Showing 12001 words to 15000 words out of 30491 words

Chapter 5 - Mijin Yarinyah Book 1 Complete Hausa Novel

muba yan jikukin mu susha"
Ai kuwa fashewa da kuka Saif yay jin za'a yi ferfesu dashi, yace" dan Allah kimin rai wlh bansan nan din wajen ku bane, dariya ne ya kama Fatu ganin da tayi yana sharbar bajina da hawaye ga uban gumin da yake keto masa, tace " tohh! Zamma afuwa domin Amma da akoi shara din da zan ginda ya maka,ka bud'e kunnuwar ka da k'yau ka tsaura reni,idan kuwa kabin sharadin toh kuwa sai na babbaka katsutsun jikinka na cin yi" na yanda wlh na yanda da sharadin ki, dariya tayi hahahaha, toh abu na farko shine idan ka yanda naji ka fadawa wani acikin gidan nan akan cewar ka kalle wani abu toh fa...bazan ma fad'a ba wlh, girgiza kai tayi tace " tom abu na biyu kuma idan karka yanda ka tsake kace bazaka tsake kwana a dakin ba daga yau daga yau nan zaka dinga kwanci ya har sai kun tafi, domin daga yau zan dinga tsama ido, tom!tom!! Na yanda zan kwanta, Amma dan Allah kimin alfarma ki fita daga rayuwata domin idan kika ce gaba da bibiya ta wlh zan iya mutuwa, dariya tayi hahahaha! Idan ko ka mutu sai mu hade tare kawai, ai gum da bakin shi yayi sai zuru_zurun idanun da yake zunzurawa, tace" toh yanzu zan tafi wajen yara na domin jina suke zan basu ferfesun wani bil adan da na musu su Sha, ko kai ma zaka sha, girgiza kansa yayi,tace "kuma ka kwanta kafin na tafi"
Da sauri ya haye katifar ya kwanta ya rufe fuskar ta, dariyar tane Fatu ta danne tare da tsolale wa daga dakin ta fita, gyera gashin kanta tayi ta koma dakinsu da sauri ta kwanta tana dariya"
Saif kuwa jin dakin yay shuru na wasu lkc ya bude idanunsa a hankali ganin ba kowa ne ya tsashe dafe chest dinsa a hankali yace "wlh Allah ya isah da waen nan mugayen Aljanun nan,wanan halin d'aya shiga duk Dad ne ya jawo masa, wanan masifar ai'kuwa gobe ba abunda zai sashe kara kwana a dakin, haka dai Saif ya zauna akan kati far sa yana ta tsake tsake ta yanda ma zaiyi yabar wanan annonar kauyen, har kusan Asuba ya tsamu ya rinsa"...

     ***************
Ruky na sauka ta samu drive gidan Anty nata yazo yana jiranta domin sunyi mgn da Anty nata, direct gida suka isa suna parking ta fito ta shiga parlor da sallama domin tasan halin Antyn nata bata daukar iskanci,amsa mata sallamar Anty tay fuskar ta dauke da murmushi tana mata san da zuwa,amsa wa tayi tare da zama kan kujeran dake parlor, tare da gaishe ta, amsawa tay cikin farin ciki tana tambayar ta yasu Yaya?" tace" Lafiya n su kalau sunce ma na gaishe ki, murmushi tayi tace"ina amsawa, yanzu dai tashi kije ki watsa ruwa kici abinci, "okay"
Mikewa tay ta haura sama.....!

Maman Khalid ✍️
👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Zahra (Maman Khalid)

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 8


Not edited

____ mikewa tay ta haura sama, wani bedroom ta shiga ta ajiye a 'kwatin ta tayi ta cire kayan jikinta, ta fad'a bathroom wanka tayi ta fito daure da towel, gaban dressing mirror ta tsaya tare da dan yin shafe_shafe ta shirya cikin doguwar riga ta atampa, ta dauki wayar ta dake kan bed din ta sauko k'asa"
Bata samu Antyn ta a parlor ba hakan ya tsata wuce wa dining area ta zauna tare da dibar abinci ta fara ci sanda taci mai isar ta tamike ta dawo parlor ta zauna, tana tunanin ta ina yanzu zata fara neman Saif, jin muryar Antyn tane ya katse mata tunanin da take, da cewa" wanan uban tagumin fa?" kinci abincin kuwa?" Murmushi yake tay domin ita kadai yanda takeji acikin zuciyar ta, tace "Eh naci nikam ina su Islam ne ban ji mutsin suba?" Murmushi tay tace " ai sunje gidan Ammin su zasu yinin mata, murmushi tayi tace kawai tay Anty kuwa ta shige cikin kichen, wayar tane ya fara ringin da sauri ta dauka ganin Iman ne ya tsata yin tsaki tare cewar" wai wannan wani irin makar naci ne dashi haka,dazun fa ya kirata bata dauka ba gashi kuma ya tsake kira, kin dauka tay har ya tsinke, ita duk a samma ninta ta aza ko Saif ne ya kirata, wani kiran ne ya tsake shigowa wayar da gawa tay Amma batace komai domin tasan indai ta bud'e bakin ta toh fa zagi zata gundu ma masa, bangaren Iman kuwa ta dagawa yace " haba sweetheart tun dazu fa nake kiran ki baki daga ba, da gatan dai kin sauka lfy?" Dan daure wa tay ta amma da lfy kalau"
Murmushi ya tsakar mata yace " alhamdulillah sai yanzu naji dadi wlh yasu Anty da hakuri?" Alhamdulillah, masha Allah kice ina gaishe su, okay yanzu dai anjuma zan kiraka Ina cikin mutane ne, okay wlh Baby miss you so much" murmushi tay tace "miss u too bye, ta kashe kiran, number Saif ta d'anda tana kiran sa amma baya shiga haka dai ta yini tana abu d'aya wato kiran Saif amma bata shiga, har Antyn ta tace " Ruky wa kike nema ne haka?"tace " ba kowa" tabe baki tay taci gaba da abunda take daman ita ba shiga har kar Ruky take ba"


********A Kauye kuwa baccin wahala ne ya dauki Saif domin ba dadin kwanciyar yake ji ba"
Washe gari da Asuba Daddy da Baffa suka fita masallacin dake kofar gidan sukayi Sallah, har suka shigo cikin gida basugan Shiba, bayan daddy ya gaishe da Inna yake tambayar ta Saif kuwa ya fito, tace " gaskiya ban sani ba sai dai bari insa Fatu ta dubushi" kiran Fatu tay, ta fitoh daga cikin zatayi mgn sai ta kalle Daddy sai tay murmushi kawai ta gaishe shi ya amma mata cikin sakin fuska, Inna tace "kije ki dubo ko Yaya n ki ya tashi" tom kawai ta fad'a ta mike tana dariya ciki_ciki domin tunuwa da abunda ya faru jiya, Daddy ma mikewa yayi ya koma dakin baffa, Inna kuwa taci gaba da aikin ta na had'a musu karyawa, tana isah turu kofar dakin tay ta shiga ko sallama batayiba ta kai me wani bugu a kafa da karfi, ai kuwa a firgice ya bud'e idanunsa akanta ganin ta da farin kaya ne ya tsashe cewa " don Allah kuyi hakuri karku yi ferfesu Dani"

Wani mugun dariya ta kece dashi daya sashi kallonta da k'yau Ashe Fatu ce, tsaki yay a file yace "uban me ya kawo ki dakin Nan?" Tace " uban me dakin ta fad'a tare da murguda masa baki tana mai girgiza gugunta kamar me son yin dambe, kallonta yay daga sama har k'asa yace " ke zo Nan" tace" bazan zuba idan kuma k'a gama baccin naka kayi Sallah sai ka fito ana neman ka domin kuwa nan gidan duka ba kafuri ehee, ta fad'a tana ko karin ficewa daga dakin, ai kuwa bata san sanda ya chanku tab'a,kama wuyan ta yayi dan gidan ku wa kike kira da kafuri?"harni zaki kalla kice wa kafuri dan bakida hankali sha_sha sha wlh idan kika sake shiga harka ta sai na kashe ki wa wiya jahila stupid bar nan ya fad'a tare da tureta sanda ta kusa faduwa"
Wani irin mai da nunfarfashi take, tace " ni Fatu naga ta kaina harna fara ganin wasu taurari fari_fari a idanuna,ya kusa kasheni tun banyi kalmar shahada ba, yana son in mutu kafura, kallonsa tayi yana faman cire kayan baccin sa harya cire rigar sa, da sauri ta rufe idonta da dan karfi tace "haram daka sa na kalleka ba riga, kuma Allah ya isah da kasheni daka kusa yi ban ya feba, tana fad'ar haka ta diba da gudu tabar dakin, shi kuwa sai daman bema kula da itaba yaci gaba da cire kayan sa yana gama wa ya shiga bayin dake gefen dakin, kallon bayin yay da k'yar dai ya samu yay wanka sama sama tare dayin Alwala ya fito ya shirya yayi Sallah, yana gamawa ne ya karasa shirin sa ya fito, Inna da SONA ya samo a tsakar gida, suna zaune akan taburmar ga abinci a gaban su da alama dai karyawa zasuyi, kara tsawa yayi da sallama ya gaishe da Inna fuskar sa adan sake, ta amma masa gaisuwar tay tace " ya baka fito ba tun dazu mahaifinka yana neman k'a?"
Dan tsosa keyar sa yayi a ransa kuwa yace " taya zan fitoh da wuri bayan jiya nayi gamo da tsinan nun Aljanu sun hana ni bacci" a fili kuma yace"zanje yanzu" gaishe shi SONA tay ya amsa mata tare da cewa da fatan dai kekam baki kiyi gamoba?" Wani kyakyalewa da dariya Fatu tayi daga bayan shi tace " Yaya kace gamo kayi jiya da Aljanu ko da bil Adam?" Me SONA zatayi inba dariya ba, Wani kallo ya mata d'aya tasa shiru da bakinta,wani haushin kansa yaji da yayi mgn nar, mikewa yayi bai ce komai yayi gaba,yana jin Fatu na masa mgn amma be kulata ba domin bakin cita k'amar ya kasheshi"
Inna ce tace" wai Fatu yaushe zakiyi hankali ne shidin ba Yayan ki bane?" Zunburu baki gaba tayi tace" dan na tambaye sa sai ya zamo laifi, girgiza kai kawai Inna tayi suka fara karyawa"

Saif kuwa dakin da su Daddy da Baffa suke ya shiga da sallama, amsawa sukayi, ya shigo ya zauna saman dardumar da yake shinfide a dakin, gaishe su yayi ciken girma mawa,suka amsa, Daddy ne yace " ya bangan k'a a masallaci?" Murmushi yay ya tsosa keyar sa yace " umm! wlh bakara nayi shiyasa ban samu zuwa ba, murmushi baffa yayi yace " da alama kauyen nan yama dadi fa" Daddy yace "wlh ina ga kawai mubar shi ya muku ko da wata d'aya ne, ya fad'a ta tsigar tsokana, Zaro ido Saif yayi Aransa yace " tab a wanan kauyen Aljanu ai ko kwana bazan kara gangancin yiba balle wata, a zahiri kuwa murmushi yayi bai ce komai ba"
Karyawa suma suka farayi suna dan tab'a hira"
Su Fatu kuwa suna gama karyawa Fatu ta mike tace "Inna nidai na wuce gidan su Saude yun tunda safe ban ganta ba, Inna tace "yaushe ma gari ya waye da har zaki jewa mutane gida?" Turu baki tayi tace" haba Inna kina gani fa har rana ta fito, murmushi SONA tay tace "jirani mu tafi tare domin nima naga gari, washe baki tayi tace "kinga ai Inna SANO ma zata bini mutafi kinga nima sai k'amshim birnin nan ya rab'e ni ko SANO" dariya SONA tayi tace "eh kuma SONA nake ba SANO ba kinji, ta fad'a tare daukar gelei ta,oho dai koma me ai kinsan dake nake mgn ko, eh na tsani mutafi ko, sallama suka ma Inna suka fita"..

Su Daddy ma suna gamawa kenan suna hira wayar Saif tayi ringin fita daga dakin yayi domin amsawa, Daddy yace " daman baffa inason muyi mgn, kallonsa Baffa yayi yace " ina jinka, gyran murya yace "daman baffa mgn ne akan Auren Fatu da Saifundin shine muke so a daura kafin mu tafi domin muna son mu tafi da Fatu"

Baffa ya d'anyi shiru na d'an lokaci kafin yace " shi din yana sonta ne?"


Daddy yace " Baffa kar dai har ka mance alkawarin da ya dauka tun shekaru goma da suka wuce kuma ai yar uwarshi ce ba zai gujeta ba"

Baffa yace " nasan da wannan but amma karka manta a lokacin besan duniya ba kuma yanzu duba da shi yana da ilimi kuma itako ko a rabin ma bata gama ba, kaga kuwa baza a lakawa d'an birni jahila ba, murmushi daddy yayi yace"ai itama karatun zamu tsata, nidai ka sanar gobe da Asuba a d'aura musu Aure"

Baffa yace " toh shi ya sani?"Daddy yace" no but ai mun isah dashi
baffa yace" baza ayi haka ba muji ra shi ya zo"

Daddy yace" in kace haka toh"

Saif kuwa yana fita amsa kiran yayi amma ba network sosai ya kashe wayar yana dawowa zai shiga cikin dakin kenan yaji duk abunda suka tattauna akan Auren shi da wannan k'azar mayon, ai jirine yaji yana debar sa a hankali yake furta innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n!!" domin ransa yayi mugun baci ba kad'an ba, tunawa da abunda ta ce masa da safe, sai kuma ya cizi bakin sa tare da tsakin murmushi mugunta ya kara sa shigowa dakin, samun su yayi suna hira, ya zauna a gefen su ya sunkuyar da kansa k'asa yana lasar wayar sa domin baya son su gani yanayin da yake ciki, Baffa ne ya kira sunan sa, amsawa yayi ba tare daya kalle sab'a, bayanin komai Baffa ta masa akan abunda suka tattauna, yace" kana sonta" dai dai ta nusuwar sa yayi yace " eh murmushi dukan su sukayi Baffa yace " alhamdulillah gobe da Asuba za a d'aura muku Aure ka ga sai k'a tafi da matar ka dan Allah kayi hakuri da kanwarta ka wani lkcn ta nada yanayin Aljanai kayi hakuri sosai da ita"

Mikewa tay yace " nagode baffa"
Yana fita wani mugun jiri ya dibeshe yace.....!

Comment and sharen fisabilliah Habibaty🥰😍


More comment
More typing

Maman Khalid ✍🏻

👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻

Story and written

By Fatima Zahra (Maman Khalid)

ELEGANT ONLINE WRITERs 📚

Bismillahir rahmanin Rahim

Page 9

____ yace "yarinya zaki gane kurkuren ki zaki san wa kike wa iskanci, da k'yar ya iya zuwa d'akin shi, yana zama kenan keran Ruky ya shigo wayar shi, tsaki yaja tare da kashe wayan ma gaba d'aya domin ahalin yanzu baya son mgn da kowa, yau dai yama k'asa babbace wani irin yanayi yake ciki domin yanda zuciyar sa ke masa suja ta wani bangaren kuma idan ya tuna da irin muguntan ya tana darwa Fatu sai yayi murmushi"
Su Fatu kuwa suna fita gidan su Saude suka wuce ko sallama Fatu batayi ba tashige kamar gidan uban ta haka ta shige dakin su Saude inda ta tsame ta kwance tana nishi da k'yar da k'yar kara sowa tay bakin gadon da sauri tace " Saude me ya tsame ki kike nishi haka k'amar wacce aka lakadawa d'an banzan duka da safen Nan"
Bud'e ido d'aya tayi ganin ba kowa a dakin sai Fatu ne ya tsata tashi zaune tace " wa 'kuwa ya isah ya dokeni da wanan sanyin safen, wlh wanke_wanke na gudoyi shine nace musu jikina ciwo yake" dariya Fatu tay tace " gaskiyar fa yanzu dai tashi mu zaga gari kad'an, kinga SANA ma tace muzaga da ita, murmushi Saude tay tare da mikewa tasa takalminta  tace" mutafi tun kafin Malam ya dawo idan ya dawo hanani fita zai yi, fita waje sukayi suka samu SONA na jiransu,  da gudu Saude ta bar gidan kafin Maman ta tay mgn ta bace, binta a baya sukayi, sosai suka zaga gari har ana Sallah a zahar suka dawo,suna dawowa SONA ta zauna sai mayar da numfashi take, Inna tace" tunda kince su Fatu zakibi ai kad'an kika gani, murmushi tayi tace " ai kuwa naga ta kaina domin nasha wahala sosai tana fad'ar haka ta shege d'aki"

Saif kuwa tunani yake har bacci ya dibisa sai Azhar ya tashi yay Alwala yawoce masallaci jiki ba k'wari"
Haka dai yinin ranan ya k'asan ce mishi ba walwala sosai, da d'andare Baffa ya kira Inna ya fad'a mata komai akan gobe da Asuba za'a d'aura Auren Fatu da Saif kafin su wuce, Inna tace" alhamdulillah hakan yayi k'yau Allah ya sanya alkairi, amen ya amsa dashi sun dad'e suna tattauna wa kafin ta mike ta koma d'akin ta inda ta tsami Fatu na kwace ita da SONA tana ta zuba mata surutu,itama bata ce komai ta kwanta tana jin hiran tasu duk akan labarin birni suke yinsa domin Fatu akoi ta dason zuwa birni sosai"
Da Asuba ko aka d'aura Auren *FATIMA*
*da*
*SAIFUNDIN*

Cikin bacci ta ji ana kiranta amma ta baasar domin komar ta bacci kenan bayan ta idar da Sallah taji Inna na kwala mata kira, bugu Inna ta kai mata a tsakiyar baya, sai ta mike a firgice tana cewa"haba Inna irin wanan bugun ai sai kisa bayana ya karye na rasa mijin Aure, sake baki Inna tay tace" kwantar da hankalin ki indai Aure ne ai yanzu ma an daura miki Auren"
Zaro ido tayi tace"Aure kuma?" Ni fa bana som irin wanan wasan Inna daga ce miki karki ballamin baya bare na k'asa samun miji shine zaki ce wani an d'aura min Aure"
Inna tace "eh ke da Yayan ki Saifu ba" dafe kirji tayi tace"kutubar uba Aure kuma da wanan wawan ai abunda bazai yuba ba kenan, ni fa wlh bana sonshi ko ganin sama bana sonyi don Allah Inna ki dai na kawo min mgnr sa anan, ki fad'a min miyin zan miki tunda kin katsemim bacci na, har na fara mafarkin gani nan a birni ina cin Naman kaza"
Kama kunninta Inna tay ta murd'a tace "dan gidan ku in na kara jin haka daga bakin ki sai na ciri bakin nan wlh" Yaya kine kice baki sonshi ai kuwa dole ki soshi"
Daura hannunta tay akai tare da fashe wa da kuka tana cewa "ni Fatu na shiga Tara daga mgn sai ace za'a ciremin baki,
Kama hannunta Inna tayi tace "zauna in fad'a miki wani mgn, ai kowa tsit tay ta zauna, kallonta Inna tayi tace " Fatu so nake ki bud'e kunnan ki kije abunda zan fada miki k'uma kimin alkairi bazaki bijere abunda zan fad'a miki ba, kimin alkairi" shiru tay na wasu minutes tana kallon fuskar Inna da alama dai babu wasa akan fuskar ta, wani irin buguwa kirjin ta yake,amma sai kuma ta daure tace " na yanda na miki alkawarin bazan bijere miki ba, murmushi Inna tayi tace " gaskiya ne an d'aura miki Aure da Yayan ki Saifu daman kuma alkawarin da mahaifinshi ya dauka wa mahaifinki ne tun kafin yasuwar su Kinga lkc yayi d'aya kamata ya cika alkairi shine aka d'aura muku Auren ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login