Showing 3001 words to 6000 words out of 30989 words

Chapter 2 - Ido Hu?u Book One Complete Hausa Novel

ya sumbaci goshinta, cilak ya Wagata ya rungume ta a ?irjinsa sannan ya ci gaba da tafiya.
Findu ta saki wani malalacin murmushi,
Kan tafkeken Gadonsu ya direta ya zame da nufin barin gurin ta yi saurin ?an?ame shi cikin wata shu'umar Murya ta ce "Kasance tare da ni Masoyi!!!."
Salon yadda tai maganar ma kaWai abin a kalla ne ga kowane Namiji bare shi da ya ke jinta tamkar ZUCIYARSA, ya sake zuba mata narkakkun idanunsa ya yin da ta ke ?ara sarrafa Zuciyarsa ta hanyar wani shagaltaccen Murmushi, bakinta ta kai daf da kunnensa kafin ta ce "Ka ke kallona? ba ka taSa g..." rufe bakin nata ya yi ta hanyar Wora na shi a kai, ya Wan tsotsi leSenta ya saki kafin ya ce "Ba na gajiya da kallonki, ba na gajiya da komai naki."
hannunsa ya Wora daidai ?ahon Zuciyarsa kafin ya ce "Ke ce Zuciyar Jayden kuma ke ce ?arfinsa idan babu ke gangar jiki ne kawai, Zuciya itace Rayuwar kowace Halitta, ki Kasance tare da ni har ranar da na bar Duniya Rubainah!!!!!!"





Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632


Ayeesha Abdulkareem
*AA*
[6/22, 8:13 PM] Salmaish Business Center C.E.O: *IDO HU?U*

Free Page
Book 1 Ep 3


*A.A*


ELEGANT ONLINE WRITER'S





Shiru ne ya biyo baya kafin ta Wan ture shi ta na murmushi ta ce "Ba na jin akwai ranar da za ka bar Duniya nima na iya zaman cikinta, Za ka sha ruwa?"
Har lokacin idanunsa su na kanta, sai da ta yi masa tambayar ruwa sannan ya kauda kai gami da murmusawa "Mantawa na ke da komai idan ina kallonki, Yanzu ba na bu?atarsa" ya ?arasa maganar gami da dawo da kallonsa gareta, ta ?yal?yale da dariya hakan ya sa Yarima Jayden murmusawa ganin yau ta na cikin farin ciki ya sa shima ransa yai fes.

Yarima Rooh
kallon Yarima Salah ya ke yi cike da fargaba kafin ya ce "Akhi, Ba zan iya gwada gasa da kai ba domin ba a ja da gwani."
Yarima Salah ya murmusa gami da sa tattausan hannunsa ya shafi gefen kumatun Yarima Rooh, Maganarsa wadda ba kowa ya ke iya zama ya yiwa ba ya fara yi cikin nutsuwar da Allah ya ni'imta shi da ita "Ba kowane ?an Adam Win da na ke rayuwa da shi ne ya san Muryata ba, amma Yarima Rooh kullum cikin saka ni magana ka ke, ba ka tausayina ne?"
Yarima Rooh da ya saki baki ya na kallonsa ya ce "Kai Winnan sai Allah Yarima, akan magana shine zan ji tausayinka? kuma ba ka gajiya a fagen Daga sai a Fagen Magana! Girman kai ya yi muku yawa kai da Abhina shi ya sa ba kwa jituwa, to ni yanzu da ya zan iya gwabza karo da kai? gashi kuma ka ce ba a Keken-Doki zan je ba"
Yarima Salaah ya ce "Da fari ka iya Sarrafa Dokinka sannan ka iya sarrafa Takobinka sannan ka iya Sarrafa Kibiyarka, amma ba za su sarrafu ba har sai ka iya sarrafa Zuciyarka, yanayin gudunta yanayin Gudun Dokinka, yanayin Sarrafatan da ka ke shine Sarrafar Takobinka ko da kuwa a Fagen ya?i ka ke, Yanayin ya?ini da ka sawa Zuciyarka shine Sarrafar Kibiyarka, har ka yi harbi ka samu abin da ka harba, ka gwada yin haka Akhi Rooh."
Yarima Rooh ya yi shiru ya na Nazari kafin ya ce "Zan yi hakan Akhi"
Ya murmusa tare da cewa "Fatan Nasara Akhi Rooh "
sai da ya gama ?ilinbon shi ya shirya sannan su ka nufi cikin dajin tare da Dakarunsu Guda Takwas .
Sun yi ?auki-ba-daWi sosai da Damisar kafin Allah ya bawa Yarima Rooh sa'a ya soke ta a dai-dai ma?ogoronta, kafin ta yi wani yun?uri ya ?ara sukarta a cikinta ta faWi a gurin.
Wani Mugun farin ciki ne ya lulluSe shi ya dako tsalle Zuwa gurin Yarima Salah, jikinsa ya faWa ya na cewa "Akhi ya akai da suka biyu ta faWi??"
Yarima Salaah ya ce "Guba ce a jikin Kibiyarka ko kai aka harba sai Mutuwa, Na tayaka murna Akhi Rooh, yau ka yi abin da ba ka taSa yi ba, na san Ummi za ta ji daWi sosai."
?ara ?an?ame shi ya yi gami da fashewa da kukan farin ciki, ashe akwai ranar da zai iya Harbin wani namun dawa kuma ya faWi?
tambayar da ya yiwa kansa kenan.
Yadda Yarima Rooh ya ke kukan farin ciki sai da ya sa Yarima Salaah sharar ?walla, mi?ewa ya yi ya tsugunna gami da cewa "Hau in goyaka in kaika gurin Umminka."
kamar jira ya ke ya yi saWaf ya haye tare da rungume shi sosai, gaba Waya jinsa ya ke tamkar wani sabon halitta ba Rooh Win da ba.
Kan Doki Waya su ka hau domin komawa cikin Masarauta, ko da su ka isa Yarima Salahuddin ya kuma goya Yarima Rooh sannan su ka nufi Sangaren Ummi.
Sai da ya je gabanta sannan ya dire mata shi gami da cewa ''Ummi! yau Yarimanmu ya kada Damisa."
kasa Soye murmushinta ta yi cikin sauri ta ce " Alhamdulillah! Ma sha Allah! ni dama nasan ban haifi Ragon Namiji ba, Roohullah gaya min me ka ke so in yi maka?"
Matsawa ya yi jikinta ya lafe sannan ya ce "Ummi ba na son komai wanda ya wuce sa Albarkarki, amma ina so ki gaya min kin yi farin ciki, ni kuma na yi miki Al?awarin zan ?ara ninka ?o?arina akan na yanzu."
Maida kallonta ta yi kan Yarima Salaah ta na murmushi, shi ma ya yi murmushin gami da yi mata alamar ro?o.
Hannu ta Wora akansa kafin ta ce ''Na yi farin ciki sosai Rooh."
lallausan murmushi ne ya suSuce masa, daidai lokacin Sarki Abraham ya yi sallama, Yarima Salaah ya yi saurin zamewa daga kan Kujerar da ya ke zaune ya sunkuyar da kai gami da cewa "Wa'alaikassalam Abhi!."
Kamar yadda Yarima Salaah ya yi haka Bayin da ke gurin su ka yi, Yarima Rooh ya yi saurin gyara zamansa kamar yadda ?an uwansa ya yi.
Cikin takunsa irin na Toron Giwa ya ?araso wajen ya zauna Kan Kujeru na Alfarma da ke kewaye da su.
Ummi ta ce "Salamu'alaik !" ya jinjina kai kafin ya ce "Rooohh! na samu labarin ka je Farauta kuma ka yi Nasara farin ciki ya sa na zo gareka"
da sauri ya mi?e ya ?arasa kusa da Sarki Abraham, hannunsa ya ri?o kafin ya ce "Akhi Salahuddin shine Sirrin Nasarata Abhi."
Kallon-Kallo Sarki Abraham da Yarima Salaah su ka yi, Sarki Abraham ya maida kallonsa kan Yarima Rooh, ''Ina so ka cire hakan a ranka, ka Wauka ko da Babu Yarima Salaah za ka yi Nasara domin kai me Nasara ne Nasara a jininka ta ke, Yarima Salaah ka yi ?o?ari"
ya ?arasa maganar gami da satar kallon Yarima Salaah.
Murmusawa ya yi kafin ya ce "Ban yi ?o?arin da za ka yaba ba ZAKI, Sarauniya Dama ina son yin magana akan Sa?on Gaiyata da Masarautarmu za ta tura wa wata, ni ban Amince da hakan ba."
ya yi maganar ya na Kallon Sarauniya kamar da ita ya ke maganar.
Ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba.
Sarki Abraham ya gyara Zamansa ya Wan kashingiWa kafin ya kalli Ummi ya na Wan murmushin da bai wuce kan laSSa ba, "Sarauniya Ki gayawa ?anki cewa hakan ba wai kuskure bane, shi zaman mutunci Alkairi ne ga kowa , ko kuma ki tambayar min shi dalilinsa na faWen haka.
Yarima Salaah ya mi?e ya koma kan kujera ya zauna sannan ya ce "Ina son Babana ya faWa min tashi hujjar ta Gaiyatar Masarautar can, in ba haka ba ya gaggauta ?ona wasi?ar sannan ya cire sa rai akanta, Ni ne da Alhakin saita Kambun Masarautarmu kar a aikata ba tare da an Wauki Shawarata ba."
ya na kaiwa nan ya mi?e yabar wajen.
Sarki Abraham ya raka shi da ido cike da mamaki da takaicin halin Wan nashi na nuna masa iko da ?in bin ra'ayinsa.
Sarauniya ta ce "Sai ha?uri halin Yarima Sarki Abraham!, amma ina ganin ya fi kyau idan ba za ka bi ra'ayinsa ba to kar ka ce sai ya bi naka, kowa ya yi nashi hakan zai fi."
bai yi magana ba ya mi?e hannunsa ri?e da na Yarima Rooh wanda takaicin MurWiyar Yayan nasa ya hana shi cewa komai.

A hanyarsu ta komawa Sashin Mai Martaba Yarima Rooh ya ce "Abhi! kenan yanzu ka ha?ura da aikata abin da ranka ya ke so?"
Sarki Abraham ya murmusa kafin ya ce "Ba yadda na iya da Yarima domin kuwa yanzu ya na jin ?arfinsa ya kawo har ya wuce nawa, dole zan bishi sau da ?afa domin kuwa shine ?usar Ya?ina, Mahaifiyarku itace ta ke tunzura shi ya ke min abin da ya ga dama, amma ba komai lokaci ne."
Sosai haushin Ummi da Yarima Salaah ya cika Zuciyar Yarima Rooh taff, a Duniya duk wata soyayya da sha?uwa da zai yi da wani to a bayan Mahaifinsa ne, shi kaWai yafi ?auna fiye da kowa kuma zai iya ha?ura da kowa akan Mahaifinsa, duk abin da Sarki Abraham ya faWa masa yarda ya ke kuma ya sa a ransa shi ne daidai, yawan faWen aibun Yarima Salaah da kushe shi Win da Sarkin ya ke a gaban Yarima Roooh yau da gobe ya sa ya fara jin haushin shi har Ummin tasu wadda a cewar Sarki itace ta ke zuga Yarima sannan kuma ta ke nunawa Yarima Rooh tsana.
Cikin su Biyun kowa da tunanin da ya ke yi.

Masarautar Moomin.
Gimbiya Zaina ce zaune gefen Sarauniya Ameena, Magana suke akan shirinta na tafiya Masarautar Munwaz, Sarauniya Ameena ta na cike da fargaba domin kuwa abin firgici ne shigar Gimbiyarsu wannan Masarautar.
Gimbiya Zaina ta ce "Na riga na yi wa kaina Al?awarin zuwa koda abin da na ke so ba zan same shi ba."
"Amma a Nazarina ina ganin ki fara aika sa?o zuwa Masarautar kafin shigarki, hakan zai temaka mana wajen gane halin da Masarautar ta ke da shi da kuma irin zafin kansu akan Muslimci, ta hakanne za ki fi jin daWin shiga ta sigar da komai zai tafi dai-dai.
Gimbiya ta Wan numfasa kafin ta ce "Sai in ce zan zo kenan?"
Sarauniya Ameena ta murmusa cike da manyance ta ce "Abin da za ki rubuta daban abin da za ki aikata daban, ki ?ir?iri wani abin daban ki rubuta."
Gimbiya ta ce "Na amince da hakan, zan tura sa?on a yau."
murmushi kawai Sarauniya Ameena ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Gimbiya ta tashi ta fice, turakarta ta koma ta nemi guri ta zauna ta zuba tagumi.
Ta Webi lokaci a hakan kafin ta tashi ta Wakko abin rubutu ta fara rubuta wasi?ar, bayan ta kammala Ta fito zuwa wajen Masarauta don bayarwa me isar da sa?o.

Cikin kwana Ukun hankalinta sam ba'a kwance ya ke ba, ko da yaushe tunaninta ?an aikenta ya dawo lafiya sannan wace irin amsa za ta samu daga Masarautar Munwaz.

Masarautar Munwaaz.
Cikin nutsuwa ya shiga turakarsa kamar daga sama ya ji Muryar Rubaina ta na cewa "Daga......

Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632
__________________________

*SALMAISH* Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN 500 MB 150. 1GB 280.
2GB 550. 3GB 840
4GB 1,100. 5GB 1,380

AIRTEL 500 MB 160.
1GB 290. 2GB 580.
3GB 870. 4GB 1,150
5GB 1,450

GLO. 500MB 170
1GB 300. 2GB 600
3GB 900. 4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE. 500 MB 130
1GB 250. 2GB 500
3GB 750. 4GB 1,000
5GB 1,250
........................................
Account No: 8067123232

Account Name: Halima Ukashatu Abdullahi

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09079885632
____________________________

Ayeesha Abdulkareem
*A.A*
[6/22, 8:13 PM] Salmaish Business Center C.E.O: *IDO HU?U*

Free Page
Book 1 Episode 4


*A.A*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




"Daga ina kake??"
cakk ya tsaya don kuwa daga jin muryarta cikin Sacin rai take.
Shiru ya yi har ta ?araso gabansa ta tsaye ta na fuskantarsa, cike da ba?in Kishi ta ce "Ba ka ji ba??"
"Daga gurin Bauta nake wajen Gunki Gurmus" ya faWa gami da jefa narkakkun idanunsa a cikin nata.
juya masa baya ta yi kafin ta ce "Wacece Zaina???"
"Zaina??" ya maimaita tare da ?urawa dogon gashin da ta juyo masa ido.
juyowa ta yi a fusace ta ce "Ka na nufin ba ka san ta ba??, ya akai har ta turo maka Wasi?a? kuma ita Win Musulma ce."
?ar Dariya ya yi tare da girmama Mugun Kishi irin na Rubaina, Ya juye duka idanunsa akanta kafin ya ri?o hannunta cikin tattausar murya ya ce " Kin fi kowa sanin waye Mijinki akan Musulmi, ke ce wadda za ki bada labarina domin kin fi kowa sanin ba na haWa Ala?a da Muslimci ko Musulmi."
"Na sani" ta faWa gami da mi?o masa Wasi?ar.
ba dalili kawai sai ya tsinci Zuciyarsa da bugawa ta na raya masa fargabar buWe Wasi?ar a take ya shiga takokin abin da zai gani a cikinta.
Muryar Rubaina ce ta katse masa tunanin "Jayden! ba ka san ta ba ya akai ta kira ka Masoyinta?? kasancewar ba ka kusa shi yasa na karSa na karanta ta a Fada domin kowa ya ji, kuma Sarki ya na nemanka"
cikin sauri ya ware ta ya fara karantawa
"Assalamu alaikum, Masoyina Jayden, Gimbiya Zaina Masoyiyarka ke nema maka Aminci daga Allah, Na san ko ba ka fusata ba za'a sa ka fusata, to ka kwantar da hankalinka ni ba da faWa ko tashin hankali na zo maka ba, Ina gaiyatarka zuwa Shagalin da zai gudana a wata me kamawa a Masarautar Moomin ka daure ka zo ka ci Abinci tare da ni. ZAINA"
Dam?e Takardar ya yi gami da Zubawa Rubaina ido don jin abin da za ta ce, ita kuwa ta yi masa banza hakan ya sa ya ce "Rubai Kin sani ba zan iya aikata hakan ba ko dan kaina bare ina da ke."
Murmusawa ta yi sannan ta ce "Na san haka Jayden amma ka faWa min wane martani za ka bata??"
Nazari ya Wan yi kafin ya ce "Zan gaya mata cewa ba ta isa ba."
ba haka Rubaina ta so ji ba amma sai ta murmusa ta ce "Ka je gurin Mahaifinka"
ba tare da ya yi magana ba ya fita daga sashin.
Murmushi me cike da manyan manufofi Rubaina ta saki a baiyane ta ce "Tabbas zan sa ka yi wa wannan Gimbiyar abin da ko sunanka ba za ta so ta ji an ambata ba.

Yarima Salah
shi kaWai ne a wani keSaSSen Sashi da aka ware dominsa, Takobi ce a hannunsa ya na wasa da ita don kuwa ba ya ?aunar zama kawai.
"Salamu alaika Yarima Salaah"
Bai ko motsa da sunan ya ji anyi magana ba ya ci gaba da abin da ya ke yi, ya Wan Wauki lokaci me tsayi sannan ya yi magana, ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce "Wa'alaikissalam Fateemah"
Murmushi ta yi gami da cewa "Assalamu alaik" "Wa'alaikissalam" ya ?ara amsa mata gami da soke Takobin a cikin Kubenta ya Wora fararen idanunsa akanta.
murmushi me sauti take yi kanta a ?asa, a Wan diririce ta ce "Idan ka na kallona ne duk rasa abin da zance na ke yi."
Kauda kai ya yi cikin ko'in kula ya ce "Hakan na nufin Aiken Sarki ne ba na Sarauniya ba."
cikin sauri ta ce "Haka ne Yarima ya ce ka sameshi."
"A sanar dashi yanzu ina da abin yi." zaro idanu ta yi ta ce "Ba zan iya faWe ba, na san kai za ka iya yafe min amma shi kam tsire ni zaiyi da raina."
Ido ya zuba mata kafin ya murmusa ya ce "Ki zo ki tayani hira da daddare, a cewa Sarki zan zo." "Ni kuma Yarima?? yau nice zan tayaka hira?? ba laifi na yi ba kuwa??"
da hannu ya yi mata alamar ta fice ta bashi guri, ta juya cike da farin ciki da murna, bayan ta isar da Sa?on ta wuce wajen Sarauniya ta zaiyana mata abin da Yariman ya ce. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce ?ala ba.

Masarautar Moomin
Noor Salma ce zaune gaban Ummu Noor cike da damuwa ta ce "Ummi Gimbiya Zaina fa ta na son barin Masarauta ta tafi Munwaz."
Ummu Noor ta ce "Na kamu da jin tsoro sosai domin idan mu ka rasa ta mun rasa dukkan wata kima ta Masarautar nan."
"Hankalina bai kwanta da tafiyarta ita kaWai ba, shi yasa na yanke hukuncin zan bita don temaka mata ta wasu Sangaren.
cikin alamar razana Abu Noor ya juyo ya na kallonta kafin ye ce "Noor Salma shin me ya shiga tunaninki ne? Idan an rasa Gimbiya Zaina an rasa ki ai an rasa goben Masarautar Moomin."
"Ba abin da zai faru Abu Noor, in sha Allah lafiya za mu dawo, kuma idan ba ma nan ma akwai Yarima Rayan.
"Ki dena lissafawa dashi, da Gimbiya Zaina ake ta?ama a Masarautar nan, mu kuma kece Duniyarmu kece komai namu, rashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login