Showing 24001 words to 27000 words out of 42382 words

Chapter 9 - Sirrin Dake Boye Book 1 Hausa Novel Complete

Amid   

20 Dec 2024

289

ruwanta da shiga cikin yan mata biyun nan,dama tun kafun SULTANA tazo take rayuwa ita kadai abunta ,batada kawa ko a boki.

A hankali hakuwa ya fara shiga tsakanin ta da SULTANA,saboda ganin yanda take kwana ta tashi da zazzabi ne yasa ta tausaya mata ta tambayeta meya same “cikin karfin hali sultana tace wallahi zazzabi ne yake damuna,ji nake kaman zan mutu.

Cikin tausayawa back beauty tace Allah sarki ,Allah ya baki lafiya ,meye sunan ki”SULTANA “suna mai dadi,kefah sultana ta tambaya ,ni sunana ilham can we become friends,cikin jin sanyi sultana tace”why not “ dan koba komai za tayi amfanin da wannan daman wajan samun mafita a gidan anan.

Tun daga wannan lokacin sultana da ilham suka zama ka waye,ko yaushe suna tare ammafa duk da haka sultana tana fama da zazzabi ,da haryau bai warke ba.

Zaune suke a fillin babban gidan suna magana inda sunan ganin duk wani mai shiga da fita a gidan,kuma security basa hana kowa fita wajan karuwancin sa,jikinsu sanye da dogon ruga ba’a ganin jikinsu,sultana kam da hijabin ta da tazo dashi kullum yana jikinta ,bata iya rabuwa dashi.

Sultana tace”amma ilham bakya tunanin guduwa daga wannan gidanne ,dan naga kowa yana iya fita,ban taba ganin kin fita daga gidan ba ,tace hmmm”sultana kenan ai sunsan wayanda suke bari su fita dan ba karamin tsaro suka saka ba.

Yanzu kina nufin a gidanan zamui ta zama kenan “eh toh zan iya nema miki hanyan da zaki iya guduwa amma nikam ko na gudu bani da inda zanje.

Kina nufin bakida wanda kika sani a cikin familyn iyayen ki,”ai sune ma suka kawoni wannan wajan wai bazasu iya rike maraya ba,cikin tausayinta sultana tace kiyi hakuri ilham ,komai mai wuce wani”Insha Allah ilham ta fada”

Mikewa suka yi suka wuce cikin dakinsu.


2024/2025🔥

Written by AMID ✍️



*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

page 📃 19



7:22pm

Junaid ne zaune akan kujeran dake indoor,yafito hutawa,sanye yake da jallabiya milk color a jikinsa yayi masa kyau,gabanshi a Kwai abun tabawa a gabansa.

Wayansa ne yake ringing,yasa hani yadauka,sunan besty ne a jikin wajan,daga wa yayi yace suka fara magana bansandai mai besty ke fadamasa ba kawai gani nayi ya miki jikinsa yana rawa ya fito,dakin ashman ya wuce dan yasan har yanzu “boss lion” bai dawo ba.

A dakinsa yasa mu ashman yana kwance akan gado da waya a hanunsa,sallama yayi yashiga,ya zauna a gefen gadon yace”yaya ash please inaso naje wajan besty ,yanzu aka kirani a waya akace yayi hatsari.

“Junaid amma dai kasan wannan ba mai yuwuwa bane ko,ina zaune lafiya bazaka dakko mun masifa ba ,kawai ka koma daki ka zauna .

“Please yaya ash yanzu zan dawo kafun yaya ya dawo bazan wuce 30mins ba please kaji yaya na”Shikkenan junaid kaje ka amma karka kuskura ka dade,dan yaya boss yana tambayana cewa zanyi nima bansan lokacin da kafita ba kokuma nace na hanaka kakiji sai da ka fita,dan haka saika kuka da kanka.

“Insha Allah ma hakan bazai faru ba,bye saina dawo”ok kadawo kafun ya dawo fah,Toh ya fada ,yana fita daga dakin.

Fitowa yayi sojojin da suke gadainsa suka dauko wata mercedeze benze 350 ,junaid ya shiga sukuma suka shiga bakaken jeb nasu suka tafi.

Junaid da kansa yake driving na motan sukuma suna binsa a baya,gashi sai gudu ya keyi dan ya isah asibitin da wuri ,su samu su koma kafun “boss lion “ ya dawo ya samu ba sanan.


_________________________________________😉


8:00pm

Kance SULTANA take akan gadon ta ,jikinta yayi tsanani tunda ta tashi daga baccin safe,take amai gashi ta kasa cin komai,ba wanda yake kulata,kuma sunsan batada lafiya.

Ilham ne zaune a gefen ta ,tana ta mata sannu cikin tausayawa,ganin ba wanda yake kula sultana sun barta ko ta mutu kotayi rai wannan ba damuwansu bane.

A hankali ta mikar da sultana tace”sultana ki daure ki tashi ki gudu daga gidan nan ,dan wallahi kika cigaba da zama ba kulaki zasuyi ba,barinki zasuyi ki mutu ba ruwansu,dan dan bake kadai suka taba mawa wannan abun ba.

Mikewa tayi da kyar suka fito daga dakin ba wanda ya gansu ,suka bi wani lungu ,sun danyi tafiya mai tsayi kafun suka isa wajan get suka tsaya,ilham tace”kiyi hakuri sultana amma ya kamata kibar wajannan dan kina bukata kilawan gaggawa ,dan haka ki tsaya anan zanje na dauke hankalinsu idan yaso saiki bi ta bayansu ki wuce kafun su ankara dake” yanzu kina nufin badake zamu gudu ba ,kuma idan na gudu suka gane cewa kice wacce ta taimakamun wajan guduwa,zasu iya cutar dake.

“Dariyan yake ilham tayi tace “karki damu ba wanda ya isa yamun abunda Allah bai mun ba,dan haka ki kwantar da hankalinki ,kuma kiyi yanda na ce miki,cikin muryan mara lafiya da baya fitowa sosai tace jikinta duk yayi sanyi .

Wajan get din ilham taje ta tsaya,securities uku ne a wajan ,yi tayi kam zata fita ,ai kuwa da sauri mutum biyu daga cikinsu suka nefe ta ,daya daga cikinsu yana cewa “hey hey where are you going,shiru tayi cikin tsawa ya ce bazaki bude baki kiyi magana ko saina fasa miki kai a wajan nan.

Bude baki tayi tana ginisa ido ciki ido tace”fita zanyi ko akwai wanda ya’isa yanani fita ne ,”ki koma dan ba’a bamu izinin barinki ki fita ba ,cikin tsawa tace “har kaisa kace zaka hanani fita ,nagadai biyanka akeyi ,da har zaka tsaya kamun magana da gadara sai kace ubana.

Dayan dayake zaune tundazu yana ganinsu ,yaga yanda yarinyar take musu a sauran tsawa kaman sa’an ninta,mikewa yayi ya’isa wajan yace”ke ilham wato wiyanki yakai yanka kin girma dole ki fara rashin kunya ,amma bari kiji ki shiga hankalinki dana dan zan kasheki kuma na kashe banza.

Wannan fadan da sukeyi ne yabawa sultana daman tafiya a hankali yanda ba wanda zai jita ta wuce ba wanda ya ganta. Dan hankalinsu yana kan ilham “da gudu ta fita daga get din batare da sun sani ba.

Cikin sauri ogan nasu ya juya yaga wayene ya fita da gudu dan sunji karan gudunta ,ai kuwa da sauri suka bita su biyu .

İlham tana ganin lokacin da sultana tabi ta bayansu har suka sakarwa juna murmushi mai hade da hawaye dan ba karamin shakuwa sukayi ba a cikin kwana hudu da sultana tayi a gidan ba .

Gudu sultana takeyi da iya karfin da Allah ya bata take gudu ,duk da kuwa a kwai zazzafan zazzabi dayake damunta ,dan kunsan gudun cetan rai takeyi,juyawa baya tayi taga sun biyo ta daga Riganta ta daga,ta kara gudun nata har ta fito babban kwalta ,amma basu daina binta ba.

Saura kadan su isota gashi harta galabaita,dishi dishi take gani amma hakan bai sa ta daina gudun ba.

Ji tayi mota yayi sama da ita batare da tasan ya kan ta faru,faduwa tayi kasa kanta yana zubar da jini kaman da bakin fanfoo ,tana kwance a kasa ,bazan iya gane suma tayi ne kokuma dai rai ne yayi halinsa ne dai bansaniba 🥺🥹😭🤧

Securities din da suka biyo tane suka ja dabaya da gudu suka koma ganin abunda ya faru sunsan koma wacece aka bige tariga da ta mutu,dan su fah basusan ma wasuka biyo ba ,kawai dai sunga ta fita da gudune alamun gudu takeso yi shiyasa suka biyota ,Ashe ita kamma lokacin ta yayi 🤧

(Allah sarki sultana,Allah ya ji kanki da rahma yasa mutuwa hutune a gareki , munyi babban rashi yan group🥹😭🤧)

2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️




*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏

Allah ya jikanka aymann.

pages 📃 20


Cikin tashin hankali junaid ya taka burki,jikinsa har rawa yakeyi saboda tashin hankali,bude murfin motan yayi da sauri ya fito ,yayi kan sultana da hijab din jikinta ya fadi ,gashin kanta duya bazu ya rufe mata fuska ,ga jinin daya bata mata fuska kuma,bazaka taba iya gane sultana bace.

Sauran sojojin ma saukowa sukayi daga motansu hankalinsu a tashe ,ganin Kanin “boss lion “ ya bugi a bu,sufa tsoronsu kar wani abu ya samu junaid,basu damu da ganin ya buge mutum ba.

A tsugune junaid yake a gefen sultana ,hanun sa sai rawa yake yi wajan taba sultana ,tsoronsa kar ace sultana ta mutu.

Hanunsa ya saka ya dauke ta ,jikinta a sake tayi nauyi amma dake suma junaid in yanada karfi dan kullum sai yayi training,umarnin boss lion ne wannan. Wani sojane daga cikinsu ya mikawa junaid hanu akan ya bashi ita ,girgiza mishi Kai junaid yayi dan bashi da bakin magana.

Dan tuni hawaye ya wanke masa fuska,a bayan motansa ya sakata ya kwantar da ita ,ya shiga wajan mai zaman banza,dan bazai iya driving ba,wani sojane yashiga cikin motan ,sukayi reverse suka koma gida .

Bayan sun İsa gida,da kansa ya dauke ta ya shigo da ita cikin main falon gidan ya kwantar da ita akan kujera .

A falon ya tarar da uncle tareeq,uncle Ibrahim suna tsaye suna jiran dawowansa dan har lokacin “boss lion “ bai dawo ba,sai kuma Ashman da yanzu shigowansa falon bayan junaid ya ajiye sultana.

Sojoji ne suka kirasu a waya suka fada musu abunda ya faru,shine dalilin dayasa suka fito suna jiran isowansu.

Ashman ne ya je ya samu junaid dake tsaye yana yace”yanzu junaid abunda kayi ka kyauta kenan ,gashinan wata kila ka kashe yar mutane a banza ,tsaki ya ja cikin takaici,”Allah yaya Ashman itace ta shiga ga bana da gudu, kafun ba danna bugurki ma na bigeta,nagadai alamun biyota akayi ne shiyasa ta hau kan hanyan bata sani ba.

“Amma dai kasan wannan abun bazata zauna mana a gida bai dai ko,uncle Ibrahim ya fada Yanya huci,”haba ya İbrahim wannan wani irin magana ne inadai kana ganin yanda aka kawota,kaga duk jikin kujeran can jinine kaman an ganka dabba ,uncle tareeq ta fada cikin rarrashi .

Ashman kam yana tsaye yana jin abunda suke ta fada”shima a ganinsa bai kamata ka kawo musu mace gida ba dan mata a sun muna furce su,kuma suka rabasu da kowa nasu ,tundaga wannan lokacin suka tsani ganin mata a rayuwansu,ko a gidanan babu wata mace da ta taba shigowa cikin gidan nan sai yar president na kasar ne ta taba shigo ,shima bata fita lafiya ba dan sai da “boss lion “ya harbe ta a kafa dan a rayuwansa ya tsani harka da mata,ita a dole “boss lion” takeso.

Yana tunanin gwanda shi akan “boss lion” dan yasan wannan maganan ma bamai yuwuwa bane,dan bazai yarda wata mace ta zauna masa a gida ba,dan haka shima bai goyi bayan zamanta a gidan nan ba .

Cikin tada jijiyoyi wiya uncle Ibrahim yace,kanada hankali kuwa tareeq mace fah kuma a gidan nan ai wannan ba mai yuwuwa bane ,bari “my son” ya dawo sai na sashi dole ya fitar da yarinyar nan ,dan nasan shima bazai bari ta zauna ba, idan kuma yayi kokarin bari ta a gidan nan zai ga abunda zan masa ,dan koshi bai isah ya hanani fitar da ita daga gidan nan ba,ya karasa magana cikin ga dara,yanda kasan yasa naira biyar dinshi acikin gidan.

Ashman kam gizgiza kashi yayi kawai ya tsaya yana ganinsa, sai kace bashine yake tsoron magana ma ya hadashi da boss lion ba,yayi murmushi a zuciyansa yace zanga yanda cika bakinan zai kare.

Cikin tafiyan kasaita ya shigo cikin falo jikinsa sanye da farin wando da white long sleeve ya daura farin jacket akan kayan ,Tabarakallah masha Allah,Allah yayi halita a wajannan,fuskansa sanye da face masks ,ga black curly hair da yasha gyara sai sheki yakeyi kamshi yana tashi.

Shigowansa ne ya ankarar da yan falon,koya yashiga taitayinsa bakajin karan motsin kowa ,falon ya dauki shiru ,zama yayi akan wani one seeter yayi crossing na legs nashi,yasa hanu ya cire face marks na fuskansa ,kyakyawan fuskan mai cike da kwarjini ya bayyana ,fuskanan a tamke ya ke ,kaman baysan wani abu shi murmushi ba bare kuma dariya ,fuskan a tamke kaman zaiyi aman wuta,dago da idonsa yayi yaga junaid a tsaye a gefen kujeran da aka ajeye sultana,yayi kifi kifi da ido irin na marasa gaskiya ,kafun ya maida idonsa kan Ashman da shima shidin yake kallo ,dauke idonsa yayi ya maida kan uncle tareeq ,kafun ya maida kan uncle Ibrahim.

Ganinsa yayi kafun ya bude reddish lips nasa a hankankali kaman bayaso yace “continue what you’re saying “ya fada yana daga masa gira daya ,wannan sigh ne na zaiyi rashin mutunci,yawu mai daci uncle Ibrahim ya hadiye,ya kasa magana jikinsa har rawa yake yi saboda tsoro,nandanan yayi na daman abunda ya fada, dan kuwa tabbas yasa yaji duk abunda ya fada,dama wai shi burgansa ya musu Jan ido ,su fitar da sultana kafun ma boss lion yazo,sai koma burgansa bai yi amfani ba.

Tsare sa da ido “boss lion”yayi gashi dama indai ya kalle ka da wayanan grey eyes nashi masu ladab tarwa.

Since you can’t talk ,I will talk” kace zaka fitar da ita daga gidan kuma ban isah na hanaka ba,Toh Bismillah,dauketa ka fitar

Tsayawa kawai uncle ibrahim yayi yana kallonsa dan bamashi da bakin magana,ya tsaya kawai yana kallon “boss lion”bakinsa yana motsi alamun magana yake yayi amma ya kasa.

Please am sorry, Nifa wasa nake musu ,so nake naga sunada hankali ne kokuma dai har yanzu da sauran yarın ta a jikinsu”amma ni ni ni ya fada yana nuna kansa da yatsa ,waye ubana a garinan Dana isa nace “kafitar da ita daga gidan “ah’ah babu ba kina acikin wannan maganan.

Cikin tsawa yace “nace ka dauke ta kafitar da ita ,before the count of three 3”one ……….two “jikin uncle Ibrahim rawa yake yi sosai ,kana ganin idanunsa kaga tashin hankali tun kafun yace three ya durkusa akan gwai wansa ya fashe da kuka ……


2024/2025🔥

Story and written by AMID ✍️





*_💋 SIRRIN DAKE BOYE _*❤️
( The hidden secret 🌹)

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


🌍 Destiny,Love ❤️& Romance 💋

2024/2025🔥

Written by AMID ✍️

Bismillah Rahmani Raheem

Wannan littafin na kudi ne 300 ne kacal ba yawa ga mai bukata ga wannan account number 7068845514 OPAY Fatima mala umar,zaki iya tura shaidan biya ta wannan number 08161857656 Nagode 🙏


page 📃 21



Cikin tsawa yace “nace ka dauke ta kafitar da ita ,before the count of three 3”one ……….two “jikin uncle Ibrahim rawa yake yi sosai ,kana ganin idanunsa kaga tashin hankali tun kafun yace three ya durkusa akan gwai wansa ya fashe da kuka ……

“Wallahi Allah dagaske nake,wasa nake musu,kayi hakuri wallahi bazan sake kwatanta irin abunda nayi yau,”kuma ai a ganina da na kowa ne,kuma mu ne da laifi tunda junaid ne ya bugeta,Allah ya huci zuciyar lion .

Junaid kam tunda yaga yanda uncle ibrahim ya durkusa akan gwaiwansa,bai san lokacinda dariya ya kwace masa ba ,ganin yanda ya zake da cewa”ko “boss lion”ne yace ta zauna bai isa ba,”huuh uncle Ibrahim a kwai dan drama”ya fada a zuciyansa”.

Ashman ma abunda uncle Ibrahim yayi ya sashi yin murmushi,dan dama yasan za’a rina,indai yaya boss ne”dan ya tsana kace zaka nuna mishi isa ko kace zaka bashi umarni or kace kai sam baza’ayi wannan abun ba,annan zaku samu matsala .”dan muddin kace haka to,wallahi ko bakason wannan abun sai anyi,kuma koda shima bayaso zaiyi,dan yanuna maka kai ba kowan kowa bane.”hakan ne yasa yake ganin “tabbas boss lion “ zai bar sultana ta zauna a gidan ,badan komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login