Showing 12001 words to 15000 words out of 42382 words

Chapter 5 - Sirrin Dake Boye Book 1 Hausa Novel Complete

Amid   

20 Dec 2024

283

kifi tare da souce.

Dining takai ta jerasu,dan har lokacin babu Wanda ya fito ,masu aikine kawai suke aikinsu , koma wa tayi kitchen daura abincin Rana ,jallof rice with coslow take son yi.

Bayan ten 10mins taji maganan mommy tanata masifa” wai Ina yarinyar nan takene batazo tayi saving namu ba,ko so takeyi ni na tashi nayi saving abincin”cikin sauri ta fito daga kitchen din tanufi dining area ,anan ta tarar dukansu suna zaune amma banda Zainab,dan yau weekend ne basa zuwa school.

Gaishe dasu tayi cikin sanyi muryanta mai dadin sauraro,amsa wa sukayi amma banda mommy dan ciki ciki ta amsa yanda ba kowa ne zai san ta amsa ba.

Saving nasu tayi cikin nutsuwan da a jininta yake ,bayan ta gama zata koma kitchen taji muryan mommy “ki zuba abinci ki kaiwa zainab dan batajin dadi,ta fada hakane saboda idon daddy a waje shiya tayi maganan da ladabi.

Toh tace tare da zubawa ta daura akan Trey,ta dauka ta wuce dakin zainab dashi ,knocking tayi amma ba ayi responding back sai data sake wajan sau uku kafun taji ance yes ,shiga tayi bakinta dauke da sallama .

(Yan uwa ku kula dayin sallama a duk inda zuaku shiga koda kuwa kasan babu kowa agurin “kuma wajibi ne ka amsa sallama muddin kai musulmi ne dan haka akiya ye a yawaita yin sallama dakuma amsa wa, mun manta da zantukan” annabi Muhammad (s.w.a) yace karami shi zai fatawa babba salama ,Wanda yake kan abun hawa shi zaima Wanda yake tafe sallama “kuma annabi (s.w.a) ya kara da cewa mai rowa shine Wanda baya wa mutane sallama
*Assalamu Alaikum [lada 10]
*Assalamu alaikum warahmatullah [lada 20]
*Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatihu [lada 30]
“ Allah ya bamu ikon amfani dashi “ Ameen)

A kan gado ta ganta ,garau babu alamun rashin lafiya a tattare da ita , jikinta sanye da kayan bacci ,da kusan komai na jikinta Ana gani, a hakan dan tana da kyau sura.

Ajiye Trey tayi akan bed side drawer,ta juya zata tafi ji kawai tayi an fisgo ta , saura kadan ta fadi dan unexpected ne.

“Ke wave irin jakace ,ni kike tunanin zan matso da trey din,kuma idan na gama ci ni kikeso na fitar dashi,,dan haka ki tsaya daga can wajan kijirani har sai na gama cin abinci ki fitar da plate din.

Ran SULTANA in yayi dubu to ya baci dan ta tsani wulaqanci dan bata dauka, cikin muryan bacin rai ta fara magana “ wallahi ki iya bakin ki , ce miki akayi dan Muna aiki a gidan ku ,shine zai baki daman yi mana abunda kika ga dama ,toh bari kiji “idan bakida hankali ne toh kije ki nemi hankali,dan na tabbatar harda duhun jahilci ke damun ki, da rashin sanin darajan dan adam ,Allah daya halicce ki shiya halicce mu, bawai dan yafi sanku bane yayi ku masu kudi,ba kuma dan baya San mu bane yayi mu talakawa ,dan haka kishiga hankalin ki ,idan ba haka zan iya miki abunda bazaki ji dadi ba.

Zainab kam tsaya wa tayi tana gani ta ,sai kuma ta kwashe da dariya” hmmm Lallai biri yay kama da mutum,dama nasan badan Allah kike yi shiru ba ,kinayi Abu sum sum irin na Muna fukai masu fuska biyu,har kınada bakin ce mun jahila ,kinsa ba’a jahila daya sai biyu k………….” Cikin sauri SULTANA ta ce “Karki kuskura ki karasa dan ranki zai baci ne ,dan haka kowa ya tsaya a matsayin sa ,koda wasa karki shiga harkana , abinci kuma indai nizan ajiye miki toh zaki mutu baki ci ba ,trey ma in kinga dama kibarsa a dakin har duniya ta nade “tsaki ta ja tare da fita daga dakin.

Zainab kam baki bude abi bayata da kallo tare Dayi kwafa tana ayyana abu a ranta.

Kitchen ta koma dan duba girkin data daura ,zuwa biyu da rabi ta koma gida ,shima keke nafep tahau,idan tace zata tafi da kafa zata makara ne.

Bayan dawowanta gida bata samu kowa ba ,harda innah”adda deeje kawai ta samu a gidan itama fita zatayi dan kicibuss sukayi a bakin kofa zata fita,sai hararanta takeyi.

Cikin sauri ta shirya cikin blue and white uniform din ,blue wando da Riga sai hijab har kasa, tana gamawa tarife gidan takai key makwabtansu ,wuce wa islamiya tayi dan bashida nisa da gidansu,tana isa ta wuce ajinsu ,dan kowa ya zo dan kullum itace mai zuwa latti,zama tayi gefen wata yarinya ,zasuyi sa’anni da ita black beauty abunta.

Yarinyar gefeta tace”ke kam da zuwa latti yana tabo,toda yayi miki,kullum sai kinzo latti “kedai Bari bada san Raina nakeyin lattin nan ba kaw……..”maganan ya tsaya ne ganin mala minsu ya shigo class,tilawa suka farayi kafun ya fara karban hadda ,har ajazo Kanta ,cikin nutsuwa da muryanta mai dadi ya fara bada hadda kowani harafi hakkinsa na tajweed,har ta gama ba’a cita gyara ko daya ba,dan Allah yayi mata brain na daukan abu da wuri.

Sai 5:30pm aka tashe su ,kowa ya kama hanyan gida ,tare da asmau suke tafiya suna hira jifa jifa,kafun zuka rabu asmau ta shiga gida takuma ta cigaba da tafiya harta isa gida.

Tana dawo wa ta samu har yanzu basu dawo ba ,sai tashiga makwaftan ta karbo kin abude gida tashiga .daki tashiga ta cire kayanta ta daura zani,tawuce bandaki tayi wanka ta canja kaya zuwa material.

Girki ta daura ,bata gama ba sai bayan magrib ta gama ,a lokacin an fara kiraye kirayen sallan isah,tana cikin sallah taji haya niyansu alamun sun dawo .

alqur’ani tafito dashi tana koyan haddan da aka basu,tana gama ta kwanta dan har yanzu babu Wanda yashigo dakin dan indai suka zo da abun dadi ,a dakin innah suke tsayawa su cinye”cikin kankanin lokaci bacci yayi awun gaba da ita.

🔥 sai mun hadu gobe idan Allah ya kaimu❤️

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️





*_💋 SIRRIN DAKE BOYE_*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


🌎 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

Written by AMID ✍️

2024/2025🔥


Bismillah Rahmani Raheem

Book 1

page 📃 10

_______________________________________________💞

Abuja , Nigeria 🇳🇬


7:30am

Zaune take akan dining tana breakfast,sauri takeyi dan yau zasu fara exams,bataso tayi late.

Tana gama cin abincin ta tashi zata fita taji muryan Ammi “ autar Ammi tafiya ne babu sallama “yi hakuri Ammi bana so nayi late ne”Toh Allah ya kiyaye ya bada sa’a” Ameen ta amsa tare da ficewa daga falon.

Bayan kaman minute biyar 5 sai gata ta dawo ,Ammi da to wanta Kenan daga kitchen tace “ ah ah autar Ammi meya faru naga kin dawo ko kinyi mantuwa ne.

Girgiza kai tayi cikin shagwaba har idanta ya fara kawo ruwa tace “Ammi musa driver ne bashida lafiya wai baizo ba yau gashi nakusa yin latti” sai kije ki samu yayan naki ki fada masa idan yaso sai ya kaiki,Toh tace tare da wuce wa dakinsa ko sallama batayi ba tashiga dakin.

Shikuwa alameen bai Nima da fitowa daga toilet ba da towel a kugunsa yana kokarin saka kaya kawai ya ga mutum daga sama babu sallama bare excuse. Cikin tsawa yace”wai ke wace irin marar hankali ce da kishigo dakin mutum ba sallama “Anya shukrah kina fahimtan abunda ake koya miki kuwa kodai kawai barnan kudi akeyi a banza da har yanzu bakya gane abu mai kyau da mara kyau”zaki wuce ki fita daga dakin nanne ko sai ba balla ki.

Cikin sauri ta fita daga dakin ta sharar kalla ,komawa tayi main falo ta zauna a gefen Ammi “auta mai ya faru naga kin fito kina sharar kwalla,”babu komai Ammi ,kafana na bige a jikin gini,yaya ma cewa yayi na jirashi a falo yana zuwa”Toh sai kijirashi danni daki zanje na kwanta ,tashi Ammi tayi ta wuce dakin ta falon ya saura yusrah kadai.

Zaman 6mins tayi sai gashi ya fito,jikinsa sanye da dark blue yad daya amshi jikinsa ,dinkin zamani aka yi masa , key ne a hanun sa dan musa driver jiya yace masa bazai samu zuwa ba bayajin dadi ,shiyasa ya tashi yayi wanka dan yazo ya kaita.

Hanyan fita yayi ,batare daya ce mata komai ba ,shukrah ganin bai kula taba yasa ta tashi tabi bayansa ,packing space ta nufa , anan ta gansa a cikin BMW white color, bude wa tayi tashiga tare da cewa yaya alameen Ina kwana,Dan Allah yaya kayi hakuri mantawa nayi ne shiyasa”lafiya , nangaba ko bani ba karki sake shiga dakin mutum ba tare da kinyi sallama ba ,babu kyau kiji ba , sai ki gyara “ Toh tace.

Har suka isa ba Wanda sake cewa komai, zata fita yaba ta pocket money tare da cewa “ kiyi karatu banda wasa fah uhmmm tace tare da yi masa godiya ta karba kudi tasaka a pocket nata .

Tashiga school shikuma ya juya motan ya koma gida .


_______________________________________________✍️

USA 🇺🇸

Yau kwana uku Ashman yana jinyan jikinsa ,kuma Alhamdulillah jikin nasa yayi sauki sai abunda ba’a rasaba dan kullum sai “boss lion “sai yazo yayi masa treatment din wajan ,dan yanzu baya clinic ya koma dakinsa sai dai baya zuwa office ya rubuta letter a ogansa wato “boss lion “ a kan bashida lafiya,dan haka tsarin aikin yake.

“Boss lion “

Kwance yake akan gadonsa,jikinsa rufe da bargo,amma bai rufe kansa ba iya kafa da.

Motsi ya fara alamun zai tashi ,bakinsa dauke da addu’an tashi daga bacci .

(Alhamdu lillahil-lathee ahyaanaaa ba’da maa’amaaatanaa wa’ilayhin nurshoor).

Bude idanun sa yayi da sukayi grey color sai shining sukeyi kaman ba yanzu ya tashi daga bacci ba ,mikewa yayi ya sauko da kyawawan kafafunsa farare tass ,ya mike ya shiga toilet.

Fito wa yayi daure da towel a kugunsa ,wucewa yayi wajen dress mirror ya sha mai dasu lotions,kafun ya wuce dressing room ,after some minutes sai gashi ya fito sanye da kakinsu na sojoji ,tubarkallah Masha Allah,Allah yayi baiwan kyau anan ,ya fito a balaraben sa ,ga curly hair nsa daya sha gyara ,Moses nashi dukda yana cikin riga zaka shaida kakkarfa ne bana wasa ba.

Sai kamshi theatre yake masu masifan kamshi dake sa nutsuwa da kuma tafiya da zuciya mace ko namiji.

Cikin Tafiyan kasaita irin na ingarman namiji main falo,sojojin dake falon sai Sara masa suke yi ,jikinsu har kerma yakeyi wajen ganin basu ji kuskure ba , fito wa yayi cikin gidan anan ma sai kamewa sukeyi suna sara masa ,kaman zasu masa sujjada,ko kulasu bai yiba kaman baisan sunayi ba.

Wajan wasu jahilan motoci ya nufa na millions of dollars kusan goma sha biyu ,shadaya 11 bakake ne masu tinted sai na tsakiyan BMW 7 series,bude masa james yayi tare da Sara masa.

A tare convoys din suke gudu kaman zasu tashi sama,direct head quarter suka wuce a jere abun gwanin sha’awa .

Sunkai 10mins da tsaya wa kafun aka bude masa ya fito,fitowa yayi fuskanan a murtuke ta cikin face marks din dake fuskansa.

Head quarter ne babba anan office na jiga jiga sojoji suke ,ga sojoji ta ko Ina suna yawo,upstairs 10 ne gashi na glass ne daya kawata wajan.

Suna shiga ciki sojojin sai mekewa sukeyi suna sara masa tare da kame wa,direct wajan lifter yaje shida james dake rike da document bashi a hannu,suna shiga james ya danna 10 wato na karshe kenan ,within seconds lifter ya bude ,fitowa sukayi suka tsaya a bakin wani kofa mai kyau ,ta saman an rubuta “FIELD MARSHAL office “.

James ne ya bude kofan ,”boss lion ne ya fara shiga kafun james ya biyosa da document din ya ajiye akan table din tare da Sara masa ya juya ya fita.

Office ne mai girma sosai daya kawatu da ababen more rayuwa,komai white color ne a office din,ga sanyi ac da kamshi ne kawai ke tashi a office din, a cikin office din akwai falon a cike shima komai white and golden ne sai resting room shima yanada girma sosai mai dauke da furnitures masu kyau da tsada.


2024/2025🔥

Written by AMID ✍️





*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥


🌎 Destiny,Love ❤️ & Romance 💋


Written by AMID ✍️

2024/2025🔥


Bismillah Rahmani Raheem

Paid book ne

Book 1
page 📃 11


Zama yayi akan kujeran table din ,tare da bude system ya fara aiki cikin kware wa da basirah ,aikin yakeyi cikin nutsuwa .

So yake yi ya gama aikin daya rage masa dan yana so yaje Spain gobe yayi kwana daya ya dawo,shima gayyatan sa akayi . 3:50pm ya fito daga office din suka koma gida .

Wanka yayi ya shiya cikin black jeans and black t-shirt,p-cap ,face marks,booth ,watch,Duk komai black colour ne ,kafun ya daura black jacket akai ,idan ka gansa akan hanya ma ba lallai ka ganesa ba .

3 floor ya nufa, direct dakin Ashman ya nufa ,ya samesa zaune yana duba wasu files.

Ashman zake zaune kamshin turaren “Boss lion” ne ya ankarar da shi da zuwansa, nufan inda yake “Boss lion “ yayi tare da tambayansa “ how are you? And your body ,I hope your felling good 😌 da kyar ya karasa maganan tsabar miskilancin.

“Good afternoon yaya”am felling ok,Alhamdulillah “ zanyi tafiyane kuma na sirri nakeson yi ,dan haka kakula da kanka da kuma junaid cewan “Boss lion “ .

Hugging nasa Ashman yayi tare da sakar masa
Kiss a gefen kumatunsa ,shima maida masa yayi tare da juya wa zai tafi yace muryan Ashman “safe trip yaya”.

Bai kula saba yayi ta tafiyansa, cikin wani Boyayyen hanya yabi ya fuddashi daga gidan batare da kowa ya gansa ba ,anan ya tarar da james a cikin mota,cikin sauri James ya fito ya bude masa kofan ya shiga sai airport, yana isa private jet nashi ya shiga ,shigansa within 6 minutes jet din ya daga.

(Allah ya kiyaye boss lion)


________________________________________________🙏

Gombe ,
Nigeria 🇳🇬

Tana tashi da Asuba tayi sallah,ta zauna bitan karatun qurani kafun ya fito dan yin aikin da ta saba ,tana cikin wanke wanke taji muryan innah na ce mata” garbati jiya ya kawo kudin auren ki ,kuma ansa nan da sati daya zaki tafi dakin mijin ki dan ninagaji fenada kujecan Ku karata ,a tsiya ce”

Cikin shega adda Habiba da adda deeje suka tafa,yau sun tashi da wuri wata kila akwai abunda zasuyi ne.

Adda Habiba tace” ah ah SULTANA anyi goshi ,haka kawai sai kiyi wuff da bawan Allah, adda deeja tace “ basai zai iya zama da ita ba ,dan wannan daga gani ko sati baza AYI da auren ba zata dawo bazawara dan nasan shima ba iya zama zayyi da ita ba “

Cikin sauri innah tace”Ina zata dawo ai wallahi ta tafi ta tafi Kenan ,ba zancen dawowa sai dai tashiga duniya ,yan duniya suganta ,idan ya so sai su kwashi ragowan garbati .

Cikin dariya adda Habiba tace “ a kwai shagali har walimah sai mun yi idan ya bar mana gidannan muma mu huta da fitinah .

Wasu hawaye masu zafi da na bakin ciki suka zubowa SULTANA , tayi saurin sha rewa ta dau alwashin ko zata rasa ranta ne bazata taba bari ayi aurenta da garanti ba .

Tana gama wanke wanken tayi wanka tashiga cikin riga da skirt na atampah yayi nata kyau ,sauri tayi ta gama dan yau har tayi latti ma.

Sauri tayi ta fita daga gidan ko sallama bata musu ba ta tafi.

Sauri takeyi sanye da maroon color hijab tareda niqab,blue eyes nata kawai zaka iya gani a jikinta, tana isa tashiga tafara aikinta har sukaci abincin safe ,tagama zuwa 2 na rana ta shirya ta fita daga falon,kicibuss sukayi da jabir a bakin kofa .

Ko kulasa bata yiba,zata wuce ta gefe kawai ya sha gabanta tareda Mika mata key “ga kinnan ki kaimun abincin Rana dakina,SULTANA kam kallon baka da hankali take masa,magana ya farayi cikin serious yace” abinci zaki Kai mun fah ,Kona taba aikenki dakinane yimun wani abun “ni bazan kai ba kabani hanyan na wuce tun Muna mutunta juna “ please kikai mun daki ni’ina garden da abokina ,idan muka gama abunda mukeyi zai ci abincin ne.

“ toh bani key na kai dan kana batamun lokaci ne “mika mata key yayi tare da juyawa ya nufi garden, SULTANA kam komawa tayi kitche ta zuba abinci a plate ya daura akan Trey ,ta dakko ruwan sanyi da Coca Cola a fridge ya daura akan tare da cup agefen.

Tana fita daga part din ya wuce boys quaters din, shiga tayi falone mai dan girma daya kawatu da furniture brown sai kofa biyu Wanda daya zai sadaka da dakin jabir daya kuma
Na khalifa,gefen dama shine na khalifa na hagu kuma na jabir na hagun ta nufa tare da sa ki ta bude kofan.

Tana shiga warin sugari da na shisha ya bugesa alamun ba’a dade da shaba sai da ta toshe hancinta dukda akwai niqab a fuskanta amma ta Tosha hancı ta kafun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login