Showing 15001 words to 18000 words out of 30491 words
Chapter 6 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel
da sanin ki ba, kuma ina fatan bazaki bani kunya ba Fatu, kuma zaki dauki wanan abun a matsayin haka taki kaddaran ya k'asan ce, kuka sosai Fatu tay kafin tace " insha Allah bazan tab'a baki kunya ba Inna na yanda da Auren kuma na dauki duk wata kaddaran da Allah ya d'aura min, murmushi Inna tayi tace "Allah ya miki albarka kuma Allah ya had'a kanku, da Amin ta amsa mata, amma a cikin zuciyar ta kuwa abunda take kissimawa daban, Nasiha Inna ta mata wanda yana shiga yana fita, kukan ma da takeyi bai kai zuci ba, domin hankalin ta ya tafi wani wajen tana tunanin irin muguntar da zata dinga mishi ne, domin bazai mata abu tayi suruba tana dai dai da kugunshi, SONA ne ta shigo dakin da duk abunda ya faru ta jishi da zama tayi kusa da Fatu tace "kiyi hakuri Fatu ki dai na wannan kukan kar kanki yazo yana miki ciwo, Kinga yanzu zamu tafi dake kema kin dawo yar birni ko, murmushi tayi tace "haka ne fa kinga zan dinga shan Madara ko yaushe a birni nima na zama yar gayu k'amar ki, murmushi SONA tayi tace "sosai kuwa yanzu dai tashi kiyi wanka kinga an juma zamu tafi, mikewa tayi tace "toh yanzu kowa sai naje muyi ban kwana da Saude, fita tayi ta dauki bokiti ta cika ruwa dashi ta shige bayi bata dad'e ba ta fito ta shirya cikin atamfa riga da zani"
Tana gamawa ta wuce gidan su Saude sukayi Sallama Saude na kuka tana kuka tare da ce mata wlh duk dan hammatan daya tab'a ki indan tazo sai ta rama miki da haka suka rabu, ta dawo gida,in da ta samu har su Daddy sun gama shiryawa, har kofar gida Inna ta rakasu, Daddy yace" ki shiga motar mijin ki"
daman drivern daddy ya zo, bud'e bayan motar tayi ta shege ta hade rai ita a dole fushe take da su
Wani wawan kallo Saif yayi mata ta burgud'a masa baki ya girgiza kai alamun zaki hadu dani
Sallama sukayi da baffa sai hakuri baffa yake basa akan yayi Fatu a hankali domin akai ta da wautan ci, murmushi kawai yay ya ja motar"
Su Daddy ma Sallama sukayi da baffa suka tafi, Inna ne ta fashe da kukan rabuwa da jikar tata, baffa na lallashin ta"
Tuki yake sai kawai ya fara jin dariya k'asa k'asa, basar wa yayi tun dariyar baya damunshi har ya fara bata mishi rai, juyuwa yayi kawai sai ya ganta kwance tana dariya, wani b'acin rai ne ya k'amashi kawai sai ya paka ya zagaya in da take ya.....!
More comment
More typing wlh
Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰
Maman khalid ✍🏻
👧🏻 *MIJIN YARINYA* 👧🏻
Story and written
By Fatima Zahra (Maman khalid)
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 10
( Not edited)
____ Ya bude motar ya wani fisgota har ta kusa fad'iwa, a fusace kai Malam lafiya zaka kashe nine?" Shima a fusace yace "wallahi zanci mutuncin ki ni zaki shigowa mota kina dariya k'amar sabuwar kamu, kallonshi tay sai kuma ta kara fashewa da dariya tace " ko kuma sabbin kamu ba"
Kallonta yay ranshi na suya yama rasa mai zaice yace " wlh zan b'alla ki in kika ce zakimin rashin kunya zan ragargaza ki"
Murgud'a be baki tayi tare da rike gugu tace "inka tashi karka bar ko da kashi d'aya ne a jikina dan rainin wayau mutun ne sai shegen masifar tsiya, sai kuma ta fashe da kuka tace" Allah ya isah wlh da aka had'ani da mugun mutun sai kabar zuciya kamar bakin tukunya"
Kallonta yay sama da kasa takaicinta ya kamashi yace"ai bake ya kamata kija Allah ya isah ba ni ya kamata ace naja domin an hadani da mara hankali fisarenriya"
Kukan da take ne ya tsaya tay wani irin shewa tace "gani fesarenriya Kai kuma a kira dame nifa bana son mgn da kai domin yau dinan ina cikin farin ciki don haka bazan bari ka lalatamin shiba da wani katon bakinka awajen,tana fad'ar haka ta shige motar ta zauna ta wani hada fuska tana yan harare_harare a dole ita ta kame kenan"
Yama rasa abunda zai wa wanan yar figigiyar yaji sanyi Aransa, domin wani irin b'acin rai ne ya tsake debar sa, wato ma dad'i takeji da Auren ai kowa zai sata taji dadin da bazata tab'a mantawa dashi ba" bud'e motar ya sakeyi ya finci kota ta fito ya jefata a gaban motar har sanda ta buge kanta a gaban motan, ta tsaki wani ihu tare da fashewa da kuka tana cewa" baka ganine zaka wani tureni haka kasheni zakiyi, rufe kofar da karfi yay, shima ya zaga ya zauna tare da jan motan yana jinta tana mishi surutu tana fad'a mishi mgn, be kulata ba,yana Addu'a ya ga kanshi a garin Kano ya ajiyeta ya huta wanan wani yarinya ne aka had'ashi dashi"
ganin yay banza da ita ya tsata jan bakinta tayi shuru tana shafar inda ta buge"
Tuki yake ransa duk ba dad'i yaji da wanan masalan ne ko koma yaji da kiran da Ruky take masa, tsaki yaja ji yay Fatu tace "kai ma haka dan rainin wayau wa akafi iya tsakin, be kulata ba yaci gaba da Tukin sa, Fatu kuwa sanyin dake motan ne ya fara rasata har bacci ya fara d'aukanta ta fara gyangydi har ta fado kafadar shi, wani irin hankade ta yayi har ta ji zafi kara ta sake tace "haba ai sai ka tashe ni mugunta babu k'yau wlh"
Be kulata ba yaci gaba da tukin shi"
Da haka dai har suka isa garin Kano gida sukayi direct tun a gets Fatu ke ta kallon gidan har suka isa parlor, SONA ne dake zaune a parlor ne tace " sai yanzu brother ina kuka saya haka?"
Be kulata ba ya haura sama, tabe baki tay tace "kaji dashi" kallon Fatu tay dake kalle _kalle murmushi tay tace" mushiga daga ciki ki huta Fatu" kallonta Fatu tayi sai kuma kunya ya kamata a ranta tace " kai gaskiya na kwasa ai bazan bari wanan wawan ya gane kauyen cena yay yawa ba, tab'a ta SONA tayi tace " ya dai Fatu kinyi shuru, fasuwa da kuka tayi tace "Allah sarki Inna wlh ita nake tunani yanzu ace na barta a Kauye tana fama da wanan kuran, wlh harna tausaya wa Saude da bata shigo birni ba, dariya SONA tay tace "don Allah kibar wanan zancen mu shiga daga ciki, d'akin ta SONA ta kai ta tace "yan dai kiyi wanka ki kwanta ki huta ta"
Tace "ina wurin wankan?"
SONA tace " ga toilet nan"
Tana fad'ar hka ta fice daga dakin, sanda ta gama kalle_kalle da tabe tabe kafin ta shiga inda SONA ta nuna mata toilet, kallon ko ina na toilet din take tace " ikon Allah bayi fa nace ta nuna min ta nuna min nan"
Leka bathtub din da ta gani ne tace " nan bashi da maraba da makabarta wlh ta dad'e tana tabe tabe kafin ta fita ganin SONA tay tana lasar wayar ta ne ya sata cewa "ni fa bayi zaki kai ne shine zaki kawoni Nan" SONA tace "bayi ai ki kunna shower kiyi wanka"
Tace " Sha'awa kuma ai na baruta a Kauye"
Dariya ne ya kama SONA tace " muje in nuna miki inda zakiyi"
Tace" da dai yafi kam ai wannan sai ku" shiga sukayi SONA ta nuna mata komai tace " yanzu dai shiga kiyi wanka"
Tabe baki tayi tace" hmmm Allah dai ya raba bawa da wahala, yanzu ace sai mutun ya shiga dogon ahonan kafin mutun yayi wanka Allah dai ya k'yauta" murmushi kawai SONA tay tace "kinga ne kuwa?"
Tabe tabe tay tace "eh nagane ai ni mutun na nunamin abu sau daya nake ganewa"
Fita SONA tay ta bata waje, ta dade a tsaye kafin ta shiga ta fara wanka washe hakura tay tace " Ashe da dad'i" fitowa tayi ta samu har yanzu SONA na kwance tana lasa wayar ta tace " Hmm daman ance yan birni ba abunda suka iya sai lasar wanan shegiyar abun, mutun ko yna jin yunwa ma hka zai zauna yunwa na kakulan sa tana zauna, nifa gaskiya bazan iya zama da yunwa ba ehee"
SONA dai bata kulata ba, taci gaba da abunda take, itama zama tay ta dauki k'ayan ta doguwar riga tasa, taje gaban dressing mirror turarun ruka ta gani jere da dai abubuwan ado, murmushi tay ta dauki turare ta fishe jikinta dashi tace " kai kai gaskiya wanan akoi shi da k'amshi yafi nawa k'amshi, SONA dai jinta kawai take domin hankalin ta duka nakan wayar ta da take chatting dashi"
Goga wanan murza wanan haka Fatu tay tayi sanda ta gama penta fuskan ta gaba d'aya tayi wani murmushi ta juya gaban mirror tace" kai gaskiya ni dinnan kyakyawace wlh duk wanda ya Aure ni ai yaji dad'i, rike gugunta tay ta wani irin yuyawa ta dan daga hannunta tsama kad'an tace" masoyi na wai baka ga adon da na maka bane ta fad'a tare da kissing din madubin, wani irin dariya ne SONA ta kece dashi har ta kusa fadowa, tace " Fatu wanna duka Yaya kike ne?" juyawa tayi tace" Allah ya tsareni ni fa a wani indiya film na gani shine nake kwaikoyun su ta fad'a tare da murgu da baki ta zauna akan gadon"
SONA dai k'asa barin dariyar tay tace ' gaskiya kinyi kyau kuwa ko zaki sake yimin na kalla?" Turu baki tay tace " ni dai ynwa nake ji wlh, dariya sosai tay tace " okay muje muci abincin, tashi tayi suka fita daka d'akin"
Bangaren Saif kuwa yana shiga dakin fadawa kan bed dinsa yayi yana mai da numfashi yace " daga yau zaki fara dana sanin shiga rayuwa ta da kika yi mara kunyan yarinya kawai keda kanki sai kin koma kauyen ku da kafar ki"
Ya dad'e kwance kafin ya mike ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin kana nan kaya ya sauka k'asa, direct dining area ya nufa zama yay ya fara cin abinci kenan su SONA suka fito, kallo d'aya ya musu ya dauke kai yaci gaba da cin abincin shi, zama SONA tayi Fatu k'uma ta tsaya a tsaye tana wurgawa Saif harara k'amar idanunta zasu zuba, kallonta SONA tay tace " ki zauna mana Fatu kina a tsaye, murmushi tay ta zauna, zuba musu abinci tayi Fatu tace "kara min wlh wanan bazai ishe niba, tabe baki yayi ya ture plale din dake gaban sa ya mike ya bar wajen, tabe baki tay ta fara cin abincin ta tana lumshe idanunta tace " Allah sarki Saude ko yanzu taci abinci ne oho k'amar na dawo shunsun na kai mata wanan kazar, kai bomar abinci tay a bakin ta tace....!
Kuyi hakuri da wanan sai gobe insha Allah
Comment and sharen fisabilliah Habibaty 🥰
Maman Khalid ✍🏻
👧🏻 *MIJIN YARINYA* 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
💃💃💃💃💃💃💃💃💃
Lokaci yayi🔥🔥🔥🔥 💃💃 lokaci yayi 💃💃 lokaci yayi 💃💃🔥🔥🔥🔥
*INA KUKE MASOYA NA MASOYAN LITTAFIN MAIRO'YAR KAUYE, MIJIN YARINYA, DOCTOR KABIR*
To gani Nan tafe da sabon littafi mai suna *NADAMAR ZUCI* me cike da fadakarwa ilmantarwa fa dakar wa tare da nishadartarwa,
Labarin me dauke da tsansar cin Amana, yauda ra, da kuma tsarka kiyar soyayya mai dauke da rikitar wa.
Umma! Umma!! Umma!!! RIYAH ce take kiran sunan ta lokacin da aka k'ai da soka mata wuka a cikin cikinta,wani irin ihu tayi lkcn da mutun min ya kara soka mata wukan tare da tureta ya fice daga gidan, da gudu ta kara so tare da tare Umma kafin ta kai k'asa, kiran sunan ta kawai take tana girgizata, bude baki Umma tayi da niyar yin mgn amma mgnr kasa fitowa yayi, domin numfashi ta na kokarin fita, cikin kuka take cewa" a'a Umma ki tashi kar ki min haka Umma ki tashi, hannunta tasa akan wukan da aka chaka ma Umma a cikinta ta cireta, tana rike da wukar kenan tana ARJUN ya shigo cikin parlor, bakin shin na rawa da k'yar ya iya furta mahaifiyar tawa kika kasheeee! Bai iya karasa maganar ba saka makon wani mugun jiri day'a dauke sa yayi baya luuuu!.....
Bangare guda kuwa ga mahaifiyar RIYAH da take daure a dakin duhu, dakin
da ba inda mutun zai iya shakan iska a cikin sa.....!
Shin suwayen wadan nan mutane da suke son ganin bayan RIYAH?"
Shin soyayyar RIYAH da take wa ARJUN shin zai amshi ta kuwa?
Tunda da dai da idanunsa ya ga ta tana rikeda wukar?"
Bangare guda kuma zaki koyi girki iri_ iri na gargajiya dana zamanin wanda zaki ringa tsarawa ogan ki dashi, ki zama taurarowa a gunsa,
Wanan book din na kudine duk mai son complete zai iya biya domin samun wanan chakwakiyar labarin,
300 ONLY zaku iya ta wanan asusun
0431560118 fadimatu Babangida gt bank, ko kuma ko min mgn ta WhatsApp number 07061204735,
Ku NUNAMIN soyayyar da kuke min ta hanyar tsatan book din na, mai suna NADAMAR ZUCI Msr Ahfat
07061204735 nagode masoya
Page 11
____tace" gaskiya dad'i ya wuce ki Saude, dariya SONA tayi tace"ke dai akoi ki da abun dariya wlh" murmushi kawai tayi taci gaba da cin abinci tana lumshe ido"
Suna gama cin abinci suka dawo parlor suka zauna Fatu dai sai kalle _kalle kawai take, momy ce ta sauko ta Kara so dining din tana kallon Fatu da murmushi a fuskar ta tace " sannu da zuwa yata" washe baki tayi tace " yawwa ina yini" Mun same ku lafiya?" Murmushi mommy tay tace" lfy k'alau alhamdulillah"
Saif ne ya sauko daga sama da alama dai fita zaiyi, mommy tace " Babana ina kuma zaka bayan yanzu dawo?" Dan ya motsa fuska yay lokacin da idanunsa suka sauka akan Fatu tare wasa mata harara, murgud'a masa baki tayi, murmushin munta yayi ya kalle Mommy tare dan ya motsa fuska yace " yanzu zan dawo ba dad'e wa zanyi ba domin jikina duka a gajiye yake"
Murmushi kawai tayi shikuma ya fice daga parlor, wucewa kitchen momy tayi domin ba zama zatayi ba, SONA ma mikewa tayi tace" gaskiya na gaji sosai bari na watsa ruwa na d'an huta kad'an" tabe baki Fatu tayi tace " tom nidai bari na zauna anan nuna parlor tay da hannu, murmushi SONA tayi tace" parlor zakice ba wanan ba, baki ta tabe tace " Tom naji, sauko wa parlor sukayi SONA ta wuce d'akinta ita kuma zama tayi akan kujera sai zazzare idanunta take"
Saif kuwa fita yayi daga gidan bai wuce ko ina ba sai wani babban super market yayi parking shiga yayi cikin tsayayya yayi sosai"
Ya biya kudin suka zuba masa abayan Booth"
Shiga motan yayi zuciyar sa cike da farin, bai tsaya ko ina ba direct gida ya dawo, d'ebo k'ayan yayi ya shigo dashi parlor Fatu kawai ya samu a parlor sai kalle_kalle take, tsaki yaja ya haura da kayan part dinsa, zubesu yay a parlor ya wuce bedroom d'insa, kayan jikinshi ya rage ya shege bathroom sakar wa da kansa shower yayi ya jima kafin yayi wanka tare da d'auro Alwala ya fito daure da towel a k'ugunshi d'aya kuma yana goge suman kanshi dashi"
Gaban dressing mirror ya zauna daukan bodylotion d'inshi yabi jikinsa dashi a hankali, gyara gashin kansa yayi ya feshe jikinsa da turarunruka masu k'amshi, mikewa yayi yana tafiya a hankali har ya karaso ganan drawer d'insa ya bud'e zaro farin jallabiya yayi, da farin singlet ya sanya a jikinshi, ya sake feshe jikinsa da turarunruka sai k'amshi yake zubawa, fita daga d'akin ya da sauri domin zuwa masallaci sbd yaji ana faman yin sallah baya son ya makara kicibus sukayi karo da Fatu, tsaki yaja ya wani tureta harta buge kanta a gini"
Yar kara ta tsake tace " Allah ya isah mugu k'awai ai nima ban kula bane da me zaisa nabi inda kabi,bai kulata ba ya wuce abunsa, yana jinta tana mgn"
Goge goshinta tayi tace " Allah ya isah bazan yafe ba, wlh sai na rama ai dani kake zancen sha shasha k'awai"
Shigewa d'akin su tayi tana zunburu baki, toilet ta shige Alwala tayi ta fito, SONA dake kwance ta kalleta tace " meya sameki naga tun shigowar ki kinata zunburu baki?" Ba komai Inna ta nake tunani"
Murmushi tayi tace " kinyi kewarta sosai ko?" Nasan Inna ma yanzu tana can tana tunanin ki"
Bata ce komai ba tad'a Sallah tayi, SONA kuwa taci gaba dayin lazumin ta daman ta gama Sallah"
Tana idar da Sallah ta cire hijab din ta hau d'ayan gadon ta kwanta tayi shiru duk kewar Inna da Saude takeji, ga bangare gud'a kuma tana tunanin wani abu zatawa wanan sak'aran taji dad'i"
Saif kuwa yana dawowa daga masallaci ya shigo parlor da nufin inya sameta a parlor sai ta fad'a masa wa takema rashin kunya,
Ganin bata nanne yace " Allah ya taimake ki yarinya"
cize lips d'insa yayi tace " daga gobe zaki fara karb'an saka makon ki"
Wucewa part d'insa yay zuciyan sa fes,
Washe gari da Asuba su Fatu suka tashi bayan sunyi Sallah basu koma bacci ba SONA tace " sufita suje su d'aura breakfast sai ta dinga nuna mata abubu, tom Fatu tace suka fito, kitchen suka shiga breakfast suka fara had'awa Fatu dai sai tambaye_ tambaye takeyi, da haka har suka ferfesu kaji da joluf din dankalin turawa wanda yaji kayan lambu wato vegetables, da dafafen coffee, Fatu dai har wani tsinkewa yawunta yake ta gagu tagan ta tana cikin abincin kazan nan, sbd yanda ta dafo sai k'amshi take, jere komai a dining area sukayi domin Indo mai aiki harta share ko ina ta goge"
Dawowa kitchen din sukayi suka gyara ko ina kafin suka wuce bedroom d'insu don zuba ruwa"
Saif kuwa bayan yayi Sallah Asuba bacci ya koma hankali kwance, bai farka ba har 8 mikewa yayi ya shige bathroom wanka yay ya fito ya shirya cikin kana nan k'aya wanda ya masa bala'in k'yau, sai k'amshi yake zubawa, wayoyinsa ya dauka ya fito a hankali yake sauko wa a'kan strep yana lasar wayan sa, dago da kansa yayi ai kuwa 4 eyes sukayi da Fatu, harara ta wasa mishi ta dauke k'anta"
Murmushi