Showing 1 words to 3000 words out of 30449 words
[12/24/2019, 21:47] Takori: RAYUWAR RAYHANAH - 2
Ji ta yi kamar an dora mata dutsen Uhudu a kanta, sabida nauyin da kalamansa yayi mata, a gigice ta dago ta dubi Khalipha jikinta na bari na rudewa da gigicewa.
Ta shiga waiwaye-waiwaye kada wai ko wani ya ji abinda Yaya Khalipha ya ce. Amma ga jin dadinta kowa harkar gabanshi yake yi da iyaye da ‘yan’uwansa nesa dasu sosai, don sai da ta ware kanta can nesa da jama’a kamin ta zauna.
Shi kuwa Khalipha ko a kwalar rigarshi, bajewa ya kara yi a gabanta yana gaya mata duk kalaman soyayyar dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa ba daga fatar baki ba. Idanunshi a lumshe, ya yi kyan da bata taba lura ashe yana da shi haka ba.
Karkarwar da jikinta ke yi ya karu, don Khaliphan ya ki yin shiru. Ita kuma gaba daya a gigice take kada kannensa dake matukar ganin girmansa su zo su ga abin da yake yi, wanda ita bata sani ba.
Sauran kadan ta tsuge da zawo da ta hango Jawahir ta nufosu da sassarfarta. Da karfi ta ce, “Yaya Khalipha ka cika min hannu, ga Jawahir nan”. Lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannun nata daya rike cikin nasa da karfi kamar zai balla ta.
Amma Khalipha ko gezau bai yi ba, juyawa kawai ya yi yana tsimayen isowar Jawahir din.
Mikewa ta yi da karfi ta fizge hannunta saura kadan ta fadi. Cikin zafin nama ta zauna a kan kututturen iccenta tana kokarin dai-daita numfashinta, nutsuwarta, bugun zuciya da yanayin fuskarta kafin isowar Jawahir.
To ita ma Jawahir din duk da ta ga abin da ta ganin, amma da yake wayayya ce ba ta nuna komai a fuskarta ba, a zuciyarta cewa ta yi, “Na san wata rana irin wannan na zuwa, tsakanin Raiha da Yaya Khalipha, Intimacy din ya isa, haka kulawar da suke wa junansu a gida kadai abin a digawa ayar tambaya ne.
A gaban Khaliphan ta zube tana dariya.
“Yaya Khalipha yau kai ne da visiting, ina Mami ina Zizah? Ina Daddy?’
Ta jefo masa tambayoyin duka a lokaci daya bakinta kamar zai tsage don fara’a da farin ciki.
Ya ce, “To duk wadannan queries ni kadai Jawahir, wanne zan fara amsawa?”
Dariya ta yi tana kallon Raiha ta ce, “Don Allah Rayha Yaya Khalipha bai kara kyau ba?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Ni bana yiwa mutum kallon kurilla”.
Ta ba shi dariya sosai, ya ce, “Har da ni RAHANE?”
Ko don albarkacin wannan suna da ya kirata da shi ya isa ya sata dariya.
Ya mike yana duba agogon hannunsa, lokacin rufe makarantar ya karato.
Ya ce, “Ku zo muje mota ku kwashe kayanku har na wannan shashashar (Abida)”.
Suka mike suka bishi har boot din motar ya kwaso ya basu. Haka ya ware na Rahane. Wannan karon ma Jawahir ta diga ayar tambaya, amma wayewarta yasa ba ta nuna komai ba. Saboda yawan kayan sai juniors dinsu suka sa suka tayasu kai kayan hostel.
Tun daga wannan ranar Rahane ta kasa samun sukunin zuciyarta. Tunanin Yaya Khalipha da al’amarinshi day a zo mata dashi kadai zuciyarta ke yi dare da rana, yini da safiya.
Sai dai bata barin hakan ya shafi karatunta ko kadan saboda alkawarin da ta daukarwa ranta na farantawa Baba Dacta wannan karon da kyakkyawan sakamako. Amma fa duk sanda ta kwanta, ko ta kadaice tunanin Yaya Khalipha take yi. Ba abin da take so irin ta ganshi, ko ta ji muryar nan tasa mai sanyi yana cewa ‘RAHANE’.
A haka suka zana WAEC da NECO har da JAMB, suka yi sallama da Ulul-Albab. Ya yin da Rahane ta zana (qualifying) wato jarrabawar shiga aji shidda.
Sun zo gida hutu a lokacin Khalipha an tura shi kwas a kan aikinsa a Nigerian Embassy na kasar Marocco. Wanda zai yi tsayin watanni tara.
Khalipha ya yi murna da wannan tafiya, ko babu komai zai yi nisa da Rayhanah na dan wani lokaci mai tsaho. Ba tare da al’amarin dake zuciyarshi ya bayyana ga kowa ba. Ya na da relief tunda ya bayyana shi gareta. Duk da bai san me ke wakana a tata zuciyar ba.
Sai dai kuma ya bar ita Rahanen cikin dabaibayi mai yawa, da soyayya mai cin zuciya. Duk da ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da ita ba.
Ta san dai tunda Yaya Khalipha ya tafi ta shiga kewa, rashin kuzari a cikin gidan da makaranta duka. Tunda ya tafi ko waya basu taba yi ba, domin Baba Dacta ya hana kowaccensu rike wayar hannu, ya ce sai ya ga kamun ludayinsu a jami’a tukunna. Hakan ne yasa ko Khalipha ya yi waya da Mami ko Daddy sai dai ya a ce a gaishe su. To da haka rayuwar ke mikawa.
Lokacin da Abida da Jawahir suka samu gurbi a Jami’ar Bayero, lokacin ne Rahane ta zana jarabawar barin sakandire. Cikin watanni uku ta fito, kuma Raihanah ta bai wa kowa mamaki daga ‘A’ sai ‘B’ a dukkan takardunta. Maki ne da daga Abida har Jawahir babu wadda ta same shi a kamala sakandiren ta.
Wannan farin ciki da Rahane ta sanya Dr. Mansur, shi ya yi sanadin da ya fara tunanin abin da zai mata as a gift don ya kara karfafa mata gwiwa, ta kuma fahimci cewa babu maraya sai rago. Nakasa ba hujja bace ta mutuwar zuciya.
Bincike suke iya bincike wajen manya-manyan likitocin kunne na gida da waje. Dr. Philips, Baturen Sikotilan ne, kuma malami ga Dr. Mansur tun zamanin yana karatu a jami’ar Trinity.
Dr, Philips tsohon likitan kunne da makogwaro ne (ENT Surgeon) wanda a lokacin ya tsufa, har ya aje aiki, yana zaune a kauyensu na haihuwa (Braemar) shi da iyalansa.
Tsufan Dr. Philips bai hana har zuwa lokacin ana kawo masa cases masu tsanani har gida (Braemar) ba. Idan al’amarin ya gagari manyan likitoci, haka nan manyan kasashen duniya na hayarsa domin ya yi musu aiki a fanninsa. Shine mutum na farko da Dr. Mansur da Dr. Imam suka tuno a lokacin da suka gama gwaji na karshe (hearing test) a kan lalurar Rayhanah.
Ko Mami ba ta san me ake ciki ba, sai da aka zo tafiya Abuja yin visa wanda ya kama dole ita Raihan ta je. Bai yi mata bayanin komai ba sai ana i gobe tafiyarsu Abujan da daddare yake gaya mata.
An ce zuciya bata da kashi, sannan Mami ‘yar Adam ce kamar kowacce mace, tunda zuciyar ta irin ta kowacce mace ce da Allah ya halitta da kishi. A lokacin da ya gaya matan ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa.
Me Dr. Mansur ke nufi da ita da bai yi shawara da ita ba? Bai nemi jin ra’ayinta ba? Yana nufin shi da Raihanan za su kama hanyar Abujan ko me? Yana nufin da santaleliyar budurwa za ta barshi ya sata a mota su bar gari? Ko yana nufin haka zai sa yarinyar a gaba su bar kasar? Babu dangin iya babu na baba, ita mahaukaciya ko shashashar ina ce? Wannan kauna da kulawa da Dr. Mansur ke yiwa Rayhanah fiye da ‘ya’yan cikinsa ta magani da mece ce?
A take yanayin fuskarta ya sauya, kishi karara ya bayyana a kyakkyawar fuskarta. Sannan ranar da ta ga Khalipha rungume da Rayhanah a asibiti ta kara fado mata, da halin da Khalipha ya shiga a lokacin da hirar da suka yi. Tiryan-tiryan ta dinga dawo mata.......’an kasa ni! Soyayya ce Mami!!’
Nan da nan kwakwalwarta ta soma kimsa mata abubuwa daban-daban cikin ranta wadanda a zahiri ba haka suke ba. Wato uban na so, dan ma na so. Dalilin shigar Khalipha halin da ya shiga kafin ya tafi, yana nufin Daddy ya kasa shi. Tunda ya ga ba zai iya tarayya kan soyayya da mahaifinshi ba.
Hankalin Mami ya tashi kwarai, wata irin firgita ta kamata. Ta mike tsaye kawai ta yi daki, ba tare da ta ce da Dacta Mansur komai ba.
A lokacin ma cike form din neman visa yake yi a ipad dinsa. Jin Mamin ba ta yi magana ba ya daga ido ya dubi sashen da take, sai ya ga har ta kai kofar dakin barcinta.
Ya yi dan jim yana ‘yan sake-sake. To me ya bata mata rai cikin wannan maganar? Ya aje biro ya mike ya bita dakin, sai ya ganta zaune a bakin gado ta yi tagumi da hannuwa bibbiyu, yanayin fuskarta kuwa ba zai karantu ba.
Zama ya yi kawai kusa da ita kafadunsu na gugar na juna.
“Asma’u Zatun-Nidakaini (ma’abociyar mayafi biyu). Mai sunanki ma’abociyar hikima da ilmi ce diya ce ga Sayyadina Abubakar As-Saddik. Lokacin da Manzo (S.A.W) ya yi Hijira zuwa Kogon Hira ita ke kai masa abinci tana rufe da mayafin..........”
Sauran maganar makalewa ta yi a makogaronsa ganin Mami ta soma kuka. Hankalin Dr. Mansur ya tashi, kololuwar tashi kuwa.
“Me ya faru Asma’u? Na fadi abin da ya bata ranki ne? Ina so ne kawai in gaya miki kissar mai sunanki, ba ta fushi a kan abin da ba ta da sani a kansa, ko kuwa abinda bai kai ya kawo ba”.
Mami ta sharce hanci da ido da tishun dake gefen gadonta. Magana ta farko da ta furta masa tun shigowarsa ita ce,
“Hausawa baku da kirki, baku da amana wallahi”.
Ido ya dan bude kadan yana kallon ta, ya ce, “Mu din kuwa? To me muka yi mu Hausawa rainon Musulunci?”
Ta ce, “Kuna kafa hujja da addinin Allah ku ci amanar matayenku, ku kuntata musu ku saka musu hairan da sharran. Ayi Magana ku kafa hujjah da addini bayan shi addini ne mai adalci ga kowa. Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke tsorata masu niyyar Musulunta su ga addinin Musulunci very scary, don baku da sanin yakamata da amana, musamman aka zo maganar kara aure.”.
Dr. Mansur kallonta yake sosai cikin idanunta dake ta kwararar da hawaye, ya ce, “To wane Bahaushe ne zai kara aure?”
Idanunta jage-jage da hawaye ta balla masa harara ta ce,
“Ba ga ka nan ba? Ka rasa da abinda za ka saka mini sai da son auren Rayhanah? Hakan ba cin amana bane? Duk taimako da karar dana yi maku?”
Ya kama kanshi yana girgizawa don ma ya rasa ta cewa, ya ce, “Da shekaru hamsin da biyar din zan auri ‘yar sha bakwai? Tukunna ma, wai wace Raihanan kike nufi ne?”
Gaba daya ranshi ya gama baci, Mami ta ga wani irin fushi cikin kwayar idonsa da ba ta taba gani ba. Tsigar jikinshi ta tashi gaba daya, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun kada sunyi jawur.
Ganin yanayin da ya fada yasa ta kasa bashi amsa. Ya mike tsaye zai fice daga dakin yana cewa,
“Lallai kuwa duk inda mace take, komin girmanta da iliminta da shekarunta kamar dabba take”.
“Nice dabba Dacta Na?”
“Ai ina ga ma wata dabbar za ta fiki hankali”.
Ya yi ficewarsa ya rufo mata kofar, ji kake garaam!.
Kai tsaye dakin su Raihan ya shiga, dukkansu karatu suke na Alkur’ani irin (pieces) din nan mai kowanne izfi biyu. Su kan taru ne har Azizah da ta dan kara tasawa duk sati biyu suyi saukar Alkur’ani, su yiwa kansu da iyayensu addu’a da ‘ya’yan da za su haifa a gaba.
Bai tsaya ba ya ce, “Rayhanatu ke da Azizah ku yi shiri zamu tafi Abuja karfe shida na safe in Allah ya kaimu”.
Suka daga mishi kai ba tare da sun katse karatun nasu ba.
****
Daddy na sharara gudu a kan titin Abuja da Rayhanah da Azizah, Azizah na gaba Rayha na baya. Basu jima da fara tafiya ba Azizah ta yi barci, don haka Daddy ya mika hannu ya rage mata karfin A.C.
Karfe goma sha daya na rana suna Abuja. Sai da ya kaisu suka yi break fast sannan suka karasa British House dake Maitama, suka bi layin neman visa. Don haka zuwa karfe biyar na yamma sun dawo Kano. Ya sauke su, ko gida bai shiga ba ya kada kan mota ya yi asibiti.
Ga mamakin Rahane sanda suka shiga falo Mami na zaune a kan carpet cikin wani yanayi da Raihanah ba ta taba ganinta a ciki ba. Tana yi mata wani irin kallo kamar ba ta san daga inda ta fito ba.
Ta yi sallama, Mami ba ta amsa ba, sai juyawa ta yi kan Azizah ta soma fadin “Da izinin wa kika tafi rakiyar? Kin gaya mini?”
Jikin Rahane ya yi bala’in sanyi. Azizah ta soma kyarma don ta san fushin Mami ba kyau, kamar ta saki kuka ta ce, “Mami kina barci lokacin, Daddy ya ce in shirya mu tafi”.
Ta ce, “Wuce ki ban wuri ko in yi kwallo dake wallahi”.
Da gudu Azizah ta karasa daki inda ta tadda na Abida na jiranta, ta harareta ta ce, “Ke yanzu don lalacewa shine kika raka wannan jakar yin visar fita waje tare da ubanki, ita ba matarsa ba, ba ‘yarsa ba, ba kowan kowa ba babu dangin iya babu na Baba?”
Jawahir ta ce, “Ai ba ita za ki gayawa haka ba, wanda ya yi mata umarnin zuwa rakiyar shi ya kamata ki je ki yi mishi wannan tunasarwar ba ita ba”.
Ta ballawa Jawahir din harara ta ce, “Nasa dake a ciki? Na ce na sa ki?”
Yadda ta hayayyako mata sai ka rantse da Allah ita ce babba ba Jawahir din ba.
Ta ce, “Sai na ji duka sannan in baki amsa”.
Abida ta yi tsaki ta fice daga dakin.
Mami ta juya kan Rayhanah ta kalleta da kyau, jikinta a matukar sanyaye ta kasa cira kafa daga inda take, a darare ta ce, “Mami mun dawo”.
Tace “to barkanku da zuwa”. Ta shige dakin ta ta bar ta anan.
Ta kwanta a gadonta amma barci ya ki zuwa. Hankalinta a masifar tashe yake. Me ya faru da Mami? Me ta yiwa Mami ta canza mata haka farat daya kamar ba ta taba saninta ba?
Yadda ta kwana da wadannan damuwoyi da tambayar kai da rashin mai amsa mata, haka Dacta Asma’u ta kwana.
Sai dai ita nata damuwoyin nema suke su fitar da ita daga hankalinta da tunaninta. Takun sakar da suka yi da Dr. Mansur ranar da ya kawo Rahane ke dawo mata filla-filla. Suna shiga sikeli na optical-illusion, wato tana fassarasu da abin da ta gani a fuska, ba wanda ke cikin zuciya ba.
Cewa da ya yi, “Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa, ki sa ranki a inuwa sassanya, Allah zai bawa Rayhanah miji na ban mamaki, wanda zai kaunace ta domin Allah, ya rungumeta da LALURAR ta, ba lallai ‘ya’yanki ba, masu hali da dabi’u irin naki. ‘Ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba, sannan basu fi ‘ya’yan kowa ba!!! MAZA ma tukunnah, baki gansu ba Mami.....” Wanda a yau ta fassarasu kai tsaye, yana nufin shi da kansa zai auri Rayhanah!!!
Tunanin Mami ya gushe kwata-kwata, ta yadda da fassarar zuciyarta. Daman ita mace duk shekarunta da hankalinta, da iliminta in aka zo batun KISHI gushewa suke yi.
Tun daga wannan ranar Rayha ba ta kara ganin hakorin Mami a gidan nan ba, ita ba ta kore ta ba, amma ta fita sabgarta. Ita da Abida take sha’aninta ko Jawahir ta san Mami ta canjawa Rahane fuska. Damuwar duniya ta yiwa Rayha yawa.
To wa za ta gayamawa damuwar da take ciki ya taimaketa koda da shawara ne? Babu, Yaya Khalipha ne da Jawahir, to amma wace ce Jawahir kuma wane ne Khalipha? ‘Ya’yan Mami ne, za ta kai musu karar mahaifiyarsu ne ko ya ya? Me ta yiwa Mami? Rashin wadannan amsoshin sai su sa ta kwantar da kai cikin cinyoyinta ta yi ta kuka.
A haka aka gangara har sati biyu. Daddy ya je Abuja ya karbo visa. Ko da ya dawo ko Mami bai tsaya nunawa ba balle ya bata lokacinsa wajen yi mata bayani.
Gaba daya ya fita sha’aninta tun ranar da ta yi masa wannan haukan. Muraran ya gane yanzu kam bata bayan zaman yarinyar nan a gidanta. Don haka ya tattarata ya watsar ya gani ko da gadon ubanta aka cika aka saya mishi gidan? Ya tabbata da hakan ne da tuni ta koreta watakila.
Ranar tashinsu ta kama Asabar, Azizah ce ‘yar rakiyar Rahane. Ta Lagos suka tashi a daren Lahadi, da shi da Dr. Imam, Rayha da Azizah.
A cikin jirgin ‘boeing 709’ da suke ciki Rahane kanta ta kwantar a kujerar dake gabanta, ba ta kuka sai tunanin rayuwa da kalubalen da ke cikinta.
Daddy ya juyo ya mika mata wani kyakkyawan carbi dan Madina ya ce ta yi ta maimaita “Wa-man-nasaru illa min indillahil Aliyul Azeem, Allahumma ashfiny wa afani, ya shaafee ya mu’afee”. Har suka sauka.
A Aberdeen suka sauka, basu kwana ba a ranar suka wuce ‘Braemar Village’ ta Aberdeenshire.
Ba kamar yadda suka tsara ba, cewa za su sauka a hotel. Dr. Philips ya ce, “A’a, yana da gidan gona a jikin gidansa inda yake kiwon kaji da tattabarun Ingila farare sol da agwagin ruwa, kifi da kangaroo (babba da jaka).
A cikin wannan gidan dakuna ne falle biyu ko ko a ce hut, domin hutawarshi da iyalinsa ko sauke bakinsa na nesa. A nan ya yiwa su Daddy umarnin su sauka, har su ga abin da Allah zai yi. Amma bai dauki nauyin abincinsu ba (kun san Bature) da tsimilmila. Duk da haka ya yi umrnin Rayha da Aziza su zauna cikin iyalinsa.
Matar Dr. Philips ita ma dattijuwa ce ‘yar shekaru hamsin, sunanta Mummy Regina. Amma da wuya ka bai wa Regina wadannan shekaru a zahiri za ka ba ta arba’in da uku ko da biyar ne. Baturiyar Dundee ce, kuma tsohuwar lauya mai zaman kanta. Yaranta biyu, Cynthia da Chelsea duka ‘yammata ne a jami’ar Aberdeen.
Sai dai sun girmewa Rayhanah sosai, don dukkansu degree holders ne a bangarori daban-daban. Yanzu haka ita Cynthia MBA take yi (Master of Business Administration). Chelsea kuma ba ta fara masters din ba tukunna. Turawa ne ‘yan asalin Sikotilan iyaye da kakanni.
Kauyen Braemar kauye ne mai tsohon tarihi a Scotland. Braemar wani dan kankanin kauye ne a tudun Grampian (Grampian High Land) wanda ke yankin Scotland.
Braemar kauye ne mai kayatarwa da za ki ga gulbi na kwarara a kan duwatsu masu dadadden tarihi, ga tsaunika masu kyau tare da tsofaffin gine-gine na gargajiya, wanda suke ba da wani launi mai ban sha’awa. Kyawun kasar Scotland ya shafi wannan kauye na ‘Breamer’.
Akwai wani dutse dake mahadar kogunan ‘Clunie’ da ‘Dee’ ya zama wata mahada ta shakatawa ga