Showing 57001 words to 60000 words out of 115623 words

Chapter 20 - Tsutsar Nama Book Two Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

349

coffee kenan harna taho masa da waya. Bakina kawai na taɓe na cigaba da harkar gabana, dan damuwar data daman daban, duk da kuwa tana da alaƙa da shi. Sosai ina buƙatar zama dashi a wannan gaɓar, dan ina son jin yanda akai har ya je gidanmu ya nema aurena. Ai abin da mamaki, dan Mansoor mahaifiyarsa ta hanashi aurena shi kuma ace yaje ya auran bayan babu wata alaƙa data alaƙanta tsakanina da shi bayan ta kidnapping ɗina da yayi da hira da nai da shi a station ɗinmu...
            Zuwa yanzu aikina ya koma sashen Hajiya Mammah, nice kullum mai mata gyaran sashenta safe da yamma. Da farko dai abinda na fara fahimta ga halayyar matar shine nuna isa da mulki. Na biyu shegen kallon raini na ƙurillar tsiya kamar zata cinyeka da idanu. Sai masifa komai kayi sai ta maka jaraba kamar itace ta halicceka. Shiyyasa idan na tashi kafin ma ta tashi a barci na gama gyara ko'ina nabar sashen, sai kamar 11 sai na koma na gyara mata bedroom lokacin ta fito. Yau ma kamar kullum da wuri na kammala aikin nawa, sai dai ina ƙoƙarin sauka dawn stairs na jiyo kamar sautin kuka na fitowa ta sashen Hajiya Babba. Tsamm nayi da raina kusan mintuna uku, jin dai da gaske tanan ɗin ne bamma san lokacin dana juya cikin sauri da sassarfa ba. Idanuna a rufe na faɗa sashen batare dana tuna da wahalar dana sha a hannunta kwana biyar da suka wuce ba. Ganin key a ƙofar ya sani murɗawa na afka ido rufe, jikina har rawa yake jin sautin kukanta da yanda take ambaton kiran sunan “Muhammad” dan zuwa yanzu na fahimci Maash kadai suke kira Muhammad a gidan ita da Paah. Zubewa nai a inda take zaune can karƙashin ƙafar bene ta cure jikinta waje guda fuskarta cikin ƙafafunta.
         “Ummi miya sameki? Baki da lafiya?”. Na faɗa cikin rawar murya ina kamo hannayenta dake ɗauke da sayin ɗauri har yanzu amma duk ciwukan sun warke. A mamakina sai naga ta ɗago a hankali. Yanda idanunta suka kumbura sukai jaa sosai ya sake tayar min da hankali. Ga hawaye face-face da fuskar tata. Sai kawai nima na fashe da kuka tare da faɗawa a jikinta. Tsamm ta rungumeni itama tana ƙara fashewa da kukan da cigaba da magana cikin sambatu. “Muhammad ciwo, kaina ciwo zai fashe Muhammad. Ga jikina ƙaiƙayi yake min. Muhammad ina jin yunwa”.
       Kuka na sake fashewa da shi ina mai ɗagowa a jikin nata. Amma sai ta hanani tashi ta sake matseni sosai. Duk da zafin da nake ji ban sake yinƙurin tashin ba. Tsahon mintuna biyar muna a haka har na fara numfashi da ƙyar. Sai kuma ta sakeni ta dafe kanta da riƙe cikinta. Zumbur na miƙe jikina na rawa, ga hawaye sun kasa tsaya min, “Kiyi haƙuri Ummie ki daina kuka dan ALLAH, yunwa kike ji ko?, Zakici abinci na kawo miki?”.
     A mamakina kai ta ɗaga min tare da kamo hannuna ta ɗaura a saman cikinta hawaye na sharara ta shiga jujjuya min kanta. Ta ce, “Yunwa Muhammad yunwa”.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_


.......Da sauri na jinjina mata kai ina ƙoƙarin miƙewa. “To Ummie in sha ALLAHU yanzu zan kawo miki abinci bani ɗan lokaci ƙalilan.” ban jira amsawarta ba na tashi na fita a guje dan nasan bama amsawar zatai ba. A falonta na farko naci karo da wasu mata guda uku sabbin fuska daban sani ba a gidan. Nayi mamaki dan ɗazun ban gansu ba, ko kuma ban lura dasu bane oho. Takan kowa banbi ba a cikinsu nafice zuwa downstairs na afka kitchen, ganin an gama komai har an gyara kitchen ɗin ma fito dining, komai an shirya na breakfast, sai dai babu kowa a kai dan sai sun gama barcin safensu suke fitowa karyawar. Hajiya Ƙarama ce kawai bata a gidan ta wuce wajen aiki. Komai sai da na ɗiba tare da haɗa shayi mai ƙauri na ɗauka ruwa. Da gudu na koma saman, inda na barta nan na sameta, sai dai yanzu tana kwance ta naɗe a waje guda sai nishi take alamar yunwar tacita ta cinye matan nan na tsaitsaye a kanta kamar a tsorace. Ina shigowa duk suka zabura kanta. Tsawa na daka musu tare da nuna musu ƙofa alamar su fita. Har rige-rigen fitar kuwa sukeyi. Basket ɗin hannuna na ajiye, sannan na durƙusa gabanta na ɗagota. A jikina na sanyata ina kuka da bata haƙuri, shayin dana haɗa dai-dai zafi na ɗauka na kai bakinta, jikinta har rawa yake wajen damƙe kofin, tsam ta dafesa tare da hannayena kamar mai lafiya, kwal-kwal ta shiga kwankwaɗar shayin tamkar ta samu ruwa. Kafin wani dogon lokaci ta shanyesa gaba ɗaya, sai ga zufa na karyo mata tako ina ta fara sauke ajiyar zuciya jikinta na saki. Jinai hawaye sun ƙara ziraro min, na kwantar da kanta sosai a saman cinyata ina shafa cuɗaɗɗen gashinta daya danƙare saboda datti. Tabbas ɗiya mace daban ce, da ace baiwar ALLAHr nan nada ƴa mace a cikin ƴaƴanta duk tsanani bazata dinga barinta a cikin wannan dattin ba. Amma kalla yanda aka saketa kamar mara gata. Dukiyar tatace, gidan ma nata ne, ɗan da suke taƙamar da shi a yanzu haka nata ne. Amma ita bata san daɗin ko ɗaya a ciki ba, sai wasu banzaye da sukazo suka cika gidan badan su amfana mata da komai ba. In sha ALLAHU na ɗauki alƙawarin daga yau koda baiwar ALLAHr nan zata halakani sai na ƙwato mata ƴancin rayuwarta a gidan nan, tun daga kula da ita har zuwa sanin tushen wannan ciwo nata da nake ji a raina ba banza ba. Kai harma ɗan nata da alama ba haka suka barsa ba shima. Sai da na tabbatar shayin da tasha ya faɗa mata sosai sannan na jawo abinci, ban tasheta a jikin nawa ba, a haka na dinga bata da kaina kuma tana amsa. Sai kallona take dan har ta kauda kanta alamar ta ƙoshi idonta a kaina ƙyam. Lemo na ɗakko zan bata ta kauda kai, sai na ajiye na ɗauki ruwa. Ina saka mata a baki kuwa ta hau sha. Sosai tasha tana sauke numfashi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikina, mintuna bai fi biyu ba barci mai nauyi ya dauketa. Ganin barcin nata yay nisa na fara kwance mata kitson kanta da yay bala'in danƙarewa, da naga ta motsa sai na ɗan dakata, sai ta koma barcin sai na cigaba. A haka na kwance gashin tana barci a jikina. Sosai take da gashi, da alama shima a wajenta ya gaji wannan gashin nashin da yakema mutane iyayi da shi. Ganin barcin nata yayi nisa na lallaɓa na kwantar da ita, gyaran sashen na fara, harda wancan ɗakin da naci duka a ciki wancan karon. Da yake na saka aikin a raina kuma an rage dattin da yay wancan karon sosai koma nace an gyara komai ƙal sai dai ban san wanda ya gyara ba kafin wani dogon lokaci na kammala tsaff, amma ina zargin matan nan dana gani sabbin ma'aikata ne aka kawo mata, maybe kuma sune sukai aikin. Ko'ina sai ƙamshi yake kamar ba shi ba, ruwa na haɗa inata tunanin ta yanda zatai wanka, dan harga ALLAH jikinta na buƙatar wanka, saboda alamu sun nuna an ɗan rage dattin jikinta ba kamar a ranar farko dana sameta na, harma kayan bana waccan ranar bane ba, sai dai kamar kuma ba'a sake mata ba tun waccan ranar ɗin. Ni kuma bamma san ta yanda zan iya cewa zan mata ba dan ina jin kunya. Dabara ce ta faɗo min, na fita zuwa kitchen dan nasan yanzu sun dawo aikin rana. Babu kowa a falon kuwa, cikin sa'a kuma na samu Mama Balki a dining tsaye tana waya. Tana ganina ta yanke kiran. Sai da ta wawwaiga ta tabbatar babu kowa a wajen sannan ta kama hannuna. Can ƙarƙashin stairs muka je, fuskarta cike da damuwa ta ce, “Ina kika shiga Kandala? Tun ɗazun ake nemanki a gidan nan amma babu ke”.
    Kaina tsaye nace mata, “Mama ina sashen Hajiya Babba fa. Yanzu ma kiranki nazo yi ki taimakeni”.
      Sosai fuskarta ta nuna mamaki, ta ce, “Sashen Hajiya Babba fa?”.
    “Eh wlhy Mama. Dan ALLAH kizo ma muje kiga taimakon da zaki min kafin wani ya gammu anan a hanamu. Bata musa ba muka hau upstairs. Ni kaina tsaye nake tafiya, yayinda ita kuma take ta faman waige-waige da gani duk a tsarge take. Ita kanta sai da tayi mamakin yanda na ƙara gyara sashen, Hajiya Babba dake kwance na nuna mata. “Mama ki taimakeni jikinta na buƙatar wanka ne. Idan akai mata zataji sanyi. Ga kanta na buƙatar wanki ma, sannan matan can dake zaune a falon farko wai su wanene?”.
       Ɗan jimm tai alamar tunani, sai kuma ta amsa min da, “To yanzu yaya za'ayi kenan? Kin san fa dole aka saka mata ruwa a jiki dole ta farka. Kuma hakan akwai matsala shiyyasa ma Alhaji ƙarami ya hana a jika mata kai ranar. Waɗan can matan kuma sune sabbin masu aiki da Baba ya kawo tun ranar da abin can ya faru tsakaninku”.
     “Mama in sha ALLAHU baza'a samu matsala ba. Dan yanzu da kanta taci abinci. Kota farka kuma da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru mama. Su kuma ki gargaɗesu dan ALLAH ko kuma suje waje idan anjima sa dawo”.
    Badan ta gamsu ba ta yarda da magana ta, da taimakona muka kamata zuwa bathroom. Sannan ta fita ban san yaya tayi da matan ba ta dawo. Sake ɗaukar ta mukayi zuwa toilet. Ganin ta buɗe idanunta alamar ta farka cikin ruwan dana haɗa a bathtub muka sakata. Da farko taso zabura, sai da na dafe mata hannu da sauri cikin lallashi da roƙo ga hawaye a fuskata ina tofa mata addu'a sannan ta haƙura ta koma ta zauna. Kanta muka fara ƙoƙarin wankewa, sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjere. Yanda wata muguwar dauɗa ke fita ban san lokacin dana ƙara ƙarfin kukana ba dan tausayi. Kai da kaga wannan baiwa kasan kafin lalurar na anyi manyan hamshaƙan mata. Amma jiba yanda ƙaddara ta maidata, ɗan adam kenan ba'a bakin komai yake ba. Bamu bar kan ba sai da ya koma fidda farar kumfa sol da ruwa mai ƙyau, baiwar ALLAH sai sauke ajiyar zuciya take, barci ma ɗibarta yake. Fitowa nayi nabar Mama Balki tai mata wanka, duk da na fahimci ita tana komai a tsorace ne. Sai dai Alhamdullah ta daure ta mata wanka na gaske duk da ni na fito duba kaya kozan samu. Anan dai ɗakin da muke babu, sai da na duba ɗayan kusa da ita dake a kulle sai nayi sa'an samu, ashe ɗakin duk kayan sawarta ne da duk wani abun buƙata na gyaran jiki. Da alama tana ɓatawa ne shiyyasa ake rufesa abar key ɗin a jiki, sai dai kuma babu tabbacin ana mata amfani da su, dan da jikinta baiyi wannan masifar dattin ba ai. Komai da za'a iya buƙata na ɗauka harda towel sannan na koma inda suke. Har lokacin basu fito ba, dan haka na miƙama Mama Balki towel guda biyu, na ajiye duk abinda zasu buƙata na fita dan ta samu damar shiryata. Ina daga falo zaune kusan mintinan talatin sai ga Mama Balki ta fito tana sharar hawaye ga murmushi akan fuskarta. Zumbur na miƙe ina tambayarta ko lafiya. Maimakon amsa saita jawoni jikinta ta rungume tana mai fashewa da kuka mai ƙarfi da sanya min albarka. Ban iya kwace jikina ba har sai da tayi mai isarta ta ɗagoni dan kanta. Hawayen nima na share kafin na sake tambayarta abinda ke faruwa.
        “Babu abinda ya faru Kandala. Ke dai ALLAH yay miki albarka. Kin kwatanta abinda wani bai taɓaba a gidan nan. Ashe baiwar ALLAHr nan ba kowane lokaci bane take a yanayin da ake gudunta. Dama ƙyaƙyƙyawar mace ce mai ƙyawun siffa da cikar haiba amma ƙaddara ta maidata haka. Zo ki ganta Kandala zo kiga cikar zati da asalin kwarjinin manyan mata dan ALLAH”.
    Jiki na rawa nabi Mama Balki. Muna shiga ciki sai da na kusa faɗuwa dan mamakin abinda naci karo da shi. Lallai anan Awwab ya gado cikakken ƙyawu da asalin kwarjini. Hatta da idanun magen nan nasa irin nata ne. Bamma san lokacin dana ƙarasa gareta cikin sassarfa ba na durƙushe, hannayenta duka na kamo a cikin nawa na runtse, tamkar wadda ke cikin hankalinta sai ta sakar min wani guntun murmushi tare da lumshe idanunta a lokaci guda ta buɗe sai kuma ta sake maidasu ta lumshe. Bamma san lokacin da ƙaunar matar ya ƙara mamaye jini da ɓargona ba. Nai zaman dirshan a gabanta na cigaba da kallonta tamkar na samu television. Tsahon lokaci ina a haka har sai da mama Balki ta fargar dani muyi mu fita kafin mutanen gidan su farga da zamanmu a ashen. Gashi su kansu wadancan matan bamu san a ƙarƙashin ikon wa suke ba. Kaina tsaye nace “To mama minene dan sun san muna anan? Dama ba so suke su sami mai kulawa da ita ba? Nifa waɗan nan matan bazasu cigaba da zama da ita ba sai dai su koma inda suka fito”.
     “Hummm” kawai Mama Balki tace dani batare da fashin baƙi ba. Daga haka ta fita tana mai tabbatar min nayi sauri na kammala tunda tayi barci na fito ita zata koma akan bakin aikinta. Da to kawai na amsa mata badan zanyi yanda tace ɗin ba, dan tana fitar ma kayan gyaran gashi na jawo tare da gyara zama na hau gyara gashin Ummie. Gashine mai uban yawa ga tsayi shiyyasa nasha wahala sosai. Ban bar mata shi a haka ba nai zaman kitsa mata shi. Nan ɗin ma dai ansha cakwakiya kafin a kammala, dan takan farka ta dafe hannuna tana yamutsa fuska. Har sai na tsaya ta huta ina tofa mata addu'a sannan nake cigaba. Sanda muka gama barcinta yayi nisa sosai, dan haka na miƙe na tattare kayan dana kawo mata abinci ɗazun da wanda nai gyaran gashinta na maida inda suke na fita da sauran samo mata wani abincin. Kusan cin karo mukai da yarinyar da Bahijja tace min agola ce a gidan, tana ƙoƙarin hawowa upstairs ina ƙoƙarin sauka ni kuma. A ɗan yamutse da kallon raini tace min nazo ana nemana........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_


.......Uffan bance da ita ba na cigaba da sauka ƙasan. Tunkan na ƙarasa nake jiyo hargowa da ihun Hajiya Mammah. Nadai dake na cigaba da sauka ina kallon Mama Balki dake durƙushe gabanta kamar ma kuka take yi, sai matan nan guda uku suma durƙushe a gefenta, ai kafin ma na ƙarasa gabanta nima naji saukar mari. A take azaba ta sakani watsar da kayan hannuna suka tarwatse a wajen. Ban gama dawowa a hayyacina ba ta shaƙure min wuya da faɗin, “K wai wacece? Ƴar uban wacece a ƙasar nan dazan ce ga abinda zakiyi ki canja da naki tsarin?”.
     Sam bana ma fahimtar mi take faɗa, sai kakari neman fitar rai kawai nake ga idanuna sun gama firfitowa waje. Wani marin ta sake yarfa min sannan ta hankaɗani baya. Buguwa nayi da kujera da Azizat dake ta wajen, sai itama kawai ta sake hankaɗoni na dawo. Na gama sallamawa sai na kai ƙasa, amma a mamakina sai na jini a jikin mutum babu zato...
      Tun faɗowarta jikinsa a bazata ya tsaya cak tamkar bishiyar kuka. Bai kalleta ba, bai kuma motsa ba, bai kuma janyeta a jikinsa ba. Sai dai fuskar ta sake wani irin tsukewa mai tsanani dake sake fidda ɓacin ransa muraran ga duk wanda zai iya kallonsa. Duk da shi dama ba abin wasan kowa bane a gidan yanayin fuskar yasa ta sake saka kowa firgita. Hakan yasa numfashinsu ɗaukewa gaba ɗayansu a lokaci guda. Daga masu ɗora hannaye duka a saman kai, sai masu wage baki, sai masu waro idanu waje. Hatta da ita kanta Hajiya Mammah ɗin ta shiga shock da ganinsa dan babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon. Amma da yake macece data goge a iya barikanci sai ta zaburo inda suke tana cigaba da masifa.
         Har isowarta inda muke na gagara tashi a jikinsa. Saima ƙanƙamesa dana sake yi ganin takai hannu zata finciko ni. Jin bata fincikonin ba na buɗe idanuna dana rumtse. Sosai na warosu waje dan mamakin ganin shine ashe ya tare hannun nata da nasa. Ai zumbur na miƙe kan ƙafafuna na. Cikin ƙara zaburowa ta ce, “Barni Awwab naci uban yarinyar nan da bata da kunya da mutunci.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login