Showing 21001 words to 24000 words out of 30989 words

Chapter 8 - Ido Hu?u Book One Complete Hausa Novel

ta rabo da magana, duka su Biyun ganinsa a ruWe ya matu?ar tashi hankalinsu sai dai duk sun kasa nuna alamar a zahiri, Sarauniya Sadiyya Manyance ne ya hanata nuna razanarta, Fateema kuwa tsoron ta yi gargajiga akansa ta ke yi har Mahaifiyarsa ta iya fahimtar sirrin Zuciyarta.
"Fateema kawo min ruwan sha" ya yi maganar Murya ?asa-?asa, cikin sauri ta tashi don aiwatar da abin da ya faWa, Sarauniya Sadiyya ta ce "Yarima ba lafiya ba, me ke faruwa?" rausayar da kai ya yi kafin ya ce "Ummi bansan me Abhi ya ke yi da ?a?an Mutane ba, ko shakka babu yanzu Zuciyata ta gazgata zargin da ta ke yi, shine ya ke Kwashe ?an Matar ?asar nan, ban san me su ka tare masa ba." Mutuwar Zaune Sarauniya ta yi, ta tsira masa idanu Zuciyarta na tsalle, tabbas da ya faWa itama ta gazgata domin kuwa zargin da ta ke yi kenan itama, "Salahuddin Bansan wace irin rayuwa Mahaifinka ya Weba mana ba, sai shuka mana bala'i ya ke yi wanda nasan Alhakin har ku ?a?anmu sai ya bibiya, tabbas in wani abu ya sameka ba zan iya yafe masa ba." Shiru ya yi ya na nazarin ta ya akai ma ya yi wannan suSutar bakin, dan dai kawai tunanin abin ya addabe shi ne amma bai so faWa mata ba don yasan sai ta fishi tada hankalinta, murmushi ya yi cikin son kawarda zancen ya ce "Zargi fa kawai na ke yi ban gama tabbatarwa ba, kawai abin ya na bani mamaki ne, amma kar ki damu Allah zai warware, Ya labarin Auren da zai min ya samo min Abokiyar haWin ko kuwa??" ya ?arashe maganar ya na ?ar dariya ta ?arfin hali "Wai ya ce ya aika Masarautu biyu ba sakamako me kyau, duk sun ?i Amincewa" ta ?arasa maganar ta na gyatsine baki, dariya ma abin ya bashi don haka ya dara sannan ya ce "Duk da irin girma da Arzi?in da ya ke jin ya na dashi ya akai su ka ?i tayinsa cikin sau?i haka?" Ta taSe baki kafin ta ce "Abin da ba a gina da gaskiya ba kai kuwa ai ba ya tasiri, ni ina tsoron ma ya je ya yo mana Mugun HaWi a wata Masarautar." "Ki kwantar da hankalinki Ummina ya gama zagayen da lalube-laluben duk Masarautar da ya je ba za su taSa Amincewa ba, sabi da ni na riga na yi Mafarkin suffar wadda zai Aura min" Murmushi ta yi gami da cewa "Amma na ji daWin hakan, Kyakkyawa ce??" sai a lokacin Fateema ta dawo hannunta Wauke da ruwan, salalo salalo ta ke tafiya don kuwa damuwa ta kusa nakastata, Girgiza kai ya yi kafin ya ce "Ba Suffar Fuskarta na ke nufi ba, Kawai dai abin da na iya sani shine Wadda tunaninsa ya ke kaiwa ba ita bace, shi ya na harin Dukiyar Mutane ne, ita kuma Talaka ce ba kowa bace, sannan ?as?antacciya ce a Gurinsa, ba ta da Darajar komai, kuma a cikin Masarautar nan take" kwantsam!!!! Fateema ta jefar da Ruwan da ta kawo masa, gaba Waya ta buWe idanunta wanwar akansa jikinta har tsuma ya ke yi, "Wacece?????" Zuciyarta ce ta ke tambayarta, shima Yarima Salah yadda ta zazzaro masa ido haka ya zare mata nasa Fararen idanun cike da mamakin abin da ya sa ta burkice haka, Sarauniya kuwa idan ta kalli Yariman nata sai ta koma ta Kalli Fateema, yadda su ke wani ShaWanannen Kallo wa juna ya sa ta sakin Murmushi


Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632
______________________________________

*SALMAISH* Special DATA


*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN 500 MB 150. 1GB 280.
2GB 550. 3GB 840
4GB 1,100. 5GB 1,380

AIRTEL 500 MB 160.
1GB 290. 2GB 580.
3GB 870. 4GB 1,150
5GB 1,450

GLO. 500MB 170
1GB 300. 2GB 600
3GB 900. 4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE. 500 MB 130
1GB 250. 2GB 500
3GB 750. 4GB 1,000
5GB 1,250
........................................
Account No: 8067123232

Account Name: Halima Ukashatu Abdullahi

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09079885632
___________________________________

_Akwai ingantaccan maganin
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_





Ayeesha Abdulkareem
INDO
[6/22, 8:13 PM] Salmaish Business Center C.E.O: *IDO HU?U*

Free Page
Book 1 Ep 12
Shafi na Goma Shabiyu


*A.A (INDO CE..)*


ELEGANT ONLINE WRITER'S


*(An fara Payment, Ku yi sauri ku lallaSo ku biyoni ta wannan Number=?I??s? Mutum Goma 10 Masu Payment na Farko akwai Rahusa da GaraSasa gareku, Kar ku kasance na 11 Lokacin Rahusa ta tsare @&, sai na ji ku, INDO CE=??)*





Sannan ta ce "Yarima! Fateema! Ina Fatan Lafiya." Cikin sauri ya sunkuyar da kai gami da cewa "Ba komai!" Fateema kuwa cikin Rawar baki ta ce "Zazz.. zamewa nayi shine sai ruwan ya faWi." Sarauniya ta murmusa gami da cewa "Za ki iya kawo wani??" cikin sauri ta gyaWa kai gami da juyawa za ta koma Yarima ya tsayar da ita da cewa "Fateema Ki barshi kawai naga kamar ba ki da lafiya, tafi ki kwanta ki huta." Da kai ta amsa sannan ta kaWawa Bujenta iska, jiki na tsuma har neman yin tuntuSe ta ke yi. Ya furzar da huci kafin ya ce "Rawan kanta ya yi yawa Yarinyar nan." Murmushin Yaro ba Mutum ba sai ya girma ta yi masa kafin ta ce "Kai ma ka na Bu?atar hutawa ka je ka huta." ta na rufe baki ya mi?e gami da cewa "To Ummi" shima dama jiran kaWan yake, cikin sauri ya bar sashin Ummi a memakon ya nufi ?angarensa sai ya yi ?angaren Hadimai ko zai ga Fateema, cikin sa'a tin kafin ya ?arasa ya ganta a hanya ta raguSe a jikin bango ta yi lamo! ita ba kuka ba ita ba Bacci ba ita ba Ido biyu ba, "Salamu Alaiki Fateema!" ya faWa gami da zuba mata idanu. cikin sauri ta Wago tare da wani sassanyan murmushi murya a cunkushe ta amsa da cewa "Walaikassalam!" Ya murmusa gami da cewa "Meke damunki cikin kwana biyun nan? ko akwai abin da ya faru ban sani ba?" girgiza kai ta yi ta ce "A'a Ranka-yadaWe ba abin da ya faru, bansan me yasa ba kawai fargaba nake ji a koda yaushe, Don Allah ka koma kar a ganmu tare" "Akwai wanda aka bawa kiwona ne?? ki ?yalesu ki yi abin da ya shafeki, ki ri?e Addu'a ki dena sanya tunane tunane a Zuciyarki. ta gyaWa kai alamar ta gamsu, shiru ne ya biyo baya sai aikin kallonta ya ke yi ita kuwa ta yi ?asa da kai, kwarjinin da yake mata tin da ne ya dawo yau don kuwa tin da ya fara janta a jiki ta manta matsayinta gareshi, sai yanzu da Zuciya ba ta da ?ashi ta ke raya mata wani abu mara yuwuwa akansa. jin Shirun ta yi yawa ya sa shi cewa "Idan Anyi Magrib ki sameni a Turakata, na samu wani labari da ya shafi Abhina, za mu tattauna akai" ta gyaWa kai gami da raka shi da ido har ya Sacewa ganinta. Sassanyar ajiyar Zuciya ta sauke a ranta ta na aiyana Allah i sa itace wannan ?as?antacciyar da ya gani a mafarkinsa.

Fiddha sai haki ta ke ta na tafiya ta na harWewa sai Wuridin Zuci ta ke yi, ta nufi Fadar Sarki Abraham, ta na zuwa ta kwashi Gaisuwa ya amsa sannan ya bata damar ta yi magana don ya ga bakinta sai motsi ya ke yi, kuma ya san Bincike ya sa ta. ta gyara bakinta kafin ta ce "Ai Ranka-yadaWe ko shakka babu ?auna ce a tsakanin Yarima da wannan Hadimar Fateema, don kuwa tin da ka sa ni bincike akai na ke ankara da haWuwarsu ko yau ma haka, kuma yanzun ma ya ce ta same shi a Turakarsa, Allah i sa ma Alkairi za su tufka a Turakar, kuma nakanji su na yawan magana akanku Ranka-yadaWe ba na shakka akan cewa shirinsu akanka ba Alkairi bane" Sarki Abraham ya murmusa Kafin ya kalli Waziri ya ce "Ka ji Abin da Yarima Rooh ya faWa gaskiya ne, sai mu san Matakin ?auka, kuma Fiddha anyi ?o?ari sosai don haka za a samu Tukuici, amma yanzu a ?ara bibiyarsu don ?ara tabbatarwa." cike da farin ciki ta yi godiya ta tashi ranta fess,
Waziri ya ce "Lallai Yaro, a koda yaushe girma ya ke yi ya na ?ara ganin damarmu, yanzu har ji yake zai iya ja damu??" Sarki Abraham ya ce "Hmm ka barshi kawai, ko farcena bai isa ya taSa ba." "To wai Ranka-yadaWe na ce tinda mun yi aike Masarautu sun ?i yarda kuma Allah ya sa mu ka samu ya na son wannan Baiwar me zai hana mu Aura masa ita??" Waziri ya faWa cikin ?asa-?asa da murya, tsabar gulma har wani ran?wafawa ya ke yi, Sarki Abraham ya ce ''Za mu ?ara bincikawa wasu Masarautun, abin da na ke so ka fahimta shine, Ba za mu taSa yarda mu Aura masa wadda ya ke so ko wadda ta ke son shi ba, ina fatan an gane?" Waziri ya ce "?warai kuwa ai ana faWa na Fahimta, hakan za a yi, bari a dawo da sa?on wannan Masarautar ta ?arshe idan ba su Amince ba sai mu sake shiri." Sarki Abraham ya jinjina kai sannan su ka ci gaba da tattaunawa.

Moomin
Salma
Ta daWe a kwance ta na malelekuwa sannan Magenta ta fito daga cikin Dajin, itama ta mugun sha wahala ta na zuwa ta kwanta ta na hutawa.
Sai da su ka yi bacci sosai a gurin kafin Kyanwar ta farka ta hau kan Noor ta na ?o?arin tashinta, a hankali ta buWe idanunta wanda su kai wani mugun nauyi ta zuba akan Kyanwar tata, farin ciki ne ya lulluSe ta da ta ga Magen don kuwa a tunaninta ma Dajin ya cinyeta. tashi ta yi ta zauna ta kwanto jakarta ta bayanta ta Wakko ruwa ta sha sannan ta Bawa Kyanwarta su ka tashi su ka ci gaba da tafiya don komawa Cikin Masarauta, kasancewa ba cikakkiyar Lafiya gareta ba ya sa ba ta iya sauri a hankali ta ke tafiya har Allah ya maidasu gida lafiya.

Akhi Usman ya na zaune ya zuba tagumi ya na jiran dawowarta, Ummu Noor kuwa ta shiga cikin gidan Don aiwatar da aiyukanta da ta ke yi ana basu Wan Abinci ko kuWi. Ko Sallama ba ta iya yi ba ta na shigowa ta zauna jikinta duk a mace. Cikin sarewa Akhi Usman ya ce "Noor ya na ganki haka? me ya faru??" lumshe ido ta yi sannan ta ce "Daji ya kusa cinye ni yau, wata Murya na ji ana ta kirana, ba don Siha (Magenta) ta hanani amsawa ba da na amsa, Allah ne kawai ya fito damu lafiya daga cikin Dajin nan don kuwa ba a hayyacina na fito ba, sai da mu ka yi bacci a gurin ma sannan mu ka iya tashi mu ka yo gida." "Allah ya temaka ai da kin amsa Allah ne kaWai ya san abin da zai faru, Allah ya ?ara kiyayewa, amma kar ki ?ara komawa Dajin nan, mu ha?ura zuwa nan gaba ai tinda Ummu Noor ta na aikatau za mu samu mu tara Dukiyar har mu Bawa Jakadiya idan kuma ba haka ba sai dai mu ha?ura don ba na son abin da zai taSa lafiyarki" "Hmm!! ba zan taSa ha?ura ba har sai in numfashina ya ?are, kuma da iya abin da Ummu Noor ta ke tarawa ba za mu iya tara Dukiyar bawa Jakadiya Gameela ba, Ka bar komai a hannuna Abu Noor ni zan samo kuWin, amma ba'a Dajin ba, bari in samu jikina ya yi ?wari.
"To a ina za ki samo??" "A cikin Dukiyar Masarautar nan zan samu, abin da mun san inda su ke ajiye Dukiyar? kuma sai mu zuba ido mu na gani ba za mu taSa ba?"
Akhi Usman ya murmusa gami da cewa "Kin yi tunani me kyau, amma ki taka a hankali kar su kama ki." ta gyaWa kai sannan ta mi?e ta nufi Gurin wanka don rage ?asar da ta ke jikinta.

A Sangaren Sarauniya Ameena da Gimbiya Zaina, shirin Fitar Gimbiya daga Masarautar shi su ka kama kan jiki kan ?arfi.
a Sangaren Sarki Zunnur ma ya gama haWawa Sarakuna da ?a?ansu shagali ?awatacce, yanzu rakanu kaWan su ka rage Shagali ya gudana, a cikin Sarakunan Nasa Tawagar ?ayansu har ta sauka a Masarautar Moomin.

Washegari
Salma Allah ya kawo mata sau?i ta samu lafiya tangaran sai dai akwai kakkarcewa a jikinta da ?an ciwuka, wunin Ranar ta ?are shi a ?angaren da Sarauniya Hakima ta ke Ajiye Kadarorinta Irin su KuWi Dun?ulallun Gwal Azurfa Sar?o?i da Zobuka da sauran abubuwa iri-iri, Binciken ta yadda za ta sata ba tare da kowa ya sani ba ta ke yi, kuma ta kammala lafiya ba tare da rashin sa'a ba.

Misalin ?arfe 03:00 Na dare ta tashi, ta Waure Fuskarta kamar yadda ta saba sai iya idanunta ake iya gani, ko takalmi ba ta sa ba ta Wauki Fankon jakarta ta fata bayan ta zare tarkacen ciki sannan ta nufi sashin
SaWaf-saWaf da ta ji alamun motsi ko ba na mutum ba sai ta yi sauri ta Suya, kasancewar ta saba Sata ba ta sha Wahalar shiga ba, Mutum ?aya ne su ka yi IDO HU?U da shi wanda bai yi bacci ba ya na aikinsa na gadi, shima da salon yaudararta ta yaudare shi ta sille, Kasancewarta Kyakkyawa ko iya ?wayoyin idanunta ma Namiji zai iya shagala gurin kallonsu, sai da ta yi masa Al?awarin gobe za ta dawo su shuka tsiyarsu shi da ita kuma shi ma ba zai faWawa kowa ba sannan su ka lamunce wa juna ta wuce.
Ba ta Sata lokaci ba Ta ta?e Jakarta mankass sannan ta fice, Mutumin nata ya bita don yi mata magana ta samu wani Icce ta sambaWa masa ya baje a gurin ita kuma ta ci gaba da tafiya.
Akhi Usman Da Ummu Noor sun yi matu?ar farin ciki da Samun Nasarar Satar da ta yi.
Washegari tin Asbahi ta fice daga Masarautar domin haWuwa da ?an Kasuwar da ta ke Fansarwa abin da ta samu ko Halak ?inta wanda ta ke nema a Daji ko na Sata.

Zuwa Azhar ta dawo cikin Masarauta tare da Dun?ulalliyar Dukiya wadda ba ta yi kama da ta Masarautar ba bare ma ayi zarginta, Ta na dawowa Akhi Usman ya Warewa Jakadiya Gameela tata sannan ya nufi inda su ke haWuwa.
Bai dawo ba sai da su ka gama magana kaf.

Gobe ne Taron Sarki Zunnur ya kama, gabaki ?aya Sarakuna da Iyalinsu sun baiyana, Moomin ta san ta yi ba?i don kuwa ko'ina hada-hada ake yi ba kama hannun Yaro Masu girki na yi masu Tsara biki na yi, Masu abin kuwa Shagalinsu kawai su ke yi.

Tin Farkon dare kafin ya yi nisa
Gimbiya Zaina ta shirya tafiya
goge hawayenta ta yi kafin ta ce "Karki damu Ummi zan dawo in sha Allahu." Sarauniya Ameena ta ja numfashi kafin ta fara binta da Addu'o'i, da haka su ka yi sallama Gimbiya zaina ta Waure fuskarta sai iya idanunta ne a waje sannan ta fice.
Kasancewar a yamutse Masarautar take ya sa ba ta sha wahalar fita ba don kuwa ba ruwan kowa da kowa, kowa harkar gabansa ya ke yi.
a bayan gari ta haWu da Jakadiya Gameela da Wakilin Kiwo tare da Dan?areren ?oshashshen Doki wanda za ta hau.
ba ta jira komai ba su ka yi sallama ta karSi guzurin da su ka haWa mata ta yi gaba.

Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632
_____________________________________

*SALMAISH* Special DATA


*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login