Showing 45001 words to 48000 words out of 115623 words

Chapter 16 - Tsutsar Nama Book Two Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

341

sai ga awa ta shuɗe. Awa ɗaya, biyu, uku itama ta shuɗe. Tsaye take akan kula da girkin rana dasu Kubrah keyi amma kaɗan-kaɗan sai ta fito daga kitchen ɗin, tun ma basu fahimtaba suma har suka fara tsarguwa. Cikin gulma suka dinga nunama junansu ita da ido da baki. Sam Mama Balki bata san ma sunayi ba, saboda hankalinta a rabe yake. Ƴar hayaniyar su Arwa dake falo da zagin da taji sunayi ya sata fitowa zumut daga kitchen ɗin. Hannu taga duk sun saka suna famar toshe hancina. Yayinda tuni Muhsin ya fara kakarin amai. Dai-dai nan itama mahaukacin warin ya daki hancinta, da sauri takai hannu ta toshe hanci, sai kuma ga jama'ar gidan suma sun fara fitowa daga sassansu kowa na tambayar warin minene haka?.
     Rasa mai bama wani amsa akai sai nuni da sama saitin sashen Hajiya Babba kawai akeyi. A dai-dai nan katifar da Samraah ta jingina jikin ƙarfen da aka ƙawata adon wajen da shi da bata zauna dai-dai ba ta sulmiyo downstairs ɗin gaba ɗaya. Ihu yaran suka buga a tare suna tarwatsewa. Sai kuma yunƙurin amai dan gaba ɗaya falon ya ƙarasa gumamewa. Cike da fusata Hajiya Mammah ta koma upstairs ɗin tana ƙwala kiran Samraah da “K!! K!! K!!” dan ko sunanta bata sani na. Ihun nata yaja hankalin sauran iyayen dama su Azizat ɗin suma suka bita. Hakama su Falilah ba'a barsu a baya ba. Mama Balki ce ƙarshen bin bayansu.

       Isowarsu ƙofar dai-dai da ƙwalla ƙarar azaba da Samraah tayi, a take kowa ya tsaya cak. Ƙarar da Samraah ta sake fasawa kuma duk sai suka ja da baya. Dan basa buƙatar ƙarin bayani ta ƙwaɓe ne tsakaninta da mai sashen. A matuƙar tashin hankali Mama Balki ta juya da gudu ta sauka downstairs ɗin jikinta na ɓari. Bama tasan sanda takai kanta sashen Maash ba. Kawai tsintar kanta tayi a gabansa durƙushe cikin kuka da roƙo ta kama ƙafafunsa....
         “Alhaji ƙarami dan ALLAH ka taimake mu. Kandala. Kandala ce gata can a sashen Hajiya Babba...” numfashinta ya nema ɗaukewa gaba ɗaya saboda yanda take a kiɗime. Shiko Maash da tun shigowar tata a guje da tsawar da Hayatu yay mata na son ta dakata ya tsaya cak daga duba abinda Hayatun ke nuna masa a tab sai dai bai ɗago ba sai da ta ambaci Hajiya Babba dan shi bai ma san waye wani Kandala ba. Idan ka cire ita a gidan da mijinta sai wasu tsiraru a masu aikin da suka daɗe a tare da su kawai zai iya cewa ya sani har ma ya shaidasu koda a wajen gidan ya gansu. Amma daga basu ɗin ba babu wanda zai iya shaidawa a cikinsu.
     Cak Hayatu shima ya dakata da ga yunƙurin maganar da yake, dan sai a lokacin yama fahimci wacece ɗin. Shine yay ƙarfin halin faɗin, “Mama waye Kandala? Mi kuma ya faru da Hajiya Babba?”.
        So take tai magana amma ta kasa, sai nuna ƙofa kawai take ga hawaye na kwaranya mata. Ƙarasowa Hayatun yay da sauri inda take. Ya kama hannunta ya miƙar daga gaban Maash da take durƙushe. “Kinga relax. Calm down kiyi magana yanda za'a fahimta. Rufe idonki ki shaƙi iska ki fesar Mama”.
     Kai mama Balki ta shiga jinjinawa tana haɗiyar kukan da sauri-sauri. Yanda duk Hayatun yace tayi tayi, ya miƙa mata ruwan gabansa ta sha maƙwarwa biyu sannan ta sauke nannauyan numfashi. Shi dai Maash kallonsu kawai yake amma ya gagara cewa komai. Cikin ƴar nutsuwar data samu ta sake faɗin, “Kan...kandala ce sabuwar mai aikin da Aunty Mama ta kawo. Ta..ta tafi sashen Hajiya Babba gata can tana ihu da alama....” sai kuma ta kasa ƙarasawa. Sosai Hayatu ya waro idanu a firgice. Yayinda Maash yayi wani masifar runtse nashi da ƙarfi, sai kuma ya ajiye tab ɗin hannun nasa ya miƙe. Baima tsaya ƙarasa jin zancen ba ya nufi ƙofar da kan sadashi da sashen mahaifiyar tasa kai tsaye daga sashensa. Sai dai kuma a kulle take. Jikinsa ya shiga shafawa neman key, amma da alama baya tare da shi, har ya kalla Hayatu zai yi magana sai kuma ya fasa. Komawa yay da baya ya fito, da sauri Hayatu da Mama Balki suka take masa baya. Ta babban falon gidan da ya gama gumamewa da warin katifar nan ya ratsa, da bibbiyu ya dinga haɗa stairs ɗin tsabar tashin hankalin da yake a ciki. Dan duk duniya bai haɗa al'amarin mahaifiyar tasa da komai ba. Cikin rufewar ido da ɗimuwa yake sa hannu ya ture duk wanda ya tare masa gaba. A haka har ya shige ciki gaba ɗaya dan su mutanen gidan suna a falon farko ne cirko-cirko sun gagara shiga ciki dan tsoro. Sai hayaniya da suka cika wajen da shi. Yana shiga securitys ɗin da sukai kira na cikin gidan na isowa. Suma takema Maash ɗin da Hayatu baya sukayi...

        Sosai nake kakarin mutuwa. Idanuna kam sun gama firfitowa. A wannan gaɓar na sallama da rayuwa. Ta ALLAH kawai nake jira ta kasance. Wata irin bugawa da tama kaina a bango ya sani fasa wahalalliyar ƙara da ko sautin kirki babu yanzu saboda galabaita dana gama yi. Daga haka ban sake sanin mi kuma duniya ke'a ciki ba...
    
       Shigowar Maash dai-dai da wancakalo Samraah da Hajiya Babba tayi kai kace irin an yadda magen nan. Baya yay taga-taga zai faɗi, sai da Hayatu ya riƙesa. Da sauri ya kai dubansa kan abinda ta wurgo ɗin, a kuma dai-dai nan itama ta sake wawuro abin morpping irin na wutar nan da Samraah ta ajiye tare da sauran kayan shara. Ji kake bummm!! Akan goshinsa. Kamar ƙyaftawar ido ta sake rarumo wani abun, jifan kan mai uwa da wabi ta shiga musu kamar yanda take yi a duk sanda take a irin wannan yanayin. Dole su Hayatu suka shiga fita a guje. Yayinda Maash ya kasa yin hakan shi. Dan shi damuwarsa ba ciwon data jimasan bane. Kar ita ta jima kanta ciwon. Ƙoƙarin nufarta yayi da son kwashe sauran kayan sharan. Amma ina jifa kawai take kai masa dasu tako ina...
Cikin wani irin karyewar murya ya shiga ƙoƙarin kai hannu gareta yana faɗin, “Please Ummie na kar kiji ciwo, dan ALLAH ki ajiye zai ji miki ciwo. Hannunki Ummie hannunki.”
     Ina ita bama tasan yanayi ba. Jifan kawai take kai masa har sai da taga kayan sun ƙare, sai kuma ta koma kai masa duka da hannu. Cikin sa'a shima ta shaƙuro wuyarsa. Dai-dai nan masu kula da lafiyarta da akai kira a waya suka iso. Da ƙyar aka ɓanɓare Maash a hannunta bayan sun mata allura mai ƙarfin gaske. Zama yay ƙasa batare da jin ƙyanƙyamin komai ba ya riƙeta a jikinsa ya zubama fiskarta idanunsa da suka rikiɗe gaba ɗaya. Yanda Adams apple ɗin sa ke kai da kawo zai tabbatar maka da kukan zuci yake yi. Yafi mintuna goma zaune a haka shiru, duk maganar da su Hajiya Mammah suke masa bai ko motsa ba. Sai da Paah ya shigo ya kai duƙe kusa da shi, hannu ya fara kaiwa ya riƙo na Ummie dake kwance ka shirɓan allamar barcin nata yay nisa matuƙa, idanu ya zubama hannun cike da tausayawa shima nasa na cika da hawaye, dan har yanzu har gobe yana matuƙar ƙaunar matar tasa rufin asirinsa kuma. Hawayensa ya share kafin ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Maash da bai ko motsa ba.
      “Muhammad”.
   A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Paah ɗin nasa batare da ya iya cewa komai ba, sai kuma ya ɗauke ya maida kan (Ummi) Hajiya ƙarama da ke tare da sauran masu kula da lafiyarta dan itama likita ce. Sake ɗaukewa yay ya maida kan Samraah dake kwance gefe a sume babu wanda yabi takanta. Yanda ya tsurama wajen ido na tsahon mintina kusan biyu ya saka kowa maida kanhalinsa ga kallon abinda yake kallon. Shima kansa Paah sai a lokacin ya lura da Samraah ɗin.......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_


.......Cikin tashin hankali ya miƙe yana ambaton, “Subahanallahi. Ita kuma wannan mike faruwa haka?”.
        Idanun Muneef cike da hawaye ya ce, “Paah ai itace ta fara shigowa yima Hajiya Babba shara shine sai....” ya gagara ƙarasawa saboda hararar da Hajiya Mammah ta wurga masa. Duk da kowa ya fahimci Hajiya Mammah ɗin ce ta kwaɓi yaron babu wanda ya iya tankawa. Shi dama Maash kansa a duƙe yake kawai yana duban mahaifiyarsa kamar bai san mi sukeyi ba. Yanda bai kallesu ba bai tanka musu ba ya miƙe ɗauke da Ummiensa. Fita yay daga ɗakin gaba ɗaya da ita. Dole suka shiga darewa suna bashi hanya. Can falon da Samraah ta gyara yaje ya kwantar da ita. Anan ɗin ma sai dai ya tsira mata ido na kusan minti ɗaya kafin ya juya ya koma ɗakin. Yanzu kam ya samu Azizat na ƙoƙarin sheƙa ma Samraah ruwa a jiki cike da mugunta da wulaƙanci, wani irin kallo daya wurga mata ya sakata daburcewa taja da baya tana faman sinne kai. Yanzun ma baice da kowa komai ba ya ƙara da inda Samraah ɗin ke kwance. Sunkuyawa yay gaba ɗayanta ya ɗauka. Dukansu sai da kowa ta waro idanu waje musamman Malika da Azizat da Arwa, yayinda ran Hajiya Mammah ya gama ɓaci amma bata ce komai ba. Kamar ɗazun darewa sukai suka bashi hanya, cike da takun nan nasa na bajinta da ƙarfin jini ya fice ɗauke da Sam-G dake a sume batama san inda kanta yake ba. Kallon kallo aka fara yi, kafin Paah da shi dama komai bai canja ba daga garesa ba sai ma daɗin kulawar da Maash ɗin ya bada akan yarinyar yaji ya bi bayansa. Dan shi dai abinda kawai ya sama ransa dole Maash ya taimaka ma yarinyar, amma yana mamakin ma yaya akai tazo har nan ɗin tunda yasan babu mai shiga sashen Hajiya Mammah ɗin kai tsaye haka sai masu kulawa da ita, tunda kuma waccan ta gudu kusan wata guda kenan ba'a sake kawo wata ba. Ganin Paah ya fita duk suka zabura suma suka bi bayansa. A falon ƙasa suka samu Maash na ƙoƙarin sauke Samraah saman kujerar falon tare da kaiwa zaune shima ya kwantar da kanta a jikinsa. Dai-dai nan Hayatu ya iso gabansa da first eld box. A gabansa ya dire, jikinsa har rawa yake wajen fara fiddo abinda za'a fara buƙata. Maash ɗin ya miƙawa auduga, da farko zubama audigar idanu kawai yayi kamar bazai amsa ba. Sai kuma miya gani oho masa ya kai hannu ya amsa. Jinin goshinta da har lokacin ke fita ya fara ƙoƙarin gogewa, ganin kamar kaɗar bata masa yanda yake so sai kawai ya jawo handkerchief dake jikinsa fari tass ya shiga kwashe jinin da duk ya gama ɓata mata fuska. Sai da ya goge shi tass sannan ya saka ƙaramin bandage dan ciwon ba wani ƙato bane can sosai amma ba laifi da ɗan girmansa. Ganin ya kammala komai Hayatu ya miƙo masa goran ruwa. Karɓa yay ya zuba kaɗan a cikin hannunsa ya shafa mata a fuskar zuwa wuyanta. Numfashi mai nauyi sosai ta kawo, sai kuma ta zabura cikin yanayin firgita ta ƙanƙamesa jikinta na rawa. A hankali ya lumshe idanunsa batare daya ko motsa daga yanda yake ba.. kusan mintuna biyu suna a haka kowa ya zuba musu ido kowai, yayinda zukatan wasu suka gama hasala, wasu ko na tausaya mata...
       Shigar ƙamshin turarensa a cikin hancina ya sakani tsayawa cak, wani irin bugawa ƙirjina yayi, ga zuciyata na tafiya da sauri-sauri a cikin ƙirjina, komai daya faru ya shiga dawo min daki-daki. Fara sassauta riƙon da naima koma wanene nayi, sai kuma na sakesa gaba ɗaya na yunƙura zan tashi, sarawar da kaina yayi ya sani kai hannu na dafesa tare da faɗin, “Wash ALLAH na” na koma na kwanta a inda naken. A bazata naji saukar tattausan hannu mai zafi sosai a saman nawa hannun, janye nawan akayi a hankali, hakan ya sani sake buɗe nauyayyun idanuna. Harga ALLAH sai da zuciyata ta harba da ƙarfi Bily saboda saukarsu a cikin na wanda banyi zaton gani ba. Duk kuma yanda naso janyewa hakan ya gagara, kallonsa nake a tsakkiyar ido kamar yanda nima yake kallona. Ga hannunsa riƙe da nawa shi bai sakar min ba, bai kuma ajiye ba....
         “Are you okay?!”.
     Ya faɗa cikin yanayin motsa lips batare da fitar sautin murya ba, gaba ɗaya naji wata irin kasala ta saukar min, sanyi ya shiga ratsani a cikin ƙashi da ɓargon jikina. A maimakon bashi amsa sai kawai na lumshe nawa idanun a hankali nima, wasu hawaye ne da suka jima maƙale a cikin idanun nawa suka sami damar silalowa batare da nasan dalilin hakan ba...
      “Hayat muje hospital”.
   Furicin sa cikin sauƙaƙa harshe ya sani buɗesu da sauri. Kaina na girgiza masa da sauri ina ɓata fuska da tura baki, sai kuma na yunƙura zan tashi a jikin nasa ina faɗin, “Ni dai bance ina son zuwa asibiti ba ai”.
     Bai tanka min ba, sai maidani da yay a yanda nake ya sake kwantarwa a jikin nasa. Jinai kamar na fasa kuka, amma dole na haƙura dan nasan koma sake yunƙurin tashi bazan iya ba. Saboda wani irin sarawa kaina keyi da juya min.
        Azizat ce ta fara jan sirrin tsaki ranta a ɓace tabar wajen duk da bajin abinda suke faɗa sukai ba, sai Maleeka da hawaye suka gama wankema fuska dan tsabar takaici. Dan lokaci ɗaya taji tsanar yarinyar ta gama baibaye rayuwarta. Wata mace kwance a jikin Awwab ɗinta ba ita ba...
     Dawowar Hayatu ya katsema kowa zancen zucinsa. Cike da girmamawa ya sanar masa ga Doctor nan a hanyar zuwa. Kamar ko yaushe bai amsa ba. Sai Hajiya Mammah ce cikin ɗan faɗa-faɗa ta furta, “Yanzu ga Hajiya ƙarama a gida matsayin doctor sai an kira wani likita dubata kuma dan ɗigimi?”.
     Hayatu rasa abinda zaice mata yay, sai kallon ogan nasa da ya ɗan yi. Da gaske bashi da alamar bama Hajiya Mammah ɗin amsa, dan kansa ma na a ƙasa ne yana faman latsa waya. Sai da Hajiya Ƙarama ta furta, “Ciwon nata ma kamar bamai tsanani bane, magani kawai zata sha in sha ALLAH jikin zai mata sauƙi.” ta ƙare maganar da ƙarasowa ta duba magungunan first eld box dake gefensa. Duk maganin daya kamata nasha ta ware, sannan ta nunama Mama Balki duk yanda zan sha su. Tana kammalawa Hajiya Mammah tace su kamani su tafi dani can sashen masu aiki. Batama rufe baki ba na yunƙura na tashi daga jikinsa hannuna dafe da kaina. Mama Balki da A'i ne suka kamani. Muna ƙoƙarin barin wajen na ɗan ɗago na kallesa, idanu muka haɗa, sai kawai na tura masa baki. Dan luuu yay da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya ɗauke kansa gaba ɗaya...

      ❤️★❤️★❤️

  Kwanaki huɗu kenan da ɗaura auren Abba da Halime. Har zuwa yanzu kuma bai sanarma Mom ba. Dan bama shiga sabgarta yake ba har yanzu. Itace dai take son su shirya saboda ko abincin gidan baya ci. Ga abubuwa teacher ya bata amma ta rasa yanda zatai da su. Yau ne ma da saurayin Baby ya sake zuwa Abban ya ɗan sake a gidan har suka ga haƙoransa a waje. Kai tsaye kuma batare da kwana-kwana ba ya bashi damar turo magabatansa har hakan yaso bama Mom ɗin mamaki. Amma dai batace komai ba sai da ta kira Ummanta take sanar mata sai tace mata aikin malamin ne ya fara cinsa. Tunda dama yace zai musu wani a bayan fage bayan na abincin da aka basu a saka masa. Wannan ne ya sanyaya zuciyar Mom ta samu nutsuwar cigaba da warisarta akan kuɗin da saurayin Baby ɗin ya danƙara musu yau ma.
        Kwana ɗaya da zuwan saurayin Baby kwana biyar da ɗaura auren Abba ya fara gyaran gidansa. A haukar Mom dama kowa dake gidan shine Abba ya ƙirƙiri gyaran ne domin auren Baby ɗin. Shiko baicewa kowa komai ba. Garama kwana biyu da fara aikin ya zauna da Musaddiq ya buƙaci ya bashi aron kuɗi. Babu musu kuwa Musaddiq ɗin ya bashi kuɗin, jin daɗin hakan ne ya saka Abba kwancemasa abinda ke faruwa game da auren nasa. Duk da zuciyar Musaddiq ta girgiza sai da ya saki murmushin da har ya so bama Abba mamaki.
      “ALLAH ya sanya alkairi Abba. Amma baka ganin akwai damuwa a haɗa Mom da Auntyn a gida ɗaya kuwa?”.
    Murmushi shima Abba yayi a karo na farko, sai kuma ya dafa kafaɗar Musaddiq ɗin. “Gaskiya ka faɗa Musaddiq, sai dai hakan da zanyi zai fi bani kwanciyar hankali ni kuma. Dan Maman nan taku zata iya aikata komai saboda bata ƙaunar kishiya. Amma kaga idan suna a tare waje guda koyaya zamu dinga sani wani motsinta ai ko”.
            “Hakane kuma Abba. ALLAH ya sanya alkairi to. Ya kuma kauda fitina”.
     “Amin ya rabbi Musaddiq. ALLAH yay maka albarka. Ku ƙara haƙuri dani kunji”.
    Murmushi Musaddiq yay kawai amma baice komai ba.

     An kammala gyaran gida tsaff a cikin kwanaki uku, duk wanda ya kalla

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login