Showing 114001 words to 115623 words out of 115623 words

Chapter 39 - Tsutsar Nama Book Two Complete Hausa Novel

22 Oct 2025

354

cikin son aro jarumtar dole. Sai kawai Maash ya zare takardar daga hannunsa yana faɗin, “Okay bama sai ka amsa ba anan. Next time kawai”. Ya ƙare maganar cike da rainin wayo yana kallon takardar. Yana gama karantawa ya saki wani shegen murmushi, a saman lips ɗinsa ya furta “Mr Paul” dan ya fahimci kai tsaye daga inda saƙon yake. Nuni yay ma Hayatu da ya tashi. Babu musu kuwa ya miƙe ya nufosa. Hannu yasa a aljihu ya ciro wayar TJ daya amsa da key ɗin bedroom ɗinsa ya miƙa masa.  “Ka bama Mama ta dubata. Idan akwai matsala kuje da ita asibiti zan sameku acan. Juliet taje ta ƙarasa meeting ɗin jiya”.
     “Amma sir...”
Ɗauke kansa yay alamar baya buƙatar jin komai da ga Hayatun. Tj ya kalla tare da faɗin, “Bani key ɗin mota”. Cikin sauri TJ ya zaro ya miƙa masa. Batare da ya kalla ko inda su Hajiya Mammah suke ba ya matsa ga jami'an tsaron. Wani ne ya yunƙuro da Handcuffs a hannunsa da sauri. Wani banzan kallo da Maash ɗin ya masa bai ma san ya taka burki ba harda cin tuntuɓe. Wucewarsa yay ga motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin driver. Sai da yazo saitin ogan nasu ya tsaya, batare da ya kallesa ba ya furta, “Zan iya wucewa ni kaɗai?”.
         Kallonsa kawai shugaban jami'an yake. Dan shi kam yanzu yake sake tabbatar da rashin mutuncin Maash ɗin da ake faɗa ya zarta duk yanda aka gaya masa ashe. Ga yaron da shegen kwarjini. Duk da kasancewarsa jami'in tsaro, a shekaru kuma zai iya haifar Maash ɗin, wata irin shakkarsa yake ji har ƙarƙashin zuciyarsa. Har takai ya fara jin nadamar amsar wannan aikin da yay. Yaransa biyu ya bama umarnin shiga bayan motar, shi kuma ya shiga gaba kusa da Maash ɗin. Sauran kuma suka fita da sauri wajen gate inda motocinsu da sauran ƴan uwansu suke.
         Shi Maash ma sai abin yaso bashi dariya ganin yanda aka cika kusan rabin street ɗin da jami'an tsaron kai kace sunzo kamo wani ƙasurgumin ɗan ta'adda ne daya addabi duniya. Lalataccen Murmushi ne ya suɓuce masa kaɗan. Dan in ba kallonsa kake ba bama zaka taɓa fahimtar yayisa ba. A nutsensa yake jan motar tamkar wanda baya so, har suka iso babban headquters ɗin DSS ɗin dake a garin na Lagos babu wanda yay ko tari a motar.....

       ★★★

      Motocin na gama fita a harabar gidan Hayatu yay wani irin sauke numfashin damuwa. Sai kuma ya maida kallonsa gasu Paah dake ƙoƙarin nufar motoci alamar zasubi bayansu. Nufarsu shima yayi, cikin girmamawa ya dakatar da su. Bayani yay musu akan suyi haƙuri kar suyi gaggawar binsu har sai ya sanar da lawyers ɗinsu yanzu.
     Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shima sai yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran lawyers ɗin nasu har su uku. Yayinda shi kuma Paah ke ƙoƙarin neman Baba prof.. da baya ma ƙasar kusan sati uku kenan. Hayatu na gama kiran lawyers ɗinsu ya isa ga Mama Balki dake ta faman share hawaye ita da su Bahijja. Key ɗin da Maash ɗin ya bashi ya bata, tare da mata bayani. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke a karo na farko, dan dama hankalinsu a matuƙar tashe yake tun sabe na rashin ganin Samraah ɗin, ita a zatonta ma ko guduwa tayi. Dan ko'ina na gidan babu inda ba'a duba ba har sashen Hajiya Babba daya zama na farko amma babu ita. Batare da kowa ya farga ba Mama Balki ta zare jikinta sashen Maash. Dan su Hajiya Mammah sunata bige-bigen waya ne...

       Matuƙar tausayin Samraah ne ya cika Mama Balki har sai da tayi hawaye. Bata kawo a ranta wani dalili ne ya saka Maash yin wannan ɗanyen aikin ba, sai ƙila gardama Samraah ɗin ta masa. Amma yanda tasan Maash da tausayi da ƙoƙarin tsare hakkin kowa a rayuwa da mamaki wannan al'amari. Dan gaba ɗaya al'amarin babu tausayi a ciki. (Koda yake ƙila shima ya kasa riƙe kansa ne) zuciyarta ta ayyana mata tana mai ƙoƙarin ganin bataji zafin Maash ɗin ba a ranta. Ruwa ta shafa ma Samraah ta kawo numfashi, kukan data fashe da shi cikin zabura ya saka Mama Balki riƙota jikinta ta rungume. Sai kawai itama ta fara hawayen tana lallashinta.
      Jin muryar Mama Balki yanzu ba shi ba ya sakani jin nutsuwa. Sake ƙankameta nai cikin kuka ina mata magiyar dan ALLAH ta fita dani a ɗakin, idan ta barni kasheni zaiyi bashi da imani. Lallashina ta shiga yi da kalamai masu sanyi, sai da taga na sake nitsuwa sannan ta kwantar dani tana faɗin na jirata. Hawayena na cigaba dayi harta dawo bayan wasu mintina. Babu abinda ke mun kai kawo sai abinda ya farun. Sam hawaye sun gagara ƙafe min, koda Mama Balki ta kamani domin tashi sam na kasa. Sai ma kukan fitar hankali dana sakar mata dan wata irin azaba ce ta ratsani tun daga yatsun ƙafata har tsakkiyar ƙwalwata. Itama ganin bafa zan iya tashin ba ya sakata sake jin matsanancin tausayina. Rigar wankansa data ɗakko daga bathroom ɗinsa ta saka min ta sake gyarawa, sai kuma ta kamani cike da jarumta ta ɗaga gaba ɗaya na. Haka tana nishi baiwar ALLAH ta kaini har Bathroom ɗin. Sai da tamun gajeriyar nasiha da lallashi sannan ta taimaka min na shiga ruwan data haɗa. Bakina na dumtse ina mai fashewa da kuka jikina na rawa. Haka ta rirriƙeni tana cigaba da mun nasihar duk zaburar da nake bata yarda nabar cikin ruwan ba sai da ya huce. Wani ta sake haɗawa, sai da tamun haka sai uku abinka da dattiwar data san takan duniya sannan ta baroni nayi wanka.
       Kuka naci sosai har sai da tamun knocking ƙofar sannan nayi wankan. Cikin jarumta da son daurewa na ɗauka wata rigar wankan na saka dan wancan ta jiƙe saboda bata cireta a jikina ba ta sakani a ruwan da ita. Duk yanda naso taka ƙafafuna na fita da kaina hakan ya gagara. Kuka na sake sanyawa mai sautin da har sai da Mama Balki taji ta shigo. Kallona ta tsaya yi, kafin cike da tausayi ta furta, “Samraah bazaki iya tafiya ba yanzu ma?”.
        Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye. A sanyaye tace, “Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU zaki ci riba a rayuwarki tunda bata hanyar banza kika tsinta kanki a wannan halin ba. Amma lallai dole zamuje asibiti kenan”.
     Kuka na sake fashe mata da shi batare dana iya cewa komai ba. Yanzun ma itace ta fiddoni. A saman kujera ta ajiye ni. Ta gyara ɗakin fes kamar bashi ba. Dan hatta da bedsheet ɗin ma ta canja wani. Kayana da ban san waya kawo mata ba ta bani tace na saka. Ita kuma ta koma bathroom ɗin bayan ta shinfiɗa min abin salla. Kayan na saka ina hawaye na sakko domin yin sallar, da ƙyar na iya yinta a tsaye, inayi ina kuka. Ina idarwar na zame a wajen na kwanta, kafin mama Balki ta fito zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni.
     Barci ya ɗan fara figata mama Balki ta tasheni nasha tea, kasa sha nayi, sai kuka nake mata kawai. Baiwar ALLAH duk ta shiga damuwa sai lallashina take yi. Wani barcin ne ya sake figata, gigitaccen bugun ƙofar da ake ya farkar dani. Buɗe ƙofar Mama Balki taje tayi, ɗauuuu kake jin saukar mari a fuskarta. Kafin Hajiya Mammah ta hankaɗota ciki. Taga-taga tayi zata faɗi ALLAH ya taimaketa ta rike ƙarfe net ɗin gado. Har cikin rai naji zafin marin nan da taima Mama Balki yau. Cikin matuƙar masifa ta shiga surfama Mama Balki zagi wai itace kawaliyarsa dake kawo masa yara ashe yana musu fyaɗe, to yau kam sai sunci ubanta a gidan nan. Duk yanda take son musu bayani kowa yaƙi yarda da ita, sai tambayoyi suke jefe mata kuma sunƙi bari ta basu amsa.  
         Shiɗewa numfashina ya farayi saboda yanda hayaniyar Hajiya Mammah ke shiga har cikin tsakkiyar kaina dake ciwo. Sama-sama nake jiyo muryar Hajiya ƙarama na bada shawarar kaini asibiti. Daga haka ban sake gane komai ba........✍️

_Huuuum tofa masu karatu ƙaƙa raƙa ƙaƙa.._

    *_Yaya zata kaya kenan? Maash zai sanarma ahalinsa wacece Samraah a yanzu ko zai cigaba da ɓoyewa?._*

    *_Shin waye Mr Paul daya saka a aka kama Maash? Mi kuma kuke tunanin zai faru?_*

   _Samraah!! Samraah!! Wane hukunci kuke tunanin zata iya ɗauka akan Maash kan abinda ya faru, da labarin da taji na al'ummar wannan gida?._

     *Hajiya Mammah?*
*Hajiya ƙarama?*
*Paah?*
*Uncle Abdullahi da matarsa?*

_Shi kansa Maash bakwa tunanin akwai abinda yeke binnewa kuwa?._

_Gidan Abba, gidan su Mansoor, nan ma fa duk akwai sabuwar cakwakiya._

    *_Hummm kar dai na cikaku da surutu, mu tara ranar Monday in sha ALLAHU. Banda pages dole zanyi hutun weekend ɗin nan insha ALLAHU. Dan munzo gaɓar da komai yake buƙatar fita da fitarsa. Ku muje zuwa TSUTSAR NAMA BOOK 3 Guys._*


_Bana son naga numbers ɗin na tsaho ganda rubutun nake ji wlhy, dan haka zamu tafi part 3 yanda zamuyi maza kafin salla mu kammala in sha ALLAH 😘😘😘_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login