Showing 99001 words to 102000 words out of 113152 words

Chapter 34 - Dr Khaleel Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

437

ya daga kai yana kallonta yace "da safe hka sister, baki yi breakfast ba ae" Ashfah tace "bana breakfast da safe sae eleven, ina da lecture ne" Khaleel ya mike yace "OK, bari in dauko makulli in ajiye ki" tace "A'a wlh ka bar shi xan samu napep idan na fita" bae saurareta ba ya nufi sama ya dauko makullin motarsa ya shiga bedroom da Ashnaah take, xaune ya sameta tsakiyar gado ta hade kai da gwiwa tana kuka, ya karaso kusa da ita yana kallonta bata jira me xae ce ba ta mike ta shige bayi ta kulle kofar, ya dan yi murmushi ya juya ya fita daga dakin, a hanya yake ce ma Ashfah ta bar Ashnaah tana ta kuka, Ashfah tayi murmushi tace "wae baxan tafi ba ga shi yau Abbanmu xae dawo, kuma bae san na tafi ko ina ba" Khaleel yace "gskya ne" har kofar gidansu ya ajiye ta ya bata dubu biyar tare da cewa ta gaida masa momy ta karba da kyar snn ta shiga gida yyi reverse ya bar anguwar, a tare suka yi parkin da Najeeb a kofar gida, Khaleel ya rike kai yana dariya har Najeeb ya fito daga motarsa snn shi ma ya fito, Najeeb yace "Allah ya sa sun tashi" Khaleel ya fashe da dariya yace "ynzun nn na mayar da ita gida, ko karyawa ta ki yi wae tana da lecture, lkci daya mood din Najeeb ya canxa yace "ya xa ka min hka Khaleel?" Khaleel yace "its nt my fault frnd" juyawa Najeeb yyi ya shige motarsa ya fixgeta a guje ya bar anguwar Khaleel ya bi sa da kallo yana murmushi. Washegari Asabar ba tare da Najeeb ya Bari Khaleel ya sa ni ba ya lallaba abokanan dad dinsa shi ma ya bisu xuwa can gidansu Ashnaah don ganin Abbanta, Abba na gida a lkcn, as usual da fara'arsa ya tare su snn suka gabatar masa da abinda ya kawo su kan cewa sun xo neman auren Ashfah, Abba ya dan yi shiru snn yana kallon Najeeb yace "ita ta ce ka turo koh?" Najeeb ya girgixa kai da sauri yacec"A'a Dad, hasalima ni bata taba kulani ba wllh shi yasa na ce bari in xo neman ixini a gida" Abokanan dad din nasa suka tsaya kallonsa da mmki don ba hka ya fadi masu ba, Ca yyi yarinyar tace ya turo manyansa in ji babanta, Abba ya dan yi murmushi yace "gskya ne" maida dubansa yyi ga bakin nasa yace "to xancen gskya 'ya ta karatu take ynxu, kuma sae ta gama xan bada aurenta kuyi hkuri dob Allah, kae in kaga kana sonta xaka iya jiran ta gama, saura mata shekara uku idan Allah ya yrda" mikewa abokan dad din Najeeb suka yi kowa ransa a bace, bbu wani kwakkwaran sallama suka fice daga falon, Najeeb kam kasa tashi yyi, ya marairaice ma Abban yace "wllh dad xan bari tayi karatunta baxan hanata ba" Abba yace "to ni bnyi niyar aurar da ita ynxu ba sae nn da shekara uku," mikewa Najeeb yyi jiki ba kwari yyi masa sallama ya fita daga falon.

108......
Dayz went by followed by month, wasa wasa yau cikin Ashnaah ya cika wata shidda da sati biyu cif ynxu kam bbu wani laulayi sae nauyin da tayi, tayi garau abunta cikinta ya fito ssae but bata da kwanciyar hnkli kullum cikin tunani da xubda hawaye take, hkn yasa bata kumari, bbu abinda ke sa Khaleel farin ciki sae idan ya tuna cikin yan biyunsa Ashnaah ke dauke da, sae dae har lkcn bbu wani improvement daga parent dinsu maxa gaba daya barin ma Ashnaah, duk da dad din Khaleel baya nuna mata komae yana mata kmr ynda xae yi ma Rukayya kuma yana tausayinta, Khaleel kam baya samun fuskarsa, amma duk da hka bae hanasa shigowa gidansa ba, har lkcn gidan Al-ameen suke xaune, lkci lkci Al-ameen din ya kan kawo masu xiyara da Maryam, ko mgnr neman aiki Khaleel baya yi duk da ynda frnds dinsa na arxiki suka damu ko wannensu na kkrin ganin yyi masa hanyar samun aiki amma Khaleel bae damu ba don har lkcn kwalinsa na gun dad dinsa, lkci lkci Najeeb kan kawo masu ziyara kuma yana taimakon abokin nasa ssae da foodstuffs, kuma yawanci duk shi ke siyo masu lafiyayyun kayan babies masu tsada, tun Khaleel na nuna masa baya so har ya gaji ya daina ya kyalesa kawae. Yau Sunday Ashnaah na kwance gefen Khaleel dake kallon football, jin tayi lamo jikinsa ya sa ya juya yana kallonta yace "ya dae wife" tayi shiru bata ce komae ba, hkn yasa ya ajiye remote din hannunsa ya dagota da damuwa don kusan ko da wani lkci bata da aikin yi sae tunane tunane yasan ta fara knn tunda tun da ta tashi bata yi ba, ya rungumeta a hnkli ya lumshe ido yace "wat again wife" ta kwantar da kanta kan kirjinsa a sanyaye hawaye na bin kuncinta tace "doctor ka kai ni in gaida Abbana yau," shiru Khaleel yyi bae ce komae ba, a hnkli tace "ka ji?" A sanyaye yace "toh ki shirya mu je wife"
Karfe sha daya da rabi Ashnaah ta gama shirinta ta sa hijab dinta har kasa ta sakko downstairs ta samesa ta ce ta gama. Makullin motarsa kawae ya dauka don shi ma ya shirya suka fita daga gidan, sae kallon ynda take sa hannu cikin hijab dinta tana kare cikin jikinta take wae kunya, don Ashnaah akwae kunya ba kadan ba, dariya ma take basa duk lkcn da ya ga tana hka, barin idan sun je gidansu, sae da suka kama hanya snn ya juya yana kallonta ya ga duk tayi sanyi, lkci daya ya mayar da dubansa ga titi, a hnkli yace "me xa mu siya ma Abba wife?" Ta girgixa kai hawaye ya shiga xarya a kuncinta tace "bbu komae, gaishesa kawae nake son xuwa yi" shiru yyi bae ce komae ba, can yace "to momy fa?" Nn ma ta girgixa masa kai tace "A'a ka bar shi kawae" bae kuma ce mata komae ba har suka isa kofar gidansu wajajen Karfe sha biyu na rana yyi parkin yana kallonta, bude motar yyi ya fito ya xagaya ya bude mata ya taimaka mata ta fito. Hawaye ta shiga yi a sanyaye ta nufi gate dinsu yana biye da ita a baya.

Nasan ba lallai ne ku iya gama karanta wnn ba har sae da rana tsabar yawan shi. Amma idan kun gama sae ku sanar da in ci gaba don ban san kanku ya dau xafi. Gud Mrnin Anties nd Momies.



~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
109....
A hankali Ashnaah ta murda kofar shiga falonsu duk da ta ga motar Abbanta a parkin space din gidan amma ta dake, a rufe taji kofar falon, hkn yasa ta dan yi jim snn ta danna bell jiki ba kwari ta dan koma baya, Khaleel kam kasa karaso balconyn yyi ya tsaya daga kasa, ba a dau lkci ba aka bude kofar falon, Ashnaah da gabanta yyi mugun faduwa tayi baya da sauri, Ashfah ce ta bude kofar, kasa cewa komae Ashfah tayi sae kallonsu take da mmki, Ashnaah tayi karfin halin yin murmushi tace "sister" Ashfah ta kasa amsawa ta dalilin tambayar da Abbansu dake xaune a falo ya jefo mata na cewa "waye?" Ta juya tana kallonsa ta kasa ba sa amsa, mikewa Abba yyi ya karaso bakin kofar yana ce ma Ashfah halan bakya ji na ne, kallo daya yyi ma Ashnaah ya juya ya bar gurin, Ba Ashnaahr ba har abinda ke cikinta na tabbata sae da suka tsorata, Ashfah ta sakar mata murmushi bayan Abba ya bar wajen tace "shigo mana sister" can ciki tayi mgnr kmr me gudun kadda Abbansu ya ji ta, Ashnaah ta juya tana kallon Khaleel snn ta shiga falon a sanyaye, Ashfah ta kalli Khaleel din shi ma tace "ka shigo mana" murmushi yyi mata duk da bae yi niyar shiga ba ya shigo da confident din xae yi toleratin duk wani rashin mutuncin da Abbansu xae yi masa, Ashnaah bata ga Abbanta a falo ba, hkn yasa ta nufi sama dakin momynta, momy ta mike da mugun mmki tana kallonta, kuka Ashnaah ta fashe da ta silale nn kasan dakin, momy ta karaso da sauri ta dagota tana tambayarta daga ina take kuma me ya faru, da kyar Ashnaah ta saida kukan ganin ynda hnklin momynta ya tashi, a sanyaye tace "daga gida nake momy" momy tace "mijin naki fa" Ashnaah ta sunkuyar da kai tace "tare muke, na xo gaida abba na ne ko baxae amsa min ba" tana fadin hka ta kuma fashewa da kuka, momy ta sauke ajiyar xuciya cike da tausayinta tace "to ya isa ki daina wnn kukan, in ma bae amsa ba kansa"
Abba kam dakinsa ya koma ya dauki makullin mota ya sauko falo fuskar nn tasa a daure, Khaleel da ke xaune falon tun da ya kallesa sau daya bae bari sun sake hada ido ba, Abba ya karaso cikin falon ya kwashi wayoyinsa dake kan centre table, Khaleel ya sakko har kasa ya gaishesa, ba tare da ya kallesa ba ya amsa har da tambayarsa ya aiki snn ya fice daga falon gaba daya, fitar motarsa momy ta ji ta tabe baki, ta kalli Ashnaah da ke shirin binsa dakinsa tace "to gashi ya fice, kar ki damun kanki Allah ya ga nufin ki" Ashnaah ta gyada mata kai tana kkrin mayar da hawayen da ke neman xubo mata ta koma ta xauna, momy kuma ta sauka downstairs suka gaisa da Khaleel, ranar ce rana ta farko da ta fara ganinsa shi ma hka ranan ya fara ganinta, Ashfah ta kawo masa ruwa ta ajiye masa yace ya gode, ko minti sha biyar ba ayi da fitar abba ba ya kira momy, da kmr baxata daga ba sae kuma ta daga, bbu yabo bbu fallasa ya fara mgna "kina ji na koh, to wllh na kuskura na dawo gidana naga yarinyar nn duk abinda nayi mata ita ta siyar ma kanta, maxa maxa ta bar min gida in ma ke kika gayyato ta kar ran ku ya bace daga ke har ita" momy ta tabe baki ta ajiye wayar, ko kadan bata nuna ma Ashnaah Abbanta ne ya kira ba amma ta gane, ko minti biyar bata kara ba ta mike a sanyaye tace "xa mu tafi momy" momy ta bata addu'o'in da xata dinga yi ta mata gdya snn suka wuce. Har suka isa gida bata ce komae ba hka ma Khaleel, through out ranan rasa gane kanta yyi ga shi ta ki cin komae sae kwanciya. Yana dawowa daga mosque bayan sllhn isha ya xauna gefenta da damuwa yace "plss wife, ki daina daga min hnkli don Allah" a sanyaye ya karashe mgnr, Ashnaah ta mike xaune bata ce komai ba, ya dauko abincin da ya karbo mata a gida yace "ga abinci Ummi tace a kawo maki" ta kalli abincin snn ta mike da kyar tace "xan wanke baki" bayi ta nufa ya bi ta da kallo cike da tausayinta ko minti daya ba ayi da shiganta ba ta fasa wani ihu, ya mike da sauri yana tambayarta me ya faru a rude ya shiga bayin.

Wnn kam nasan har gobe ba lallai ne wasu su gama karanta shi ba tsabar yawa, all the same in kun gama goben koh da rana ne ku sanar da ni in daura plss..






~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
110.....
A durkushe Khaleel ya sameta a bayin, ya karaso da sauri shi ma ya durkusa yace "me ya faru" cikin kuka tana yarfe hannu tace "faduwa nayi" da damuwa yace "faduwa kuma? Garin ya?" Kin basa amsa tayi sae kuka take, ya dagota yana kallonta yace "ta ya kika fadi?" Ta girgixa masa kai tace "ni ma bn sani ba" kama hannunta yyi suka fita daga bayin ya xaunar da ita gefen gado yace "ki gaya min ta ynda kika fadi mana wife? Kuma me ya fadar da ke?" Ta share hawayen fuskarta tace "bn sani ba na xubar da ruwa sae na xame" yace "to ina ke maki ciwo ynxu?" Ta kalli kafarta tace "kafata amma ya daina ynxu" ya dudduba mata kafar snn ya Mike ya dagota a hnkli suka koma bayin, ya taimaka mata ta wanke bakin snn suka fito ya xuba mata abincin ta karba ta fara ci a hnkli. Da daddare ya fita ya siyo mata magunguna ta sha ganin sae complain take masa kafarta na ciwo, tana gama sha bacci ya dauketa, shi ma ya gama abinda xae yi ya kwanta. Can cikin dare kukanta ya tashe shi, ya mike xaune yana kallonta yace "me ya faru kuma?" Sanin wani lkcn hka take sa shi gaba cikin dare tai ta yi masa kuka ba dalili, da kyar ta iya bude baki tace "Cikina ke man ciwo da mara" ya sakko daga kan gadon ya dawo inda take yace "ciki kuma?" Gyada masa kai kawae tayi, yace "ki gaya min plss wife, ta ya kika fadi?" Cikin kuka tace "ni bn sani ba, kawae na ga na fadi ne" Khaleel ya girgixa kai da damuwa ya dagota yana mata sannu, hka ta hanasu bacci daren ranan sae kuka take ita cikin ta na ciwo, da asuba yana idar da sllhn ya tafi hsptl da ita ko scan ne ayi mata tun da bae san ta ynda ta buge ba, Karfe sha biyu saura suka dawo gida da Najeeb, suna shigowa falo ta kwanta kan kujera nn da nn bacci ya dauketa, Khaleel ya ajiye ledan magungunan hannunsa kan table ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar, Najeeb yace "she wil b alryt frnd in'sha Allah," Khaleel ya gyada masa kai kawae bae ce komae ba. Sae kusan Karfe biyu Ashnaah ta tashi, Khaleel da ke xaune har lkcn a falon ya dawo gefenta ya dagota yana kallonta yace "sannu wife, ya cikin ya daina?" Gyada masa kai tayi kawae, ya cire mata hijab din jikinta yace "gobe xa mu je a gyara kwanciyar bby koh?" Ta hade rae sae kuma ta fashe da kuka tace "ni dae bna so, irin na daxu xa ayi min" ya girgixa Kai yace "A'a wife wnn daban" mikewa yyi ya dagota yace "mu je sama ki sha tea"
Sae da aka kusa sati biyu Ashnaah ta samu saukin ciwon cikin, ta dawo nml sae dae me, kwata kwata Khaleel ya kasa gane kanta shirunta ya fi na ko wani lkci, abinci sae yyi da gske da ita take ci, idan ya tambayeta abin da ke damunta sae tace Abbanta, hkn yakan sa yaji tausayinta ssae, kullum yyi sllh sae yyi mata addu'an Allah ya daidaita ta da mahaifinta ko hnklinta xae kwanta, kusan duk kwana biyu sae ya kira mata momynta sun gaisa hkn ya lura na sa ta farin ciki, duk lkcn da ya ga mood dinta da kyau ya kan kai ta can gidansu gun umminsa ta wuni, wani lkcn su dawo ranan ko kuma Washegari, ana hka har watan haihuwarta ya tsaya. Yau Sunday tana kwance idonta biyu sae dae tayi xurfi cikin tunanin da take Khaleel ya shigo dakin rike da abincin da ya je gida ya karbo mata, juyawa tayi tana kallonsa ya sakar mata murmushi ya dawo kusa da ita ya xauna ya dagota yace "sannu da kwanciya wife, nace ki dan dinga motsa jikin ki ba kya ji koh" shiru tayi bata ce masa komae ba ya tsura mata ido, tayi masa wani mugun kyau ga hasken da ta kara, wara masa manyan idonta tayi ganin ynda yake kallonta sae kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, shi ma murmushin yyi ya rungumota a hnkli yace "I've a surprise for yhu wife" dago kai tayi tana kallonsa, ya fiddo wasu takardu a aljihunsa ya mika mata yana murmushi, ta karba ta shiga budewa, idonta ya sauka kan receipt da admission lettern ta da ta taba xubarwa da ddewa farkon fara remedial dinta, dago kai tayi da mmki tana kallonsa tace "ina ka ga wnn?" Yyi mata murmushi yace "ran da kika xubar da su ranan na tsince su?" Ta wara ido tana kallonsa, yyi yar dariya ya rungumeta ya lumshe ido yace "su nayi niyar baki ranan da kika mareni, I helped yhu pick them" hawaye ne ya cika idonta a hnkli tace "to ka yafe ni plss" dago kae yyi da sauri yana kallonta yace "kuka kuma? Haba bbyna ae dat day was the happiest day of my life wllh, baxan taba mance ranan ba wife, nd beside its nt ur fault its mine, I caused everything," Ashnaah ta kwanta kan kirjinsa a hnkli tace "ni dae ka yafe min duk abinda nayi maka tun daga farkon haduwar mu har xuwa yau" rungumeta yyi a sanyaye yace "ni ma ki yafe min wife" tayi murmushi hawaye na bin kuncinta shi ma sae ya samu kansa da xubda hawayen, a hnkli yace "kin san me yasa na kawo maki wife?" Ta girgixa Kai, yana shafa gashin kanta murya can kasa yace "today mark a year da haduwar mu, yau shekara daya da tsintar takardun nn da nayi" murmushi tayi yace "I love yhu" a hnkli tace "I love yhu more"
Da daddaren ranan ta dame shi tana son ya kai ta gun momynta ta gaisheta, bae mata musu ba yace su shirya to su je. Karfe takwas da rabi suka isa kofar gidansu, sae a snn gabanta ya fara faduwa ta dae dake ta fito daga motar, Khaleel na kallonta a hnkli yace "amma Abba baya nn koh?" Ta girgixa kai tace "ni ma bn sani ba." Yace "to ki shiga xan jira ki a nn" ta gyada masa kai ta nufi gate dinsu

101......
A bude Ashnaah ta samu falonsu, ta tura a hnkli ta shiga,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login