Showing 57001 words to 60000 words out of 113152 words

Chapter 20 - Dr Khaleel Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

435

fito dagadakinta jin shigowar motar Khaleel,tsayawa tayi tana kallonsu, juyawatayi ta koma dakinta cike da takaici,Ashnaah kam har tayi bacci abun ta,har bedroom Najeeb ya kai sa yakwantar da shi snn ya shiga budedrawers dinsa yana dubawa ko xaega alluran da xae masa, ba a dau lkciba yyi masa alluran snn ya kwantarda shi, yana nn tsaye bacci yadaukesa, har da minshari, murmushissae Najeeb yyi snn ya fiddotakardan aljihunsa ya kuma linketaneatly snn ya bude drawernmadubin Khaleel ya ajiye karkashinwani dictionary da ke ciki, ya juya yakuma kallon Khaleel snn ya fice dagadakin. Da asuba wajajen Karfe huduKhaleel ya farka dae dae lkcn daAshnaah ma ta farka ta mike xauneda sauri tunawa da tayi Khaleel baedawo jiya ba har bacci ya dauketa,mikewa tayi ta nufi window tanalekan ko xata ga motarsa, bata gamotar a inda yake parkin ba, hkn yasata nufi kofa xata fita ba tare da tasantakamaiman abinda xata fita yi ba,Khaleel kam yana xaune gefengadonsa ya dafe kansa da yyi masanauyi ssae, lkci daya ya ji cikin sa yahautsine ya mike da sauri yana ganinjiri ya nufi bathroom dinsa kasa shigayyi ya fada nn bakin kofar ya shigakwarara amae, dae dae lkcn daAshnaah ta fito daga dakinta da yakeko ina was very cylnt lkci daya tajikakarin aman nasa, da sauri ba tareda tayi wani tunani ba ta budekofarsa ta shiga ta nufi bedroom dinnasa, durkushewa tayi gabansa arude ta rikoka ta shiga tambayarsame ya faru, warin giya taji ya buge ta,ta kauda kanta da sauri shi kam harlkcn aman bae tsaya masa ba.



~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
66.....
Ashnaah ta koma baya tana kallonsa har ya gama aman taga ya rike kai, dawowa tayi gabansa ta dago kansa a hnkli tana kallon fuskarsa, ya bude Idonsa da ya kada yyi jajir yana kallonta, samun kanta da yi masa sannu murya can ciki tayi, ya shiga kkrin mikewa tsaye yyi baya xae fadi ya rike kofar bayin da sauri, a hnkli ya kuma durkushewa wajen, Ashnaah da duk ta ma rasa abun yi ta matso kusa da shi ta shiga cire masa rigar jikinsa a hnkli tana kallonsa ya rage masa singlet, mikewa taga ya kuma yi ita ma ta mike tana kallonsa da kyar ta iya bude baki tace "ina xa ka" bedroom ta ga ya koma, hkn yasa ta shiga gyara gun da yyi aman, har ta gama snn ta hada masa ruwan dumi dae xae yi wanka ta dawo cikin dakin ta samesa xaune gefen gado ya dafe kai, durkusa wa tayi kusa da shi tana kallonsa tace "na sa maka ruwan wanka" dago kansa yyi yana kallonta bae ce komae ba, can ya mike da taimakonta ya shiga bathroom don yin wanka, kasa fita tayi daga dakin ta gyara masa gadonsa, tana tsaye ya fito daure da towel, dauke kae tayi da sauri, ya karaso gado ya xauna ya kuma rike kae, juyawa tayi tana kallonsa ta rasa takamaiman abinda xata yi, a hnkli ta nufi inda ya ke ta durkusa gabansa murya can kasa tace "baka da lfya ne" ya gyada mata kai kawae yana kallon fuskarta tace "to in kira maka Khadija" girgixa mata kai yyi, hkn yasa ta mike ta nufi wardrobe dinsa ta ciro masa gogaggiyar jallabiyarsa da ta gani, da taimakon ta ya saka, snn yyi kwanciyarsa kan gado nn da nn bacci ya daukesa, Ashnaah dae na xaune gefensa ta kafa masa ido tana kallonsa, Juyawa tayi ta kalli agogo taga an ma kusa kiran sllhn farko, ta dan jigininar da kanta jikin gado nn da nn ita ma bacci ya dauketa nn a xaunen, kiraye kirayen sllh ne ya farkar da ita ta bude idonta ta ganta rungume jikinsa ya kankameta ga jikinsa xafi, daga kai tayi tana kallon fuskarsa suka hada ido don idonsa biyu, ta boye fuskarta a kirjinsa da sauri, taji ya dauro bakinsa a hnkli kan gashin kanta, har lkcn sllh yyi idonsu biyu gaba daya, ita dai kin dago kanta tayi daga kirjinsa, a hnkli taji ya kwantar da ita ya mike ya nufi bathroom ta bi sa da kallo, alwala yyi ya fito ya shimfida darduma nn cikin daki don yin sllhnsa, don bae jin xae iya xuwa masallaci, ita ma ta mike ta shiga bayin tayi alwala ta fito ta nufi dakinta don yin sllh, tana idar da sllh ta kasa xama dakinta hkn yasa ta fita ta koma dakinsa ta ga har lkcn wae sllh yake, ta dae gaji da tsayuwa bae idar ba ta juya ta koma dakinta tana tunanin wani irin sllh ce hka yake, ko da ta dawo dakin ta samu Ameesha durkushe kusa da shi yana kwance gefen gado, juyawa tayi ta fice daga dakin daga shi har Ameesha suka bi ta da kallo. Karfe bakwae da kusan rabi Najeeb ya danna bell, Ameesha da ke kitchen ta fito ta bude kofar, shi ya fara gaisheta ta amsa fuskarta daure, yana murmushi yace "ni kuma meye nawa xa ki daure min fuska kinsan wahalar da mjinki ya bani jiya kuwa, ina gida aka kirani na xo na samesa a buge kinsan jiya birthday din Maska ni dama bn samu xuwa ba" a hnkli Ameesha tace "to Allah ya shiryesa nayi xaton ya ma daina don tun da na shigo gidan nn bn ga ya sha ba" Najeeb yyi dariya yace "xae dae daina, ynxu ya tashi ko ko" Ameesha tace "ehh ya tashi na basa tea kuma nayi masa allura bacci ma yake ynxu" Najeeb yace "to bari in dubo sa, Fateema fa" Ameesha tace "tana dakinta" sama ya nufa don xuwa dakin Khaleel ita kuma ta koma kitchen ta ci gaba da wanke wanken da take. Ashnaah da shigowarta dakin Khaleel knn bayan ta ji saukar Ameesha downstairs ta mike da sauri don duk a tunanin ta Ameeshan ce ta shigo don bata son tana ganinta a dakin, da mmki take kallon Najeeb, ya sakar mata murmushi yace "jinyarsa kike" da sauri tace "no shigowa na knn, shi ma abu na xo dauka" karaso wa yyi kusa da Khaleel yana kallonsa, ya dan taba goshinsa yace "jiya giya ya sha yyi over doze a wani birthday da suka tafi da abokanansa," Ashnaah ta tabe baki bata ce komae ba, Najeeb ya nufi gaban madubin Khaleel yana cewa "idan ya tashi ga magani nan ki dauka ki basa ba don halinsa ba, promise me yhu wil do dat" Ashnaah tace "OK" bude drawern yyi ya saka ledan hannunsa snn yyi saurin fiddo da takardan da ya sa karkashin dictionary ya daura kan dictionaryn ynda dole sae mutum ya gani idan ya bude drawern, ya rufe drawer din ya juya yana kallon Ashnaah ya fada mata dosage din magungunan snn yace "yhu make sure yhu giv him idan ya tashi plss" juyawa yyi ya fita daga dakin ta bi bayansa da sauri har suka fito corridor snn tace "yhu promise me something sometimes ago, nd I have been lookn fwrd...." Murmushi yyi yace "I tried my best sister, my plans didn't go, but kar ki samu damuwa i wil look for another, though kwanaki naji yana fadi cikin frndz ya kusa sallamarki vry soon shi yasa nayi relaxing" Ashnaah tace "to ka dae min kkri pls" murmushi yyi ya gyada mata kai ya juya ya bar wajen, ita kuma ta nufi dakinta, dae dae lkcn da wayarta da ta mance gaban madubi ya katse daga vibration din da yake, da sauri ta nufi gaban madubin ta duba taga mis calls din usman har hudu, kiransa ta shiga yi da sauri, bugu daya ya dauka tare da sauke ajiyar xuciya yace "ina kika shiga hka Ashnaah" ta ce "ina falo ne hope lfya ka kira da sassafe hka" yace "Karfe nawa mijin ki ke fita aiki da safe" shiru tayi kmr me naxari can tace "usman ni fa nace maka lfya nake son mu rabu da shi wat re yhu tryn to do" yace "baki yrda dani ba fateema, I told yhu am doing him no harm" tace "to shknn amma bana tunanin yau xae fita aiki da wuri don bae da lfya, hold on tukunna"



~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
67.....
Ashnaah ta ajiye wayar hannunta ta nufi kan gadonta jiki ba kwari ta kwanta tare da lumshe ido, duk ta ma rasa me ke damunta, bacci ne ya dauketa nn take. cikin bacci ta ji an bude kofarta lkci daya ta farka ta mike xaune tana kallon kofar, Ameesha ce ta shigo dakin tana kallonta tace "ba kiyi breakfast ba ga shi har tara ya wuce, baxa ki sch bne yau." Ashnaah ta kalli agogo snn tace "xan je, bari inyi wanka" Ameesha tace "OK snn ta juya ta fita" mikewa Ashnaah tayi ta nufi cikin bathroom don yin wanka, cikin riga da skirt dinta ta shirya ta dan gyara fuskarta snn ta daura dankwali ta fita, har ta fara sauka stairs sae kuma ta tsaya tana kallon kofar falonsa , juyawa tayi ta koma sama ta bude kofar ta shiga a hnkli snn ta nufi bedroom dinsa, xaune ta samesa gefen gado yana shan coffee, ya daga kai yana kallonta, ji tayi kmr ta nutse don bata san me xata ce ya kawota dakin ba bata yi tunanin idonsa biyu ba, shi dae bae ce mata komai ba ya ci gaba da shan coffen hannunsa, juyawa tayi da sauri ta nufi gaban madubinsa ya bi ta da kallo, bude drawern tayi idonta ya fara sauka kan farar takardan dake linke neatly kan dictionary ta dauki ledan maganin da xata dauka ta juya tana kallon Khaleel bbu yabo bbu fallasa tace "dama abokin ka ne yace a baka wnn idan ka tashi" kallon ledan kawae yake, hkn yasa ta hade rai ta karasa kusa da shi ta mika masa, karba yyi ya bude yana kallon magungunan snn yace "I've taken drugs ynxu, ki mayar sae anjima" ta karba ta juya ta nufi gaban madubin ta ajiye ledan, idonta ya ku ma sauka kan takardan, rufe drawern tayi ta juya tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "xan tafi sch" bai ce komae ba sai shan coffe din hannunsa yake, ta juya xata fita taji yace "ki bari sae gobe" juyawa tayi tana masa wani irin kallo tace "sbda me" ya ce "sbda bbu wnda xae kae ki" bae jira cewarta ba ya mike ya nufi bathroom, tayi tsaki ta juya ta fice daga dakin. Through out ranan Ashnaah a falo suka yini da Ameesha suna ta hiransu duk da Ashnaah hnklinta na gun kallon da take, shi kam Khaleel yana sama, har suka yi azahar Ashnaah bata ga ya sauko xuwa masallaci ba, samun kanta tayi da ce ma Ameesha baki dubo mijinki ba khadija" Ameesha dake cin abinci tace "gwara ke in kin je ba lallai ne ya gwale ki ba, daxu da na shiga Ca yyi ina damunsa bacci zae yi" Ashnaah ta tabe baki tace "ya ce maki hka bare ni karan kada miya". Har aka yi la'asar suna falo ita Ashnaah na kallo Ameesha kuma na danna waya, hudu da rabi Ameesha ta mike tace "bari in daura girki" Ashnaah tace "OK" Ameesha na shiga kitchen Ashnaah ta mike da sauri ta nufi sama, falonsa ta shiga ta karasa bedroom, kwance ta samesa ya lullube da bargo har kansa, ta dde tsaye tana kallonsa daga bisanni ta karasa gadon a hnkli ta durkusa gefensa tana kallonsa, yaye bargon tayi a hnkli suka yi ido hudu da shi ta mike da sauri xata bar wajen ya jawota ta fado jikinsa, ssae jikinsa yyi xafi, ya rungunmeta tare da lumshe ido tayi lamo jikinsa, ganin bae kyaleta ba yasa ta janye jikinta a hnkli daga nasa ta mike xaune amma ta kasa kallon cikin idonsa, murya can kasa tace "ka sha magani" girgixa mata kai yyi ta mike da sauri ta nufi gaban madubinsa ta bude ta dauko ledan maganin ta shiga ballesu kmr ynda Najeeb yace tayi, fridge ta bude ta dauko ruwa snn ta dauki cup din da ta gani kan fridge din ta bude ruwan hannunta ta dauraye cup din da shi ta xubar a bathroom snn ta kuma xubawa ta karaso kusa da shi ta durkusa tana mika masa, da kyar ya karba ya xuba maganin a baki snn ya kora da ruwa, mikewa tayi ta dauki ledan maganin ta nufi gaban madubin da shi xa ta ajiye, farar takardan daxu idonta ya kuma tozali da, hka kawae taji tana son gnin takardan meye, ko don ynda taga an mai linki, ta dauka ta shiga warware shi har ta gama snn idonta ya sauka kan dan guntun content din papern sunanta ta ga boldly a rubuce tun kan ta fara karatun, muryar Khaleel taji yace "wats dat?". Ta juya ta kallesa snn ta mayar da dubanta kan takardan, "Ni ibraheem Khaleel MD na sake ki Fateema saki daya,
biyu, har uku, Allah ya game kowa da rabonsa Ma'salam" cak komae na Ashnaah ya tsaya a lkcn tana
maimaita abinda ta gani a rubuce jikin takardan" mikewa taga khaleel yyi ya nufo ta ganin bata basa amsar tambayar sa ba don shi dae yasan bae ajiye takarda a nn ba, ta juya da sauri ta fice daga dakin, da gudu ta afka dakinta ta sa ki ta jingina jikin kofar tana mayar da numfashi, kuka ta fashe da tana kallon takardar, na farin ciki ne na bakin ciki ne ta kasa tantancewa, hawayenta ta shiga gogewa a hnkli tana murmushi lkci daya wasu sabbin hawayen na saukowa.



~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
68.....
Da sauri Ashnaah ta bar jikin kofar jin yana bubbugawa ta bude handbag dinta ta saka takardan a ciki snn ta shige bathroom, komawa khaleel yyi bedroom dinsa ya dauko spare key din dakinta snn ya dawo ya bude kofar, bin ko ina na dakin yake da kallo snn ya nufi bathroom ya murda ya ji shi a rufe, daga ciki tace "wae meye ne hka ni ka kyaleni wanka xan yi" bae ce Mata komae ba ya jingina jikin bangon kusa da kofar bayin duk da jirin da yake gani, ya kusa minti sha biyar tsaye a wajen Ashnaah taki fitowa, ita kam bbu abinda take sae hawaye, ta rasa meyasa kuka ya ki tsaya mata, jin shirun yyi yawa yasa ta bude kofar bayin a hnkli ta fito don a tunaninta ya bar dakin, ba karamin kara ta saki ba da ta gansa ta juya da sauri xata koma yyi saurin rikota ya rungunmeta lkci daya, sakar masa kuka tayi ta shiga kkrin kwace kanta yaki saketa yana kallonta yace "me kika dauka a drawerna? ina yake" ta hade rae har lkcn tana kiciniyar kwace kanta tace "da'alla ni ka ka sakeni bn dauki komae ba" kallon cikin idonta ya tsaya yi ta dauke kanta da sauri, ya saketa a hnkli ya juya ya fita daga dakin, Ashnaah ta bi sa da kallo snn ta sulale kasan dakin ta shiga rusa kuka kmr warce aka aiko ma da sakon mutuwa. Har kusan shidda Ashnaah bata mike daga inda take ba sae dae ta daina kukan da take, sae da ta fara jin kiraye kirayen sllhn magrib snn ta mike da kyar ta nufi bathroom ta wanke fuskarta ta fito ta xauna gefen gadonta, duk ta rasa particular tunanin da take a xuciyarta, tana jin an tada sllh ta mike da sauri ta ciro hijab dinta snn ta dauko handbag dinta ta nufi kofa, a hnkli ta tura kofar ta fita ta sauka downstairs, bbu kowa falon hkn ya bata damar fita da sauri, gate a rufe yake bbu ko wani mai gadi a nn, tasan suna masallaci, ta shiga bude gate din da sauri snn ta fice, sauri sauri gudu gudu ta nufi bakin titi ta sayar da adai daita sahu ta gaya masa inda xata snn ta shiga. Bakwae da kusan rabi Ashnaah ta isa kofar gidansu, ta fiddo kudinsa ta mika masa snn ta nufi gate dinsu, a sanyaye ta karasa cikin gidan tana kallon motar Abbanta da ke Parke, a hnkli ta tura kofar falonsu ta shiga bata samu kowa falon ba ta nufi sama da sauri ta bude dakin mum dinta ta shiga, xaune ta sameta kan darduma caxbi a hannunta, da mmi take kallon Ashnaah, Ashnaah ta sakar mata murmushi tace "sannu momy bari in yi alwala" bathroom ta nufa da sauri tayi alwala ta fito snn ta tada sllh, sae da ta idar snn momy ta juya tana kallonta da mmki tace "daga ina hka" Ashnaah ta kirkiro murmushi tace "ya xo gun wani frnd dinsa ne a nn wajajen shine nace ya bar ni in karaso gida" momy bata ce komae ba, Ashnaah ta gaisheta amsa tana kallon yar tata, ko kadan Ashnaah bata Bari momynta ta lura da komae ba, tace "Abba na nn ko momy" momy tace "yana dakinsa" Ashnaah bata tambayi yar uwarta ba don tasan tana gidan inna, tambayarta momy tayi ko ta ci abinci Ashnaah tace ta ci, don bata jin cin komai, har tara da rabi, momy bata ga Ashnaah na cewa xata tafi ba, momy ta shigo dakinta tana kallonta tace "wae ba yau xaki koma bne, kinsan Abbanku fa bae san kin xo ba" Ashnaah tayi shiru snn tace "sae gobe momy" momy tace "to tun da kwana xa kiyi ki tafi ki gaida Abban ku kar ya gan ki gobe ya xame min abun mgna" Ashnaah ta gyada ma mum dinta kai kawae, momy ta juya ta fita, kuka Ashnaah ta shiga rerawa a hnkli tana tunanin ynda iyayenta xasu dauki xancen da ta kawo masu. Khaleel kam na dawowa daga masallaci ya nufi dakin Ashnaah, bae sameta a ciki ba hkn yasa ya nufi bathroom nn ma bata nn, fitowa yyi ya shiga dakin Ameesha ya sameta xaune kan darduma, yace "fateema fa" Ameesha tace "tun hudu ta hau sama, tana dakinta" juyawa yyi ya fice daga dakin, bbu inda bae duba ba a gidan amma bae ga alamar Ashnaah ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login