Showing 21001 words to 24000 words out of 42382 words
ya fada cikin nishadi.
Ka ajeye wannan a kanka “kaganin nan ta fada tana nuna kanta tace”wallahi nafi karfin ka ,irinku ne fa ya kamata ace yanzu ma kuna gidan yari,insha Allah “sai gani sai hange ,hangen ma idan kasamu kenan “saboda bakada kunya harni zakazo kanamun maganan banza “toh bari kaji karka sake zuwa gidanan da sunan kazo waje na ,dan zan maka rashin mutuci wallahi.
Ko akan hanya ka ga mai kamata ka canja hanya dan nikam bazan dauki rainin hankali ba “Kaje can ka karata da shaye-Shayen ka ,kaji na fada maka .
Tana karasa fada bata sauraresa ba tayi koma wa ta gida ,ta barsa sai masifa yaki yi kaman ya ara baki.
___________________________________________✍️
Abuja,Nigeria
Kwance take akan gado sai juyi takeyi takasa bacci ,gashi gobe da wuri zata tashi dan zasu raka ya alameen airport dan hutunsa har ya kare,tana jin ba dadi cikin ranta zai tafi dan duk abunda yake mata tanason yayanta kuma shima yana sonta,kawai dai muddin suka hadune sai sunyi fada koda kuwa abun bai taka kara ya karya bane.
Taya ma za’a ce basa san junansu bayan suna uwa daya uba daya .
Cikin ikon Allah bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba .
Washe gari
Ta danso ta nakara sallan asuba dan bata samu bacci da wuri ba jiya ,Allah ya sota ma yau weekend ne ,tashi tayi tashiga toilet tayi alwala tayi sallah .
Shiyawa tayi cikin dogon rigan atampha nevy blue and ash dinkin irin fitted din nan ne daidai Jikinta da akwai shape kam ba kaifi tayi daurinta mai kyau ,Masha Allah tayi kyau kaman ka saceta ka gudu.
Daukan ash gyale tayi ta fito dashi a hanun ta dan jirginsa 7:00am zai tashi gashi yanzu har 6:33am tayi ,,a falon kasa ta samesa da shida Ammi dan yanzu macewa yake “wai Ammi yariyar nan bazata fito bane saita batamun lokaci .
Cikin sauri tace ganinan yaya ina shirya wani,batar da yaganta ba yace ki dakko mun akwatina a daki ,kisame mu a mota,ta amsa da toh ,shikuma ya wuce parking space.
Gurin Ammi taje tace,”good morning Ammi “cikin kulawa ammi tace” morning daughter “ kintashi lafiya”,lafiya kalau ammi ,toh kije ki daukko masa abunda ya aike ki Nima ganinan zuwa,idan yaso saiki samemu a parking space”kinji? Eh baji ammi.
Dakinsa ta wuce taga karamin a kwantin a kan gado ta daukko ta fito ta samu har ammi ta wuce,itama sai ta fita .
Ta samesu a cikin motan ammi tana baya ,ta bude motan tace”yaya alameen ka budemun boot in din na saka akwatin,bude wa yayi batare da yace komai ,ta bude ta saka yashigo sai a lokacin yaga irin kayan data saka dan tayi mishi kyau amma yashi zafi yanda ammi bata mata magana akan kayan ba ta fito a haka kamar arniya.
Shiga tayi yaja mota da gudu har Ammi tana cewa”sannu alameen harka gaji da ganin mu kenan kakeso ka kashemu,cikin kwantar da murya yace ammi kiyi hakuri baza’a sake ba.
A haka har suka isa Nnamdi Azikiwe International Airport sauka sukayi dan har an fara kiran passengers dan sunyi latti ,daukan akwatinsa suka yi sallama da ammi “alameen dan Allah akula banda kula abokan banza ,ka tsaya kayi abunda ya kaika kaji,,Toh Insha Allah “Yauwa Allah yatsare ya bada abunda akaje nema ,,saduwan alkhairi “Ameen ya amsa.
Shukrah ma tace yaya Allah ya kiyaye hanya sai yaushe zaka dawo “hararanta yayi yace”Ameen amma dai nasan dama Allah Allah kikeyi na tafi dan kina ganin kaman ta kura miki nake ,yanzu saboda Allah kiga irin kayan da kika saka tsa kani da Allah kin kyautawa kanki kenan ,yayi kasa da murya yace please koda banan karki sake sa irin wayanan kaya koda a gidane dan bakisan wa zai shigo “kinji?
Eh yaya alameen insha Allah bazan sake ba “good sai na dawo kuma badda rashin ji please bye “Insha Allah tace tare da daga masa hannu ya wuce.
Ammi kam tana cikin mota batasan me suke fada ba ,sai da ya tafi kafun ta fito tawuce driver site ta zauna ,shukrah tana zauna a kujeran mai zaman banza ammi ta ja motan suka wuce gida.
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
Bismillah Rahmani Raheem
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
page 📃 17
Yau saura kwana daya daurin aurenta damuwa da rashin mafita ne ga kuma rashin cin abinci ne ya sata agaba har tayi wani uban rama tayi wani fayyaw,sai haske data kara tass da ita kaman jini ya fito,ga kashin wiyan daya fito mata saboda rama.
Tayi kukan ,tayi kukan har ta godewa Allah,gashi ba mai kulata a gidan ,dan ko zulaihat da take kulata yanzu ta daina
,abun ba karamin damunta yake yi ba “tariga da ta yake shara datake ganin shi zai fisheta .
Habiba ce ta shigo daki ba sallama ba komai ,cikin rangwada da iyeyi tace,sai ki tashi kije babba yana kiranki munafuka aurene dai sai anyi sai dai bakin ciki ya kashe ki ,dan mu kokin mutu ba’abun daya damenu,tan tarasa fada tafice daga dakin tare da jan dogon tsaki tabar dakin.
Mikewa tayi ta dauki hijab nata dake gefenta tasaka ta fito daga saki,gidan shaw ba kowa ,kumawai a haka gobe ne daurin auren .
A kofan dakinsa ta tsaya tayi sallama kafun ya bata izinin shiga ciki ,shiga rayi ta samesa zaune akan taburman dake shimfide a tsakiyan dakin,ta durkusa har kasa ta gaishe shi.
Bayabo ba fallasa ya amsa,tsayawa yayi kawai yana ganin ta yana saka wani abu a ransa,danshi wallahi bai tsaneta ba kawai dai indai zai ganta ne,zaiji kwata kwata baya dinta a kusa dashi.
Gyara murya yayi yace”ga wannan kayan,gobe kishirya dan na daurin aure ne,idan yaso saiki saka wannan din,dan shikadai na samu na iya miki ,dan babu kudi a wajena .
Cikin jin dadin koba komai dai yau ya kulata irin na shekarun baya ,daga bayane ya daina kulata,kuma tariga da tasan wannan ba yin kansa bane aikin innah ne,shiyasa bata wani jin zafin abunda yake mata,cikin sanyi murya tace”abba Nagode hakanma kayi kokari,Allah ya saka da alheri ya biya maka da gidan aljanna.
Cikin jin ba dadi idan ya tuna abunda yayta mata yace”Ameen nagode da irin biyayyan da kike nuna mun sabanin sauran yan uwanki”Allah ya miki Albarka a duk inda zaki tsinci kanki,ki kara mutuncin ki dan nasa kına iya bakin kokariki amma dai ki kara kinji.
Muryanta yana rawa irin wanda yake shirin fashe wa da kuka tace”Ameen abba Insha Allah bazan baka kunya ba,bata karsa ba hawayen datake rikewa ya zuba mata a kan fuskanta,tayi saurin sharewa dan kar abba ya gani,amma abunda bata saniba yariga da yagani yace”kiyi hakuri nasan na kasa sauke nauyi daya rataya a kaina wajan zaba miki abokin rayuwa na gari,ki yafemun nima bada son raina hakan zai faru ba ,bayanda na iya ne.
Yaken dole sultana tayi tace “bakomai abba ai kai mahaifine a gareni,ni mai biyayya ce a gareka,dan haka karkasa komai a ranka,jiyayi an yaye masa rabin abunda yake masa nauyi a zuciya”Shikkenan zaki iya tafiya .
Toh tace tare damike wa tafita daga dakin,ta koma dakinsu daya har lokacin sallan azahar yayi, alwala tayi ta koma dakinsu tayi sallah ,sai data dade a sujjada tana kaiwa Allah kukanta “ya Allah na rokeka kanema mun mafita,ya Allah kaga zuciyar wannan baiwar taka batasan wannan auren “ta dade tana addu’a harda hawayenta ta daga hannunta sama ta rikoki Allah .
_______________________________________________🙏
AFTER SOME HOURS 🤧
Bayan isha,
Kwance take akan gado bacci ya dauketa ba tareda ta shirya ba,soboda kukan da tasha ga rashin baccin dare ishashe da bata samu tanayi saboda damuwa, ta dukun kune a cikin hijabi tana rawan sanyi ,alaman zazzabi ne ya rufe ta.
Yarone yashigo cikin gidan ,lokacin ina suna zaune akan taburma dan kullum da daddare a waje suke zama hira ,wani lokacin ,idan da zafi a waje suke kwana amma badda sultana komin sanyi haka komin zafi a cikin daki take kwana.
Yaron yace”ana sallama wai da sultana a waje, tane baki innah tayi tace “inji waye ,”ban sani bazai amma bari inje na tambaya, bayan 1 minutes ya dawo yace “cewa yayi garbati ne”toh kace masa tana zuwa yanzu” Uhmmm yace ya fita daga gidan.
Innah ta kali zulaihat tace”Kira wannan munafuka kice mata tazo tawuce mijinta yana kiranta a waje,kuma saura ta bata masa lokaci jikinta ya gaya mata”cikin zumburo baki zulaihat tace”nidai innah ba inda zanje dan nii bana mata magana,dan nafi karfin ta class namu ma ba daya bane,takarasa maganan tare da jan tsaki.
Ba abunda ina tace ,kafun ta kalli deeje dake latsa waya tace toh ke deeje kije ki mata magana “deeje ta bata rai tace”innah har zulaihat zata ce miki ta fi karfin ta bare kumani ai basa’ar ta bace” hmmm bare kumani Habiba ta karbe zancen alamun tana ba tashi zatayi ba,cikin washe baki innah tace Yauwa yan albarka ,dama abunda na dade nake son fada muku cewa ba sa’arku bace dan kunfita komai”ba wanda ya kuta a cikinsu kowa harkan gabansa yakeyi,ganin hakan yasa tamike tace”bari naje na fito da ita ,ta fada tare da wuce dakinsu SULTANA.
Tana zuwa ta ganta kwace a kan gado cikin masifa ta İsa kan SULTANA dake rawan sanyi tace”munafuka zaki tashe kije ana kiranki na ko kokuma ranki inyayi dubu to sai ya baci, baiwar duk bataji abunda ina take fada ba,bacci nata yayi nauyi.
Ganin bata kulata ba yasa innah jan kwafa ta fita tabar dakin ,bayan 2 minute sai gata da roba a hannu na ruwan da suka shanya dan yayi sanyi,tana zuwa batayi wata wata ba ta juye mata ruwan gaba daya a jikinta ,gashi ruwan yanada sanyi.
A firgice SULTANA ta tashi tana fadan”inalillahi wa’inna ilaihir-raji’un,,Allahumma ajirni fi musibati, bakinta kawai ta iya fada,ta mike daga kwancen da take ,tabude idonta da sukayi jaah kuma sukayi mata nauyi akan innah dake ta huci kaman zaki.
Zaki tashi ne ,kokuwa tsayawa zakiyi kina kallo na da mayun idanunki ,a hankali ta mike da harwani jiri jiri take ji,”ki wuce kije kin bar bawan Allah a’a waje ,tana kara fada ta fita daga daki.
Cikin sanyin jiki da kuma zazzabin dake damunta sosai ta cire kayan da ya jike ta saka wani materials na dogon riga,ta tacan ja hijab ta fita daga dakin dan har yanzu jikinta rawa yake yi ,wuce su tayi ba tare da ta kalli inda suke ba.
Tana fita ,sai kuma bata ga kowa ba layin ba mutum ko daya a waje ,juyawa tayi zata koma taji an danneta an shaqa mata abu a hanci,daganan bata sake sanin inda kanta yake ba.
Mutumin da ya shaqa mata abun ne ya dauke ta ya kaita har cikin mota,ya saka ta a ciki yaja motarsa ,gashi bakaken kayane a jikinsa .
(Ohhh jama’a ina za’akai mana sultana baiwar Allah,daga wannan jarabawan sai wancan)
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋
2024/2025🔥
Written by AMID ✍️
Bismillah Rahmani Raheem
Follow this link to join my WhatsApp group:
Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏
page 📃 18
Tafiya sukayi mai nisa,tafiyan kwana daya ,kafun ta farka daga suman da tayi saboda chamical in da suka shaka mata,
Zazzafan zazzabi ne daya rufeta.
Tashi tayi ta zauna da kyar,abunda ya faru jiya daddare ne ya dawo mata yasa cikin sauri ta fara dube dube,ba kowa daga ita sai mai driving na motan da batasan kowaye ba ,ga yunwa takeji kaman da ta mutu.
A hankali ta isa jikin murfin motan,ta murda kuma bai bude ba,hakan da tayi ne ya ankarar da wanda yake driving akan ta tashi kenan,bai kula taba saida suka samu wajan siyar da abu ya tsaya ya siya ya koma cikin motan.
Kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciya dan,ba’iya magana zatayi ba,batada karfin yin magana,ji takeyi kaman ta kurman ce ,zata iya bude baki amma bazata iya magana ba sai dai tabika da ido.
Mika mata ledan akayi batare da taga fuskansa ba,da sauri ta karba dan Yunwa take ji,bude ledan ,fried rice with chicken ne a ciki ,Bismillah tayi a zuciyanta ta fara ci ,tacı fiye da rabi kafun taji zuciyanta yana tashi,ta bubaga masa kujera ,juyowa yayi yana ganinta ya gane me take nufi yasa ya bude mata murfin motan ta fito”tana fitowa kuwa ta fara amai kaman an aikota ,ruwa ya Mika mata ta wanke bakinta,suka koma cikin motan ,suka cigaba da tafiya.
Tafiyan hour 3 suka kara kafun suka shigo cikin kasar niger 🇳🇪 direct airport ya wuce da ita,a lokacin karfe 7 na safe a kasar niger,Mika mata passportyayi, batare da musu ba ta karba ,ji takeyi kaman asiri yayi mata ,bata iya yi masa musu.
7:30am jirgin zai tashi zuwa wani kasar,time yana cika,aka fara kiran passengers suna shiga ,waje daya suka zauna tare da wanda ya dakkota a mota,a gefen site nasa ta zauna.
Tafiya 13hrs 42 minutes sukayi kafun suka isah USA 🇺🇸 ,bayan sunyi landing passenger suka sauka ,taxi ya tara musu,suka shiga ,SULTANA abun har yayi mata yawa ga zazzabi ,damuwa,rashin ma fita,gashi gari sanyi kaman ka daskare.
A wani gida suka tsaya mai girma ginin turawa,suka shiga ,yan matane da samari kala kala,kowa da kalan shigan dake jikinsa ,mazan wasu da three quater,wasu kuma dogon wando jeans,matan kuma mini skirt da riga iya cibiya ko boom shot,bra and pant,kowadai da irin shigan da yayi,alama dai gidan karuwai ne.
Shiga cikin wani falo mai kyau sukayi,a Kwai maza da yawa aciki ,sai mutum daya dake zaune akan kujera ya juya baya,suku ma sauran a tsaye suke wasu kuma a zaune akan kujeran falon.
Tunda suka shiga jikinta ya fara rawa kaman mazari,ganin wanda batayi tsammani ba”sai yanzu ta samu ta iya furta “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”kafanta ya gagara daukanta ji takeyi dama ta mutu kowa ma ya huta.
Mikewa wanda da ta gani yayi ,ya matso har inda take ba kowa bane face JABIR sanye da three quarter da bai kai gwaiwansa ba, wani askin yan iska yayi tare da die hair sa zuwa red,yellow,green ,ga wasu sarka a wuyansa kaman kafuri,kana ganinsa kaga tantirin dan iska.
Tsugunnawa yayi a gabanta tare da cewa “hey baby,yau ina jijji dakan naki yake ,dama na fada miki dan halaq kafasa,kuma abunda kike boyewan ma muma sai mun dan dana munji, tare da abokan harka ta”koba haka ba guys”
Yes jab ,mikewa yayi wakoma inda yake zaune Dazu ,ya dauki telephone in dake falo yakira waya banji mai yace ba “ko one minute ba’ayi ba saiga wata jigegiyar mata baturiya tashi go cikin falo.
Direct inda take matar ta nufa tace “tashi muje”ba musu sultana ta tashi tana sharar kwalla dake zobo mata kaman famfo,bata taba tsammanin tsanan da jabir ya mata yakai haka ba ,kawai saboda san zuciya irin nasa yasa ya dakko ta daga gidan ubanta ya kawota gidan karuwai.
Wallahi kozasu kashe bazata taba basu abunda suke soba,wani part matar tanufa da ita ,duk yan matane a part din yawanci daga su sai pant,da bra ne a jikin su.
Tunda suka shigo cikin falon yan mata suke mata kallan raini,daga karshe ma da abun ya isheta ta sunkuyar da kanta ,bata sake kallon kowa ba har suka shiga wani daki yan mata uku ne a dakin,gado hudu ne a dakin nuna mata gadon da ba kowa tayi tace”wannan shine dakinku ga gadonki”cikin sanyi murya SULTANA tace toh ,nemi waje ta zauna dan jiri takeji anytime zata iya faduwa.
Abinci matar ta fita ta kowo mata mai rai da lafiya ,kara tayi taci amma duk da haka saida tayi amai,ba wanda ya kulata a cikin yan matan dake dakin kowa harkan gabansu sukeyi.
Wanke bakinta tayi kafun ta fito daga toilet in ya kwanta akan gadon da wancan matar ta nuna mata sai rawanan sanyi take,zazzabi ne ya take rufeta mai bala’in zafi “Tana blanket in data gani akan gadon taru fu.
________________________________________________✍️
Yau kwannan ta biyu za zuwa, jikinta yayi tsanani,gashi babu wanda ya taba kulata a cikinsu ,sun hade kansu basa mata magana,abun ta kaicin ma”wani lokacin sai dai taji gurnanin su da ihunsu,idan suna neman junan su wato lesbian ,yanzu kamma hawayenta sun kafe idanunta sun kumbura suntum .
A na kawo mata abinci,ko taci sai tayi amansa,ta rame sosai ,sai haske kawai da take yi.tunda aka kawo ta bata sake haduwa da jabir ba .
Damuwanta shine yanda zata samu hanyan guduwa daga gidan,dan ta tabbatar idan aka kamasu,ba wanda zaice badda ita a cikin karuwannan.
Akwai wata black beauty a dakin nasu , ba