay ta bishi da kallo k'amar maiya har ya karasa dinning din ya zauna"
Murmushi tay haka k'awai ta tsinti kanta dason zuwa ta takura masa,
Cikinta ta dan shafa tace " yunwa ma nakeji wlh dole naci abinci idan ba hakaba akoi matsala"
Mikewa tyi a hankali, kallonta SONA tayi tace" ina kuma zuwa?"
Fuska shugub'e tace " nadan fara jin yunwa ne zanci abinci"
SONA tace " ko dai kice bin mijinki zakiyi ba"
Murgud'a mata baki tay tace" Allah tsareni, ina ma mijin yake?" Ai wanan baza'a kirashi d'ana miji ba, domin na miji baya tab'a daga hannunsa ya doki mace"
Murmushi SONA tayi tace" sorry hakane fa dear jekici abincin ki, nidai nasan wataran duk abunda ake boyewa zai fito fili, taci gaba da kallonta"
Tabe baki tayi tace " ohoo dai ai sai kiyi tayi, don ni yunwa nakeji masu bacci da ido d'aya kawai, tayi shigewar ta abunta"
Duk abunda ta fada duk ya shiga kunnen Saif, murmushi k'awai yay amma kuma har cikin ransa Kalmar data furta ya dukesa"
K'araso wa tayi ta zauna kan kujera tanà kallonsa, ganin yanda ta zuba masa idone ya sashi daga da kansa sukayi ido biyu da ita, zare masa ido tayi tana murmushi, tsaki yaja ya dauke kansa yace "wlh idan na tsake k'amaki kina kallona sai na k'wakule meki idanunki"
Lah da gaske Yaya?" da kuwa wlh nayi dad'i k'aga kuwa zaka zamomin dan jagora ko"
Naga kuma ai kai ka fara kallona har muka had'a ido,ni bance zan kwakule maka ido ba sai kai"
nifa jiran ka nake ka zubamin abinci naci yunwa nakeji"
Wani kallo ya watsa mata, har zaiyi mgn sai kuma ya fasa, aransa yace " wato wanan yarinyar duk abunda ka fada mata sai ta baka amsar sa"
tsaki yaja yaci gaba dacin abincin sa hankali kwace yama manta da wata zaune a wajen"
Ganin ya mata banza ne ya tsata dibar abincin ta faraci tana ya tsina fuska"
Ko kallon inda take bai tsake yiba har ya gama cin abincin sa ya mike yabar wajen, rai ba dad'i domin mgnr data fada masa"
*Bayan sati daya*
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya inda Fatu ta fara zuwa islamiya ita da SONA ba laifi kuma tanà dan gane karatun sbd idan suka dawo SONA na kwaya mata duk abunda bata ganeba" rashin kunya kuma ba abunda ya ragu ko d'aya sai tsulawa Saif tsiya take son ranta, duk da yanzu ya daina kulata sosai domin mgnr data fada masa ranan"
**************Bangaren Ruky kuwa bayan kwana uku suka koma wajen Boka, inda ya bata wasu magungunan kusan k'ala bakwai na wanka dana hayaki, na kwana uku, idan ta gama kuma akoi wani turaren daya bata akan ta shafashi, kuma ta tabbatar idan ta shafashi Saif ya shaki k'amshin, idan tay haka dai shikenan aikin ta ya biya, karb'a tayi tana zuba godiya suka bar wajen, tana komawa gida ta jika magungunan ta fara amfani dashi"
Kwance take saman bed dinta tana tunanin gobe ne maganin ta zai cika, amma ta yaya zata samu ta hadu da Saif gobe dun cika aikin Boka"
Murmushi tay tace " dolene nasan abunda zanyi nan da gobe,
Wayar tane yay ringin, kallon wayar tayi Iman yake kira answering tayi tace " Hello" daga can bangaren Iman yace " haba sweetheart tunda kikazo Nigeria kika manta dani ko call na miki baki dagawa why Baby"
Murmushi tayi tace" am sorry Baby wlh ina busy ne shiyasa amma don Allah kayi hakuri"
a ranta kuwa cewa take idan har na samu Saif a hannuna ma ai bazaka tsake jin k'oda murya taba"
Okay ba laifi amma gaskiya nayi missing dinki sosai"
Murmushi tay tace" nima nayi missing dinka sosai, murmushi yay sukaci gaba da hiran su cikin farin ciki"
********** Yau su Fatu basu dawo islamiya da woriba har karfe 6:30 domin sun biya gidan Hajiya Zainab sun bata sakon da Momy ta aikesu, suna dawowa, bedroom ta shiga, tanà shiga toilet ta fada tayi wanka ta fito domin yanzu dai Fatu ta fara zamuwa yar gayu sbd SONA tyi tsayin d'aka sosai kafin yanzu ta dage dayi" shiryawa tayi cikin kayan bacci wando da riga red color yay matukar amsar jikinta sai k'amshi takeyi, parlor ta sauko direct dining ta wuce taci abinci, kitchen ta shiga ta wanke duk abunda ta bata ta fito, bedroom dinsu ta wuce tanà shiga ta sami SONA na kwance, kallonta tay tace " meke damunki na ganki a kwance ko wanka bakiyi ba?"
K'asa mgn tayi sai murgususun da takeyi