Showing 33001 words to 36000 words out of 42382 words
number 08161857656 Nagode 🙏
2024/2025🔥
Story and written by AMID ✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
Bismillah Rahmani Raheem
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
Page 📃 25
Junaid yana riqe da hanunta daya ,dayan hanun kuma ya janyo ledodin dake bakin kofan lifter.
Shiga cikin lifters “boss lion “yayi batare daya sake kallon inda su junaid da sultana suke ba,dashi ko za’a daura masa gun a kansa bazai iya cewa ga yanda sultana take ba,shi dai kawai yaji mutum a jikinsa kuma da kayan mata,shiyasa kawai ya chass keta da mari,shiga yayi ya wuce ya bar junaid rike da sultana.
Ganin “boss lion”ya tafi ne yasa junaid din sauke ajiyan zuciya,kafun ya saka hanun sa duka biyu ya dauke ya direct dakin ta ya wuce da ita ya kwantar da ita akan gado,ya tsaya yana ganin fuskanta da yayi jaa,ga shatin yasun yaya boss akan fuskanta ,ba karamin tausayi ta bashi ba,dan yasan koshi aka mawa wannan Marin sai haka.
Dakinsa ya wuce ya dauko maganin da zai shafa mata a fuska,suka hadu da yaya Ashman ,Annan yake sanar masa da cewa yaya boss ya mari sultana,jin hakan yasa Ashman cewa”muje na duba ta naga fuskan nata,tare suka wuce dakin,lokacin da Ashman yaga yanda fuskanta harya kumbura sai daya tausaya mata,shi karan kansa ya sani ,duk wanda yasha Marin boss lion Toh akwai matsala.
Junaid ne ya shafa mata maganin a fuskanta,har zasu tafi sai kuma yaya Ashman yace”amma dai ba haka zamu tafi mu barta baka shafa mata ruwa ba,aaa ya Ashman wani shafa ruwa kuma,bayan tayi bacci ,yanzu sai kawai ana zaman lafiya,ince zan shafa mata ruwa,ai sai ta iya Hajja ce wa ma,kallon bakada hankali Ashman yayima junaid” junaid nikam ka koma shaye-shayen ne bamu sani ba”bata rai junaid yayi yace”yanzu tsakani da Allah nayi maka kama da wanda yake shaye-shaye,”yeah tunda ,kana ganin mutum a sume amma kana cewa bacci take yi,ko kuma dai so kakeyi daga suman sai ta wuce can,”
Zare ido junaid yayi yace “wani can zata wuce,kaikam ya Ashman kana fadan Alkhairi mana kokayı shiru,naji yanzu zan sha fa mata ruwan kafun bakinka ya kamata,ya fada da sauri ya shiga toilet ya ibo ruwa a cup ya matso wajan sultana,a hankali ya shafa mata ruwan akan fuskanta ,shiru bata motsa ba,ya sake shafa mata shima shiru bata motsa ba,kawai sai junaid ya fashe da kuka”yanzu ya Ashman meye amfanin irin wannan maganan da kayi,yanzu kasa bakinta ya bita,Shikkenan fah ta rasu,wayyo Allah na shiga uku ba,wayyyo Allah na shiga uku na ,ya Ashman ka cuceni wallahi,Shikkenan one and only sister na ta ,tafi ta barni,wallahi bansan haka mutuwa take da zafi ba,amma dai yaya boss ya cuceni ya kashe mun ita,gaskiya sai Allah yasaka mata,sai munyi shari’a daku,baiwar Allah bataji ba bata gani ba ankashe ta ,kuka yake yi bilhaki yana sumbatu,shikaran kansa ka tambayesa meyace bai sani ba.
Me Ashman zaiyi idan ba dariya ba,dan wallahi yanda junaid yake ta zaginsu yana kuka,ba karamin dariya ya bashi ba ,sai da yayi dariya mai isansa,daya dade bai yi ba ,ya matso wajan junaid ya marairaice fuskan yace”haba junaid sai kace bakasan kaddara ba,lokacin tane yayi , shiyasa ta tafi,dama Allah yayi ita bamai nisan kwana bace,”tabdijam sai wallahi ba zaku kashe ya a banza ba ,saina dauka mata fansa,sai wani hawayen sharrr.
In serious face ,Sake dafa ka fadan junaid yayi yace haba junaid sai kace marar wayo wa yace maka mutuwa tayi kai da kanka fa kace ya mutu,ganin babu alamun wasa a maganansa ne yasa junaid goge hawayensa yace da gaske bata mutu ba”gyada masa kai ashman yayi”Toh ai kaine ka kasa nutsuwa ka gane cewa tun ruwan farko daka shafa mata ta farfado,dan yasun hanunta sun dan motsa sai kuma bacci ya dauke ta,kazo ka wani sani a gaba kana ta mun kuka har dacewa saika dauka mata fansa,kan abunda muka mata,kenan sawa zakayi a daure yaya boss ni kuma a kaini magarkama ko,ai kaman a kunen yaya boss cewa ka fifita bare akan sa.
Ai ba shiri wasu sabin hawayen suka fara zobowa junaid jin za’a fadawa yaya boss abunda ya fada ,kuma bai masan ya fada hakan ba”wai yanzu yaya Ashman saika fada masa ?,haba dan Allah nifah wallahi ban masan na fada hakan ba ,dan Allah karka fada masa ,kayi hakuri subutan baki,amma banmasan na fada hakan ba,kaji please ya Ashman dina.
Uhmmm junaid har dayimun dadin baki kuma yanzu,ba dazun nan ka gama zagi na ba ko ba haka ba”Toh ai na baka hakuri ko,Toh Shikkenan na hakura amma duk lokacin da ka kuskura ka sake irin wannan maganan ba zata tsaya iya muka dai ba,kaji ko’eh insha Allah ma bazan sake ba,”Allah yasa.
Tashi mu tafi ,ka barta tayi bacci ko zata samu relief din abunda yake damun ta ,tashi junaid yayi salun alun suka fita daga dakin tare da kashi mata ruta,suka rufe kofan.
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
2024/2025🔥
Story and written by AMID ✍
️ *_💋SIRRIN DAKE BOYE❤️_*
( The hidden secret 🌹)
Page 📃 26
🦋🦋🦋🦋🦋🦋
9:30pm in USA 🇺🇸
Zaune yake a gefen gadonsa,jikinsa sanye da boxers amma bai damesa sosai ba ,singlet ne a jikinsa duk da kuwa sanyin da akeyi,coffee ne a gabansa ,yana aiki a cikin system,hankalinsa gaba daya yanakan system din danabu yakeyi mai muhimmanci.
Kaman daga sama ya fara jin ihun sultana,ciki gaba da abunda yake yi yayi,duk da kuwa bayason hayaniya kwata kwata,amma kam wanda ake kara wa ihu dan ihu takeyi tsakani da Allah,cikin bacin rai ya mike dan yasan junaid da Ashman basanan,gashi shikuma basan hayaniya .
Mike wa yayi ya fara tafiya anutse ga jikinsan a murde irin na wanda yayi gym harya gaji,dansen hanunsa ma kadai abun kallo ne,cikin tayiyan kasaita ya wuce dakin daya San zai ganta ,dan ya sawa ransa sai yaci uban yarinyar nan kafun zasu daidai ta.
Yana zuwa ya shiga cikin dakin babu excuse,a kwance ya sameta ta dukun kunu a cikin bargo jikinta sai kar karwa yake yi dan tunda ta tashi ta tuno abunda ya faru ta tsorata har ta fita a hayacin,ga radadain da fuskanta yake mata,kaman an kona fuskan takeji saboda radadi ,dan ba wanda zaisha marin boss lion ya tashi zamm wannan karyane.
Matsowa yayi jikin gadon dan cikin kaniyanta,yaye bargon yayi ,hanu yakai zai sake wanke ta da mari aganinsa wanda yayi mata dazu bai isheta bane.
Har yakai zai mareta sai a lokacin ya fara ganin fuskanta duk da marin da tasha hakan bai hana ganin kyakyawan fuskanta ba,ga shatin marin da yayi mata ya kum bura fuskan ,lips nata sai kyarma yake yi gashi yayi wani irin dark pink dinan,wanda duk wani lafiyayen namiji,dakyar idan sha’awansa bata motsa ba.
Duk kallonan within some seconds ya mata ya dauke kansa,jiyayi bazai iya yi mata abunda yayi niya ,duk dadai shi karan kansa yayi mamakin haka,danshi ba ruwansa duk wanda yayi masa laifi hukuntasa yakeyi.
Sultana kam tunda ya yaye mata bargo,ta kasa daga kanta dan gani takeyi kaman sake dukanta sa’ayi koma wanene,dan ba karamin tsorata tayi ba,inda wata ce ma sai ta iya haukace wama,idonta a rufe yake ruf .
Dressing mirror chair ya janyo ya ajiye a gabanta ,ya zauna tare da yin crossing na legs nashi,kafun ya dubeta cikin kara hade fuska yace”hey open your eyes before I give you another slap,jin hakan ba karamin tayar wa sultana hankali yayi ba jin muryan mutumin dazu daya mare ta ,jikinta har rawa yake yi wajan tashi dan bata kaunan ya sake mata wani dukan,zama tayi taga yin da yake zaune ba wani rata sosai a tsakanin su .
Dagowa tayi a hankali gudun kar tayi laifi,kalonsa tayi da blue eyes nata masu daukan hankali,zuciyanta sai daya bada wani irin dummm,dummmm,dummmm,gani kyakyawa mutum a gabanta da zata iya cewa tunda aka haifeta bata taba ganin kyakyawa irinsa ba,batasan ta shagala da ganin ba,har ta mantama da cewa shine ya mareta.
Gyaran murya yayi”ganin yanda ta wani kafe sa da ido sai kace mayya,”idan na sake kamaki kina ganina saina cire miki idanu,ki bari na sake ganin kina kallo na ki gani,idan bakisha mamaki ba,numfashi yaja dan wallahi daure wa kawai yayi yake mata magana,dan miskilancin bazai barsa ba.
“ sannan nan ba gidan mahaukata bane ,idan ke mahaukaciya ce Toh tun wuri ki fada mana mukai ki gidan mahaukata,idan ba haukaba kawai kisa mutane a gaba kin ihu,last warning nake baki ,kuma kakı sake bari ko a hanyane mu hadu ranki zai baci,mikewa yayi ya fice daga daki.
Sultana kam ganinsa ba karamin tafiya yayi da imanin ta ba ,yanda ta gansan nan,tanajin ko kashe ta zaiyi sai ta kalle sa,ji tayi ma duk haushi marinta da yayi ya tafi,idan ya tuna kyakyawan fuskansa sai tayi murmushi,dan ba karamin burgeta yayi ba.
A haka ya dawo ya sameta ,a yanda take,zama yayi akan kujeran tare da Mika mata maganin da zata shafa a fuskanta,hanunta har kyarma yakeyi wajan karba ,ko kallon nasa ma ta kasa tsayawa tayi Dan mugun kwarjinine dashi na bala’i ,bude murfin roban tayi ,dan ta gane maganin meye ne ajiki akwai hotan dake nuna nakuburin waje ko radadin ciwo,shafawa tayi a hankali ta kasa dagowa ta kalesa,damashi kam boss lion amfani yakeyi da wayansa,dan tun kallon farko da yayi mata bai sake ba,dan wannan ba halinsa bane.
Tana gama shafawa ta mika masa roban,amma sai taga bai karba bama,ganin bai kulata bane yasa ta dago da idonta a hankali irin na munafukan nan ya kalesa,sai alokacin ya jiyo hada ido ,harara ya wulla mata tare da sake tamke fuskansa kaman an aiko Masada sakon mutuwa “ba tareda yace mata uppan ba dan yan miskilancin sun matso ,fice wa yayi daga daki zuciyansa nayi masa zafi dan ganin yake yi wannan abun da ta masa ma ai rainine dan haka gobe,saita bar masa gidansa tunda ba tare suka siya ba.
Lumshe idonta tayi tana shakan daddadan turaren dakesa mutum ko ransa ya baci indai ya shaka to wannan perfume din to tuni hankalinsa zai kwanta ,dan ko Ina na dakin kamshin turarensa yakeyi kaman anan ya fesa.
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
2024/2025🔥
Story and written by AMID ✍️
*_💋SIRRIN DAKE BOYE❤️_*
( The hidden secret 🌹)
Page 27
________________________________________✍️
Kwance take a falo,jikinta sanye da dogon riga yar kanti peach color mai design na roses a jiki kanta sanye da peach veil bakaramin kyau kayan ya mata ba daidai jikinta ,fuskanta ba wani kwaliya tayi ba power,kwalli,dakuma lipsticks,ga gashin tanan yasha gyara , ta gaban kaman wanda ta saka jel ,sai dai muce Tabarakallah Masha Allah,dan Allah yayi halita,junaid ne da kansa ya nuna mata yanda ake amfanin da abubuwan da suka siyo,bayan yayi mata ya jiki,kuma yayi mamaki ganin fuskanta ,ba kumburin dayayi jiya ,fuskanta fess kaman ba jiya tasha mazga ba,dan maganin da tasha ,sha yanzu mafani yanzu.
Zaman dakin ne ya isheta shiyasa ta dawo falo bayan ta gama break fast,bakowa dan duk kowa ya kama harkan gabansa, junaid ya tafi school amma tasan yanzu haka ya kusan dawowa shiyake ibe mata kewa,mikewa tayi da sauri tuno da maganin da ya bata,tabass kaman bata ganshi,a zuciyanta tace”tab yau na shiga uku agun mugun mutumin nan gwanda na shi naje naduba tukafu ya karyani a gidan nan,da gudu ta nufi elevator ta dan hawa na hudu ,sai kuwa ya budu,kawai shege wa tayi da sauri ,hankalinta ma baya jikinta jikawai tayi ta bugu da mutum.
Tariga da tasan wata buge ,ai take jikinta ya fara rawa ganin yanda ta bugesa,kuma ta buge wayansa,a kasa ,dagowa tayi ta kallesa kaman munafuka,saikuma taga ba’ita yake kallo ba wayan data buge masa yake kallo,dan jira yakeyi yaga zata mika masa kokuwa ciga da ganinsa zatayi”hanunta rawa yake yi kaman a jona mata igiyan lantarki ,mika masa wayan tayi yiyayi kaman baisan tanayi ba ,sai kuma can ya dago idansa ya kali yawan ,ba abunda ya sameta dan ba normal waya bace irinta kowa ,musaman ya bada a company aka masa ,ba wanda yake rike irinta,kuma shi kadai zai iya sarrafata.
Hanuntan yabi da kallo ganin yanda suke kerma ga kanta a sunkuye sai ruwan hawaye takeyi babu kakkaugawa,karban wayansa yayi a zuciyansa ya”ahh yarinya dakin bar kukannan kin tanada sa a inda zaifi miki amfani dan wallahi babu abunda zai hana yau bai hukuntata ba,shifa wani lokaci har mamamakin tsoronta yakeyi,mutum abu kadan tsorata kam farar kura,sake tamke fuskansa yayi sosai ,yanufi hanyan fita tare da cewa “ki biyoni,iya abunda ya iya fada kenan,jin hakan ne yasa sultana sake fashe wa da kuka dan wallahi kana ganin sa kasan ba wasa a maganan nan ubanta zaici.
Sum sum tabi bayansa ta koma main falon kan wani hadaden kujera ya zauna da ba wanda ya isa yazauna idan bashi ba yayi crossing na legs nashi ko ina fess fess a gyare sai kamshi yakeyi,”acan kasan cafet ta yi Neil down,shiru kusan 10 minute bai ce da ita komai ba ,sai daya bushe iska dan kanshi kafun kafun yace” up and down zakiya babu adadi, harsai idan nice nace ya isa idan kika kuskura kika tsaya zangani,a duk inda nake,so warn your self,one single mistake…..I will kill the hell out of you, so start right now”da sauri ta mike ta fara yin,guda biyar tayi sai da taji kafanta sun fara rikewa dan ba irin wannan wahalan ta saba ba,ta cikin ye taji haushi kare a bayan ta.
Nandanan jikin ta ya fara rawa fiye da nada dan wallahi ba karamin tsoran kare takeyi ba ,ganin wani zudumeme kare tayi irina turawa katı dashi ga gashi sosai a jikinsa yanda kasan karen brolers haka yake,irin ne wayanda akayi musu training sosai ,ba abunda zaka ce su musu baza suyi ba,wajan boss lion yaje ya fada jikinsa yanata tsale alamun yaji dadin haduwa da boss lion dan da kullum suna tare wani lokacin ma tare suke kwana a daki,danshi Rainon boss lion ne,saukar shiyayi daga jikinsa yace” lucky kakula kasa ka yarda ta huta kokadan,idan ta tsaya kuma just bite her,understand,jijiga jikinsa yayi alamun ya gane tare dayin haushi,ganin hakan ne yasa boss lion ficewa daga falon yabar sultana da lucky tare abunsu.
Sultana kam tun da taga lucky ji duniyan gaba daya bayayi mata dadi ,numfashi ma dakyar take iya fitar wa dan ba karamin tsorata tayi ba jikinta kaman a tada jen sai rawa yakeyi ,cigaba dayi tayi dan wallahi tasan idan batayi bama zai sanine dan tasan gidanshi ne,yanada iko akan komai,idan batabi bama ita zata sha wiya,Lu koma dayake shima dan iskane ne sai ya wani zauna a waje daya yanata kallonta,duk dadai sa’an ta daya bai matso inda take ba ,shiyasa ta iya cigaba dayi har zuwa lokacin da boss lion zai ce ya’isa.
______________________________________________🥶
AFTER 40 MINUTES 🥹
Tun tana iyayi har abun ya gagara ,numfashita yana bara zanan daukewa,cinyanta yayi tsamin bala’i ,har ta fara dana sanin zuwa gidan,dan idai haka akeyi kullum to bada ita za’ayi ba,numfashintane ya dauke dipppp,jikinta ya saki,ya fadi akan carpet din,kafunta fadi wani abun al’ajabi sai ga lucky ya je ya tsaya a wajan ,cikin da bara irin na wannan Karen ya daga hanayensa sa sama wajan tareta dan karta fadi direct zataji ciwo,faduwa tayi a jikinsa kafun ya kwanta da jikinsa ya sauketa a hankali,dan irinsu lucky kawai ka gansu ka barsu dan ba karamin horo aka basu ba.
Zagaye ya cigaba dayi a wajan ,suna haka saiga junaid ya shigo falon bakinsa dauke da sallama ,shiga yayi kwata kwata hankalinsa baikai kansu sultana ba yana wani waje ,har ya kusa isa jiki elevator,kaman da sama yaga lucky a gabansa ,Allah idan yace bai tsorata ba karya yake kawai dai ya mazge ne ,ganin lucky ne ya sashi Jan tsakin,ya hayayyako masa”kai wallahi lucky anyi dan iska ,wato ka dawo dole kazo mun oyoyo,Toh bari kaji kamun haukan anan kagani jikin ka ya gaya maka.
Haushi lucky yayi masa yana kokarin nuna masa inda sultana take a kwance amma Ina bai gane ba,haya juya zai tafi,aikuwa yaja rigan sanyin dake jikin junaid ,yana haushi ya janyosa inda sultana take,ai kuwa sai idonsa ya kyallara masa inda sultana take a kwance kamar matacciya,ai baisan lokacin da yayi wufff ya isa inda ya gata ba,ganin yanda idanunta suka kumbura saboda