Showing 30001 words to 33000 words out of 113152 words
ta dan leka kofar taga fuskar Ummi, wani kara ta saki ta bude kofar da sauri ta rungumeta ba tare da ta lura da sauran kawayen nata ba, Aisha tace "wato ummi kadae kika sani ko" juyawa tayi da sauri tana kallonsu ta wara ido cike da jin ddi tace "waw amma kun burgeni wllh don Allah ku shigo, kai naji ddi ganin ku wllh" rasa abinda xata basu Ashnaah tayi, ta nufi sama da sauri ta Ciro dubu daya cikin kudinta ta sauko tace masu tana xuwa ta nufi gun mai gadi, ta basa kudin tace soft drinks da ruwa ba duka xae karbo mata, ya karbi kudin snn ta juya ta koma cikin gidan, "amma wa yyi maku kwatance ku ka gane hka" Ummi tacev"Anty shafa mana, wae Ashnaah ya maganar karatun ki, baxa ki lallaba mijin ki ba ya bari ki koma, Kinga next month xa mu fara exams fa" Ashnaah ta marairaice ta xauna tana kallonsu tace "Ku ce Allah next month be exams" bilkisu tayi dariya tace "Sae ma mun ce Allah ko" Ashnaah kmr xata yi kuka tace "to wa xae bar ni in koma ynxu..." sae ta fashe masu da kuka abun dariya abun tausayi, ummi ta danne dariyarta tace "to meye abun kuka, baxa ki lallaba mijin ki ba ya bari ki koma" nn da nn Ashnaah ta daina kukan ta hade rae tace "waye mijina kuma" Ummi da sauran suka kwashe da dariya suka ce "mai gidan nn mana" Ashnaah ta hade rae tace "kun ga in kun san xarafi na ku ka xo ci to ku tashi kuyi tafiyar ku ngdd" ssae suka dinga dariya Ashnaah da ta kulu matuka ta rasa ma me xata ce masu, Khadija tace "kinga ynxu dae ayi facing reality, wllh ki lallabasa ya bari ki ci gaba da karatun ki kar ki cuce kanki" Ashnaah tace "in lallaba wa? tabdi" tsaki tayi dae dae lkcn da aka bude kofar falon, Ashnaah ta mike da sauri kuma a tsorace don ganin Wanda xae shigo, Khaleel ne ya shigo falon yana sanye da farar 3qtr da bakar polo yana rike da leda a hannunsa, hanjin cikin Ashnaah sae da ya kada dob tsoro amma ta wani hade rae duk da irin ynda gabanta ke faduwa ta koma ta xauna,cikin tafiyarsa ta kasaita ya karaso cikin falon yana kallon frnds din nata, Ummi ce kadae tayi karfin halin gaishesa, ya amsa murmushi dauke a fuskarsa snn sauran ma suka gaishesa ya amsa duk yana tambayarsu ya hanya, suka amsa da lfya lau snn ya ajiye ledan hannunsa nn gaban Ashnaah ya nufi sama, Aisha tace "wae wnn shine mijin naki Ashnaah" Ashnaah ta tabe baki tace "gashi kin gane ma idon ki kuwa" Bilkisu tace "waow amma ya hadu ya hadu har ya gaji kai!" hade rae Ashnaah tayi amma bata ce komai ba sae tabe baki da tayi, Aisha tace "tabdi, wnn din ne baki so Ashnaah, wayyo ina ma ni na samesa" Ashnaah ta kuma hade rae bata dae ce komai ba, Ummi kam hmmm kawae tace, Maryam tace "to baxa ki tafi ki masa sannu da xuwa ba" a fusace Ashnaah tace "Don Allah ku rabu dani" ummi ta mike tace "kun ga muna da lecture Karfe daya ku tashi mu kama hanyar sch, gashi ma mijinta ya dawo mu kama gabanmu" Ashnaah tace "haba plss da wuri hka dama ba yini Min kuka xo ba" kmr xata yi kuka ta karashe maganar, Ummi tace "kar ki damu xa mu dawo fateema, muna da test ne Yau wllh" Ashnaah ta bude ledan da Khaleel ya ajiye mata taga take away na abinci ne da drinks, tace "to ga abinci ku tsaya ku ci plss" duk suka ce a koshe suke, ta bata rae tace "au hka xa ku min" dariya suka yi suka ce kar ta damu sae sun kuma dawowa, suna tsaye bakin kofa Khaleel ya sauko shima xae fita, Ashnaah ta juya tana kallonsa tace "wae xa su tafi fa" rasa ma me xae ce mata yyi, can yace "OK ina xuwa" snn ya koma sama, ummi tace "kai Ashnaah to me xae mana" saukowa yyi yana rike da car key yace "mu je in sauke ku to" da sauri Ashnaah tace "A'a kudin mota fa xa ka basu kasan inda xa su ne"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
39.....
Dubu biyar Khaleel ya ciro ya mika mata yana kallonta, ta karbe
kudin ta bi bayan frnds dinta da sauri don har sun bar falon suna
dariya, bin ta yyi da kallo ganin ynda take tafiya har ta isa gun
frnds din nata snn ya kauda kai, da kyar Ashnaah ta tilasta su
suka karba kudin don kin karba suka yi da wae sun gode, Khaleel
dae na tsaye daga bakin kofa yana danna wayarsa lkci lkci ya kan
daga kai ya kallesu, ummi tace "to ki taya mu yi masa gdya
Ashnaah, sae wani lkcn kuma" da sauri Khaleel ya daga kai yana
kallon Ashnaah jin sunan da ummi ta kirata da shi wae Ashnaah,
meye kuma Ashnaah, Ashnaah kam har bakin gate ta rakasu snn
ta dawo abunta, har lkcn yana tsaye daga bakin kofa, ta gefensa
ta bi xata shiga falon ya fixgota yana mata wani irin kallo yace "wa
ya baki izinin shigo min da baki gidana?" Duk da ta dan tsorata
amma hkn bae Hana ta dakewa ba tace "to ni nasan ma wa ya
kawo su ba kawae ganinsu nayi ba nima" kallon cikin idonta yake,
ita ma hka, sunkuyar da kanta tayi da sauri don hka kawae taji
kunya ya kamata tuna abinda ya faru jiya da daddare da tayi, ko
hkn ya tuna shima oho, don kawae gani tayi ya dauke kai shima
ya saketa ya nufi gun dayan motarsa da ke Parke a parkn space
din gidan, don Wanda ya saba fita da ya baro shi a clinic,
Ashnaah ta shige falon da sauri abunta, sae da ta ji fitar motarsa
snn ta bude abincin da ya kawo mata, tuwo ta gani da miyar
vegetable yaji nama da kaza, nn da nn ta mike da sauri ta hau
sama ta wanke hannunta ta sauko ta shiga tura kayanta, bude
kofar falon aka yi ta juya da sauri har xata boye abincin ta ga
Meenah ce, ta Mike da sauri tana washe fararen hakoranta tace
"lah ashe dae xa ki xo, shigo mana kika tsaya daga bakin kofa"
Meenah tace "amma dae Khaleel baya nn koh" Ashnaah tace
"waye kuma Khaleel" tsakaninta da Allah tayi tambayar don manta
sunansa take, Meenah ta harareta, da sauri tace "ohh ya fita ynxun
nn, kinsan ni manta sunansa ma nake wllh wllh" Meenah ta karaso
falon har lkcn tana hararan Ashnaah tace "sunan mijin naki kike
mancewa" Ashnaah tace "wllh mance sunansa nake, khaleed ko
wa yake, to wae ma ba sae ka damu da mutun xaka rike sunansa
ba" Meenah ta fashe da dariya tace "ban gane ba, ke da sweetyn
naki kuma" Ashnaah ta tabe baki tace "sweetyn su dae, Sweetyna
na inda yake, Allah sarki usman" Meenah da mmki tace "ban gane
ba" Ashnaah tace "ae idan da Akwae Wanda na tsana a duniya a
ynxu bae wuce dan uwanki ba, Allah yasa baxa ki ji haushi na ba"
Meenah ta xaune nn gabanta tace "ke bani in sha, ae nima duk
duniya bn jin Akwae wnda na tsana irinsa, amma ina kuka hadu
da shi to har kika yrda kika auresa, ae da na ganki kafin lkcn bikin
da na baki shawaran kar ki auresa don...." Ashnaah ta fashe da
kukan takaici ta shiga ba ma Meenah lbrin ynda Khaleel ya aureta,
har ta gama lbrin bakin Meenah a bude yake, don kanta daga
Karshe ta rufe bakin tace "ikon Allah, sae kace a film, amma shine
kike xaune har Yau a gidan sa baki san ynda kika yi kika fidda
kanki ba" Meenah ta girgixa Kai da mugun mamaki tace "kan bu,
amma naga kkrin ki ae in nice wllh wllh bna kwararren sati biyu a
gidan ka, ka hada ni da abbana ka raba ni da momyna, kayi
sanadin daina karatuna uban me xan yi gidan ka, kai har kin bn
haushi wllh, wayyo ina ma ni ce" Ashnaah ta dan marairaice tace
"to bn san ya xan yi ba Meenah, bbu irin fitsarar da bana masa
amma sae dae ma ya nakada min shegen duka" Meenah ta xaro
ido tace "duka? Kika tsaya yake dukan ki, amma ke bnxa ce wllh"
Ashnaah tace "to ae ba iya ramawa xan yi ba baki ganin ynda
yake ne, Kinga wani lkcn ma da yunwa yake bari na fa wllh, ynxu
ki tafi kitchen ki ga a kulle yake tun safe yar shinkafa na bada
kudin a siyo min" ta karashe mgnr kmr xata yi kuka, a hnkli
Meenah tace "amma dae tsaya, baki basa kan ki ba dae koh"
Ashnaah tace "sae kace ina hauka tabdi" Meenah tace "to
alhmdllh, amma dae meye to na kishi da kika ji ya ce xae aure
Zeenat har da wani daukan nmbr babanta" Ashnaah tace "kishi
kuma, ae so nake in gaya ma Baban Zeenat din shine ya dauke
masu yar su don su hukunta shi" Meenah ta fashe da dariya tace
"kuma fa hka ne, to ynxu kin kirasa din ne, Ashnaah tace " ina
naga wayar kiran, ae bani da waya, ki ara min naki ynxu in kira"
Meenah ta xaro ido tace "baki san xa a iya ganowa ba, kuma
gashi Zeenat din tasan nmbr na" Ashnaah tace "to ina da dubu
takwas in baki ki siyo min waya karama sae a sa Min sim, ae
kudin xae isa ko" Meenah tace "to mu tafi tare mana" Ashnaah ta
xaro ido tace "ae ya gaya ma masu gadin kar su bar ni in fita, da
ana bari na in fita da tuni na gudu na kara gaba ae" Meenah ta
fashe da dariya, Ashnaah tace "bari in dauko kudin" meenat tace
"to amma ba ynxu xae dawo ba dae ko, kar ya xo ya sameni in
shiga uku" Ashnaah tayi dariya tace "ae sae dare yake dawowa
gantalallen"
~Dr Khaleel ~ By Khaleesat Haiydar
40.....
Ashnaah ta sauko rike da dubu takwas din da ya rage cikin kudin da aka bata ta mika ma Meenah, Meenah ta kirga snn ta xuge jaka ta xuba su ciki ta kulle, tana kallon abincin gaban Ashnaah tace "to ina kika samo tuwon nn" Ashnaah ta dan tabe baki tace "wae fa kansa ya siyo ma xae ci to da ya gan ni da baki sae kunya ta kamasa kmr xae nutse shine fa ya ajiye min, kinsan dae ba sata kadae bne abun kunya" dariya kawae Meenah ke yi, ita kam komae na Ashnaah dariya yake bata, gata dae yarinya amma in ta xaro maka mgna sae kace babba yyi ta, Ashnaah na kallonta da mamaki tace "ae gskya ne, ko ruwan fa da xan sha gidan nn bbu sae dae in je in sha na famfo duk tsutsa, ko me aikin gidan mu wllh ruwan gora take sha, to ina dalili" Meenah tayi dariyarta me isarta tace "to shi wani ruwa yake sha tunda bbu ruwa a gidan" Ashnaah tayi murmushi ta mike tace "ina xuwa in nuna maki" sama ta nufa ta bude falonsa ta shiga snn ta nufi fridge dinsa, a rufe ta tarda fridge din ta cije dan yatsa a xuciyarta tace "ae sae na nema wllh" bbu rabon xata wahala ta hango keyn kan fridge din ta bude da sauri tana kallon ciki, wines din basu fi biyar ciki ba, biyu iri daya, uku iri daya, kinkimansu tayi gaba daya ta nufi gun Meenah ta dire su gabanta ta nemi guri ta xauna tace "kin gansu nn" da mmki Meenah ke kallon kwalaban ta daga tana kallon Ashnaah tace "wnn ae giya ce fateema" Ashnaah ta tabe baki tace "to su ne ruwansa a gidan nn, in ya kafa kai baya ajiyewa sae ya kwankwade gaba daya" Meenah da kanta yyi mugun daurewa tace "dama Khaleel na shan giya" Ashnaah tace "gashi ko kin gani, suna can da yawa a fridge dinsa kala kala" Meenah tace "haba shi yasa ko da yaushe xan ji fridge dinsa a rufe idan naje can gidan su" Ashnaah tace "to ynxun ma an gaya maki a bude na samu, da kyar na samo makullin," Meenah tace "dole ko da yaushe xaka gansa cikin rashin fara'a, kin san Allah tunda nake kallon arxiki bae taba hada mu ba" Ashnaah tace "ga tuwo ki ci bari in je inyi sllh, ko azahar bn yi ba" Meenah tace "to je ki dawo in baki wata shawara" Ashnaah tace "to" snn ta nufi sama don yin alwala tayi sllh. Khaleel na xaune office bayan ya fito daga theatre ya jinginar da kansa jikin office chair dinsa idonsa lumshe kmr me bacci aka bude office dinsa, ya bude ido da sauri don ganin wanda xae shigo, Ameesha ce ta shigo office din da sallamarta, ya mayar da kansa ya lumshe idonsa, ta dan tsaya nesa da shi tace "ka gaji koh" ya bude ido yana kallonta yace "yep, bacci ma nake ji" tace "to abinci fa, ina tuwon da na kawo maka daxu" ta fadi hka tana dudduba abincin a office din, da kmr baxae ce komae ba sae kuma yace "sorry na bayar da shi" shiru tayi tana kallonsa, ya mike xaune da kyau yace "kin yi fushi ne" girgixa masa kai da sauri tayi, yyi murmushi yace "amma ae na ci kadan, vegetable din yyi ddi, kin yi kokari, u re a gud cook" murmushi tayi da ya kara fito da ainahin kyanta, a hankali tace "thank yhu" ya gyada mata kai yana murmushi snn yace "gida xa ki ynxu ne" ta gyada masa kai alamar eh, ya mike ya dauki makullin motarsa yace "mu je gidana ki min girki sae in kai ki gida" shiru tayi tana kallonsa, yace "ko baxa ki bne" a hnkli tace matarka fa, ya galla mata harara yace "waye hka" kasa cewa komae tayi sae kallonsa take, yyi tsaki ya kwashi wayoyinsa yana kallon agogo ya ga Karfe biyar saura, Yace "mu je in xa ki" ba musu ta bi bayansa suka fita ya kulle office dinsa, sae da ta fara xuwa office din dad dinta ta dauki handbag dinta snn ta sauko tayi ma sauran nurse din sallama ta nufi gun motar Khaleel don yana ciki yana jiranta. Ashnaah da Meenah na xaune har lkcn a falo, Ashnaah na digestin duk abinda Meenah tace mata, bbu irin abinda Meenah bata kintsa mata ba, gate suka ji an bude, Meenah ta mike tsaye da sauri tace "waye hka xae shigo" Ashnaah ta wara ido tana kallon agogo, jin karar motar Khaleel yasa ta kalli kwalaban wine din dake xube gabansu har lkcn bata mayar ba, mikewa tayi a tsorace tace "wayyo na shiga uku shine ya dawo, me ya dawo da shi ynxu" Meenah ta xaro ido ita ma a tsorace tace "kin shiga uku ko na shiga uku," kwashe kwalaben Ashnaah tayi ta nufi kitchen da su da gudu jikinta na rawa sae kuma ta fito da su duk a rude, sae ca take na shiga uku ina xan Kai su xae iya shiga kitchen ya gansu, kitchen ta kuma komawa da sauri ta boye su cikin store, ko da ta fito bata ga Meenah a falon ba, xata bar falon ita ma aka bude kofa, ta juya da sauri tana kallonsa nn da nn ta hade rae, ya kwaso takalman da ya gani bakin kofa da mamaki yana kallon Ashnaar yace "takalman waye wnn"
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
41
Shiru Ashnaah tayi tana kallon Ameesha da ke bayan Khaleel ta ki shigowa, ya daka mata tsawa yace "ba kya ji na ne, nace takalmin waye wnn" Ashnaah tace "wacece wnn a bayan ka" bude baki yyi da mmki yana kallonta yace "ina maki tambaya kina min tambaya" dauke kanta tayi fuskarta a daure taki cewa komae, ya kuma daka mata tsawa yace "nace takalmin waye wnn" ta juya tana kallonsa tace "sae ka fara gaya min wacece wancan a bayan ka" ta karashe mgnr tana hararansa, ihu ta fasa ganin ya yo kanta ta nufi bayan kujera da sauri tana cewa "wayyo wllh xan gaya maka ka tsaya" ganin kamata yake son yi yasa tace "don Allah kayi hkuri na wa ne ina son in fita in siyo abu ne sae mai gadi ya hanani, sae na manta ban shigo da shi ba" tsayawa kallonta yy, yyi kwafa yace "bace min a falo" hararan Ameesha tayi snn ta haura sama. Bayan kofarta ta tarda Meenah a labe, ta fada kan gado ta dinga kyalkyala dariya, Meenah ta fito da sauri ta mata alamar tayi shiru, Ashnaah tace "ae ba shigo wa xae yi ba," a hankali Meenah tace "to ya xa ayi in bar gidan nn yau, ga shi nace ma momy ba ddewa xan yi ba" Ashnaah tace "ae xae shi ga dakinsa sae ki fita da gudu, muyi hirar mu don Allah," Meenah ta galla mata harara tace "da wani bakin xan yi hira, kin san ynda ciki na ke kara kuwa, ba mutun ci gare mijin nn naki ba sae ya iya wurga ni waje wllh" Ashnaah tayi dariya tace "to sae kiyi ta tsayuwan, nace maki baya shigo min daki sae in nayi laifi" dakinsa suka ji ya bude, Meenah ta koma bayan kofa da sauri har tana bugewa, Ashnaah ta toshe bakinta kar ta Tona masu asiri da dariya, fitowa Meenah tayi tace "to ya shiga dakin, ta ina xan bi" Ashnaah ta mike tace "ina xuwa" snn ta fice, ba a jima ba ta dawo rike da takalman Meenah tace "oya xo ki gudu yarinyar da ya kawo ma na kitchen, amma yaushe xa ki kuma dawowa don Allah" Meenah tace "gskya ba ynxu ba" Ashnaah ta marairaice tace "haba don Allah to wayata fa gashi fa kinsan abinda yasa nake son siyan wayar" Meenah tace "to xan yi kokari gobe in na siya in kawo maki amma fa baxan dde ba" Ashnaah tace "yauwa don Allah kar ki manta ki siyo min maganin ciwon ciki in xaki xo, wllh tsoro nake ji period dina ya kusa xuwa kuma wahala nake sha wllh, ynxu ma ya fara damuna" Meenah tace "to Allah sa