Showing 63001 words to 66000 words out of 113152 words

Chapter 22 - Dr Khaleel Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

451

suka yi sallama suka ajiye wayar, Ashnaah ta dubi Ashfah tace "har an kawo kayan nawa ne?" Ashfah tace "wae masu gadin basu Bari ba wae mai gidan baya nn" Ashnaah bata ce komae ba, Ashfah tace "wae Abba yace mu je ki gaida inna anjima" kai kawae Ashnaah ta gyada mata, aka bude kofar dakin momy ta shigo tana kallonsu tace "abincin waye har ynxu a kitchen," Ashfah tace "na Ashnaah ne wae bata jin yunwa" momy ta hade rae tana kallonta tace "wae wani abu na damun ki ne, ina fa sane da safe baki yi wani kwakwakkwaran kari ba," mikewa Ashnaah tayi tana kirkiran murmushi tace "kallo mu ke ne momy ynxu xan je in dauka" ta gefen momynta ta bi ta fita, momy ta bita da kallo snn ta juya tana kallon Ashfah tace "wae me tace maki ke damunta" Ashfah tace "ynxun nn na gama tambayarta tace wae kawae past take tunawa" momy bata ce komae ba ta juya ta fita. Ashnaah ta sauko downstairs ta nufi kitchen don daukar abincinta da ya kusa awa hudu a ajiye don har an kusa gama na dare, bin ta da kallo Abbanta yyi, ta fito daga kitchen din rike da abincinta xa ta koma sama ys kirata, a sanyaye ta karaso falon ta duka ta amsa tana kallonsa, ya ajiye remote din hannunsa yana kallonta yace "kina da damuwa ne Fateema" ta girgixa masa kai tace "A'a Abba daga bacci na tashi" Abba yace "ok, gobe sae ki shirya driver ya Kai ki sch, kun kusa fara jarabawa ko?" Ta gyada masa kai tace "eh sae next wk xa mu fara wae, amma ynxu sae upper wk" yace "to shknn ki dage da karatu kin ga an wuce ki ssae u have to work hard to meet up" ta gyada masa kai tace "in sha Allah Abba" mikewa tayi ta dauki plate din abincinta ta nufi sama. Khaleel na komawa gida ya shige bedroom dinsa ya saka key ya shiga neman layin Najeeb, bugu daya ya daga, a raunane Khaleel ya shiga cewa "I need yhu plss ka xo ynxu Najeeb" bae jira cewarsa ba ya kashe wayar ya dafe kansa dake juya masa. "Ae ni bbu abinda xan ci gaba da ce maki da ya wuce Allah ubangiji ya kara maki, banxa kawae da bata yo halina ba, me gare Khaleel da har kika nace masa? Ya nemi kashe mana ke, ae sae naga uban da ya tsaya ma Khaleel a garin nn, xae san ya taba min ya ta, sae inda karfin ya kare wllh" cewar mahaifiyar Ameesha ga Ameesha dake kwance bbu abinda take furtawa sae wayyo Allahna, Alhaji mukhtar da ke xaune
Sae girgixa kafa yake shi ma fuskar nn tasa a daure ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. Najeeb yyi shiru yana kallon Khaleel bayan ya gama jin bayaninsa, Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye a sanyaye yace "plss don't b surprise frnd, wllh ni kaina nasan na kamu da son fateema da dde wa, help me plss give me a solution to dis prblm I beg yhu" dafa sa Najeeb yyi a hnkli yace "its OK frnd, ka bani address din su Fateeman, I
will c wat to do" nan Khaleel ya basa Address dinsu Ashnaah, Najeeb ya kwafe a wayarsa snn yace "amma me yasa xaka xarga Ameesha har ka doketa, idan ba ita bace ba fa" Khaleel yace "don't tell me dat, ita kadae ta iya rubutu kmr nawa, snn bayan ita bbu mai shigar min daki, to wae ma mu nawa ne a gidan da xaka ce kar in xargeta, ko kwana biyar fa ba ayi da xuwan uwarta gidan ba abun nn ya faru, to wa ya sa ta idan ba ita ba" Najeeb ya mike yana kallon abokin nasa yace "kar ka damu frnd ka kwantar da hnklinka, gobe xan tafi can gidansu fateeman."



~Dr khaleel~ By khaleesat Haiydar 72..... Nan Najeeb yyi masa sallama ya fita, Khaleel ya fada kan gadonsa ya runtse ido, duk ji yyi duniyar tae masa xafi, Ashnaah da komae nata kadae ke masa yawo a ka, nn da nn ya ji kmr xaxxabi xae rufesa. Karfe shidda saura na yamma Abban Khaleel ya shigo gida ya nufi dakin Ummi fuskarsa a daure yana kallonta yace "ina ibraheem" da kmr baxa ta ce komae ba sae dae tace "me ya faru kuma" cikin tsawa yace "nace yana ina" bae rufe baki ba Khaleel ya shigo dakin kmr wani mara lfya a sanyaye yace "gani Abba" kallonsa Ummi ta tsaya yi ganin ynda ya wani rame lkci daya, Abba ya juya yana kallonsa a fusace yace "don uwar ka wae halan kana shan giya ne" shiru Khaleel yyi bae ce masa komai ba, Abba ya daka masa tsawa yace "ka fada min me yarinyar mutane tayi maka ka ne mi kasheta yau" fada ssae Abba ke yi kmr xae maresa shi dae Khaleel bae ce komae ba hka ma Ummi, Abba ya gaji don kansa ya juya ya fice a fusace, Khaleel ya daga kai ya kalli mum dinsa snn ya juya ya fice daga dakin. Yana shiga dakinsa da minti goma kiran dad din Ameesha ya shigo wayarsa, da kmr baxae daga ba sae kuma ya daga yyi masa sallama, ba tare da ya amsa ba yace "ka xo gida ka same ni" bae jira cewar Khaleel ba ya katse wayar, sae da aka yi sllhr magrib Khaleel ya samu umminsa yace xae fita snn ya kama hanyar gidansu Ameesha, xaune ya tadda iyayen nata a falo da yayyinta maxa, Abbanta kadae ne ya amsa gaisuwarsa, ya xauna kasa yana kallon Abban nata bae dae ce komae ba, Alhaji mukhtar yace "wato da abin da xa ka biya mu knn ko Khaleel, dats great" takarda da pen ya dauka ya jefa gaban Khaleel yace "bani takardan ta ynxu" daukar takardan Khaleel yyi da pen cikin minti daya ya gama rubutun da yake ya dauka ya risina ya mika masa, karba yyi yana duba content din takardan kmr hka, "Ni Muhd Khaleel na saki khadija saki daya" Alhaji mukhtar yyi murmushi ya dauki wani takardan yyi rubutu yyi sign snn ya mika ma Khaleel, khaleel ya karba ya shiga duba rubutun, sack letter ya gani, mikewa yyi ya cukuikuye takardan ya jefar nn tsakiyar falon yace "sae da safen ku" snn ya juya ya fice daga gidan, mum din Ameesha tace "duk inda xaka neman aiki baxa ka samu matsayin da ka rasa ynxu ba sha sha sha kawae mahaukaci me gare ka xaka walakanta yar mi" Khaleel na shiga motarsa ya hade kae da steering xuciyarsa na masa wani irin xugi, yes tunda ya rasa Ashnaah komae ma ya rasa, wasu hawaye ne suka shiga sakko masa, duk duniyar yaji tayi masa xafi ya rasa me xae yi ya ji ddi, y him?" Da kyar ya iya jan motar ya bar layin, har ya kama hnyar gida yyi tunanin xuwa layinsu Ashnaah ko Allah xae sa su hadu, yana shiga layinsu cikin ikon Allah ya gansu ita da Ashfah sun dawo daga gidan inna knn.



~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 73..... Parking Khaleel yyi daga gefe ya fito da sauri ya nufo su, kamshin turarensa kawae Ashnaah ta shaka ta juya da sauri tana ganinsa ta ruga a guje ta nufi gate dinsu da sauri, Da mugun mmki Ashfah ke bin Ashnaah da kallo har ta shige gate din kawae gani tayi ta kwasa a guje ba dalili, juyawa tayi da sauri don ganin me take ma gudu, suka yi ido hudu da Khaleel ita ma ba sae ta ruga a guje ba, bin ta yyi da sauri ya shiga kiranta yace "don Allah don Annabi ki tsaya sister," kasa ci gaba da gudun ta yi ta ja burki ta tsaya ba tare da ta juyo ba, karasowa yyi inda take da sauri ya marairaice mata yace "Plss kanwata, kice da fateema tayi hkuri ta saurareni ko na minti daya ne plss help me beg her" Ashfah ta rasa abun cewa can dae tace "to bari in je in mata mgna" da sauri yace "yauwa kanwata ngd ssae ina jira plss" ta gyada masa kai ta nufi cikin gidansu, dakinsu ta samu Ashnaah kwance tana ta rusa kuka, ta karaso da mmki tana kallonta tace "meye abun kuka kuma sister, Kinga fa ni bana son hka, don me xa ki dinga daga min hnkli ne" Kmr ta kara tunxurata ta kuma fashewa da wani matsanancin kukan, Ashfah ta nemi gu ta xauna fuskarta dauke da damuwa tace "don Allah Ashnaah ki daina kukan nn wllh bana so yana damuna" da kyar ta lallasheta tayi shiru sae a snn ta tambayeta a sanyaye ko Khaleel ya tafi, Ashfah ta dan yi shiru snn tace "ehh ya tafi" komawa Ashnaah tayi ta kwanta tare da lumshe idonta kmr mai shirin bacci, Ashfah ta lulluba mata bargo tace "kiyi baccin ki kawae" Washegari da safe driver ya wuce da Ashnaah makaranta kmr ynda Abba yace, ko kadan Ashnaah bata gaya ma kawayenta abinda ke damunta ba kmr ynda suka bukaci sani, through out lectures din ranan shiru kke jin Ashnaah, lectures din ma ba fahimtarsu take ba kwata kwata, Karfe uku da rabi suka ga lectures Ashnaah ta dauki Jakarta ba tare da ta jira kawayen nata ba ta fito don jiran drivernta don tasan at anytime xae xo tunda ta fada masa lkcn tashin su, motar usman ta hango ta dauke kai da sauri amma har ya ganta, ya karaso inda take snn ya fito daga motar da damuwa yace "y ain't yhu pickn my cal Ashnaah" Ashnaah tace "to ina lecture din xan yi pick din cal dinka," shiru yyi yana kallonta, hkn yasa ta dan saki ranta tace "lecture muke ne wllh ka ga fitowa ta knn" yace "bbu damuwa, ya kike ya gida" tace "Alhmdllh" yace "ynxu xa a xo daukarki ko" ba tare da ta kallesa ba tace "ehh" ya dan yi shiru snn yace "kin ko gaya min lkcn da mijin ki ke fita da safe Ashnaah, koh kina ga...." Da sauri ta katse sa tace "ka ga ni fa we re no longer togeda, ya bani takardata tun shekaran jiya ina gidanmu" da mugun mmki Usman ke kallonta yace "waow re yhu serious dear shine baki gaya min ba, waww am so..." Da sauri Ashnaah tace "ka ga, sae mun yi waya ga driver can ya xo" bata jira cewarsa ba ta nufi gun motar gidansu da sauri don ba karamin farin cikin xuwan drivernsu tayi don ko kadan bata son jin mai usman ke shirin cewa. Karfe hudu da kusan rabi Ashfah ta sauka daga a dai daita sahun da ya ajiyeta dai dai bakin gate dinsu, da ganinta kasan daga makaranta take, Najeeb da ke jingine jikin motarsa can nesa da gidansu ya karaso da sauri ganinta, sallama yyi mata ta juya tana kallonsa, wani irin kallo tayi masa xata shiga gida ya sha gabanta da sauri yace "ki saurara pls fateema" Ashfah tayi tsaki tace "ni ba fateema bace malam ka bani hanya" xae yi mgna sae ga Ashnaah ta fito daga cikin motar da yyi parkin gefensu don drivern yace baxae shiga ciki ba momy ta aikesa kasuwa, juyawa Najeeb yyi yana kallon Ashnaah snn ya kuma juyawa ya kalli Ashfah da mugun mmki, kallo daya Ashnaah tayi masa ta dauke kai ta karasa xata shiga gida, Ashfah kam tuni har ta shige gida. Najeeb yace "wait plss fateema" juyawa tayi tana kallonsa, sae kuma ta tsaya don jin me xae ce, ya karaso inda take da sauri yace "dama ku yan biyu ne" juyawa Ashnaah tayi xata shige gida ganin tambayar bae da ma'ana, yyi saurin cewa "ki saurareni plss fateema" Ashnaah ta kuma juyawa tana kallonsa tace "ka ga idan ba ka da abun cewa ka rabu dani don bana son Abbana ya gani tsaye a nn" Najeeb yace "OK but mgnr na da tsayi, ko in bari da nyt" ta daga kafa tace "Allah ya kai mu" snn ta shige gida. Ana sllhn magrib Ashnaah ta sauko kasa ta samu mai gadinsu tace "don Allah baba xan yi bako kuma bana son abbana ya sa ni, anjima kadan xae xo idan ya xo ba sae ka shigo ba kawae ga nmbrta ka min flashn sae in san ynda xan fito" Mai gadin yace "to shkkn" snn ta ba shi nmbrta ta koma cikin gida. Khaleel na kwance dakinsa idonsa lumshe kmr mai bacci aka bude kofa Najeeb ya shigo, bude ido Khaleel yyi a hnkli duk a tunaninsa umminsa ce, najeeb ya karaso ya xauna gefensa yace "y Khaleel Ummi tace tun safe ka ki cin komae" Khaleel bae ce masa komae ba ya dauke kai kawae, Najeeb yyi shiru yana kallon abokin nasa, lkci daya wani tausayinsa ya shigesa, Najeeb ya dafe kansa




~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 74...... Bayan kusan minti goma Najeeb ya dago kai yana kallon Khaleel yace "ka kwantar da hnklin ka plss Khaleel, ynxu ma daga gidansu fateema nake" da sauri Khaleel ya mike xaune yana kallonsa abun tausayi yace "pls re yhu serious frnd, ka samu ganinta" Najeeb yace "yes mun hadu but tace baxata iya tsayawa ba kar dad dinta ya dawo ya same mu, ynxu anjima da daddare xan koma" Khaleel ya kamo hannayensa lkci daya hawaye ya cika idonsa yace "pls frnd help me convince her dat I wasn't d one dat wrote dat divorce letter, plss I beg yhu" Rungumesa Najeeb yyi yace "its OK, I will try my vry best frnd nayi maka wnn alkawarin, but nt until u stop does tearz" Khaleel ya dafe kansa bae ce masa komae ba xuciyarsa na masa kuna, mikewa Najeeb yyi ya fita ya karbo abincinsa gun Ummi snn ya dawo ya ajiye masa yace "ga abinci kaci kar ka sa ma kanka wani ciwon Khaleel" Sae da Najeeb yyi da gske snn Khaleel ya ci spoon uku a abincin ya ki cin sauran, Najeeb na kallonsa yace "ko xuwa gobe da nyt sae mu je ka ba Alhaji mukhtar hkuri na tabbatar xae hkura don bn ji ddin xancen da nake ji ba" Khaleel ya mike da kyar yana kallonsa yace "am going no where" yana kai wa nn ya shige bathroom. Karfe takwas da kusan rabi Najeeb ya isa gidansu Ashnaah, mai gadin yyi ynda ta ce masa, ba a dau lkci ba ta fito ts nufi gun Najeeb dake jingine jikin motarsa, ya kafa mata ido har ta karaso ta rungume hannayenta tace "ina jin ka" Najeeb ya dan sauke ajiyar xuciya yace "ki fada min gskya fateema, re yhu happy ynxu da Khaleel ya sake ki" daga kai tayi tana masa mugun kallo tace "wani irin tambaya ce wnn" Najeeb ya dan yi shiru Snn yace "kafin ki ji abinda ke tafe da ni sae kin ban amsa gskya, re yhu happy now dat d both of u re nt togeda" Ashnaah tace "yes am happy, y won't I b happy, I'm vry vry happy coz I've..." Kuka ta fashe da ssae, Najeeb yyi shiru yana kallonta, ta hade kanta da mota ta dinga rusa kuka kmr an aikota, a hnkli Najeeb yace "karya kike fateema, yhu re nt happy, nevertheless I came on behalf of my frnd" dago kai tayi tana kallonsa har lkcn tana hawaye, Najeeb ya dan yi shiru snn yace "ba Khaleel ne ya rubuta maki takardan saki ba," Ashnaah ta tabe baki tace "kwa dae raina ma kanku hnkli ba ni ba" Najeeb yyi murmushi yace "wllh kuwa its a set up, kinsan Wanda yyi rubutun ya sa a drawernsa" Ashnaah tayi shiru tana kallonsa yace "Ameesha, can yhu still remember d day her mum came to c her" Ashnaah sae kallon Najeeb take a dan rikice, ta shiga gyada masa kai tace "ehh na tuna" Najeeb yace "to ita ta sa Ameesha tayi hka don a tunaninta Khaleel ya fi son ki kan Ameesha, ae tuni ya ma saketa ita ma" hawaye kawae Ashnaah take a sanyaye tana kallon Najeeb, ya gyada mata kai a hnkli yace "yes, wllh wllh ba Khaleel ne yyi rubutun nn ba kin ji na rantse maki fateema, ynxu hka yana can bae da lfya, tok to ur parent plss" kuka ssae Ashnaah ke yi ta ma rasa me xata ce masa, yace "shknn ni xan koma, gobe da daddare xan kuma dawowa sae ki fada min ynda kuka yi ae kin gane ko" kae kawae ta gyada masa ya xaga ya shiga motarsa ita kuma ta nufi cikin gida jikinta a sanyaye, to wae ma meyasa ta damu kanta hka bayan tasan ba son shi take ba shi ma ba sonta yake ba.


~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
75.....
Washegari da safe Khaleel na kwance dakin umminsa Rukayya ta
shigo wae mai gadi yace wani bako na sallama da shi a waje, ya
mike xaune yana kallonta yace "waye?" Tace "ni ma ban sani ba"
Khaleel ya dan yi shiru snn yace "Abba ya fita ne" Rukayya tace
"ehh tun safe ya fita," ko kadan Khaleel bae son haduwa da dad
din nasa, ganin wani irin shasharesa da yake yi tun bayan abinda
yyi ma Ameesha, mikewa yyi ya fita don xuwa ganin bakon nasa.
Da mmki yake kallon Al-ameen yace "kai ne bako kuma?" Al-ameen
yyi murmushi yace "yes ina jin kunyan Ummi ne, na dde ban xo
gaisheta ba" Khaleel yace "ae tasan ba garin nn kke aiki ba" Al-
ameen yace "na ta kiran nmbrka no answer, shi yasa nace mai gadi
yace kayi bako" Khaleel yace "wayar na bedroom dina, ni kuma
dakin Ummi nake, mu shiga daga ciki mana" bbu musu Al-ameen
ya bi sa har cikin gidan ya gaida Ummi snn suka nufi dakin
Khaleel, Al-ameen sae kallon abokin nasa yake ganin ynda ya
rame, Khaleel na dan kirkiran murmushi yace "let me get

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login