Showing 27001 words to 30000 words out of 42382 words
ba sai yanda uncle ibrahim ya daga jijiyan wiya kan cewa ,”ba wanda ya isa yasa yariyar nan ta zauna a gidan,hakan nan ba karamin bata wa “boss lion” rai zaiyi ba.
“Cikin sanyi murya yace” kasa ka kanka koda da hauka ne bada wasa ba kace zaka sake yun wannan abun ,zaka kwanane a dakin lucky “wato damusan “boss lion” bayan nan zaka hadu da punishment ina baruwa ko mutuwa zakayi sai dai kayi kaji ko”
“Hakanma yayi wallahi ai ko a mafarki ma bazan sake barin haka ya faru ba.
“Good, you can find your way out,ya fada cikin bada umarni”ai kuwa jikinsa ya na rawa ya wuce wajan lifter ya wuce dakin sa.
Maida hankalinsa yayi kan junaid,da ya takure dikinsa waje daya saboda tsoron abunda zai biyo baya,sai kuma ya maida kallansa kan Ashman ,ya masa alama ta ido ,Dan yan miskilancin suna kusa bazai bude baki yayi magana ba.
Ashman ya gane me yake nufi ne yasa “yaje wajan junaid ya daukesa a kafadansa,wanda jikinsa har bari yake yi,nan danan ya zazzabi ya kamasa saboda tashin hankali dan abune ya masa yawa,”accident na abokinsa,gana sultana ,Gana “boss lion”.”kallo daya yaya boss ya mishi ya gane shima junaid din ba lafiya yake ba ,shiyasa yasa Ashman dauke sa dan yayi mishi treatment.
Bayan fitan Ashman ya saura daga shi sai sultana suka saura a falon ,dan uncle tareeq kam tunda aka cewa uncle Ibrahim ya tafi shima ya kama gabansa,dan bayason,ganin abunda zai bata wa boss lion rai.
Mike wa yayi ya wuce wajan lifter yashiga,dakinsa ya shiga sai tashin kamshi yake yi mai sanyin dadi, wanka ya shiga yayi ,yashirya ciki pajamas white color mai laushi sai kamshi yake yi kaman wanda yayi barin turaren a jikinsa.
Fita yayi ya wuce kitchen dan hadawa kansa coffee ☕️ dan Ashman bayanan dashi zai kawo masa,koma yayi cikin dakinsa ya dauki system nasa yana aiki,yana shan coffee sa a hankali,dan baya iya bacci idan baisha coffee ba.
Sai wajen biyun dare kafun ya gama abunda zaiyi yarufe system din ya ajiye,fitowa yayi daga dakin ya koma falon kasa ,bakowa a side din ,sojojin sun koma waje dan kwana sukeyi suna aiki amma kowa smda time nashi idan wannan yayi yau Toh gobe wani ne zai yi.
Direct kujeran da junaid ya ajiyeta ya nufa ,tana nan inda take ,bata motsi ,gashin nan ya baje baka ganin fuskanta ,ga jini harkan carpet ya sauka.
Ya tsuna fuska yayi cikin kenkemi yasa hanu ya dauke ta ,kaman bai dauki komai ba haka yake ji.
Wani daki yashiga da ita ,na hawa na hudu ,dake side nashi ,kuna wutan dakin yayi”wow gaskiya daki ya hadu iya haduwa ,pink color ne furnitures din dake cikin dakin,mai shegen kyau da tsada,yana tashin kamshi a gyare yake fess fess ,kaman wanda akayi mussaman dan ita.
Kwantar da ita yayi a hankali,first eid box ya dauko ya zauna a gefen gado,tare da tattare gashin ya daya baje yayi ,fuskanta duk ya baci da jini saboda jinin daya zuba daga kanta ,batare da damuwa da jinin daya bata mata fuska ba ya fara yi mata dressing .
Cikin kankanin lokaci ya gama ,batare da ya kalla gaba daya fuskanta ba,shifa inaga baya tunanin ko a hanya suka hadu bazai ganeta ba,dan jinin dake fuskanta ma kadai ,zaisa mutum ya kasa gane ta.
Yana gamawa ko seconds bai kara ba ya fita daga dakin rashi duk a dagule,dan bakin ciki,wai yau shine da zuwa yayi wa wata mace treatment,kuma ya dauketa da hanunsa kai ina wallahi da sake,bayaso ya sake hadu wa da ita har ta warke ta barmasa gidan koda ko by mistake ne,zata sha mamaki,ya ja kwafa ya kashe wutan daki tare da rufe kofan.
Dakinsa ya koma ya kwanta dan lokacin har 2:45am tayi addu’a yayi ya Shafa a jikinsa ya kwanta fuskanan kaman an aiko masa da sakon mutuwa,dan lokaci daya yaji wani irin tsanan ta yana mamaye masa zuciya .
Dan junaid kawai yayi wannan abun,kumashi Allah ya sani ya kasan ce ba azzumi bane ,wanda za’a ce yana ganin yanda yariyar take zub da jini zai gane ba karamin ciwo taji ba,a kanta.
Bai wuce 10mins ba bacci ya daukesa mai dadin gaske🥱😴
___________________________________________😵💫
WASHE GARI
Kiran sallan farko ya tashi ,ya shiga yayi wanka ya shirya cikin jallabiya ash color yayi mishi kyau ,dadai jikinsa dan kana ganin Moses nashi ya cikin jallabiya Dan yaya boss baidai diri ba gashi kuma ingarman na miji ,bai macen da ta’isa tasa kasa a ido tace baiyi mata ba,dan yaya boss san kowa kin wanda ya rasa, first class.
Massalaci suka wuce shida ,Ashman,junaid,uncle tareeq,uncle Ibrahim ,ba wanda ya cewa kowa komai dan duk tsoron magana sukeyi dan kowa da bashi kalan laifin amma banda uncle tareeq.
Suna dawowa daga masallaci dakinsa ya wuce direct dan ya kwanta,ba karamin bacci yake ji ba dan bai samu ,bacci ishashe ba,kansa har ya hara masa ciwo,jallabiya jikinsa ya cire tare da lankayawa akan hanger,yabi lafiyan gado,Nan dannan bacci ya dauke sa.
********
Junaid kam bayan ya shiga dakinsa,ya kasa kwanciya so yakeyi yaje yaga sultana amma baisan inda aka kaita ba,dan har clinic na gidan sai daya duba amma bai ganta ba,shi tsoronsa ma kar ace boss lion fitar da ita yayi a gidan,saidai kuma yasan wannan abune me wiya ya fitar da ita tunda uncle tareeq yaso yanuna masa isa,shikuma bazai taba yarda da hakan ba.
Yanke shawara yayi zaije kawai ya samu ya Ashman ko yasan inda aka kai sultana,fita yayi daga daki ya wuce dakin yaya Ashman.
Shiga yayi da sallama a bakinsa,bakowa a daki ,kashhh matawa yayi yanzu haka yana dakin gym ,komawa yayi ya wuce can dakin gym din a tsaye ya gansa da da karfe mai nauyi a hanun sa yana up and down da karfen, ganin junaid ya shigone yasa ya daina daga karfe ya samu wajen ajiye wa ya ajiye.
Kamo hanun sa Ashman yayi suka zauna akan resting chair dake dakin yace”junaid kai da bakada lafiya me ya fito dakai ,daga daki,marairaicewa junaid yayi kaman zaiyi kuka irin yan da shagwababun yarannan suke yi yace”yaya ash na warke fah dama zuwa nayi na tambaye ka ina aka ajiye marar lafiyannan,dan na duba har clinic ban ganta ba.
Ganin yanda junaid din ya damu ne yasa Ashman ce masa”muje ba nuna maka inda take,dan shi jiya yaga lokacin da “boss lion” ya dauke ta ya wuce da ita dakin,kuma bun ya bashi mamaki ba dan kadan ba,dan shima ya fitone dan yaga an dauke tane daga falon kokuwa ba a dauke ta ba.
Gaba yayi shikuma junaid nayana binsa a baya ,har kuka isa plot 4 ,zaro ido junaid yayi yace”yaya ash dan Allah karka kaini wajan yaya boss wallahi zai batamun rai ne,dan shi harga Allah ya maida yaya boss ne yace a kira sa.
Tsayawa ganinsa Ashman yayi dan junaid har yaso ya bashi dariya wallahi ganin yanda ya wani tsure,sai zazzare ido ya keyi.
“Ba kai kace na kaika wajan wace ka buge ba?”gyada kai junaid yayi alamun eh”Toh ka kwantar da habkalinka wajan ta zan kaika,ka gane”eh junaid yace.
Kofan dakin suka tsaya ,junaid ya juyo yana kallon yaya Ashman da mamaki dan shima bai taba shiga wannan dakin ba dan a kule yake kullum tunda suka zo gidannan.
Shiga ciki sukayi dukansu biyu,Ashman ne ya kunna wutan dakin ,dan dakin da duhu,dan boss lion ya kashe wutan dakin kafun ya fita.
A kwance take yanda boss lion ya fita ya barta,tananan yanda take ,bata ko motsa ba dan har yanzu bata dawo daga suman da tayi ba.
2024/2025🔥
Story and written by AMID ✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
Bismillah Rahmani Raheem
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
page 📃 22
A kwance take yanda boss lion ya fita ya barta,tananan yanda take ,bata ko motsa ba dan har yanzu bata dawo daga suman da tayi ba.
Shiga ciki sukayi ,wajan gadon,junaid yana ganin fuskanta ,ya zaro ido tare da dafe kirji,ya juya ya kalli Ashman yace”yaya Ash Allah yasa dai ba mutuwa tayi,kaga duk jikinta jini,wannan kam sai an kara mata jini inaga kafun ya far fado.
Ashman kam ganinsa kawai yake yi yama rasa me zaice ma Ohoo,ganin yanda kan yarinyar ya bugu,dan taji ciwo sosai a kanta ,she fatansa ma kartayi loosing na memories nata .
“Yaya ash ko zamu wanke mata fuskanta ne dan naga duk ya baci da jini,ba’a gane fuskanta fah.
Wani kallo Ashman ya jefawa junaid irin na bakada hankalin nan yace”wai ni junaid ina ruwanka da ita ne kabar ta mana ,a yanda ka ganta,idan ta tashi ta wanke fuskan nata,idan haka wuce mu tafi dan bana son ,shishigi da shiga abunda bai shafe ka ba,kuma wallahi saura idan ta farka kace zaka shishige mata zaka sha mamaki dan a “boss lion “zan fadawa,dan naga ni kadai kake tsoro.
Marairaice wa junaid yayi yace”yanzu yaya ash meye yayi zafi da zaka ce zaka fada wa yaya boss ,ni ba abunda zaina hada mu da ita har ta warke ta koma inda ta fito.
“Good ,kwanda da kayi wa kanka karatun ta nutsu ,idan ba haka ba kuma kasan sauran …..
Wuce mutafi ,idan ya farka sai muzo mudu ba ta,”Toh junaid ya fada tare da bin bayan Ashman suka fita daga dakin kowa ya wuce dakinsa.
____________________________________________❤️
8:10pm
A hankali ya bude idonta da sukayi mata nauyi sosai,idonta sunyi dark blue ,saboda dadewan da sukayi a rufe ba tare da ta bude ba.
Akan chandelier dakin ta fara gani sai take ganin abun kaman a mafarki ,dan yanda dakin yayi haske,abun gwanin sha’awa da kuma burgewa ,dakin ta fara bi da kallo, tana tunanin ko mutuwa tayi ne dan wallahi daki nan ba karamin haduwa yayi ba ,komai anjera shi yanda ya dace.
Mikewa tayi daga kwancen da take,kanta yana mata wani irin ciwo da tunda aka haifeta bai taba mata ba,lokaci daya abunda ya faru ya dawo mata kai,firgita tayi,ta sauko daha kan gado ,tsoro ne da firgici ya kamata,ta fara tataba jikinta dan taji shin da gaske itace Kodai mutuwan tayi ne.
Tabbass tasan ba mutuwa tayi ba,dan mutuwa tayi kuma ta ganta a aljanna tasan baza taji zafin ciwon da kanta yake mata ba,kuma gashi kayan dake jikinta lokaci da ta gudu daga gidan karuwai ne,wannan yana daya daga cikin abunda da yasa ta gane ba mutuwa tayi ba’toh amma ina take ‘waye ne ya kawota nan wajan.
Futsari take ji amma ta kasa zuwa tayi,sai da taji ya kulle mata mara kafun ta sauka taje wanjan kofan da ta gani a cikin room din,bude wa tayi a hankali ,taja kafafunta da suke yi mata ciwo saboda buguwan da tayi,lokacin da junaid ya bugeta,Allah yaso ma bata karye ba kota gurde kawai kafan yayi tsami ne.
Tana shiga ,sai data shaga da kallon bandakin,toilet ne daya amsa sunansa toilet,komai na ciki white color ne,wajan cupboard taje dan yi futsari,tana gamawa ta wuce wajan sink ,tajikin a kwai mirror,tana zuwa wajan kaman ance dago ki kalli mirror,batasan lokacin da ta sake ihuuuuuu mai karan gaske ba,ganin yanda fukanta ya baci da jini bazama ka gane color skin nata ba ,bandage na kanta ma ya sake baci da jini,abunda ya tsoratata kenan yasa tayi ihu ba tare da ta shirya ba.
Tana gama ihuuu n taji kanta yana juyawa,idonta suka rufe,tayi baya zata fadi.
Cikin sauri Ashman ya tare ta,tare da daukanta a kafadansa ,ya fita daga dakin ma gaba daya clinic ta wuce da ita,dan annan ne zata samu ishashe ne kulawa, tunani yake yi a zuciyansa “yanda yake mamakin wannan abun ,shi bai ma san meyasa “boss lion” kawota wannan dakin ba ,wata kila saboda mugunta ne yasa yayi hakan ,idan ba haka Taya zaka je ka ajiye marar lafiya ita kadai a daki ba tare da wanda zai kula da lafiyanta ba ,yasani yanzu haka da wata manufa yaya boss ya ajiye ta a dakin.
Shima abunda yasa yaji ihuuun ta saboda,ya kaiwa boss lion coffee ne yana dawowa yaji karan Ihuuunata shiyasa yashiga dakin nata dan yaga akan wani dalili ne yasa zata wani yi musu ihuuu da daddaren Allah,sai kuma ya tarar bata cikin dakin,shi yasa ya yake shawaran shiga cikin toilet din,anan ya tarar da tana shifin faduwa.
***
Daya daga cikin dakin clinic din mai kyau ya shiga ya kwantar da ita, wani sojane ya shigo da lab coat nashi tare da wiyansa lan kaye da stethoscope 🩺 alamun doctor ne.
Yana ajiye ta ya fita domin samo mata kayan da zata saka koda kala biyar ne,idan yaso in taji sauki sai suje da junaid ya siya mata duk abun amfani.
Doctor ne ya shiga dubata,tare da goge jinin dayake fuskanta tasss ya goge nan dannan haske ta ya fito,kafun ya warware bandage 🤕 din da ke kanta yayi dressing na wajan ,tare da saka mata sobon bandage a kannata ,kafun ya dauki blood pressure monitor dan duba yanda pressure ta yake,ai kuwa sai da yayi higher dan ta saka damuwa a ranta.
Yana gamawa yayi mata x-ray a kanta dan duba yanda kanata yaje batan ya gama ya saka mata drip tare da yi mata alluran bacci ,nan da 3 hours zata tashi.
Bayan ya gama mata abunda zaiyi ya fita ya bar dakin,tare da rufe kofan.
After 30 minutes sai ga Ashman ya dawo tare da wani soja a bayansa hanunsa riqe da ledodi irin na boutique dinnan,yana ajiyewa ya fita ,shima Ashman din ,ganin ta juya baya,hakan yasa baiga fuskanta ba,shima ya fita daga dakin.
******
Boss lion kwance yake akan L-shape chair dake dakinsa idonsa a rufe kaman mai bacci amma baccin yakeyi ba,takaici kawai ya isheshi,dan wannan ihuuun da sultana tayi danshi a rayuwansa ya tsani hayaniya kwata kwata,ihuuu nata kuwa har cikin kokon kanta taji shi,shifa wallahi harya fara nadaman barinta da yayi ta zauna masa a gida.
Tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka,bayan ya fito ta wuce dressing room ya shirya cikin pajamas nevy blue masu kyau da tsada,kwanciya yayi dan shi bai cika samun lokaci yana yin bacci ba dan wani lokacin ma till down yake yi.
Karan bude kofan dakinsa yaji anyi,amma saboda miskilanci ko kadan bai nuna alamun yasan da mutum a dakin ba,danshi komin kankantan motsi idan anyi yanaji,dan kwata kwata bashi da nauyi bacci,inashi ina dogon bacci,suda da suke zuwa yaki,any time ana iya kawo musu hari.
Junaid tunda ya shigo yake dari dari dan yansa yayi lafi amma dole ya bada hakuri,cikin dauriya ya haye kan gadon boss lion ,ya rungumesa ta baya,yace”please yaya kayi hakuri,wallahi bada sanina na bugeta ba,kawai ganinta nayi a gabana,kuma kasan bawa baya taba kaucewa kaddararsa,duk inda kake sai kaje ka same ta,please yaya am so sorry it’s me your junior,please don’t be angry with,bazan kara fita ban fada maka ba,shima banyi tunanin zaka dawo ka samu bandawo ba,please and please my yaya .
Boss lion yana jinsa amma ko uffan bai ce masa ba yanda kasan ba’ayi ruwansa a dakin ba,tsabar miskilanci.
Ganin bai kulasa bane yasa ya fashe da kuka harda shesheka,dan yasan idan ba kukan ya masa ba dakyar ya kulasa,dan kwata kwata bayasan ganin kukan su.
Kukan da yake yi ne ya karyawa boss lion zuciya dan bayaso ganin kukan yan uwansa,wannan Alkawari ya daukawa kasa nace wa bazai bari suyi kukan maraici ba.
Jawo sa yayi jikisa yana bubuga bayansa alamun rarrashi ,duk da haka bai ce dashi komai ba,nan take junaid yayi shiru a jikin boss lion sai shakan dadda dan turaren jikin boss lion yake kamshi sai tashi yakeyi,tuni ya soma ajiyan zuciya akai akai ,Chan bayan 5mins dikinsa ya saki ,alamun bacci ne ya daukesa.
Tsayawa yayi yana kallon kyakyawan fuskan junaid dake sauke numfashi a hankali a hankali,abubuwa dayawa suna masa yawo a kai,janyo musu blanket din yayi ya rufe su , tare da yi addu’a ya fasha fa musu gaba daya,shima bai jima ba bacci ya dauke sa .
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
2024/2025🔥
Story and written by AMID ✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️