Showing 54001 words to 57000 words out of 115623 words

Chapter 19 - Tsutsar Nama Book Two Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

343

gagara ɓoyuwa gareta ta ce, “Maman Nana Musaddiq kuma? Shine dan Musaddiq zaiyi aure sai a munafunceni? Sannan tayaya ma shi Imam zaiyi gangancin kawo min matar Musaddiq mu rayu a gida ɗaya. Kenan ma su ƴaƴana sun rako na wasu ne duniya”.
     Ɗan jimm Maman Nana tayi, sai kuma ta jinjina kanta cike da gamsuwa. “To amma Maman Baby idan fa har ba hakan bane to tabbas Abban Abbas ne yayo aure batare da kin sani b....”
     Wata muguwar ashariya Mom ta lailayima Maman Nana tare da wanke fuskarta da mari. Tuni hankalin kowa ya fara dawowa kansu. Dan kafin Mom ta sauke hannunta itama Maman Nana ta sauke mata marin. Su kam dangin amarya tuni sun gama shigewa cikin ɗaki da amaryarsu batare da sunbi takan hayaniyar data kaure tsakanin Mom ɗin da Maman Nana ba. Zaburar Mom da nufar sashen amaryar ya saka Gwaggo Gudidi cimmata ta tare ƙofar. Ƙoƙarin tureta Mom keyi cike da raini Aunty Na'ima ta janyeta rai ɓace. “Wai ke Jalilah miyasa baki da isashiyar tarbiyya ne? Ke yanzu sai ki ture Gwaggon kike nufi?”.
        “Yo mizai hana nayi hakan, ai ni idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba, nima bazan ji kunyar kado shi ƙasa ba kuwa wlhy.”
     “K Jalilah ki shiga hankalinki wlhy dan yanzu ba da bace. Kin kuma san ko ada ɗin ma ana ƙyaleki ne darajar wanda ya kwasoki cikinmu amma badan ana jin tsoronki ba. Hauka kuma dama kin saita kanki kafin ɗan sauran mutuncinki daya rage ya ƙarasa zubewa. Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys”.
       Cak numfashin Mom ya tsaya tare da harbawar zuciyarta. (Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys) kalaman suka shiga maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarta cikin amsa kuwwa. A hankali ta ɗago tana kallon Aunty Ni'ima, sai kawai idanunta suka sauka akan Abba daya shigo. Rawa jikinta ya farayi, cikin ɗimuwa da sassarfa ta nufesa. Cak ya tsaya yana kallonta harta ƙaraso inda yaken. Yanda ta cakumo hannunsa zai tabbatar maka da bata a cikin hayyacinta, dan harshenta har sarƙewa yake wajen faɗin, “Abban Abbas wacece wannan aka kawo min gida? Matar wacece? Dan ALLAH kace min Abbas kaima aure”.
       A hankali ya girgiza mata kansa tare da riƙo hannunta. “Jalilah Please relax mana..”
   “Naƙi nayi relax ɗin Imamu ka faɗa min wacece ita?”.
      “Zan faɗa miki amma ki muje daga ciki”.
    “Wlhy babu inda zanje sai ka faɗa min anan. Kuma kaima ɗin baka isa kabar wajen nan ba....”
    Gwaggo Gudidi ce ta ƙaraso wajen. Idonta akan Abba ta ce, “Miye kake wani zazzame mata Imamu, ka fito fili ka faɗa matan tunda ita ta nema da kanta. Ai shiyyasa ake son mace ta zama matar ƙwarai kodan irin wannan ranar. Idan ka zama ɗan arziƙi mai tarbiyya taya har miji zai ɗakko maka abokiyar zama batare da saninka ba. Ai dama halinka sabulun wankanka. Mata dai taka ce muma duk mun shaida. Hargowarta ko shirmenta bai isa sakawa a goge hakan ba. Dan in har kai gigin sakin wannan baiwar ALLAHr daka auro koda bayan raina ne wlhy kaf mu ahalinka bazamu yafe maka ba. Ballema nasan bazaka fara kwatanta hakan ba dan kaima kana ƙaunar matarka. Dan haka ka fito ka sanar mata aure ka ƙara dan bazaka cigaba da zama daga kai sai ita a cikin gida ba ta kasheka watarana kamar yanda ta rabaka da duk danginka damu iyayenk.....”
        Babu wanda ya san ta yanda akai kawai hannun Mom aka gani a wuyan Abba ta cakumosa. So take tayi magana amma hakan ya gagara saboda numfashinta ma fisga yake. A mamakin kowa sai gani sukai tayi baya gaba ɗayanta alamar suma. Ƙasa take neman zubewa sai da Abban ya riƙota.....

🌜🥱🌛

     Tunda tabar falon bai iya ya motsa daga inda yake zaune ba. Sai ma tsurama ƙofar da tabi idanunsa yay tamkar tana a wajen har yanzu. Yana nan zaune kusan mintuna goma shigowar Hayatu ta katse tunanin nasa. Koda Hayatun ya gaisheshi ma hannu kawai ya ɗaga masa. Shi dai Hayatu ya riga ya saba shiyyasa bai damu ba. Sai ma kaiwa da yay zaune bayan yaje gabansa ya ajiye takardun dake a hannunsa dan yau shi bai fita office ba sakamakon yini da sukai akan Hajiya Babba da likitocinta, tare da tsaftar sashenta aka fidda duk kayan da Samraah ta tattara dama sauran duk na sashen aka canja mata katifa kafin a kawo wasu. Shiyyasa Hayatun ya kawo masa duk wani document mai muhimmanci da zai duba ya saka hannu...

          Ina fita na saki murmushin farin ciki. Yau dai na samu wayar yin magana da ƴan uwana. Duk da ko a da da nayi niyya zanyi hakan dan su Bahijja duk akwai waya a hannunsu. Abinda yasa ban taɓa ara ba saboda bana buƙatar kowa yasan sirrina. Farin cikin waya ya mantar dani wani batun aikin Hajiya Mammah. Dan amaimakon kitchen daya kamata na koma ficewata nayi daga sashen baki ɗaya ko su Azizat dake zaune acan rukunin ƙarshe na kujeru bana tunanin sun ma ganni. Ban nufi sashen mu ba na wuce garden ɗin gidan. Tsabar wuce wuri kuma maimakon babban garden sai na shige ƙaramin da akace nasa dan na samesa a buɗe da'alama aikin gyarashi akayi saboda kayan aiki dana gani an tule. Can na shige kusan ƙarshe duk dan dai na samu wajen ɓuya nai wayar a tsanake. Kaina tsaye na sake danna kiran layin Yaya Musaddiq. Sai dai harta katse bai ɗaga ba sai da na sake kira na biyu. Hayaniyar da naji ya sani faɗin, “Yaya ya nake jin hayaniya ko kana kasuwa ne?”.
      Maimakon amsa ƴar dariya yayi da cewa, “Har kin gama darun?”.
    “Kai Yaya ni har wani daru ne da ni?”.
   “Sosai kuwa Kandalata. Ai ke naki ma na musamman ne.”
   Karon farko na saki dariya, sai kuma na shiga gaishesa da girmamawa. Ya amsa min da kulawa tare da tambayar lafiyata da kuma jiyyar da nayi. Na amsa masa da Alhamdullah, tare da tambayarsa mi ake a gidan naji hayaniya. Kansa tsaye ya ce, “Mamarki akema kishiya”.
    Da mamaki nace, “Mamata kuma Yaya? Wa kenan?”.
       “Mom mana. Abba ne ya ƙara aure”.
   Tuni na miƙe daga zaunen da nake dan mamaki, sai kuma na shiga ƙyalƙyala dariya. “Wai dan ALLAH yaya da gaske kake ko wasa? Mom fa akaima kishiya? Ta yaya Abba ya samu wannan ƙwarin gwiwar haka? A ina kuma ya samo matar?”.
       Tsaf Yaya Musaddiq ya kwashe labari ya bani, tun daga zuwan Halime gidan har kawo yau da suke jiran isowar amarya batare da Mom ta sani ba. Tsabar farin ciki bamma san lokacin dana rangaɗa ghuɗa ba. Sai da Yaya yace min, “Ƙaniyarki kandala” sannan na bari ina dariya. Haka kawai nake jin raina fes da wannan al'amari. Dai-dai nan sautin muryar aunty Zakiyya data rangaɗa sallama ya ratsa kunnuwana. Bayan sun gama magana da Yaya Musaddiq yake cemata gani a waya. Amsa tayi cike da zumuɗi muka gaisa, kafin cikin raunin murya da lallashi ta ce, “Samraah shike nan kuma babu kira duk kinsa hankalinmu ya kasa kwanciya?”.
     Murmushi nayi hawaye na cika min ido. Muryata na rawa na ce, “Aunty bani da waya ne. Kuma kuma kun sallamani ga wanda ban ko sani ba kamar bani da kowa a duniya”.
      “Haba Samraah, shin bazamu iya haƙuri da karɓar ƙaddara ba a duk lokacin da tazo mana? A maimakon tada hankali a ganina godiya ya kamata muyima UBANGIJI dan a maimakon tozarcin da akaso ganinmu a ciki alkairi ne ke lulluɓe da mutuncin mu. Samraah kiyi haƙuri dan ALLAH, ki karɓa da hannu biyu sai ALLAH ya sauƙaƙa komai a yanda ba kowa yay zato ba. A kowace daƙiƙa ta rayuwa kuma kina ranmu. Kawai dan bamu san ta yanda zamu sameki bane ba”.
     Babu daɗi kalamanta suke sake saka ni. Dan haka na sake raunana murya, “Aunty kina nufin maganar da wannan mutumin ya faɗa da Yaya gaskiya ce? Da shi aka ɗaura min aure, kuma aka kawo ni garesa? Shike nan kuma kun barmasa ni?”.
        Ƴar dariya tayi, cikin wasa ta ce,.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_

_________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_____________

........“Ya zamu bar masa ke. Sai dai ya ɗauki rabi ya bar mana rabi. Ke dai ki kwantar da hankalinki kinji. In sha ALLAHU ni da Musaddiq muna nan tafe har inda kike. Dama a tunaninmu idan kinji sauƙi zai dawo mana dake gida ne shiyyasa. To amma uzirin daya kawo akan zaman naku anan yanzu dole a haƙura har sanda ya kawoki da kansa ɗin. Ni dai kawai roƙona ki kwantar mana da hankalinki, ki mance da Mansoor kamar yanda mahaifiyarsa ta buƙata, ALLAH shine shaidar mu ba laifinmu bane sune sukaƙimu. Dan a ranar ɗaurin aurenku mahaifiyarsa da kanta tazo tace sun fasa ɗanta bazai aureki ba saboda ba'a san mi aka aikata miki ba da akai kidnapping ɗinki. Babu yanda su Kawu Musa basu lallasheta ba har gwaji sukace aje ai miki amma fir matar nan taƙi sai ma cin mutunci da gori data shiga musu. Suko sun san mutuncin kansu ai, dan haka suka janye suka bama wannan bawan ALLAHn ke dan su mutuntaki da mu kammu. Dan inba hakaba wannan mugun baƙin fentin da sukai miki zaita bibiyar rayuwarki ne harma mijin ya gagara gareki a gaba”.
         Sosai maganganun aunty Zakiyya suka ratsa min jiki. Mamaki da al'ajabin mahaifiyar Mansoor ya tsaya min a zuciyata. Harna kasa daurewa na ce, “Amma Aunty shi yaya akai yasanni yazo neman aurena? Ko su kawun sun sanshi ne su?”.
“To ni dai bazance ba gaskiya. Amma dai kamar naji ance shine yazo yace yana son aurenkin da kansa. Ki dai tambayi Gwaggo tasan komai kuma nasan zata sanar miki. Ko kuma shi mijin naki ki tambayesa ai bazai ƙi sanar miki ba”.
Shiru nai tsahon lokaci na kasa cewa komai. Sai kuma can na ce, “Okay Aunty in sha ALLAHU zan tambayesa”.
Nasiha suma suka min cikin lallashi ita da Yaya Musaddiq. Bayan munyi sallama na jima zaune a garden ɗin ina tunani kafin na miƙe na koma sashenmu bayan na kashe wayar na sakata a jikina. Ina shiga Aunty Sadiy ta shigo wai naje Hajiya Mammah na kirana. Idanu na ɗan waro dan harga ALLAH nama manta da batunta...

A ɗarare na tafi amsa kiran nata, sai dai cikin sa'a ina zuwa na samu wai tana da baƙuwa sun ma fita yanzun nan. Ajiyar zuciya na sauke na juya na koma ina godema ALLAH. Dan dana sameta ban san mi zance ba wajen kare kaina.

✨★✨★✨

    Da ƙyar aka samu Mom ta farfaɗo. Tana kuwa farfaɗowar wasan ya koma sabo. Dan tuni Ummanta da su Baby da basa gidan sun dawo harma da wasu ƴan uwanta. Faɗa ne mai ƙarfin gaske ya ɓarke tsakanin dangin Mom da ita kanta da dangin Abba. Dan dangin amarya su dai ƴan kallo suka zama. Sai dai kuma ransu ko ɗar balle gezau akan ƴarsu bazata iya zama ba. Sai ma murna suke da rahamar da UBANGIJI yay mata na samun wannan danƙareren gida a matsayin gidan aurenta. Itama ɗin dai Halimen ko'a kwalar rigarta. Yo ita wane kalar masifa da bala'i ne bata gani a wajen Innarta ba. Sannan faɗan kishi babu irin wanda ba'ayi a gidansu. Dan kaf matan kawunanta ba su ɗaɗɗaya bane Innace ma kawai ita kaɗai a wajen Baba. Amma sauran daga mai mata uku sai mai biyu harma da mai huɗu. Kuma haka ake shan cakwakiya a gidansu gashi gidan yawa. Ita dariya ma abinda ke faruwa ke bata. Sai da Hajiya Asabe ta ƙwaɓeta daga yanda take kwasar dariya tana leƙe ta window sannan ta nutsu.

     Shi dai Abba ma tuni ya fita ya bar musu gidan bisa umarnin Gwaggo Gudidi. Haka aka ci uwar sabada mata anguwa nata shigowa. Masu yima Mom dariya da ALLAH ya ƙara sunfi yawa. Dan har a cikin ƙawayen nata wasu abin ya musu daɗi. Ummanta ce data fahimci al'amarin fa shiryayye ne dan dangin Abba sun kafa sun tsare yasa ta janye Mom ɗin suka shige ɗaki. Ba'a sake ganinta ba har kusan goma na dare sai ga likita wai yazo zai dubata hawan jininta ya tashi. Babu wanda yabi takan batun kowa ya cigaba da sabgarsa. Sai ita da ƴaƴanta da Ummanta ke ƙulle-ƙullensu can a sashenta su kaɗai.

      Har washe gari daga ɓangaren Mom dai babu daɗi, gashi Abba yaƙi shiga inda take tun dubatan da yaje yay na farko bai sake zuwa ba, dan yana shiga ta sake birkicewa harda shaƙeshi tana kuka da faɗin sai ta kasheshi sai dai duk su rasa. Har ita  zai tozarta yama kishiya, to wlhy ya sani ya ɗakko bala'i da masifar da bazata taɓa ƙarewa ba har sai cikin abu uku ɗaya ya faru. Kodai ta kashesa, ko kuma ya saki yarinyar a yau danginta su koma inda suka fito da ita, ko kuma idan ita ta mutu. Kuma koda ta mutu yace zai sake aure sai ta dinga masa fatalwa. Abin nata kamar wasa ya nema zama babba, dan da ƙyar aka fiddo Abba a ɗakin tana neman murɗe masa jikinsa ALLAH dai ya taƙaita masa wahala akwai babbar riga tare da shi.
        Su dai ƴan uwansa da dangin amarya sabgar gabansu suke hankali kwance dan basu san mike faruwa a cikin ba sai da su Gwaggo Gudidi suka fito da Abba ne suke jin komai. Aiko fa kowa ya shiga ALLAH wadarai da wannan baƙin hali na Mom, daga nan kowa ya sake ɗaura ɗammara a kanta. Dan a ranar dangin amarya sukai walima tare da rabon kayan gararsu cikin bajinta da aka san katsinawa da ita a wajen rabo. Al'amarin ya ƙayatar da kowa a dangin Abban, sun kuma yaba da ƙoƙarin mutanen. Ana yin sallar azhar motocin da zasu maidasu gida suka kwashesu aka bar amarya Halime na kwasar kuka. Sai da su Aunty Zakiyya suka jata ɗaki suna lallashi. Daga ƙarshe ma dai su suka cigaba da zama da ita suna ɗebe mata kewa har washe gari da suma kowa yay haramar kama gabansa bayan sun kimtsa gidan. Har kuma sannan babu wanda yaga idon Mom. Sai dai duk sun fahimci akwai abinda suke ƙullawa ita da uwarta dan sai shigi da fici Ummar tata keyi a kwana biyun nan, saboda rashin sanin ciwon kai a gidan take kwana itama har a yau da bikin ya tashi. Ƴan Gwarzo ma sun rigata wucewa. Ganin bata ma da niyyar tafiya ne yasa Gwaggo Gudidi itama ta fasa tafiya a yau duk da dai dama wasu a dangin sun kawo shawarar Gwaggon ta ɗan zauna har gidan ya dai-daita gudun kar'a cutar da yarinyar mutane. Kowa kuma ya gamsu da shawarar dan haka Gwaggon tai zamanta. Sai hakan kuma yayima Abban daɗi shima. Dan dama yana tunanin ta yanda zai fita yabar Halime daga ita sai Mom ɗin a gidan har sai ya gama saita gidan...

     💦💥💦💥💦

    Kwanaki biyar kenan da faruwar dukan da naci a sashen Hajiya Babba. Alhamdullah jikina yayi sauki, dan hatta ciwon da taji min ma ya warke sarai sai tabo. Tun wannan ranar ban sake gigin komawa ba duk da hankalina na'a kanta. Haka shima uban gayyar ban sake ganinsa a gidan ba. Sai ma a bakin Mama Balki nake jin wai yayi tafiya ai tun a washe garin faruwar al'amarin da dare. Ranar da Hajiya Mammah ta aikani sashensa kai masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login