Showing 6001 words to 9000 words out of 30989 words

Chapter 3 - Ido Hu?u Book One Complete Hausa Novel

ke kaWai tamkar rashin Mutum uku ne domin mu ma amfaninmu ya ?are, kuma kin sani shigar ku tare cikin yankinsu zai fi sau?i a wajen gano ku, amma idan ita kaWai ce ba kowa ne zai fahimta ba.
Ummu Noor ta ce ''Haka ne Zancensa Noor, lallai kar ki yi gardama garemu, ki yi ha?uri ki barta ta tafi ita kaWai, ki tuna fa mu ma mu na da abin da mu ka sa gaba kuma mu na so mu ga mun yi Nasara."
shiru ta yi tana nazari kafin ta ce "Shi kenan, zan ci gaba da ?o?ari wajen cika muku burinku, amma fa kar ku dinga manta cewa Gimbiya Zaina ba ta san komai ba kar mu saka ta a ciki."
Abu Noor ya ce "Wannan haka ya ke, yanzu ki fita ki gano mana me ake aikatawa a gari."
Da kai ta amsa cikin girmamawa sannan ta mi?e tabar sashin nasu.
Abu Noor ya yi murmushi gami da cewa "Ina matu?ar son ganin ranar cikar burina."
Ummu Noor ta ce "Nakan ji a jikina kamar lokacin ya zo." ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.

Munwaz
a Fadar Sarki Zamwal kowa ya yi shiru ya na sauraren hukuncin da Yarima Jayden zai yanke akan Gimbiya Zaina.
Banda rarraba idanu ba abin da Wan aikenta nata ya ke yi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? don kuwa ya lura dukkansu kallon ?iyayya su ke yi masa.
Yarima Jayden ya umarci a kawo masa Abin rubutu, bayan an kawo ya shiga rubuta mata amsar da ta dace da ita, sai da ya kammala ya bayar aka haWa wa ?an aiken nata ya na shirin tafiya sannan Gimbiya Rubaina ta taso.
daidai shi ta tsaya fuskarta sharkaf da hawayen Makirci, cikin nuna zallar Sacin rai ta ce "Ni dama nasan ka santa, in ba don hakan ba iya rubutu kawai zakai mata a matsayin martani?, a ganinka ba ta cancanci Kisa bane? shin Ya?ar Masarautarta zai yi maka wahala ne?? kullum fa gaya min ka ke ba za ka taSa saurarar wata mace ba bayan ni ashe duk ba haka bane?"
tin da ta fara magana ya zuba mata idanu har ta kammala, maganganunta sun bugi Zuciyarsa lokaci guda ya ?ara jin tsanar Gimbiya Zaina wadda ya ke ganin kamar ta yi hakan ne don ta tarwatsa masa farin ciki, hannu ya kai zai dafa kafaWarta ta yi saurin zillewa, ta na kallon gefe ta ce "Ba na so ka taSa ni, yanzu na san amsar tambayata, ban taSa zaton kana yi min ?arya ba Jayden." ta ?arasa maganar cikin shashshekar kuka. Mugun Sacin rai ne ya dabai-bayeshi jikinsa har rawa ya ke, cikin zafin nama ya zare Takobinsa ya sauketa da ?arfi akan Wuyan ?an Aiken Gimbiya Zaina, fit ya cire masa kai, sannan ya bada umarnin a ?one gangar jikinsa kan nasa kuma a haWa mata da shi akai mata. ya na kaiwa nan ya fice daga Fadar gaba Waya.
Gimbiya Rubaina ta saki wani Shu'umin murmushi cikin Zuciyarta ta ce "Aikinka ya na kyau Mijina, na yiwa kaina Al?awarin sai na Sata mata rai kuma burina ya cika; Mijina nawa ne ni kaWai."
da tsantsar farin ciki ta bi bayansa domin rarrashinsa.
Sarki Zamwal ya yi dariya kafin ya ce "Shi yasa na bar masa komai a hannunsa domin ya iya zubda jini." ya ?arasa maganar yana dariya idanunsa akan Findu. Murmushi me cike da ma'anoni Findu ta yi, har ?asan ranta ta na mugun jin daWin gadon ubansa da Wan nata ya yi, dukansu basu Wauki ran wani a bakin komai ba.

Yarima Salaah
bayan ya kammala duk abin da zai yi ya fito cikin shirinsa tsaff sannan ya nufi sashin Sarki.
Ya na turakarsa ya kasa zaune ya kasa tsaye don kuwa ko ya zauna sai ya mi?e a tsayen kuma sai ya ji ya gajiya.
"Assalamu alaikum" Yarima ya faWa gami da nuna alamar girmamawa ga Sarki Abraham.
Cikin matu?ar Sacin rai Sarki ya juya masa baya gami da cewa "Na rasa wane irin girman kai ?ana ya Worawa kansa."
"Girman kan a jinin Abina ya ke" Yarima ya bashi amsa ba tare da ya kalle shi ba
________________________________

Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632
______________________________________

*SALMAISH* Special DATA


*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN 500 MB 150. 1GB 280.
2GB 550. 3GB 840
4GB 1,100. 5GB 1,380

AIRTEL 500 MB 160.
1GB 290. 2GB 580.
3GB 870. 4GB 1,150
5GB 1,450

GLO. 500MB 170
1GB 300. 2GB 600
3GB 900. 4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE. 500 MB 130
1GB 250. 2GB 500
3GB 750. 4GB 1,000
5GB 1,250
........................................
Account No: 8067123232

Account Name: Halima Ukashatu Abdullahi

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09079885632
_______________________________




Ayeesha Abdulkareem
*INDO CE..*
[6/22, 8:13 PM] Salmaish Business Center C.E.O: *IDO HU?U*

Free Page
Book 1 Episode 5


*A.A (INDO CE)*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




"Amma na sa a kira min shi har sai lokacin da ya ga dama zai zo? shin ba ni na neme shi ba kuma zai zo min da wani shirin? ni ba ni da muhimmanci kenan?"
"?aukar Karatu zan wuce daga nan hakan ne ya sa na tsaya na shirya"
Juyowa Sarki Abraham ya yi kafin ya ce "Meke Damun ka da har zan yanke hukunci a Masarautata kuma ka canja min hukunci??"
"Abhi hukuncin da ka yi masa ba shine nashi ba domin laifinsa bai kai girman da za ai masa wannan hukuncin ba, na yi Nazari kafin hakan, Abhi ko za ka faWa min gaskiyar laifin da ya yi maka? Sabi da bai bi A?idarka ba ne fa ya sa ka tsane shi" "Umm!! to na ji, hakan ma sai da ka bi ka gane?"
"Abhi ni fa wakilin Sarki ne, idan ban iya Nazartar ?an Adam ba taya zan kira kaina ?anka?"
jinjina kai ya yi gami da takawa sau biyu sannan ya dakata, idanunsa ya zubawa Yarima kafin ya ce "Ina matu?ar ba?in ciki kasancewar ?ana ya ?i bin A?idata, ya kamata ya san cewa ko da bai bi ni a matsayin Sarki ba ni Mahaifinsa ne" ''Hakan kuma ba ya nufin sai Na yi A?idar taka Abhi , idan kuma ka na ganin wajibi ne to ka ban hujjoji, Uhmm!! Ka na da son Zuciya Abhi matu?ar son Zuciya ma kuwa, duk mutanen ?asarka kasa su yi A?idarka wanda bai bi ba ka yi masa sharri ka sa a kashe shi ko a kore shi daga cikin mu danginsa, hakan shine Mulki??, A?idar da duk abubuwa ne na son ranka ka ke shimfiWawa a matsayin Muslimci, ka na Wora wasu dokoki da tsari naka ka na sanya Manyan Malamai su na jefa Al'uma a ciki kai ma ka kira kanka Malamin Muslimci ka tara Malamai a Masarautarka ba dan komai ba sai don ka sami damar shimfiWa Ra'ayoyinka akan wanda Addinin Muslim ya zo da shi, Ba zan iya bin wannan A?idar taka ba Abhi, sai dai in ta ci tira kawai ka kashe ni, Malamina ma kansa ka hana shi zaman ?asarka ka fitar da shi waje duk sabi da son Zuciya, Abhi me yasa ka kasance haka ne???"
numfasawa Sarki Abraham ya yi kafin ya ce "Kai zan yiwa tambaya me ya sa ka kasance haka ?ana????, Ka ritsa ni da dogon surutu duk akan tambaya Waya, bayan ba ni na tambayeka ba, hakan ba son Zuciya bane??"
"A cikin magana ta akwai wadda za ka ce ?arya ne??, indai har akwai na Amince son Zuciya ne ya sa na tsaya ina magana da kai, saSanin haka kuma faWen Gaskiya ne ya kawo hakan, kuma wannan ha??ina ne a matsayina na ?anka dole ne na so maka Rahmar Allah, ka cire Son Zuciya ka bi Muslimci kawai kar ka ce dole sai ka shimfiWa wani son rai naka.
Sarki Abraham ya murmusa kafin ya ce "Na rasa ya akai ka yi min farin sanin da ko Matata da na ke tare da ita tin kafin a haifeka ba ta yi min irin wannan sanin ba."
"Ita a gida ka ke barinta a yayin da za ka yi harkar gabanka, ni kuma a da ni ne abokin yawonka, ba ka Soye min komai ka ga kuwa gane halinka abu ne me sau?i a gareni, Ni yanzu zan tafi, na barka lafiya.
Ya na kaiwa nan ya fice cike da takaicin banzayen halayen Mahaifin nasa.
Sarki Abraham ya raka bayansa da ido kafin ya jinjina kai gami da cewa "Shakka babu sai na yi tsaye akanka Salahuddin, zan nesanta ka da Mulki kwata-kwata hakan zai rage maka jin kan naka."

Moomin
Hankali tashe Gimbiya Zaina ta kalli Umminta idanunta cike taf da hawaye, murya na rawa ta ce "Me Hashim ya yiwa Jayden da har ya kashe shi haka??, ashe rashin imanin nasa har ya kai nan?"
Ummi da ta ke jin Zuciyarta ta yi matu?ar nauyi ta numfasa da kyar kafin ta ce "Ina ganin abin nasa har ya wuce nan, kin ga amfanin Waukar shawara da jin maganar manya, yanzu da ke ce ki ka je idan ya ganki haka zai illata ki, kinga yanzu sai ki ha?ura da zuwa mu raka har wani lokaci."
kasa magana ta yi ta na jin kamar ta fashe da kuka. Sarauniya Hakima ta ce "Yanzu gashi nan sai ki hankalta, dama in banda abinki ki rasa wa za ki so sai wannan ?aton Kafirin?" Sarauniya Ameena ta ce "Haba Sarauniya Hakima, a matsayinta na wadda ta ke da damuwa ai ba haka ya kamata ki gaya mata ba." kallon banza Sarauniya Hakima ta wurga mata gami da jan tsaki ta bar wajen.
Sarki Zunnur kuwa bai yi magana ba, a ?asan Zuciyarsa kuwa murna ya ke sosai a cewarsa yanzu dolenta ta ha?ura da soyayyar.

Noor
hawaye ta goge kafin ta ce "Ummu Noor, kenan da Gimbiya ce ma haka zai kasheta? ki duba fa ki ga ya cire masa kai, Na tsani Kafiran nan wallahi, rashin imanin ai ya yi yawa, da zan ganshi shi kaWai da sai na kashe shi."
"Kashe shi ba zai amfana miki komai ba sai ?arin ba?in ciki, ba shine shaiWanin ba na gefensa su ne su ke yi masa Gangi, Indai Jayden ne ki kwantar da hankalinki komai zai yi lafiya.
"Amma abin ya yi yawa Ummu Noor, shi ba ya jin ko kunyar Ubangiji ma?" "Na ce ki yi shiru, ki kwantar da hankalinki" Ummu Noor ta faWa cikin sigar rarrashi.
Noor ta mi?e gami da cewa ba zan iya zama ba Daji zan tafi.
"Sai kin dawo" Ummu Noor ta faWa tare da rakata da ido.

Munwaz
"Na faWa maka idan ka yi mata haka ba za ta ?ara bibiyarka ba" Gimbiya Rubaina ce ta yi maganar idanunta akan Yarima Jayden.
ya murmusa kafin ya ce "Kin yi farin ciki?" ta gyaWa kai ta na murmushi irin na munafurci, faWaWa murmushinsa ya yi gami da zamewa ya kwanta akan Gado ba tare da ya yi magana ba.
Kwantawa ta yi akan ?irjinsa gami da cewa "Wata Baiwa Ta fiye kallona, ina so ka sadaukar da jininta ga Gunki Gurmus." "Da Safe zan aikata" ya bata amsa a ta?aice, ta saki murmushi Zuciyarta cike taff da tunane-tunane da sa?i kala-kala.
Gari na wayewa kamar yadda ta sa shi sai da ya Sadaukar da Baiwar sannan su ka fara bauta.
su na tsaka da Bautar ne Malamin tsafin Sarki Zamwal ya baiyano a gurin cike da Farin ciki ya fara magana.
"Ya kai Yarima Jayden ?an Sarki Zamwal, Gunki Gurmus ya aikoni don na sanar da kai cewa Matarka ta na ?auke da Ciki na ?a Namiji, don haka daga yanzu za'a fara Sadaukarwar Jini ga Abin Bautarmu, Maza za a dinga yankawa a na Shayar damu jininsu idan aka yanka mace ?an ba zai zamo Jarumi ba ko kuma ya Mutu, an fi son Jariran Maza sabbin haihuwa."
Ido Yarima Jayden ya zubawa Gimbiya Rubaina ya ma rasa wane irin farin ciki zai nuna. Sarki Zamwal da Findu kuwa sabi da murna jikinsu har kakkarwa yake yi, su ka zube a gaban Malamin Tsafin su ka dur?usa kan guiwoyinsu kafin su kafa goshinsu a ?asa.
Malamin Tsafin ya yi dariya kafin ya ce "Wajibi ne Jayden ya nuna wa Gunki Gurmus farin cikinsa." Sai a lokacin ya dawo haiyacinsa ya yi Sujjada kamar yadda Findu da Zamwal su ka yi, Rubaina ma dur?usawa ta yi a Zuciyarta ta gama tsara abin da zai faru anan gaba bayan samun cikin nata, Don murna kuwa ji take kamar ta ci babu.
Su na gama Bautar Yarima Jayden ya bawa Dakarensa Umarnin a zagaye Masarautar a Webo dukkanin Jarirai maza ko kuma Yara Maza. ba tare da Sata lokaci ba Dakaru su ka bazama, bayan wani lokaci su ka tara Yara da Jarirai a Fadar, Kasancewar Babbar ?asa ce akwai mutane da yawa, kuma babu ruwansu da Aure Zina ce kawai aikinsu, ?aramar Yarinya ma sai ka ganta da ?a?a, cikin sau?i su ka tara ?ananun Yara da Jarirai a ?alla Talatin. Wasu Dakaru guda Biyu ne su ka ?araso Tsakiyar Fada ri?e da wata muguwar Sar?a da su ka yiwa Matashiyar Budurwa ?aurin goro da ita. ?ayansu ya ce "Gurmus ya ?ara maka lafiya Shugabana! Wannan Yarinyar ta haifi Yaro jiya amma ta ce ba za ta bayar da shi ba, ta bawa Babanta ya Soye shi." Mi?ewa Yarima Jayden ya yi ya na binta da ido, mamakin ma taurin kai na ?an-adam ya ke yi, cikin ?asaitaccen takunsa ya ?araso gabanta har lokacin idanunsa su na kanta, Murmusawa ya yi kafin ya ce "A kawo min Babanta." har su ka kamo Baban nata Ya na tsaye cokam a gurin.
"Ko Shi ya Mutu, ko ke ki Mutu, ko ku mutu Har ?an naku." jin hakan yasa Babanta saurin cewa "Gafarta min Shugabana, Zan baka Yaro amma kar a kashe min ita, ka temake ni." Jayden ya yi musu alamar su kai shi ya Wakko Wan. Kuka kawai ta ke yi ko magana ta kasa yi, gaba Waya ta tsani ganin Fuskar Jayden ji take inama ta na da yadda za tai ta kashe shi. bayan sun dawo tare da Jaririn ya na ta Kuka, Jayden ya sa Dakarun su ka karSe shi, Takobinsa ya zare ya Sukawa Dattijon ita a saitin ?awon Zuciyarsa. Budurwar ta ?walla ?ara idanunta a warwaje, har Dattijon ya faWi ?asa Takobin tana cikin ?irjinsa sai ma ?ara dannata da Jayden ya ke yi, jini kuwa sai tsiyaya ya ke yi, sai da ya tabbatar ransa ya bar gangar jikinsa sannan ya zare Takobin ya ce "A bawa Masu ci su cinye shi." a Ladabce Dakaren ya amsa da "Yanzu za ayi." "Bayan wannan ?an nata ina bu?atar wani don Haka na Baka ita, ka je kai mata cikin wani ?an" Jayden ya faWa ya na kallon Dakaren, Cikin murna da jin daWi ya amsa gami da yin godiya da samun kyauta daga Shugabansa.
Jayden kuwa juyawa ya yi ya koma kan kujerarsa ta Mulki. Gimbiya Rubaina sai Murmushi ta ke yi, Sarki Zamwal kuwa Dariya ma ya ke yi ya na Kora ruwan Giya, farin ciki ya gama mamayeshi.

Sarki Abraham
Cikin Wakin tattaunawarsa da Abokanansa da Malamai, ya na zaune kan Kujera cikin Sacin rai ya ce "Salahuddin ya gama gane Sirrinmu, saura Abu Waya ne kawai ya rage ya gano shi kuma ya kusa ganewa don kuwa ya na Zarginmu da aikatawa, kuma idan ya gane Tamu ta ?are don har ni zai iya Kashewa." ?aya daga cikin Malaman ya ce "To Yanzu yaya kenan?" "Dole ne na nesanta shi da Mulki sannan na hana masa farin ciki, hakan zai sa ya maida hankali akan rayuwarsa ya dena kallon tamu." Waziri ya ce "To me zai hana mu Kashe shi????"


Paid Book ne

Book 1 VIP 300 NOMARL 250 Idan Kati ne 300.

Book 2 VIP 300 Nomarl 250 Kati 300.

COMPLETE 1-2 500

Don ?arin bayani 09079885632


_________________________________
*SALMAISH* Special DATA


*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN 500 MB 150. 1GB 280.
2GB 550. 3GB 840
4GB 1,100. 5GB 1,380

AIRTEL 500 MB 160.
1GB 290. 2GB 580.
3GB 870. 4GB 1,150
5GB 1,450

GLO. 500MB 170
1GB 300. 2GB 600
3GB 900. 4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE. 500 MB 130
1GB 250. 2GB 500
3GB 750. 4GB 1,000
5GB 1,250
........................................
Account No: 8067123232

Account Name: Halima Ukashatu Abdullahi

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09079885632


____________________________________
_Akwai ingantaccan maganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login