Showing 66001 words to 69000 words out of 115623 words
musamman ma masu aikin nan naku munafukai. Yanzu dai ina son kimin bayanin mike faruwa?”.
Shiru kamar Hajiya Mammah bazatayi magana ba. Sai kuma cikin ƙunar rai ta shiga ma aminiyar tata bayani tun daga farkon zuwan Samraah gidan har kawo yau ɗin nan kamar yanda dai ta sanar mata ta waya. Ƙawar tata ta jima batace komai ba alamar nazari, kafin ta saki murmushi da kallon Hajiya Mammah.
“Ni ina ganin mafitace tazo mana ai akan yarinyar nan. Za muyi amfani da ita dan ta zame mana zaren ƙulla auren Awwab da Azizat. Kinga cikin sauƙi kema zaki samu cikar burinki”.
“Ban fahimceki ba Rubayya. Ita wannan abar har wacece ita da zata zama zaren cimma burukana? Sai dai burin kore ƙishi”.
“Yamzu kuwa zaki ji. Badai kince yarinyar na shishshige masa ba? Sannan tana shigema uwarsa duk da wahalar da taci a hannunta?”.
“Hakane”.
“Wannan salon nata shine ai makamin namu. Dan dashi zamuyi amfani da ita mu sarƙo wuyan shegen yaron nan mai taurin kai da rashin mutunci. Yanda yake nuna shi mata basa gabansa da ita zamu tabbatar ma duniya munafunci ne.”
“Kinfa san bana son kwana-kwana a zance Rubayya. Fito fili ki faɗa min inda kika nufa dan ni ban fahimci komai ba”.
Dariya sosai Hajiya Rubayya ta saki harda ƙyaƙyƙyewa. Kafin ta ce, “Daɗina dake rashin haƙuri Aminiya. Bari to na kaiki. Fyaɗe zamu saka ya mata na rashin imani. Mu kuma mu dinga masa barazanar yaɗa zancen ta yanda sai ya tsani kansa. A cikin tsakiyar rikicin muyi duk yanda zamuyi ya auri Azizat. Inada tabbacin bazai mana jayayya ba a lokacin dan bashi da wata mafita neman ma wajen tsira yake yi..”
“Humm to idan kuma yarinyar ta samu ciki fa? Ko kuma shi ya ce zai aureta saboda faruwar al'amarin?”.
“Mu dama ai cikin muke buƙatar ma ace ya matan. Dan aikinmu zai fi tafiya dai-dai. Idan kuma yace ma zai auretan mu dai-dai ne. Hakan kuma zai sake ƙarfafa aikinmu.”
“Ta yaya?”.
“Idan yace zai aureta kuma ga ciki ai dole dai zai bari ta haihu. Ku kuma ai ba yarda zakuyi ba matsayin iyaye musamman ma ke. Mu kuma zamuyi amfani da hakan mu zubar da cikin, a wajen zubar da shi zata bar duniyar. Sabon zance zai tashi akan shine ya kasheta, dama zuwa lokacin Azizat na tare da shi. Sai muyi amfani da wannan rikicin da yanayin da zai shiga shi da sauran mutanen gidan naku kema ki samu cikar burinki, fatanmu dai ace lokacin Azizat nada ciki ko ƙarami ne. Amma kidai zauna kiyi tunani. Sai dai fa dole ki rage wasu abubuwan ki sake jawosa jikinki fiye da kowa a gidan nan. Ta yanda idan komai ya ƙwaɓe ke kaɗai zai dinga tunkara ko tattauna damuwarsa. Itama yarinyar haka. Amma ɗan ALLAH ki shanye maitarki a kanta nasanki da ƙananun yara baki da haƙuri”.
Sosai Hajiya Mammah ta sauke ajiyar zuciya. Sai kuma tayi ɗan murmushi da faɗin, “Tabbas shawarar nan taki tayi Rubayya. Sai dai kuma kin san dai akwai matsala. Dan halin Awwab ba ɓoyayye bane akan duk wanda ke mu'amala da gidan nan. Tayaya muke tunanin zai yima yarinyar nan fyaɗe cikin sauƙi yana a hankalinsa. Kai ƙo wata ƙwaya muka bashi bazai yiba kema kin sani tunda mun taɓa gwada hakan. Ni wlhy zuwa yanzu ma gani nake kamar yaron baida isashen lafiyar mazantaka”.
Dariya sosai Hajiya Rubayya ta sheƙe da shi harda ƙyaƙyƙyewa. “Kina bani dariya Aminiyata. To wlhy bari kiji lafiya garas yake. Matsiyacin taurin zuciyane kawai ke ɗawainiya da shi. Kin san fa yaron namiji ne ɗan gaske. Akwai aji da girman kai ga miskilancin jaraba. Ai irinsu koda sha'awar mace zai kashesu wlhy ko'a fuskarsu bazaki taɓa ganewa ba sai idan sune suka so. Tabbas desire tablets bazasu biya mana bukata ba. Wajen mutumina kawai zamuje ya banko masa yasin da manya-manyan aljanuns.....”
“Nifa kin san bana son wannan sabgar Rubayya ko”. Hajiya Mammah ta faɗa cikin katseta da sauri. Baki Hajiya Rubayya ta taɓe da faɗin, “Okay to nikam na barki lafiya. Sai ki nema wata hanyar dan kin san dai wanene wannan yaron. Kuma badan munje inda kike gudunmawa ɗin ba ai da baki samu biyan buƙatar farko akansa ba da waccan shegiyar matar yayan naki”.
Riƙota Hajiya Mammah tai tana bata haƙuri, da ƙyar ta haƙura ta dawo suka cigaba da tattaunawa. Daga ƙarshe suka ɗauki hanyar data zama sanadin alaƙantasu har suka zama aminan juna.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_
.......Bayan fitowarsa ya jima tsaye a ƙofar ɗakin yana kallonta batare da ta sani ba, kamar ɗazun ma sai da ya jima tsaye tun tana bama Ummie abinci batare data sani ba sannan ya shigo. Dan yana fita ta cigaba da karatun Alqur'ani tana tofama Ummie. Wata irin bahaguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da kai yatsarsa babba ta wutsiyar idonsa alamar ɗauke hawaye. Sai kuma ya cije lips ɗinsa da sakin wani mitsitsin murmushi da ba lallai ka fahimci yayi ɗin ba sai in ka kasance mai lura. Juyawa yay a hankali cikin yanayin mutuwar jiki yabi ta hanyar daya shigo. Koda ya shiga sashen nasa kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce. Yay tsaye gaban dressing mirror ɗinsa yana ƙarema kansa kallo kawai. Tamkar abin almara ya dinga ganinta tana masa gizo ta cikin mirror ɗin. Kasa motsawa yayi, sai ma sautin muryarta da amsa kuwwar kalamanta ke maimaita kansu cikin kunnensa tamkar yanzu take zano masa su da mitsitsin bakinta na rashin kunya.
_(“Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”)_
Da ƙarfi ya rumtse idanunsa cikin wani irin yanayi. Sai kuma ya kai hannunsa saman kwantaccen gashin fuskarsa ya shafa, hoton Ummiensa a yau cikin tsafta da cikar kamala na dawo masa. Wata sassanyar ajiyar zuciya ta kufce masa, sake tuno lokacin da take bama Ummie abinci yayi. Sosai tsigar jikinsa ta shiga mimmiƙewa tuna yanda Ummien ke amsa a yanayin buƙata. Kalamanta ne suka shiga sake dawo masa. Da ƙarfi ya kai hannunsa ya harbar da kayan saman mirrorn tare da faɗin, “I hate myself Ummie! I hate myself!!”.
Yanda yay maganar cikin ƙaraji jikinsa har rawa yake yi. Tunda yake ba'a taɓa faɗa masa kalaman da suka tada masa hankali irin na yau ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duk suka miƙe. Tuni idanunsa sun jirkice sun koma golden maimakon blue. Sake dunƙule hannunsa yay ya kaima mirror ɗin naushi. A take ya shiga tsagewa. Sake kai masa naushin yayi. Sai ga jini ta gaba ɗaya bayan yatsun alamar yaji ciwo. Bai damu ba, sai ma hannuwan da ya kai gaba ɗaya saman kansa dake wani kalar mahaukacin sara masa ya dafesa gaba ɗaya, jiyay gaba ɗaya ɗakin na juya masa. (Wannan ba sabon abu bane a garesa. Aduk sanda zai zurfafa tunani ko damuwa da al'amarin mahaifiyarsa ko san ɗaukar mataki akan wani abu da bai masa ba game da ita tofa sai ciwon kai. Sai kuma hankalinsa ya gushe gaba ɗaya. Idan kuma ya farko shike nan ya manta komai bazai sake tunawa ba ko magana ko maida hankali akan wani abinda ya shafeta).
Yanzun ma dai zubewa yay a kan gadon, tare da cure jikinsa waje guda wani kalar masifaffen sanyi na ratsa illahirin ƙasusuwansa, sai zazzaɓi mai masifar zafi da nuƙurƙusar ɓargon jiki....
💥💥💥💥💥
Nutsuwar data samu game da shawarar Hajiya Rubayya ya sata ajiye batun hukunta Samraah. Sai ma zuciyarta data gama tsara mata fara shirinta a yanzu. Zuciyarta fes ta fito falon. Arwa da Muhsin kawai ta samu a falon suna kallo. Sai masu aiki dake ɗan kai kawo na tsaftace sa duk da babu wani datti. Komawa tayi da baya zuwa ɗakin Azizat. Kwance ta sameta da waya a hannu tana charting, sai Bahijja dake cikin closet ɗinta tana maida kayan data watso ƙasa. Batare data kalla uwar tata ba ta ce, “Mammah any problems?”.
Maimakon taji haushin yanda Azizat ɗin tai magana a tsaitsaye sai ma tai murmushi. Cike da kulawa takai zaune a kusa da ita tana shafa kanta. “Babu komai Baby na. Aikenki dai zanyi sashen Yayanku”.
Da sauri Azizat ta ɗago fuskarta da murmushi. Sai kuma ta tura baki tana mai haɗiyewa. “Mammah bayan Yayan ya sake fita shi da tawagarsa. Ina kuma ƙyautata zaton wata tafiyar ma ya sake yi”.
Da mamaki Hajiya Mammah ke kallonta ta ce, “Tafiya kuma? Bayan yau ya dawo?”. Sai kuma ta dauki wayarta ta shiga daddanawa batare data jira amsa ba. Kunnenta ta kai. Batare da yin ko sallama ba ta ce, “Kuna ina?”.
Cikin girmamawa da ga can aka bata amsa da, “Gamu a airport zamu wuce Chaina”.
“What! Shine ba labari?”.
“I'am sorry Maa. Da alama tafiyar gaggawace ta tasoma Boss ne.”
Ƙwafa tayi, tare da yanke kiran. Batare da tace komai ba kuma ta miƙe tai ficewarta. Da kallo Azizat ta bita sai kuma ta taɓe baki itama ta cigaba da charting ɗin ta.....
✨✨✨✨
A ɓangaren Paah shima hankalinsa ba'a kwance yake ba. Dan tun randa abin nan ya faru bai sake saka samun ko kallon arziƙi daga ɗan nasa ba. Ko jiyyar kwanaki uku da yay a gidan idan ya shiga dubasa sai ya ƙirƙiri barcin ƙarya. Yana samun sauƙi kuma ya tattara ya bar musu gidan. Sai yau ne matarsa ke sanar masa Awwab ɗin ya dawo gida. Shine dalilin barowarsa inda yake a gaggauce yazo gidan. Kai tsaye sashen Awwab ɗin ya nufa, amma tun kafin ma ya shiga Hayatu daya samu a compaund ke sanar masa Awwab ɗin na sashen Hajiya Babba.
Sashen Hajiya Babban yaso nufa shima. Sai dai hakan ya gagara saboda shakkar haɗuwar tasu. Dan yasan a rayuwa Awwab bai haɗa al'amarinsa dana mahaifiyarsa da komai ba. Taɓashin da Hajiya ƙarama tayi ne ya sashi dawowa a hayyacinsa firgigit. Cike da mamaki ta ce, “Lafiya kuwa Abban Awwab?”.
Numfashi ya sauke mai ƙarfi, sai kuma cikin damuwa ya amsa mata da, “Ba komai” yana miƙewa. Da sauri ta riƙo hannunsa. “Ya zakace babu komai bayan ga damuwa ƙarara a fuskarka? Nasan dai bazai wuce akan fushin da Awwab yake ba. Ni a ganina mizai hana kaje ka samesa. Sai ka lallashesa dan yaron nan ya fimu gaskiya, shiyyasa kullum nake nusar da kai illar biyema Addah a gidan nan. Dan koba komai Hajiya Babba uwar ƴaƴanka ce”.
Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kuma ya fisge hannunsa batare da ya tanka mata ba yaja tsaki. Fuuu ya fice abinsa batare da ko waiwayenta ba. Da kallo kawai ta bisa itama. Sai kuma ta girgiza kanta ranta duk a dagule....
💕💕💕💕
*_INDIA_*
Kai kawo take kawai tana kuka ita kaɗai a ɗakin, a kallo ɗaya zaka fahimci tana a cikin matsanancin tashin hankali da bai da misali. Kanta ta shiga girgizawa cike da sakin zantukan da suka zame mata sirrinta cikin sambatu. “Kai ina bazai yiwu ba. Bazan halaka yarona da hannuna ba wlhy. Saimah bazai yiwu ba. Na tafka kuskuren farko bazan bari na sake aikata na biyu ba”. Ta ƙare maganar tana rarumar wayarta. Number ƙanwarta Saimah dake Dubai ta shiga lalubowa. Cikin sa'a kuwa ta sameta a sama-sama dan ko a jiya sunyi waya. Kira ta danna mata, sai dai harta fidda rai da za'a ɗauka tana gab da tsinkewa aka ɗaga.
Mamy da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri tamkar zata fito ko sallama bata tsaya yi ba ta ambaci sunan yar uwar tata kai tsaye.
“Saimah!”.
Cike da mamaki da shiga tashin hankali ta amsa mata daga can. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Lafiya kuwa Aunty najiki cikin tashin hankali? Kar dai kice min mun rasa Mansoor ne?”.
Wani irin suka ƙarshen zancen Saimah yayiwa Mamy a zuciya. Dan haka a fusace ta bata amsa da, “Oh haka kuke zaman jiran ji kenan shiyyasa kika saka ƴarki ta kirasa a waya ta tada masa da hankali da yake bata da isashiyar tarbiyya. To bai mutu ba, ba kuma zai mutu a sanadin auren shashashar ɗiyarki ba in sha ALLAHU....”
A fusace Saimah ta ce, “Wace irin magana ce wannan kuma daga tambaya Sadiyya?”.
“Kin fini sani Saimah. Nace kin fini sani. Duk wata masifa kece ummul ana isin sakamu cikinta. Kai haba nagaji bazan iya jurewaba gaskiya. Maganar auren Mansoor da Husnah babu shi tunda baya so”.
Wata shegiyar dariya Saimah ta sanya daga can. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗora da faɗin, “Wannan shine kuskure mafi muni da zakiyi a rayuwarki kuwa Sadiya. Dan in har Mansoor zai ce bazai zauna da Husnah ba to kemafa ki shirya tsaff dan auren shekara talatin da takwas zai guntule shima. Zan sanarma mijinki da ɗanki abinda kika aikata game da auren Mansoor na farko. Na kuma sanarma duniya komai. Ya rage naki yanke hukunci. Kin san kuma shima Maash ɗin ba kanwar lasa bane dan ya tabbatar miki da hakan”. Ɗit-ɗit ta yanke wayarta.
A matuƙar fusace Mamy tai wani irin masifar yin cilli da wayarta. Sai kuma ta zube a saman gadon ɗakin hotel ɗin tana fashewa da kuka mai masifar ƙarfi...
“Mi kike ɓoyewa Halimatu?”.
Firgigit ta juyo tana kallonsa. Sai kuma ta mike zumbur tana goge hawayenta jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya da kaƙaro murmushi take girgiza masa kanta. “Abban Attahir yaushe ka shigo? Dama kana ɗakin nan? Ai ban san kana nan ba wlhy....”
Hannu ya ɗaga mata. Dole tai shiru. Cikin ɓacin rai ya sake maimaita mata tambayar farko. Sake daburcewa tayi. Harshenta na sarƙewa ta ce, “Ba komai. ALLAH ba komai. Ko kaji wani abu ne?”.
Maimakon amsa mata idanunsa kawai ya dasa mata. Sai kuma ya jinjina kansa batare daya sake tanka mata ba ya juya ya fice abinsa. Gaba ɗaya ji Mamy tai ɗakin na juya mata tsabar tashin hankali. Birkicewa ta sake yi tamkar sabon kamun hauka. Itako idan har Abban Attahiru yaji wayar nan tata ta shiga uku. Wannan wace kalar rayuwa ce ta jefa kanta da ɗanta a ciki saboda kwaɗayin abin duniya. Wane irin son zuciya ne? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...
Da ƙyar likitoci suka iya controlling sabon yanayin da Mansoor ya shiga. Dan a baya baya aman jini sam. Gashi yanzu iyayensa sun sake jangwaɓo abinda yafi na farko. Bayan dawowa a hayyacinsa hana kowa akai shiga ganinsa har na tsawon kwanaki uku. Sai da suka tabbatar komai ya dawo normal sannan suka barsu ganinsa bayan anja musu dogon gargaɗi.
Sunji farin cikin samun lafiyar tasa. Sai dai bai kula kowa a cikinsu ba har suka gaji da zama suka fito saboda adadin lokacin da aka basu ya cika. Suna fitowa Dad yay wucewarsa, dan har yanzu babu jituwa tsakaninsa da Mamy. Ya tattarata ya watsar da al'amarin ta. Bai kuma sake mata magana akan komai ba. Itako duk wanda ya kalleta yasan bata a cikin hayyacinta a kwanakin nan. Dan komai ya gama ƙwace mata. Ta rasa ina zata kama danta mafi soyuwa a ranta da mijinta na neman kuɓuce mata a dalilin son zuciyarta........✍️
_Humm Mamy wai mi kika aikata ne haka? Miya kuma alakantaki da Maash??🤔_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC