Showing 15001 words to 18000 words out of 113152 words
dae bata kuma cewa komae ba har suka isa gate dai dai bakin gate suka ci karo da Khaleel yyi parkin motarsa a waje xae shigo, wani mugun kallo yake ma Meenah yace "me ya shigo da ke gidana" bata ko kallesa ba tayi gaba abunta da sauri ta nufi titi, ya kalli Zeenat yace "me kuka xo yi" Zeenat tace "abinci momy ta ba mu mu kawo" yace "ok mu shiga ki dan min abu, xan mayar da ke gida" shiru tayi tana kallonsa, ya juya ya shige gidan, ta juya ta bi sa a hankali. Ashnaah na jin fitarsu Zeenat dama ta mike da sauri ta sauko kasa don ganin me aka kawo mata a kula, jollof ne ya ji nama da plantain, har wani rawa jikinta yake ta bude kulan kasa ta ga lafiyayyen farfesun kaxa, da gudu ta mike ta shige bathroom da sauri ta wanke hannunta ta kuskure baki ta fito ta xauna ta shiga tura abincin ta, Khaleel ya juya yana kallon Zeenat dake tsaye daga bakin kofa yace "abinci xa ki girka min, ko baxa ki iya ba" ta dan yi shiru snn tace "me xa a dafa" ya xauna kan kujera ya dauki remote yana canxa tashar tvn dake aiki yace "simple food, da kika ga ya fi sauri," mikewa yyi yace "mu je in nuna maki kitchen din da kayan abinci" ba musu ta bi bayansa suka isa kitchen din ya Ciro makulli ya bude, ita dae sae kallonsa take da mamaki, to meye na wani rufe kitchen" nuna mata komai yyi ya juya ya fice daga dakin ya nufi sama, Dakin Ashnaah ya bude ta tura kulan gabanta da sauri tana kkrin goge bakinta ta tashi ya shigo dakin, kunya ya kamata gashi da hannu take cin abinci, dariya ya shiga yi yana kallonta, ta wani hade rae har lkcn hannunta na boye bayanta tana masa mugun kallo, yace "duk yunwarce hka" tsaki tayi ta kauda kanta, yana shafa kansa yace "kadan kika fara gani yarinya," juyawa yyi ya fice daga dakin, ta ja tsakin takaici tace "kae dae ne mayunwaci, bnxa kawae" mikewa tayi don takaici ta shige bathroom wanke hannunta, duk sae ta ji abincin ya fice ranta, kamshin soya miya da taji kasa yasa ta kasa xama daki ta sakko kasa, to wa ke girki, bbu kowa falon hkn yasa ta nufi kitchen da sauri, da mamaki take kallon Zeenat, ita dae Zeenah kallo daya tayi mata ta ci gaba da abinda take, Ashnaah tayi tsaki tace "Aikin bnxa, da kawae yyi xaman auren da ke, karewar kawo ki ki masa girki knn" Zeenat ta juya tana kallonta bata dae ce komai va, amma ba karamin bata mata rae kalaman Ashnaah suka yi ba, ita Ashnaah duk tunanin ta kanwarshi ce, ta ja dogon tsaki ta fice daga kitchen din suka kusa cin karo da shi, yana mata mugun kallo yace "me kika sakko yi" hararsa tayi tace "kai me ya sakko da kai xaka min wnn silly tambayar" ya tsaya kallonta daga sama xuwa kasa snn ya wani wanke fuskarta da mari, ta dafe kuncinta a gigice tace ka mareni? " bata rufe baki va ya kuma sauke mata wani, ya fixgota da karfi ya nufi sama da ita ya bude dakinta ya jefata ciki, sae da taga ya kulle kofar snn cikin kuka ta shiga cewa "Allah ya Isar min mugu kawae mahaukaci kuma wllh sae na...." tsit tayi jin ya bude kofar Dakin ta Mike da gudu har tana neman faduwa ta shige bathroom ta kulle kofar da key, ya juya ya fice daga dakin, karfe daya da kusan rabi Zeenat ta gama hada masa Shinkafa da miya ta ajiye masa nn tsakiyar falon, ta dan jingina jikin kujera tana jiran saukowarsa, ta kai minti goma a tsaye sae gashi ya sakko cikin kananan kaya yana kallonta yace "har kin gama" tace "eh gida xan tafi" Bae ce komae ba ya karaso cikin falon ya xauna yana kallon abincin yace "sllh fa" ta dan yi shiru snn tace "idan naje can gida na yi" ya daga kai yana kallonta da kmr baxae ce komae ba sae kuma ya jawo plate ya shiga diban abincin gabansa yace "sae ki ce min kina period" ya daga kai yyi murmushi yana kallonta yace "ki ba hka ba" kasa cewa komae tayi, ya fara cin abincin gabansa yace "ki xo ki diba kema" ta kauda kai tace "na koshi" Bae ce mata komae ba sae cin abincin sa yake, ta kasa daina kallonsa, cokali biyar yyi ya daga kai ya kalleta suka hada ido ta dauke kanta da sauri yyi murmushi ya mike yace "kwashi abincin ki kae min dinnin anjima idan na dawo xan ci, ba musu ta karaso cikin falon ta duka ta kwashe farantin abincin ta nufi dinnin da shi, shi kuma ya haura sama, dakinsa ya shiga ya fara wanke bakinsa a bathroom snn ya fito ya dauki makullin motarsa ya fita, dakin Ashnaah ya nufa, tana xaune kasan dakin ta hade kanta da gwiwa, tana jin an bude kofarta ta dago da sauri, ya hade rae yace "ke nake jira" tayi tsaki ta dauke kanta, ya karaso cikin Dakin ta Mike tsaye a tsorace tace "ni me nayi kuma" ya wani hade rae yace dauki hijab din ki ki fita muje, ta nufi drawer dinta kmr xata yi kuka ta dauki hijab din tasa ya nuna mata kofa ta nufi kofar yana biye da ita a baya, suna sauka downstairs ya kalli Zeenat yace "mu tafi Zeenah" Zeenah ta nufi kofar fita Ashnaah ta juya tana masa kallon bnxa tace "ina xaka kai ni," irin kallon da taga yana mata yasa ta nufi kofa da sauri tana tsaki, Khaleel ya bude seat din gaba yana kallon Zeenat dake tsaye jikin motar yace "shiga" ta dan xaro ido tace "ni" hararanta yyi yace "ki shiga nace" kasa shiga tayi har lkcn tana tsaye, ganin ynda yake kallonta yasa ta dan raba ta gefensa ta shiga gaban motar, Ashnaah dae na kallonsu tayi tsaki ta bude bck seat ta shige abunta a xuciyarta tace "ki ba komae ka xama driverna dae" har suka bar gidan Ashnaah bata kalli gaban motar ba idonta na kan glass kawae, firarsa kawae yake da Zeenat da bata cewa komae, can dae ya juya ya kalleta ya mayar da idonsa kan titi yace "ni kike sharewa ko" ta kallesa tace "ae ina jin ka," Bae kuma ce mata komae ba har suka iso traffic light snn ya juya yana kallonta yace "to me nace na karshe" ko kadan bata san me Khaleel ke cewa ba don duk a takure take a motar sbda Ashnaah dake baya, ta fara kame kame tace "aa ina fa jin ka ya Khaleel" ya kamo hannunta yana kallonta yace "tsoron warcan abar ta bayan mota kike" Zeenat ta fixge hannunta da sauri duk jikinta yyi sanyi, maganar sa tayi confuse dinta, yyi murmushi ya kalli Ashnaah ta madubi yaga murmushi take ma wani mutum dake gefen su cikin lafiyayyen motarsa yana daga mata hannu, Khaleel ya hade rae yana kallonta yace "na ga alamar ke jahila ce da auren nawa a kanki kike ma wani kato dariya" Ashnaah tace "da auren ka a Kansu dae ba ni ba, don har ynxu ni bbu abinda ya raba ni da xama budurwar da nake, ko ina budurwa xata shiga nima xan shiga don ni ba matan auren kowa bace," Khaleel yyi murmushi yana kallonta yace "hka kika ce ko? xaki raina kan ki yarinya, sae kinyi da kin sanin furucin ki" Ashnaah ta tabe baki tace "kai ma hka" Zeenat ta kasa daga kai don tuni suka gama daure mata kai, Khaleel dae yyi murmushi kawae ya ja motarsa, dae dae kofar gidansu Meenah yyi parkin Zeenat ta bude motar xata fita ya riko hannunta yace "bbu sallama" ta sunkuyar da kanta bata ce komae ba, ya dago kanta yana kallon fuskarta, sae kallonsu kawae Ashnaah take da mmki, ba sae an gaya mata ba tasan Zeenat ba kanwarsa bace, nn da nn taji wata mugun tsanarta ya dirar mata a xuciya ta dauke kan ta daga kallonsu da sauri, Khaleel ya saketa yace "ltr da daddare xan xo" Zeenat bata ce komae ba don duk ya birkita mata kwakwalwa, ta fice daga motar da sauri ba tare da ta kuma kallonsa ba, yyi murmushi yyi reverse suka bar anguwar. Khaleel ya gama parkin a parkin space din gidansu ya fito yana kallon Ashnaah yace "ni kike jiran in fiddo ki koh" dauke kanta tayi, tayi kmr bata san da ita yake ba, ya bude back seat ya fixgota ta kusan faduwa ya rufe motarsa ya nufi cikin gida, kin bin sa tayi har yyi nisa ya juya ya ganta tsaye, ya dawo a fusace ta shiga tahowa da sauri dae dae gabanta ya ja burki yana mata mugun kallo yace "Ki dinga kiyayata fa" dauke kai tayi yyi kwafa ya ci gaba da tafiyarsa ta shiga binsa tana masa mugun kallo har suka shigo falonsu, sama ya nufa ita kuma tayi xaman ta kan kujera fuskarta a daure, ko ba a gaya mata ba ta ga alamar kmr gidansu ya kawota, ba a dau lkci ba ya sakko tare da mum dinsa da wasu yan uwanta suka shigo falon, kallo daya Ashnaah tayi masu ta dauke kai, suka xaxxauna suna mata sannu da xuwa taki ko da kallon inda suke, momy ce tayi karfin hali tace "ina yini amarya" Ashnaah ta dan kalleta ta maxa ta dauke kai snn tana wasa da xoben hannunta tace "lfya lau" Khaleel ji yyi kmr an Sara masa guduma a ka, ya kasa daina kallon Ashnaah ga wani kunya da ya ji kmr ya nutse, yan uwan momy suka mike kowa ya nufi sama, momy kam bata fasa cewa ya bakunta ba, ba kunya ba tsoron Allah Ashnaah tace "da gdya" momy ta mike tace "bari a kawo maki ruwan sanyi" Ashnaah tace "to" kuma ko ba a gaya mata va tasan mahaifiyar Khaleel ce don ga kama, kitchen momy ta nufa, Khaleel ya taso da sauri ya isa gabanta yace "ita mum din tawa kika ki gaidawa sbda ba a maki tarbiya gidan Ku ba" Ashnaah tayi tsaki tace "a hka ka gan ni ka aura ae, bnyi niyyar gaidatan ba sae me" ta ja dogon tsaki tana hararansa ta maida hankalinta kan kallon da take, ransa yyi mugun bace ya mike da kyar ya dunkule hannayensa ya haura sama Ashnaah ta bi sa da harara ta tabe baki, momy ta dawo falo rike da farantin Ashnaah ta mike ta dan Risina ta karba tace "dama kin bar shi momy daga gida Muke ae" momy tace "shine kuma baxa a sha ruwa ba don daga gida ake" sae da momy ta xauna snn Ashnaah ta sauko har kasa ta gaisheta, momy tace "lfya lau Fateemah ya kewan gida" Ashnaah ta dan yi murmushi bata ce komae ba, momy ta kira Rukayya ta sakko snn suka wuce sama da Ashnaah, tsaf momy ta kare Ashnaah gaban yan uwanta dake ta mitan ba yar gidan mutunci Khaleel ya auro va, bbu ynda suka iya da Yayar tasu duk suka ja bakin su suka yi shiru, karfe biyar da kusan rabi duk bakin dake gidan tun biki suka watse kowa ya kama gabansa, Khaleel ya kai kanwar mum dinsa da suke daki daya gida, ssae yaji kunyar fadan da take masa wae ya je ya auro yarinyar da va yar gidan mutunci va don bata da kunya surkarta ce xata gaisheta kuma ta amsa, in ma su baxata mutuntasu ba ae ya kamata ta mutunta uwar mijinta, har muka bar gidan ko sallama bata fito tayi mana ba sbda rashin kunya, ta girgixa kai tace "me ya kai ka Khaleel, a ina ka samo ta, kai ynxu kaji ddin abinda tayi ma uwarka, yarinyar da bata wuce xama jikarta ba idan da kae mace ne" Khaleel ya kasa cewa komae xuciyarsa sae tafarfasa yake yana tunanin me xae ma Ashnaah ya ji sanyi, irin fadar da mum din Meenah tayi masa knn jiya da daddare wae yaje ya auro ya Mara mutunci wato fitsara xata dinga yi ma danginsa ko, Khaleel yyi murmushi xuciyarsa na raya masa irin abinda xae ma Ashnaah, har ta gama bambaminta Khaleel Bae ce komae ba, bayan driving din kusan minti talatin ya isa gidanta ya ajiye ta ya bata hkuri ssae snn ya kama hanyar gida xuciyarsa na tafarfasa.
45 mins · Khaleesat Haiydar...
[10/10, 6:37 AM] +234 701 117 6189: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
23.....
Karfe takwas da kusan rabi Khaleel ya shigo gidansu, bbu kowa falo sae Rukayya da ke dan goge goge, Khaleel yace "Abba ya dawo ne ke" Rukayya tayi masa sannu da xuwa snn tace ae yana Abuja Bae dawo ba, yace "ok ummi fa?" Rukayya tace "tana daki" yace "yarinyar nn fa" rukayya tace "wace yarinya" ya harareta yace "warce na kawo gidan nn" Rukayya tace "oh ita ma tana sama ina jin, ga abinci can ummi ta ajiye maka a dinning" Bae kuma kallonta ba ya nufi sama ya bude Dakin umminsa ya shiga, ya samu ummi na sllh, Ashnaah kuma na xaune kasan carpet daga kusa da gado tana kallo don ita tayi sllhnta, Bae ko kalleta ba ita ma hka, ya nemi kujera ya xauna yana kallon wristwatch din hannunsa Allah Allah kawae yake ummi ta idar su bar gidan da Ashnaah, ummi ta sallame ta gama adduarta tace "ka dawo Khaleel, amma ka jima, ga abincin ka can kan dinnin" yace "ni na ci abinci gidan mum ummi, gida xamu wuce ynxu dare yyi" Ashnaah ta daga kai tana kallonsa tace "amma ca kayi min a nn xamu kwana fa ka manta ne" Ummi tace "nima dae hka tace min, kuma kace xa ku tafi ynxu ga shi dare yyi" kasa cewa komae Khaleel yyi sae kallon Ashnaah yake, ta hararesa ta ci gaba da kallonta, ya mike ba don ransa ya so ba ko kadan sae don Bae iya jayayya da umminsa yace "to shkkn ummi bari in yi wanka," yana fita ummi ta juya tana kallon Ashnaah tace "to tashi ki kai masa abincin da na ajiye masa kan dinnin Fateemah, sae ki ce rukayya ta nuna maki dakin sa" Ran Ashnaah Bae so ba amma bata mata musu ba ta mike tace "to momy" snn ta fita kasa xuwa falo, sae da ta dauko farantin abincin snn tana kallon rukayya bbu yabo bbu fallasa tace "momy tace ki rakani dakin yayanki" rukayya bata ce komae ba ta nufi sama don kai ta dakin Ashnaah na biye da ita a baya, suna haurawa sama ta nuna mata Dakin Khaleel, Ashnaah ta murda kofar ta bude ta shiga abunta, yana xaune kan gado ya dafe kansa, ya dago da sauri don ganin wanda ya shigo fuskarsa a daure, ta ajiye masa abincin nn bakin kofa ta fice abunta ta koma Dakin ummi, ummi dae bata ce mata komae ba Ashnaah ta xauna ta ci gaba da kallonta tana ba ummi lbrin ynda film din yake, ummi na ta sauraronta. Karfe sha daya saura bayan an gama film din ummi tace "baxa ki kwanta ba Fateemah dare fa yyi" Ashnaah da har ta fara gyangyadi nn xaunen tace "xan kwanta momy" ummi ta kira Rukayya tace ta dauko ma Ashnaah kaya Mara nauyi tasa ta kwanta, rukayya ta dauko mata wani sabon kayan baccinta ta bata, Ashnaah ta karba ummi tace "to tashi ki tafi bayi ki canxa ko" Ashnaah tace "to" snn ta mike ta shiga bathroom ta sa kayan baccin snn ta linke kayan da ta cire ta maida hijab dinta har kasa ta fito. Xaune ta samu Khaleel a dakin, ta hade rae ta xauna inda take abunta, Ashnaah xata kwanta nn inda take a xaune ummi tace "ki tafi can dakin ki kwanta mana Fateemah" ta yi shiru bata ce komae ba amma ranta Bae so ba, can dae tace "to" snn ta mike tace sae da safe ta fice daga dakin ta nufi dakin Rukayya ta dan bude ta ga har ta kashe wuta abunta, tsaki tayi ta nufi dakin Khaleel ta bude a hankali ta shiga ta kwanta ta shige cikin bargo nn da nn bacci ya dauketa don dama baccin take ji"
[10/10, 6:37 AM] +234 701 117 6189: ~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
24......
karfe sha biyu saura Khaleel ya bude kofar dakinsa ya shigo ya kulle yana kallon Ashnaah dake bacci hankalinta kwance cikin bargo, ya tsaya daga nn bakin kofar yana kallonta da mamaki, can yyi murmushi ya gyada kansa alamar xaki gane kurenki snn ya nufi bathroom, wanka ya kuma yi ya fito daure da towel yana goge gashin kansa da karamar towel, bude wardrobe dinsa yyi ga ciro sleepn robe dinsa fari ya sa, wayarsa dake gaban madubi ya shiga kara ya karasa gaban madubin yana kallon screen din wayar, karan wayar ya farkar da Ashnaah ta bude fuskarta a hankali tana kallonsa, yana tsaye gaban madubin yana kallon wayar har ya katse snn ya kashe wayar gaba daya, Ashnaah ta maida kanta cikin bargo da sauri, bargo babba ya dauko cikin wardrobe ya shimfida a kasa snn ya karasa daya side din da Ashnaah take ya dauki pillow ya ajiye kan bargon snn ya kashe wutan dakin ya kunna bedside lamp, sae a snn Ashnaah ta kuma bude fuskarta ta ga ya nufi fridge ya bude da key ya ciro wata kwalba, ya xauna gefen gado can nesa da ita ya bude ya shiga shan abun sa, sae kallonsa Ashnaah take har daga karshe taga ya mike ya kulle kwalban ya mayar cikin fridge din ya dawo ya kuma xaunawa gefen gadon ya dafe kansa, Ashnaah dae sae lekansa take ta cikin bargo don wutan dakin na da duhu, juyawa taga yyi yana kallonta, nn da nn gabanta yyi mugun faduwa ta rumtse ido da sauri, ya dde yana kallonta