Showing 9001 words to 12000 words out of 42382 words

Chapter 4 - Sirrin Dake Boye Book 1 Hausa Novel Complete

Amid   

20 Dec 2024

288

be dalilin wani kallo da “BOSS LION “ ya masa ,ba tare da yayi magana ba ,yanuna masa kofa da ido,dan bai cika yin magana ba ,dan akwai wani SIRRIN DAKE BOYE da ke cikin zuciyansa bayasan ana tuna masa da abunda ya wuce.

Tashi yayi salun alun ya fita daga dakin ,almost 9:30am ,bayan fitan “Ash” da minti goma sai gashi ya dawo da Trey a hanun sa ,mai kyau da dauka hankali golden color ne ,ajiye wa yayi akan center table dake cikin dakin.

Yakai 10mins a zaune akan king chair dake dakin,kafun “BOSS LION “ ya mike ya zauna a dayan king chair ,tare da yin crossing legs nasa,ba tare da yayi magana ba ,Ashman kam wannan abun bai damesa ba ,saving nashi yayi abinci irin nasu nacan,a hankali ya fara cin abincin ,ci yake yi kaman yana yanga, cikin nutsuwa da Jan aji.

Shap shap ya gama cin abincin,tare da mike wa ya shiga toilet dan ya wanke bakin shi ,shikuma Ashman ganin ya shiga toilet sai ya tattare kwanu kan ya fita dasu ,yakuma fesa air freshener masu sanyi dadi.

Fitowan da yayi bai ga Ashman ba ,yasan ya fita,koma wa yayi ya zauna a L-shape chair dake gefen center table din da wasu docoments da system.

Bai fito ba sai karfe daya shima sallan azahar ne ya fito dashi dan kwata kwata baya wasa da sallah komai yake yi zai bari ne yayi sallah.


________________________________________________📚

Abuja


Yau takama Wednesday,tunda ta tashi daga bacci take Jin kwadayin shan ice cream,dan yau cikin farin ciki ta tashi daga bacci.

Wanka tayi ta shirya cikin Riga da wandon makarata tareda wani mini hijab tayi Kyau sosai,daukan school back nata tayi ta wuce falo.

Falo ta sakko bata samu kowa ba ,wuce wa tayi side in Ammi, akan sallaya ta sameta dan azkar take yi,cikin murmushi ta karaso inda Ammi take “Ammi Ina kwana “lafiya kalau autar Ammi ,kin tashi lafiya”lafiya kalau ,kallanta Ammi tayi tace yau kuma autar Ammi mai muka samu mai dadi naga sai murmushi kike yi , darıya Shukrah tayi tare da cewa wallahi yau kwadayin ice cream nake yi” Toh ai sai kije kisamu alameen ki fada masa kinasan san ice cream din zai kaiki ai.

Cikin shagwaba ta turo baki tace “ Ammi amma kinsan halinsa yanzu sai yace bazai kaini ba “karki damu autar Ammi ni zan mishi magana idan ya shigo, cikin Jin dadi shukrah tace thank you best mother in the world,shiya sa nake sanki wallahi” dan dan kwalanta Ammi tayi,tare da cewa tashi ki barmun daki marar kunya kawai ,cikin darıya shukrah tace Ammi ba rashin kunya bace har cikin Raina nake fada,ta karasa magana tare da fita daga dakin tanaji Ammi na ce wa Allah ya kiyaye hanya.

A wajen stairs taga alameen zai wuce dakin Ammi ,cikin Shan kamshi tace yaya alameen good morning “morning ya ce tare da haura wa dakin Ammi .

Ita kuwa yusrah wuce wa dining tayi ,breakfast tayi cikin sauri ta gama ta fita dan driver yana jiranta , shiga tayi motan driver ya ja motan suka wuce school.

A dakin Ammi kuwa yana zuwa yayi knockingna kofan dakin,izinin shiga Ammi ta bashi ,zama yayi a kasa kafun ya fara gaisheta,Ammi Ina kwana kin tashi lafiya, kinsha maganin jiya da daddare,tsaya wa kawai tayi tana ganin sa ,soyayyarsa kullum karuwa take yi a cikin zuciyan ta ,yanda yake kulawa da ita abun ba karamin dadi yake mata ba.

Lafiya kalau”Alhamdulillah,maganina kuma nasha dana ci abincin dare saura na safe, Toh Ammi Allah ya Kara sauki”Ameen ya Allah “Ammi akwai abunda kuke buka tane idan na fita na taho miki dashi,” a’a babu komai Allah yayi maka albarka ameen yace tare da tashi zai fita .

Cikin sauri tace alameen ,komawa yayi ya zauna ,tare da maida hankalinsa Kanta ,Yauwa dama shukrah ce ta tashi da kwadayin shan ice cream “Toh Ammi baga driver ba sai ya kaita su siyo,”baza’a aika drivern ya siyo ba, kai nake so kai nake so ka kaita inda kake zuwa.


Cikin son danne baccin ransa yace Toh Ammi Insha Allah,ya fada tare da mikewa “Toh Allah ya kiyaye ,yayi maka albarka ,Ameen ,tare da fita da ga dakin.

Falo yakoma ko zai sameta ,amma batanan tariga da ta tafi.

___________________________________________🌹


7:45pm


Idar da sallanta kenan taji ana knocking na kofan dakin ,sai kuma taga ya shigo cikin dakin , ganinsa tayi ,sanye yake cikin maroon yad mai tsada anyi mishi dinkin half jampa,dinkin zamani daidai jikin sa.

Cikin takunsa mai dauke da nutsuwa ya isa inda take ,baiyi wata wata ba ya kwade Kanta ,dan har janzu bacin ran bai gama sake shiba.

Wato ni kin rainani harda zuwa wajen Ammi kice mata kina kwadayin ice cream, kuma ni kikeso na siya miki ko ,ya kara sa magana tare da Zare mata ido.

Cikin gunguni tace nifa ,bace wa nayi tace maka kakaini ba , kawai ce mata nayi Ina kwadayin shan ice cream,sai tace bari kazo zata ce maka ka kaini.

Kwafa yayi tare da cewa zaki sanine, wuce kije ki shirya na baki Nan da minti biyu kısa meni a packing space “Toh tace tareda mikewa ,shikuma fita yayi daga dakin.

Wani half Sunnah hijab ta dauka yellow color ta daura akan blue jeans and yellow t-shirt din dake jikin ta ,ta fito cikin sauri ta wuce parking space,anan taga maercese benz 350 maroon color yana kawo wuta, wuce wa tayi tare da bude front site zata shiga , tsawa ya daka mata yace wallahi idan baki koma kin saka kayan arzikiba,jikinki sai ya gaya miki,na baki Nan da one minute ki fito.

Zum buro baki gama tayi ,tare da konawa dan bata San duka.

Komawa tayi ta dauko abaya purple color mai fadin hannu daya sha stones tayi rolling na gyalen tayi kyau sosai, cikin sauri ta wuce packing space,ta bude motan ta shiga ,bai ce mata komai ba har duka Isah hadadden wajan shan ice cream dasu burger 🍔 ,shawarma,pizza,popcorn,drinks ,chocolate,birthday cake,snacks da abubuwa dai kala kala.

Shiga sukayi wajen dan babu hayaniya dan wajene na yayan wane da wane suke zuwa irin wajen.

Mentioning na abubuwan da take so tayi iri su burger ,popcorn,chocolate ,ice cream take so ,kawo mata akayi a wani bag mai dauke da tambarin shop din.

Wuce wa sukayi suka koma cikin mota,kuna motan yayi tare da daukan hanyan gida , bude bakinta tayi tare da cewa yaya alameen Nagode Allah ya saka da alheri , Ameen yace daganan babu Wanda ya sake magana a cikinsu har suka iso gida.

A falo suka tarar da Ammi da Abu zaune suna hira,gaishe da abba yayi da yimishi ya office sannan ya koma dining ya zuba abinci kadan,dan kansa ciwo yake masa,bayan ya gama cikin abincin ya dawo falo anan ya tarar da shukrah sai shagwaba take musu sukuma suna biye mata.

Sai da safe ya musu tareda wuce wa dakinsa dan ya kwanta.

Shukrah kuwa yana ta fiya ta tashi ta kwashe laidodin ta tawuce dasu daki tare da musu sai da safe,dan Ammi ba cin irin abubuwa Nan take yi ba,tana shiga dakinta zama tayi ta bude laidan data shigo dashi ta dakko ice cream in ta saka a fridge,ta fara rage kayan jikin ta ,ta shiga wanka,bayan ta fito ta saka kayan bacci Riga da wando Marasa nauyi milk color.

Dauko ice cream din tayi daga fridge da burger ta ,ta zauna a gefen gadon tana sha ice cream in ta kuma tana cin burgern ta ,dan dadi har lumshe ido take yi.

Bayan ta gama ci ,ta shiga toilet tayi brush, ta koma daki ta kashe wutan dakin ya saura iya bedside lamp ine ya rage tayi addu’a ta kwanta

Asuba tagari


2024/2025🔥

Written by Amid✍️





💋*_SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌎 Destiny,Love❤️& Romance 💋

Written by Amid ✍️

2024/2025🔥


Bismillah Rahmani Raheem

Book 1
page 📃 8

_____________________________________________✍️

USA 🇺🇸

Zaune yake a garden ,jikinsa sanye da three quarters da t-shirt armless daya fito da surar jikinsa irin na kar fafan mazannan,gaya sake curly hair sa ,ya kishin gida a man kujera ,garden din yana da girma sosai daya kawatu da red roses ,yellow,pink,purple,blue daya kawata wanjen ga tress of every kind of fruits,apples,banana, oranges, guava,grapes,strawberries etc. Gasu manya manya ,ga wasu outdoor chairs and tables wajen ya hadu iya haduwa.

Yau kwanan sa biyu da dawowa,ya karbi document din da yabawa Ashman aiki,ya duba ya gani bai gamaba amma bai ce masa komai dashi saika manta da kamasa lafi tukun zai hunkun taka a bazata zai maka hukunci.

Daga can nesa akwai sojojin da suke ta shawagi ,dan suna iya ganinsa daga inda yake zaune.

Ashman yazo garden , zama yayi a kujeran dake passing na “boss LION “ sanye yake da wando jeans da red t-shirt.

Good morning yaya boss “batare da ya amsa ba ya “meyasa Baka gama abunda na saka kaba”da ga sama yaji wannan tambayan ,jin wannan maganan sai da zuciyansa yansa tabada irin dummm ,dan a bazata yaji maganan harya manta.

Jiyowa yayi yakala “Boss lion “ idonsa a lumshe ,zaka rantse bashi yayi maganan ba ,yaya boss am so sorry,nayi kokarin naga nagama aikin amma abun yaci tura,wallahi banso har kadawo ban gama aikin ba” very good this is not a reason that will make me not to punish you, dan bansa abu aki gamamun shi akan lokaci”so I must punish that person.

Let go, mikewa Ashman yayi kaman zaiyi kuka yabi bayan “Boss lion “ wani babban fili sukaje, kana ganin wajan kaga wajan horon sojoji, suna tafiya sojoji suna binsu a baya.

Abubuwan horo kala kala parts parts, kowani punishment da bangarensa , Waje ne dayasha tiles irin mai santsin nan, zama “boss lion “ yayi a kujera mai kyau yayi resting bayansa da kujeran tare da yin crossing legs,umarni ya bawa sojojin da sutafi , mutum biyu ne suka tsaya,dan suma akwai abunda zasuyi ne.

Man abinci suka zuba a wajen tare da fasa Kwai daya wa wajan ,kankace me wajan yayi wani irin santsi da mutum yana ajiye kafansa zai fadi,suna gamawa suka bar gurin,
“Remove does trouser and the t-shirt “gyada kai yayi dan babu bakin magana ,cire wa yayi ya saura dagashi sai boxers da vest, “you can move” “boss lion “ ya fada.

Okey yace tare da daukan lemon 🍋 akan spoon in , idan lemon ya fadi zai koma farko ne .

Taku daya yayi zaiyi na biyu santsi ya ja kafansa ya fadi, saida gwiwan sa ya bugu,amma haka ya tashi ya koma baya,shima a na uku ya fadi ya buga kwankwasan sa ,runtsa idanunsa yayi jin wani zafi ya ziyarce shi.

Da kyar ya tashi ya fara ya kusan rabin wajan ya fadi ya sake buga gwiwansa ,sai daya saki karamin Kara, ya kai kusan 30mins yana abu daya ,Duk ya fita hayyacinsa abunku da farin fata,fatan tayi jajir dashi Dan yaji kiwo awaje daya wa .

Tafiya yake yi yakusan zuwa karshe wajen baifi yayi taku biyu ba yafita,kafansa ya zame ya bugu akansa dan unexpected ya fadi,sai dayayi kara dan bakaramin buguwa yayi ba , tuni jini ya wanke masa fuska.

Karan da ya yine ya janyo hankalin “boss lion “ da yanzu aka turo masa da sako,shiyasa baiga lokacin da Ashman din ya fadi ba .

Mikewa yayi yana tafiya cikin takunsa na kasaita da nutsuwa ,dan fusknsa bai nuna komai ba dan a tamke yake kowani lokaci .

Sai dai shi har cikin zuciyansa yakejin radadi abunda ya saka ashman din ,dan yana balain son yan uwansa,amma san dayake musu bashi zaisa yaki punishing nashiba a duk lokacin daya so.

Yana isa wajan ya samesa har ya suma ,dan ba karamin jini yake zubarwa ba , daukansa yayi chak akan kafadansa,ya fito daga wajan ,anan ya samu sojoji da kuma junaid da uncle tareeq da zuwansu kenan,dan sun zone dan su karbi ATM ,shopping suke son suyi,akan hanyansa na zuwa nanne suka hadu da uncle tareeq suka taho tare.

Zuwansu Kenan sukaga halin da Ashman yake ,dake hanun “boss lion” Hankalinsu ya tashi ganin yanda yake zubar da jini ,ba kaman junaid da tuni ya fashe da kuka,sukabi bayan “boss lion” hanyan clinic suka je ,clinic din yana da girma sosai kaman asibiti dan yafi wani asibitin girma ga kayan aiki available.

Direct wani babban daki ya shiga da Ashman dakin maikyau kaman ba dakin jinya ba , yana shiga ya rufe kofan dan bayasan kukan junaid ya damesa wajen treatment in.

Cikin kware wa da iya aiki ya wanke jinin tare da mishi dressing na wajen ya daure kan da bandage 🤕 ,ya kuma gasa masa jikinsa,yanda idan ya tashi bazai ji wani ciwo sosai ba ,alluran bacci baci ya masa,bazai tashi ba sai nan da 6hrs .

(Tun yana karami wannan burin ummie sa ne ya zama likita,shiyasa bayan ya gam karatun likita ya shiga aikin soja ,cikin kankanin lokaci ya tashi yayi tashe kowa yana sansa amma tsoronsa suke ji har president din da Kansa da baya daukan nonsense aiki yake yi bisa adalci dan baya zalunci,abunda yasa ya kara daukaka har yaje matakin da yake yanzu).


Fitowa yayi daga dakin ,anan ya samu junaid idonsa sunyi Luhu luhu saboda kukan dayasha bakadan ba, a tsaye suke tareda uncle tareeq da uncle Ibrahim.

Cikin sauri junaid ya rungumi “boss lion” tare da sake fashewa da kuka ,bubbuga bayansa “boss lion “ yayi tare da ce masa ,karka damu bawani ciwo sosai bane yaji nanda 6hrs zai tashi kaji.

Gyada Kansa junaid yayi cikin gamduwa da maganan yayan nasa, dan baya karya wannan halinsa ne kuma bayanso a masa, shiyasa kuka yarda dashi.

Tafiya sukayi tare ,har suka koma parts na su kowa ya wuce dakin sa .

____________________________________________✌️


After some hours ♻️


Zaune “boss lion “ yake a gefen gadon da Ashman yake,tare da junaid, uncle Ibrahim, uncle tareeq, suna zaune suna jiran tashin sa dan time yacika daya kamata ace ya tashi,shikam “boss lion “ bai wuce 5mins da zuwansa ba ,anan ya tarar da su ,suna zaune jiran tashinsa.

Bai wuce 5mins ba ya fara motsi da hanun sa alamun zai farka ,cikin sauri junaid ya karaso wajan sa,yayında “boss lion” yake zaune ko alamun motsi bai yiba ,fuskanan a tamke.

A hankali ya fara bude idonsa ,dishi dishi yake gani ,sai dai yana iya jiyo maganan su junaid sama sama” yaya Ashman” ka tashi,ya jikin naka, har dasu uncle tareeq da uncle ibrahim suna masa sannu,gefe uncle ibrahim ya koma yana dariya kasa kasa ,a hankali yace hmmmm yaro yaro ne.

Rufe idonsa yayi da yakara dark ash , sannan ya sake bude wa, sai a lokacin yake ganisu dake ,daya bayan daya yake ganinsu,kafun yafara kokarin mike ya kasa dan jikin yayi tsami, sai lokacin “boss lion “ ya tashi ya mikar dashi da samasa filo a bayansa.

A hankali kaman mai rada yace masa,ya jikin, akwai inda yake masa ciwo ne,cikin sanyi murya yace da sauki ba abunda yake mun ciwo ,kirfin jikinane kawai bai dawo ba, sai kuma ya marairaice tare da ce wa “please “ yaya boss “ am sorry, ba tare da sake ganin Saba yace it’s okey “ya koma ya zauna.

Su junaid da suke wajen babu Wanda yansan mai suke cewa, junaid ne ya sake cewa “ yaya Ashman tun dazu nake ta maka magana kaki kulani ya fada cikin ya shagwaba ya bata rai alamun yayi fushi.

Murmushi da bai shirya bane Ashman ya subuce masa”haba my little brother ai bama haka da kai ko ,ba mai shiga tsakanin mu sai Allah.

Toh ai kaine kaki kulani “ok am sorry,Shikkenan,gyada kai yayi kaman wani yaro .

Tashi boss lion yayi ya fita daga dakin ,dan shi yanada abunyi.

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️






*_💋 SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

🌎 Destiny,Love ❤️ & Romance 💋


Written By AMID ✍️


2024/2025🔥


Bismillah Rahmani Raheem

Paid book ne

Book 1
page 📃 9

______________________________________________✍️

Gombe
Gabukka

Yau ta kama asabar zataje islamiya da yamma,shiyasa ta tashi da sassafe tayi duk aikin data sabayi, ko karya wa batayi ba ta tafi .

Tafiyan hour daya da tayi ta isa g.r.a ,tana shiga gidan ta samu ba kowa ,kitchen ta wuce dan yin abunda ya kawo ta ,cikin kankanin lokaci tayi yam bolls da ferfesun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login