Showing 30001 words to 33000 words out of 115623 words

Chapter 11 - Tsutsar Nama Book Two Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

338

     Sosai naji wani irin abu mai nauyi ya soki zuciyata. Na dai danne da ƙyar ina murmushin yaƙe. Da girmamawa na amsa mata da “To mama nagode”. Daga haka ban sake cewa komai ba saboda baƙin ciki. Ni kuma haka rayuwata zata ƙare. Wahalar gidan Abba. Rabani da masoyina, auramin azzalumin mutum irin wannan mutumin da bai san komai ba a rayuwa sai kansa. Daga ƙarshe ma maimakon na shigo gidansu matsayin matar aure a ƴar aiki nazo. Nasan shine ya tsara hakan, kuma zan tabbatar masa ya tsara ramin muguntar da shine zai afka ciki daga ƙarshe. Dani yake magana Samraah Abdul-wahab gwarzo.....

       _Hummm Sam-G tamu. Koda yake aunty kike tunda matar Yayanmu ta🥱🥱🚴_

      ❤️ Kamar yanda Mama Balki ta umarceni wanka nayi nima. A'i da yanzu ta ɗan fara kulani itama ta kawo min doguwar riga ta farin Material da suma naga sun saka a jikinsu inji Mama Balki. Nayi mamakin kayan, dan sababbine ƙal kuma daga gani ba ƙanana bane ba. Haka dai na shirya ina zancen zuci. Ganin yanda Bahijja ta tsaya tana kallona ya sani mata alamar lafiya? Da idanu. Murmushi tayi da sauke ajiyar zuciya. “Wlhy Kandala baki ganki ba. Sam bakiyi kala da masu aiki ba. Kayan nan sun sake fiddo da ainahinki na ƙyaƙyƙyawar mace wayayya. Dan ALLAH idan bazaki damu ba ki sanar min labarinki. ALLAH sai nake ji a raina ko sunanki ba gaskiya kika sanar mana ba”.
      Idanu na ɗan waro mata kamar zanyi magana sai kuma na fasa nayi murmushi kawai. Dan babu abinda na ɗauki zancen nata sai shirme. A girme zan iya girmar Bahijja, amma yanayin inda take rayuwa da kuma halitta ta na mutum mai jiki yasa a ido zaka iya cewa sa'anni ne mu. Riƙoni tayi zata sake yin magana Afrah ta shigo. A wulaƙance tace, “Malamai ku Mama ke jira kuka wani zo nan kuka haɗe kawuna dan munafunc....”
      Ta gagara ƙarasawa saboda saukar idanunta a kaina. Ɗauke kaina nayi tamkar banga kallon da take min ba. naja ƙaramin mayafin Bahijja na yafa nai ficewata na barsu..
         “Kan uba Bahijja kinga kuwa abinda na gani tattare da yarinyar nan?”. Afrah ta faɗa cikin jimami da shiga ruɗani. Ƴar dariyar shaƙiyanci Bahijja tayi. “Yo mi kika gani?”.
      “Bahijja anya ba ƴar leƙen asiri bace ba. Sam yarinyar nan batai kama da wadda ta fito a cikin wahala ba. Musamman kwana biyun nan da tayi a gidan nan jikinta ya sake murjewa sai ainahinta ya fito. Duk da muma yawancinmu badaga ƙauye aka kawomu ba rashin gata ne da neman rufin asiri amma yarinyar nan fa ta fita daban a cikinmu wlhy.”
      Cikin son basar da zancen Bahijja ta ce, “Babu wani leƙen asiri. Itama dai neman rufin asirin ne ya kawota. Acikin ƴaƴan talakawan ma ai akwai ƙyawawa da yawa irinta har ma da wanda suka fita. Kin san dama irinsu gatan ne kawai babu, amma da sun samu kulawa sai ki gansu tarr da su”.
     Badan Afrah ta gamsu da bayanin Bahijja ba tai shiru. Dan Bahijjar na gama bata amsa ta nufi hanyar fita itama. Kai kawai Afrah ke jinjinawa da sake tabbatar ma kanta dole ne ta sakama yarinyar nan ido a gidan nan, dan sai ta san ko ita wacece....

      Koda na fito falon ma gaba ɗayansu suka zubomin ido. Hatta da Mama Balki naga alamar shock a tattare da ita. Tuni na ƙara gyara yanayina, dan na fahimci fa nima sai na yarda na ari wata rayuwa kafin na cimma burina akan mutumin nan dama zaman gidan nan. Sam bana fatan zama a cikinsa na dogon lokaci. Amma ina da burin son sanin sirrin cikinsa da mutumin nan keta faman ɓoyema duniya. Hakan kuma bazai taɓa ya kasance ba sai na zauna a matsayin da kowa ke kallona a yanzu na ƴar aiki. Ta wani gefen kuma begen ganin mahaifiyarsa da tausayinta na tsungulin min rai da zuciya. Sai dai ban san ta ina zan kama ba har yanzu. Gaishesu nayi kawai na koma gefe kaina a ƙasa...
      “Tab ɗi lallai akwai rigima a gidan nan. A banga laifin Hajiya Azizat ba. Anya kuwa babu alamar tambaya anan gurin?”. Aunty Falilah ce tai maganar cikin nuna baƙin cikinta muraran a kaina. Dama na fahimci ita da sauran ƙawayenta su Aunty Kubrah basa ƙaunata sam. Kafin wani ya sake magana Mama Balki tace muje. Dole kowa ya haɗiye abinda ke a ransa muka fice. Cikin raɗa Bahijja dake ta gefena ta ce, “Kiyi haƙuri karki damu da su. Su dama su Aunty ƴan neman fitina ne, sam basa riƙe girmansu a cikinmu saboda suna gadarar yaran Mammah ne a gidan. Itace mai juya akalar kowa a gidan kuma hatta da mai gidan kansa da matarsa”.
      Murmushi kawai nayi batare da nace komai ba. Dan ta gefena su Afrah ne idan har nayi magana zasu jini. Sosai an sake ƙawata gidan. Tako ina ka kalla kasan za'ayi shagali ne. A maimakon cikin gidan yau garden muka nufa. Bamma san sanda na furta “Masha ALLAH” ba a zahiri. Dan tsayawa muku misalin haɗuwa da tsaruwar da garden ɗin nan yayi ma ɓata lokaci ne. Sai dai abin mamaki bamu tsaya anan ba. Ta wata ƙofa da ganyen flower ya baibaye muka sake ratsawa sai gamu a wani killataccen waje da yafi wancan ƙatoton da muka ratso, wani irin shiryayyen adon furanni da koriyar ciyawa akai masa tako ina masu ƙamshi. Ga ƙaton swimming pool da ruwansa ke wani kalar ƙyalli da walwali tamkar ba normal ruwa ba. Ƙasa-ƙasa Bahijja dake kusa da ni ta furta, “Wannan sashen garden ɗin babu mai shigowa cikinsa sai a irin wannan ranar. Sau ɗaya a shekara kenan kawai”.
      Da mamaki nace mata, “Saboda mi?”.
      “Saboda bana kowa da kowa bane. Bakiga an zagayesa da waya ba. Uncle boss kaɗai ke shigowa cikinsa, dan tanan shine jikin part ɗinsa”. Ta ƙare maganar da ɗan nuna min wata hanya da aka ƙawata da koriyar ciyawa tamkar a irin lambun mafarkin gaibu ɗin nan. Na jima ina kallon ƙofar abubuwa masu yawa namin kai-kawo. Sai dai bance komai ba face ɗan kalle-kallen garden ɗin da nake yi. Komai a tsare a tsaftace. ga Docorretion ɗin da akai masa ya bala'in sake ƙawatashi. Hannuna da mama tazo ta kama ya sani kallonta firgigit, murmushi tamun da faɗin, “Zo muje ke anan zaki zauna har sai an buƙaci ganinki”.
       “Mama saboda mi?.
    “Saboda Aunty Mama bata bada umarni na shigo da ke har nan ba”.
Komai ban sake iya cewa ba har taja hannuna muka fito a wajen. A ƙaton garden ɗin na farko muka dawo. Ta kaini can wani ɗan lungu ta ce, “Zauna anan. Kar kije ko ina dan ALLAH dan akoda yaushe zan iya zuwa kiranki”.
    Kaina kawai na jinjina mata. Dan koda bata roƙeni ba ma bazan tashin ba. Nakai zaman mintuna talatin a wajen dukan tunanina naga Yaya Musaddiq. Yau wani irin kwaɗayin son jin muryarsa nake shi da Hafizzullah. Tamkar wadda hankalinta ke dawowa jikinta a wajen nake jin ƙarfin zuciyata da komaina dake neman ƙwacemin a kwanakin nan na fara dawowa. Sai kawai naji harshena ya ɗauki ambaton sunayen ALLAH. A jere na ringa sauke ajiyar zuciya kai kace a barci na farka. Ratsa kunnenna da sautin muryar malam tayi yana karanto addu'a ya sani lumshe idanuna a hankali. Ji nake hatta da jinin jikina yamutsawa yake yi har a cikin farautana har malam ya kammala. Ajiyar zuciya na sake saukewa a karo na babu adadi, dai-dai nan sai ga Mama Balki ta dawo kirana.
       Nasha mamakin ganin wajen yanzu dan cike. Dan komai da alama an tsarashi ne hatta da mutanen dake a wajen. Ɗan bin kowa da kallo nake ƙasa-ƙasa nima har muka isa inda su Bahijja ke tsaye jere. Dai-dai nan mc ke shelanta fitowar mai gayya mai aiki tare da tabbatar da shi a madadin  mai birthday ɗin. Tsitt wajen yayi kowa ya sake maida hankalinsa ga hanyar da Bahijja ta nunamin ta sashensa. Duk da yanda zuciyata ke tafasa na kasa ɗauke idanuna daga kallon wajen nima. Ƙanjamammiyar baturiyar nan mai shegen iyayi da yaje da ita wajen taron buɗe companynsa ce ta fara fitowa sanye cikin doguwar riga milk da wasu shegun dogayen takalmanta. Siririn tsaki na saki tare da ɗauke kaina a wajen gaba ɗaya.
       “Woow masha ALLAHU”. Da Bahijja dake a gefena ta faɗa ya sakani ɗagowa na kalleta. Ganin yanda ta saki baki da hanci da idanu tana kallo ya bani mamaki, kaina kawai na girgiza zan ɗauke caraf ta kamo hannuna. ”Dan ALLAH ki kalla ado ya namijin ɗawusu Aunty Kandala. Wlhy Uncle Boss na kasheni da salonsa, komai ya saka a jikinsa sai kiga kamar danshi dama akayi kayan, wani lokacin sai nakeji kamar na ciza uwawuna”.
      Takaicin shirmenta ya sakani dalla mata harara. Nai ƙoƙarin fisge hannuna amma ta sake damƙeshi. Haushi ya sakani kallonta, amma sai naga ma ita hankalinta sam baya a kaina. Takaici ya sani girgiza kai kawai nakai dubana ga abinda take zuzutawar batare da nasan dalili ba nima..........✍️

      _Bayin ALLAH kuyi haƙuri dani Please. Wlhy biki gareni na ƙanwata asabar ɗin nan. Jiya kuma rasuwa akai mana data bugeni sosai. Amma in sha ALLAHU komai ya kusa dai-dai da amarya taje ɗakinta zaku cigaba da ganina yanda ya kamata. Kuyi hakuri da asha ruwan tsuntsayen nan nawa na yanzu🙏_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_

......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima.

Addu'ar da aka fara gabatarwa ya saka kowa a wajen sake nutsuwa. Mu dai marasa gata duk muna a tsaye kan ƙafafunmu, yayinda suko ke zaune a kujerun da aka ƙawata wajen. Sosai yanda akai addu'ar wa kowa harda iyayenmu ya sake saka min nutsuwa har idanuna na tara ƙwalla. (ALLAH sarki rayuwa, da ace muma namu iyayen na raye babu yanda za'ai mu tsinta kammu a cikin wannan gararin rayuwar. Amma ko yanzu ma alhmdllh, koba komai mun rayu cikin aminci tunda gallazawar rayuwa batasa mun lalace ba). Kewar su Yaya Musaddiq ce ta sake taso min sabuwa har na zurfafa a tunani batare dana farga ba. Taɓanin da Bahijja tayi ne ya maidoni a hayyacina. A hankali na sauke ajiyar zuciya da nannauyan numfashi. Cikin raɗa-raɗa a saitin kunnena ta ce, “Aunty Kandala muje zamu fara bada drinks”. Kaina kawai na iya jinjina mata, dan gaba ɗaya babu wani ƙarfi a tattare da ni. Ta wajen babban table ɗin da aka shirya nau'ikan abinci dana lemuka da ruwa muka nufa. Bahijja ta zari handglob guda biyu ta miƙamin tare da mun nunin na saka. Itama ta zara ta saka a nata hannun sannan ta buɗe ƙatuwar kular da kayan ruwan ke ciki ta ɗiba lemunan da ruwa duk ta loda a babban tray data jawo guda biyu. Sai da ta gama zuba nata da nawa sannan ta ce, “Yauwa to muje. Kowa a gabansa zaki fara ajiye ruwa sannan ni kuma na ajiye lemon da suka buƙata”.
       “Kamar ya?”.
   Na tambaya cikin rashin fahimta. Ƴar dariya tayi. Kafin ta ce, “Na zuba miki ruwa ne dan kar su baki wahala. Shi ruwa zaka ajiye ne kawai. Amma lemo dole sai mutum ya zaɓa sannan”.
       Kaina na jinjina mata alamar gamsuwa, sannan na kama tray ɗin na ɗaga ina ɗan taɓe baki. Ai da sauri na maida na ajiye ina waro idanu. Ai wlhy bazan iya ɗauka ba yamun nauyi. Ragewa na fara yi, hakan ya sata zaro idanu waje alamar nuna mamaki. “Lafiya kike ragewa?”.
      “Yamun nauyi wlhy Bahijja bazan iya ɗauka ba”.
    Sake waro idanu tayi, niko ban sake kulata ba na rage fin rabi sannan na ɗauka. Kallo take mun na tama rasa abin faɗa. Ni ko na sake ɗauke kaina gefe kamar ban ganta ba. Dole itama ta barni muka bar wajen tana gaba ina biye da ita. Suma sauran kowa ya fara aikinsa dan komai a tsare yake. Mun fara da table ɗin farko. Mai ɗauke da mutane huɗu kamar ko ina. Maza biyu masu tsananin kammani, a fisge kuma suna kama da mutumin can Maash. Sai dai kawai su baƙaƙe ne. Tabbas nasan mai irin fuskar nan amma na manta a ina. Sai mata guda biyu ƙyawawa suma, ɗaya fara tas ɗaya black beauty. Su duka sunci ado sosai mai tsananin ƙawa. Ganin kallon da suke min na rashin sani yasa naji kamar duk na daburce. Amma sai na dake kaina a ƙasa na shiga haishesu ƙirjina na bugawa da sauri-sauri. Mazan ne kawai suka amsa min, yayinda baƙar matar ta dubi Bahijja a gadarance ta furta, “Wannan fa?”.
          Jikin Bahijja har ɓari yake. Cikin in-ina ta amsa da, “Au...aun..Aunty Mama ce tazo da ita randa ta iso”.
    Su dukansu ɗan kafeni sukai da kallo, sai kuma duk suka janye cike da basarwa. Jiki a sanyaye na bar wajen, batare da ina kallon gabana ba saboda zancen zuci na iso table na gaba. Ganin nayi tsaye kawai Bahijja ta ɗan zungureni, firgigit na kawo numfashi, ɗagowar da zanyi na sauke idanuna a kansa. Zaunensa yake a harɗe fuskar nan kicin-kicin tamkar ba wanda ya tara jama'a ba. Gaba ɗaya hankalinsa na akan tab dake a hannunsa ne. Yanda yay serious a kanta zai baka tabbacin abinda yake yi mai muhimmanci ne. Ga uban ƙamshin turarensa da ya mamaye wajen gaba ɗaya. Fuska na yamutse tare da ɗauke kaina. Harara na ballama ɗan koren PA ɗinsa dake table ɗin bayansu. Ƙasa naga yayi da kansa yana murmushi. Jinai zuciyata ta ƙulu da murmushin nasa, amma sai na danne tare da cije lips ɗina kawai....
        “Woow! fine girl ko ana mana rowan ruwan ne?”.
     Ɗaya daga cikin waɗan da ke zaune a table ɗin tare da shi ya dawo dani a hayyacina. Ni sai ma yanzu na lura da sauran dake zaunen a tare da shi. Su duka su nasan fuskokinsu a wajen taron buɗe Companyn sa na Kano. Dan ALLAH ya bani baiwar da dawahala nai maka gani ko ɗaya ne na manta fuskarka koda ace ban riƙe suna ba ko a inda na sanka ba. A hankali na ɗan yamutse fuska ta. Batare da nace komai ba na fara ajiye musu ruwan. Uku na ajiye abina batare da nashi ba, dan kowa a gabansa na ajiye amma shi banda shi. Na ɗaga tray ɗin zan bar wajen wannan dai da yay maganar ya ɗan waro idanunsa yana nuna min shi. “Beauty baki ajiyema boss ba fa”. Yi nai tamkar ban jisa ba sai da Bahijja tasa hannu ta ɗauka ruwan ta ajiye masa jikinta har yana ɗan rawa. Harararta nayi batare dana san dalili ba. Itako ta waro idanunta na nuna mamakina. Tray ɗin na sake ɗagawa da nufin barin wajen ina dallamasa harara ta gefen ido dan tunda mukazo wajen ko sau ɗaya bai motsa ba balle kai tunanin yama san da zuwan namu, batare da nasan yanda akai ba, ta yaya kawai tray ɗin ya suɓuce min na tafi gaba ɗaya na. Idanu kawai na runtse tare da sallamawa, amma sai na jini zaune jikin mutum, yayinda shi kuma tray ɗin ya suɓuce a ƙasa sauran ruwan suka tarwatse. Wani irin zuƙa da nayima mayataccen ƙamshin turarensa ya saka gabana faɗuwa. Da sauri na buɗe idanuna dake a rufe. Sai kawai na waro su tare da yunƙurawa da sauri zan miƙe amma hakan ya gagara. Dan sake zamewa nayi na koma jikin nasa gaba ɗayana har ma fiye da farko. 
      “Sai kice son hawa kike ba sai kinyi pretending ba”.
 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login