Showing 24001 words to 27000 words out of 113152 words

Chapter 9 - Dr Khaleel Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

464

mum dina, da sauri ta gama dialing num din momynta ta shiga kira har ya katse bata daga ba, ta kuma kira ba a dauka ba tayi tunanin kila wayar na sama ita tana downstairs, har xata ajiye wayar ta tuna usman dinta da sauri shima tayi dialing no dinsa don tana da shi a ka ta kira ta ji a kashe, ta ja dogon tsaki har xata ajiye wayar ta tuna kawayenta na makaranta, tayi shiru tana nazarin ko xata iya tuna nmbr ummi kawarta don nmbrta bae da wahala, ta dae yi dailin nmbr tana tantaman hka ne ko ba hka bne, bugu uku a daga, tace "ummi ce don Allah" muryar ummi ta ji ta daya bangaren da mamaki tace "Ashnaah" Ashnaah tayi dariya tace ashe dae xa a dani, off head fa na kirkiri no dinki, wllh Baku da kirki ko ku nemeni ummi amma bbu damuwa, ummi tace "Allah sarki fateema kinsan sau nawa muke xuwa gidanku mama tace ita ma bata san gidan ki ba hka ma Ashfah, wllh bbu san inda xa mu same ki bne Ashnaah gashi ba mu da nmbrki, wnn ne Sabon nmbrki, ya amarci" Ashnaah ta tabe baki tace "ke dae bari, ynxu dae ki je gida ki ce ma Ashfah ta raka ki gidan Anty shafa, sae ki roketa ta kawo ku gidana ae ita ta san nn, ita kuma Ashfat ki ce mata ta kyauta ngd, kin ga sae anjima kar kuma fa ki kira Layin nn don na gantalallen ne, sae kun xo" Ashnaah na kai wa nn ta katse kiran ta goge duka nmbrs din da ta kira ta ajiye wayar ta fito da sauri falo ta bude fridge don daukan ma bakin Khaleel drinks, hollandia daya kadae ta gani sauran duk giya ce ta dan tabe baki har da xata dauki hollandian, sae kuma ta fasa tayi tsit kmr me naxari, murmushin mugunta tayi ta dauki wine din kwalba biyu ta fito ta sauka downstairs, tace "sannunku" snn ta nufi kitchen dan dauko faranti da cups ta daura wine din, Khaleel ya bi ta da kallon mamaki, bae san lkcn da ya mike ya bita kitchen din da sauri ba, ya samu har ta gama daura su kan faranti xata fito ya rikota da sauri yace "ke meye hka kike yi, me ya kai ki dakina" ta fixge hannunta tace "A'ah me nayi, daga na dauko ma bakin ka lemo shine nayi laifi" kuma rikota yyi da sauri ganin fita xata yi yace "kina da hankali kuwa" ta buge hannunsa tace "Allah xan maka ihu idan baka sakeni ba, to me xa su sha sun kwaso kishin ruwa" ganin da gske take yasa ya marairaice ya rungumota yace "pls listen ba lemo bne wnn wllh, ba ki ga hollandia a fridge din bne" tana kallonsa tace "to meye" ya hade rae yace "wnn kuma ba matsalarki bne" bude baki tayi tace "ohh hka ma xaka ce min ko to wllh sae na kai masu in ba lemo bne to meye guba ce ko me? Allah sae na kai masu don irinsu kadae na gani a gidan" Khaleel duk ya birkice mata yana rike da ita yace "stop it plss wllh ba lemu bne, tarnish din image dina kike son yi ko me" ta hade rae tace "to oya cika ni na ji" a hankali ya saketa, ta juya da gudu xata fice daga kitchen din ta kai yyi saurin rikota ya matse ta jikinsa ya kwashe kwalaban dake kwance kan farantin ya ajiye su cikin sink, sae kiciniyar kwace kanta take tana cewa ashe dae kasan abinda kke to wllh sae na kai masu, matseta yyi jikinsa ganin ynda take daga murya yasa ya rufe idonsa ya saka bakin sa cikin nata da sauri, still tayi ta xaro ido a tsorace tana kallonsa, sulalewa ya ga tana neman yi hkn yasa ya hadata da bango ya shiga mata wani kiss na fitan hnkli, kuka ta saki a tsorace tana turasa jikinta na rawa, sae taga kmr bae ma san tana yi ba.


~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
32.....
Da kyar Ashnaah ta iya kwace kanta daga
hannun Khaleel ganin yana neman kai su kasa ga
zip din rigarta da ya soma xuge wa, mikewa
tsaye tayi jikinta na rawa ta dauki dankwalinta da
ya fadi kasa da sauri ta nufi kofa xata shiga falo,
yyi saurin rikota ya mayar da ita jikin bangon, ta
sulale kasa a tsorace ta toshe bakinta da
hannunta gudun kar ta saki ihun da take shirin yi,
hawaye na bin kuncinta, shi kam komawa yyi ya
hade kai da bango ta daya side din, Ashnaah ta
hade kanta da gwiwa ta shiga rera kuka, ya juya
a hankali yana kallonta, idonsa ya kada yyi jajur
hka ma lebbansa, mikewa Ashnaah ta kuma yi da
sauri xata Kuma fita ya fixgota xata saka ihu ya
bude kofar da xae sada ka da garden din gidan
dake kitchen din ya turata waje ya rufe kofar,
mayar da kansa yyi jikin bango yana mayar da
numfashi, can dae ya dago bayan numfashinsa ya
dai daita, ya juya a hankali ya jingina jikin bango
yana tunanin ynda xae koma falo gun bakin sa ga
shi bbu lemo, jikinsa ba laka ya nufi kofar da ya
tura Ashnaah ya bude a hankali ya fita, Ashnaah
ta Mike daga xaunen da take da sauri hawaye
shabe shabe a fuskarta ta koma baya a tsorace,
kallo daya yyi mata ya dauke kai ya nufi cikin
gida gun mai gadi, xama yyi kan bencin da mai
gadin ke xaune mai gadin na masa sannu da
fitowo ya dan shafa kansa yace "lemo xaka je ka
siyo min da ruwan gora Abdul, nayi baki bbu
drinks a gidan, kayi amfani da kudin hannunka
idan ka dawo xan Baka, kayi sauri don Allah xan
jira ka a nn" cike da ladabi mai gadin ya amsa
snn ya fita da sauri, bayan kmr Minti goma ya
dawo rike da five alive guda biyu a Leda da table
water biyu, Khaleel ya karba yyi masa gdya snn
ya nufi back yard don shiga kitchen, Ashnaah na
ganin sa ta kuma mikewa tsaye da sauri a
tsorace, bae ko kalli inda take ba ya shiga kitchen
din ya daura drink din daya da ruwa kan faranti
snn ya nufi falo, suna ta hira abunsu Khaleel ya
karaso falon ya ajiye drinks din hannunsa yana
kirkiran murmushi yace "Sannun ku" Al-ameen
yace "kai kuma daga ku kawo mana drink kae da
matarka sae ku makale a kitchen, minti nawa xa
muyi mu bar maku gidan ban da abin ku" Al-
ameen ya karashe mgnr yana kallon Khaleel yana
yar dariya Matarsa na taya sa, Khaleel ya ji
kunya ssae amma ya waske yace "ka ji ka da
wata magana daga na tsaya taya matata girki
shine laifi, dariya Al ameen yyi yana kallon
maryam yace "lallae kam mun ga alama girki ku
ke." Shi dae Khaleel bae kuma cewa komae ba
sae mikewa da yyi ya dauko boyz din abokin nasa
yana tamvayarsu ajin da suke a sch, da kyar
Ashnaah ta iya mikewa a hankali ta shigo kitchen,
duk jikinta yyi sanyi ji take kmr har lkcn bakin sa
na cikin nata, xakin bakinsa kawae ke mata yawo
a nata, kasa shigowa falon tayi duk sae taji ma
kunya take ji, dubara ya xo mata ta dauki
indomin ta da ta dafa da safe ta saka shi a micro
wave, sae da ya dumamu snn ta fiddo shi ta juye
a plate ta bare eggs din da ta dafa ta daura kai
snn ta dauki fork biyu ta sa a abincin ta gyara
daurin dan kwalinta ta fito falon, dakewa tayi
tana kirkiran murmushi tayi masu sannu da xama
snn ta karaso falon ta ajiye abincin kan center
table tana kallon yaran tace "ku xo ga abinci na
dafa maku children" karasawa kujera tayi ta
xauna tana kallon maryam da ke binta da kallo
duk sae ta tsargu ta fara kame kame tace "Anty
me xan girka maku, naga kar yaran su ji yunwa
ne shi yasa na tsaya dafa masu indomie"
Maryam tayi murmushi tace "haba dae yi xaman
ki amarya yaushe muka karya da har xamu daura
wani" Ashnaah tace "to Bari in bari xuwa anjima"
ko kadan bata bari suka hada ido da Khaleel ba
shi ma kuma hka don kin kallon inda take yyi, duk
suka xama kmr wasu munafukai, kasa xama tayi
a falon don duk sae ta jita a takure, ta mike tana
kallon maryam tace "bari in je sama anty ina
xuwa" Maryam tace "to sae kin sauko" karfe sha
daya saura Al ameen yace xa su wuce, Khaleel
yace "haba dae da wuri hka frnd ku tsaya kuyi
lunch mana" Al ameen yace "ma yi a gidan mu,
gwara mu Baku waje Yau Sunday ku huta da
kyau, kira mana amarya muyi sallama"
Sisters wata baiwar Allah ta kirani daxu wae ana
sa nmbrta a karshen nvl din nn kuma sae ayi ta
damunta da kira ana tsammanin ni ce, to ni kam
gskya bn san Wanda ke editin ba yana sa nmbrta,
don hka plss ba nmbrna bne ku bar kiranta bbu
ddi hka nn, masu yi kuma Allah ya shiryesu
Ameen.


~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
33.....
Kwance Khaleel ya samu Ashnaah kan gado, tana ganinsa ta mike xaune da sauri ya hade rae ya dauke kai yace "ki fito kiyi masu sallama" bae jira me xata ce ba ya juya ya fice daga dakin, ta bi sa da wani kallon tsana, bedroom dinsa ya shiga, ba a dau lkci ba ya fito ya sauka kasa, bayan fitarsa da minti uku tayi tsaki ta mike ta sa hijab dinta ta sauko kasa, kin shigowa falon tayi ta tsaya daga bayan kujera tana masu sallama tana murmushi don gani take kmr sun ga abinda Khaleel ya mata a kitchen, tsaye ma ta samesu xa su fita, Al-ameen ya fiddo dubu goma ya ajiye gefen kujera yace "gashi amarya kiyi hkuri tunda mijin naki bae ga daman gayyata ta bikin ku ba, sae kuma wani lkci, idan kuma ya ga dama ya kawo ki inda muke to Alhmdllh" Ashnaah ta sunkuyar da kanta tana murmushi tace "Ae kam xan xo ko bae kai ni ba" Maryam tayi dariya tace "Da ko kin kyauta wllh" shi kam Khaleel bae ce komae ba ya durkusa gaban kidz din abokin nasa ya Ciro dubu biyar ya damka ma babban yace "gashi ku sha chocolate boyz, kar kuma ku ba dad din ku sae mum kun ji" dariya kawae yaran suka yi, Al ameen ya nufi kofa matarsa na biye da shi a baya yace "To Dr Khaleel mun xo mun yi xumunci sae kuma wani lkcn" Khaleel yyi murmushi yace "am so greatful frnd mu ma muna nn xuwa" Har waje bakin motarsu Khaleel ya raka su, Ashnaah kam kin fitowa tayi ta dauki kudin da Al ameen ya bata ta nufi sama, bayan kusan minti goma Khaleel ya shigo gidan ya kalli kujeran ya ga ta dauke kudin, ya haura sama xuwa dakinsa, yyi kwanciyarsa. Karfe daya Ashnaah ta idar da sllh Azahar har lkcn tana xaune kan darduman ta, ta kasa manta abinda ya faru daxu a kitchen, ko wani motsi tayi sae ta tuno scene din, hkn yasa ta kasa samun rest of mynd, ga wani yunwa da take ji kuma ta kasa sauka ta nemi abinda xata ci, mikewa tayi da kyar ta dauki electric kettle dinta ta nufi bathroom ta cire socket din washin machine ta sa na kettle din snn ta kunna ta fito, ko ba komae sae ta sha tean ta me kauri, sae da ta dauraye cup din snn ta ta Debi ruwan zafin ta dawo daki ta dauko kayan tean da har sun wuce rabi, sugar kam dama bae fi cube goma ya rage ba, ko kwakwaran kwana hudu kayan tean basu yi a dakinta ba, ta hada tean ta shanye snn tayi kwanciyarta nn da nn bacci ya dauke ta. Bude kofar ta da aka yi ya sanya ta farka a dan tsorace ta mike xaune da sauri tana kallon kofar, Khaleel ya shigo fuskarsa a daure yana mata mugun kallo yace "wa kika kira min da waya ta?" Ta dan xaro ido kmr munafuka ta ki cewa komae, ya daka mata tsawa "ba mgna nake maki ba", ta sunkuyar da kai don ko hada ido bata son yi da shi ynxu, murya can kasa tace "momyna na kira" tsawa ya kuma daka mata yace "dis shud be ur 1st nd last tym, at d first place ma me ya kai ki dakina" Ashnaah dae bata ce komae ba, ya tsaya yana mata mugun kallo can yyi kwafa ya karaso cikin dakin ya jefa wayar kan gadonta ya juya ya fice, ta bi sa da harara snn tayi tsaki can ciki, daukar wayar tayi ta Duba ta ga 5 min ago mum dinta ta kira kuma ya daga, dialing nmbrta tayi da sauri, bugu biyu aka daga cike da doki tace "momyna" mum dinta ta amsa daga daya bangaren tace "Na'am fateema ya kike" Ashnaah kmr xata yi kuka tace "lfya lau momy, ya gida" mum tace "lfya lau" Ashnaah ta dan yi jim snn tace"Abbana fa" momy tace "yana Abj" a hankali Ashnaah tace "momy in na xo baxae Kore bi ba" muryarta na rawa ta karashe mgnr, momy tace "ki bari sae in yana Abuja sae ki xo fateema," Ashnaah ta dan yi shiru nn da nn hawaye ya cika idonta a hankali tace "to momy me yasa Ashfah bata xo ba" Momy tace "kiyi hkuri Abbanku ne ya hanata xuwa, amma xata xo watarana, fatan dae kuna lfy bbu matsala ko" Ashnaah ta shiga share hawayen da ke xubo mata tace "ehh momy amma ni ban san shi ba wllh" momy tayi shiru snn a hankali tace"kiyi hkuri Allah xae maki sakayya" kasa cewa komae Ashnaah tayi, hkn yasa momy tace "to sae wani lkcn knn" Ashnaah ta gyada mata kai kmr tana ganinta hawaye na bin kuncinta a hankali tace "to ki gaida Inna" katse kiran tayi ta ajiye wayar ta shiga rusa kukan takaici, ta kai kusan minti talatin tana kuka Khaleel ya shigo dakin, kallo daya yyi mata ya dauke kansa ya karasa kan gadon ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. Da la'asar tana xaune kan darduma ya bude dakin ta ya tsaya daga bakin kofar yace "in kin ga dama ki shirya xa ki je gaida kanwar Abbana" daga kai tayi tana kallonsa, shi kam tuni ya bar wajen, tayi tsaki tace "ba sae ka xo ka ja ni ba" gudun kar ya kuma dawo wa dakin ta shiga uku ne yasa ta mike a hankali ta fiddo kayanta ta, sae da ta fara shiga bathroom tayi wanka snn ta fito ta shirya, Karfe biyar ya kuma bude dakinta yana sanye da shadda sky blue colour, yana mata mugun kallo yace "amma baki san ke nake jira ba ko" ta mike ta dauki hijab dinta ta bi bayansa, bayan mota ta bude ta shiga abunta, ya juya xae mata mgna Suna hada ido ya kasa cewa komai yyi saurin dauke kansa ya bude driver seat ya shiga yyi warming motar suka bar gidan.


~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
34.....
Biyar da kusan rabi Khaleel yyi parking a compound din su
Meenah ya fito yana kallon agogon hannunsa ya nufi cikin gidan,
Ashnaah tayi tsaki ta bude motar ta fito ta kulle snn ta bi bayan
sa, bbu kowa falon ya haura sama, ita kuma ta samu kujera ta
xauna, tana karema falon kallo, ko ina tsaf sae kamshi ke tashi, ba
a dau lkci ba Anty fiddausi smll mum dinsa ta sauko dauke da
murmushi a fuskarta ta karaso cikin falon tana ma Ashnaah sannu
da xuwa, Ashnaah ta dan sunkuyar da kanta ta sauka kasa da
ladabi ta gaisheta, hkn ba karamin mamaki ya ba anty ba, ta
amsa da fara'arta tana tambayarta ya gidan, Meenah ce ta sauko
kasa Momynta tace ta dauko ma Ashnaah drinks ta nufi kitchen
sae ga ta ta dawo da faranti ta dire gaban Ashnaah tayi gaba
abunta, Ashnaah ta bi ta da harara, Khaleel ne ya sauko daga
sama ya xauna gefen smll mum din tasa yace "sannu Momy na"
ta hararesa tace "me kke min a sama" yyi murmushin da ya
bayyana dimples dinsa da fararen hakoransa yace "nothin mum
kallo na tsaya yi a bedroom din ki" Satan kallonsa kawae Ashnaah
take, ya daga kai ya kalleta ta dauke kanta da sauri tayi kmr kallo
take, ya Mike ya nufi fridge ya bude ya dauko ruwa ya dawo falon
ya xauna, hira suke tayi da mum din tasa ita dae Ashnaah mayar
da hnklinta tayi kan program din da ake a TV, momy tace "xa ku
jirani Khaleel xan dan fita in dawo ynxu" yace "its almost magrib
fa mum ina xa ki" tace "eh nasani ba dde wa xan yi ba, gidan
Hafsa xan tafi" yace "OK xa mu jira ki, ki gaida min ita don Allah
in kin je" ta hararesa tace "wato ita ce ka raina baxa ka gidan ta
ba ko kana ganin kan ku daya" Khaleel yyi dariya yace "not so
wllh mum, xan je in Allah ya yrda" sama ta nufa ta dauko makullin
motarta da mayafi tace ma Ashnaah sae ta dawo ba dde wa xata
yi ba snn ta fita don xuwa gidan kanwarta. Khaleel ya Ciro
wayarsa yyi dialing nmbr Zeenat yace "mu hadu garden mu yi
mgna Zeenat" katse kiran yyi ya mike ya fita daga falon Ashnaah
ta bi sa da kallo snn ta ja dogon tsaki ta tabe baki, Zeenat ta
sauko sanye da wani material dinta me kyau ja da milk colour ta
yafa mayafi milk colour, tun xuwan su gidan bata sakko ba sae
lkcn, ta dan yi murmushi tana kallon Ashnaah tace "Sannun ku da
xuwa" Ashnaah ta galla mata harara tace "ke dae xan ma sannu
da xuwa, gun ki na xo xa ki wani ce min sannu da xuwa" Zeenat
bata ce komae ba ta nufi kofa a sanyaye ta fita, bayan kmr minti
goma da fitan ta sae ga Meenah ta sauko ta nufi kitchen da sauri,
Ashnaah ta bi ta da kallo snn tayi tsaki, duk ta tsane su gaba
daya, abinda ta ji Khaleel ya ce a waya ya dawo mata da sauri,
wae sauko muyi mgna, to wacce mgnan xa su yi, da sauri ta
mike a xuciyarta tace "Ae sae na ji wllh wllh" ta nufi kofa da sauri
ta bude ta dan leka tsakar gidan ta ga ba kowa, hkn yasa ta fito a
hankali ta durkushe a balconyn da sauri don kar a ganta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login