Showing 42001 words to 44561 words out of 44561 words
nutsu ki gane.’’
Bintu na mai share hawaye sai gyad'a kai kawai ta ke. Inna Salti na mai nisawa ta k’ara da
‘’Ki ji ki k’i ji, ki gani ki k’i gani, ki iya harshenki, hatta bangon fada kunne gareshi, ki kyautata dangantakarki da kowa, ki sa Allah a ranki, ki yawaita addu'a da zikiri, ki kasance mai yawan zama da alwala, shin kin iya azkar?’’
Bintu ta girgiza kai alamar ah ah,
Inna Salti na mai gyad’a kai ta ce
‘’Zan yi k’ok’arin sawa a koya miki kan a kai ki ga Fabarusa, ki na yi safe da yamma, ni ma da kika ganni anan addu'a ce da tawassali ga Allah kad’ai ke zaunar da ni a wagga Masarauta bare kuma Masarauta mai girman gaske kamar Fabarusa.’’
Jakadiya ce ta shigo, yayinda ta zube gaban Inna Salti cike da girmamawa duk da dai ba yin Inna Salti ta ke ba, ba ta yi mata kyauta da cin hanci kamar sauran matan Sarki.
‘’Barka da hantsi ranki shi dad’e.’’
‘’Barka dai Jakadiya, na sameki lahiya?’’
‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e.’’
Kana Inna Salti ta maida dubanta ga Bintu ta ce
‘’Inaso na san adadin bayin da za su bi Bintu Masarautar Fabarusa.’’
Jakadiya na mai gyara zama ta ce
‘’Akwai Ladiyo da Kyallu, wanda Gimbiya Binta ce ta za6esu da kan ta....’’
Jin haka sai da Bintu ta d’ago ta dubi Jakadiya cike da fad’uwar gaba, don kuwa ta san hakannan siddin Gimbiya Binta ba za ta ta6a za6a mata kowani abu ba, muddin ba sharri ba ne. Ita kuwa Jakadiya da ba ta san ma ta na yi ba, ba ta gushe cikin jawabinta ba
‘’Sai kuma Uwanini, amintacciyar baiwar Yarima Nuhu wanda shi da kansa ya buk’aci hakan.....’’
Ihu ne kawai Bintu bata kurma ba jin wannan masifar da ake shirin had’a mata, maganar Inna Salti ne ya d’an kwantar mata da hankali, jin ta ce
‘’Ita fa Bintu? Shin an tambayeta ko ta na da baiwar da ta ke son tafiya da ita?’’
Jin haka Jakadiya ta kai kallanta ga Bintu, ta ce
‘’Bintu shin ko kina da wannan buk'atar gide? Wa ki ka za6a”
Bud’ar Bakin Bintu sai cewa ta yi
‘’Innata, dan Allah a tafi da Innata’’
Jakadiya na mai girgiza kai ta ce
‘’Innar ki gobe goben nan za su yi bulaguro zuwa marad’i bisa ga umarnin Babban Bijimi, har sai an sami lafawar al’amura za su dawo, sai dai fa ki za6i wata baiwar.’’
Nan da nan Bintu ta fashe da kuka jin Innarta za su bar gari, Inna Salti ta fara k’ok’arin rarrashinta Jakadiya ta ce
‘’Ai da kin kyaleta ranki shi dad’e, abun ga ne ya zo ga ma su shi, kukan amre da sallallami '’
Inna Salti ba ta fasa rarrashin Bintu ba, har ta samu ta d’an yi shiru kafin ta k’ara bata za6i, inda ta za6i aminiyar Inna kuma mahaifiyar k'awarta Cangwai, wacce aka fi sani da Maman Cangwai.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[5/15, 7:44 PM] +234 703 962 5239: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
Na gaishe ki aminyar arziki Ummi Aysha, ina alfahari da ke. Allah ya bar zuminci🤝
©Khadija Sidi.....✍🏼
2⃣6⃣
Da yammaci Inna ta zo mata sallama d’auke da su langar tuwo da miya, da humra da turaren wuta. Tun zuwanta Bintu ta ke kuka, har yanzu da Inna ta ke mata jawabi kamar haka
‘’Bintu kar ki damu, wani hani ga Allah baiwa Bintu. Ki yi addu'a Allah Ya sa hakan da ya zo mana shi an alkahiri, ina so ki sani Allah ne ya za6a miki wagga rayuwa da za ki shiga, ki sa Allah a ranki shi kad’ai zai miki gata.’’
Bintu ta gyad’a kai alamar toh.
‘’Duk da amren ga ba a san ranmu za a yi ba, ki na jinin barebari ba zan bari ki tafi haka ba, wagga(ta nuna kwalaban turarukan da ke aje gaban Bintu da yatsa) tun kina shekara biyar a duniya na had’a mi ki su na binne da niyyar sai amrenki ya tashi na hak’o, wannan kuma langar tuwo da miya da cokali da ludiya wanda na fara miki taro ne, duk da dai na san ba lalle ba ne a bari ki tahi da su ba, gashinan dai na baki a matsayin uwa, na hita hakkinki.’’
Bintu na kuka ta ce
‘’Wallahi ba na so! Ba na so Inna! Inna makaranta na ka so, dan Allah Inna ki taimaka kin ga dai sati uku ya rage mu koma....’’
Rungumeta Inna ta yi cike da tausayawa, Allah kad’ai yasan iya adadin lokacin da su ka d’auka a haka, kafin Bintu ta zame jikinta daga na Inna, kayanta ta nufa ta na mai bincikawa, nan ta fito da turarikan da Aisar ya bata, ta dawo ta durkusa gaban Inna, ta na mai mik’a mata ta ce
‘’Inna ga wagga, dan Allah ki kar6a ko da kuwa ba za ki yi amfani da su ba, wannan kyauta ne tsakanin uwa da d’iyarta, dan Allah Innata, wagga shi ne kad’ai abunda na mallaka nawa na kaina’’
Hannun Inna na rawa ta kar6a ta na mai fad’in
‘’Allah Ya sadamu da alkhairinsa d'iyar arziki, Allah ya sada mu ko da a darussalamu ne, saduwa ta alkahairi......’’
Kuka ne ya su6ucewa Inna, nan su ka yi mai isarsu, har dai Inna ta ga abin ba na k’arau ba ne, dakyar ta janye jikinta ta fice ta na jiwo kukan Bintu.
Yarima Nuhu kuwa har da jinya don kuwa babu yanda baiyi ba na ganin an fasa aurennan amma abu sai dad'a kankama ya ke, haka kuma ya so k’ara ganin Bintu amma Jakadiya ta k’i. Ta wannan dalili ya sa ko ganin Gimbiya Binta ba ya san yi, don kuwa ba zai manta da asarar da ta jawo masa da kuma halin da ta sanyashi ciki ba. Haka kuma bai fasa zayyanawa amintacciyar baiwarsa yanda ya ke san ta kula da al’amuran Bintu yanda zai kasance ba zai cutu ba har ya samu ta dawo gare shi.
Ana gobe d’aurin aure da daddare aka yiwa Bintu k’unshi irin na amare. Yanda ta ga dare haka ta ga rana, haka ma Yarima Nuhu wanda zazza6i ya rufe har da k’arin ruwa. Aisar kuwa farin cikin zai ga Bintu ne ya hana shi bacci, don da an bi ta tashi da tun aranar zai d’au hanyar Sa’ayrasa, sa idon Junaidu da gudun sharrinshi ya sa ya hakura. Haka ma Yarima Barde wanda farin cikin zai had'u da Gimbiya K'amariyya ya hana shi bacci, da ita kanta Gimbiyar.
******* ******
Washegari tun da sassafe Jakadiya ta sa Bintu wanka da wani ruwan magani gudun kar bak'in da su ka zo daga Fabarusa d’aurin aure su buk'aci ganin amarya, ko kuma Sarki Abdulrahman da kansa ya buk’aci hakan bayan an d’aura masa aure da Bintu ba tare da an shiryawa hakan ba. Leshi fari kyal mai adon koren duwatsu ta ce ta sanya. Farar alkyabba Jakadiya ta d’aura mata bisa, da wani takalmi kore. Kai da ka ga Bintu ka ce d’iyar Sarkin ce, ita kanta Gimbiya Binta da ta shigo ta gan ta sai da ta girgiza, ta kasa zama bare kuma dama tunda Allah ya wayi gari ta ke fama da fad’uwar gaba na ba gaira ba dalili.
‘Bangaran d’aurin aure kuwa, misalin sha biyu na rana tuni babban masallacin fada ya cika mak’il da jama’a, mutan Fabarusa, Mai Martaba Sarki Abdulrahman ya iso tare da tawagarsa, hakimai da dogarai, har da ‘ya’yansa biyu, Sadauki da na shi abokan, haka ma Barde da abokansa biyu, d’aya taubashinsa(cousin) wanda ake kira da Yarima Jafar, sai kuma d’ayan mai suna Khalil wanda ya ke babansa hakimi ne a Masarautar Fabarusa.
Haka ma su Aisar tare da Ministocin da su ka taho wakiltar mai girma shugaban k’asa, sun sami isowa, inda aka musu mazauni daga cikin Masallacin. Ba k’aramin kyau Aisar yayi ba, dan kuwa ado ya sha na burgewa musammam saboda Bintu. Dokakkiyar shadda ce jikinsa, ruwan toka, ya sha d’inki da aiki irin na manya, ga hularsa da takalminsa kalar zaran da aka masa aiki da shi, wato ruwan toka mai turuwa, da ka gansa ka ga d’an manya masu ji da mulki. Allah Allah ya ke ayi d’aurin auren a gama ya nemi Bintu don shi ita kad’ai ta kawo shi cikin wannan taro, yak’i jinin taro saboda yanayin aikinsa.
Yarima Barde kuwa daga waje yayi zamansa, gudun kar ya shiga ciki taro da turnak’in jama’a su hana shi ya fito da wuri don zuwa ga sahibibar ta shi wato Gimbiya K’amariyya. Sanye ya ke cikin farar shadda d’inkin babbar riga, ga rawani ya sha kai, ka ce za a kira shi Sarki ya amsa. Ango kuwa Sarki Abdulrahman tare da hakiman sa da kuma su Sadauki suna daga cikin masallaci.
Dake taro ne na manya da Sarakuna, shaddodi kala-kala tsadaddu ki d'aukar ido da kukama kalar kayan dogarai daga Masarautu iri-iri, abun dai ba a cewa komai, don kuwa wuri ya yi wuri, taro ya yi taro sai kamshi da kid’an algaita, kirari da kiran lafiya na dogarai da marok’a ke tashi. Sarakunan yanki da sassa na cikin jamhuriyyar Nijar babu wanda be sami halarta wajan ba, Sarkin Agadaz ne, Diffa, Marad’i, Zindar da dai sauran su.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[5/15, 8:24 PM] +234 703 962 5239: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
💌 SAK'ON NA MASOYA NE🤗
Ina godiya da babban murya ga masoyan Bintu d'iyar bayi, na gida Nigeria da kuma mak'ota Nijar. Ina alfahari da ku.
Sidiya ce ke mu ku fata na alkhairi🤝
2⃣7⃣
Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci waliyin Ango da Amarya su matso kusa. Waziri ne ya fito daga 6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki Abdulrahaman ne ya nuna kan sa a matsayin waliyi.
Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi ina hankalinsa na ga Gimbiya K'amariyya, Allah Allah ya ke a shafa fatiha ya tafi garera don jin soyayyar ta ya ke har ransa, bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za ta kau, za su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an shafa fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in.
‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’
Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin marok’a na fad’in
‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya Fatima* akan sadaki (50000 CFA)"
Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga abokannasa ya na mai fad’in
‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da Gimbiyata.’’
Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin hali ya ce
‘’Da ma kai ne Barde?’’
Cikin rashin fahimta Barde ya ce
‘’Ni ne wa?’’
‘’Angon da aka amrawa amren.’’
Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce
‘’Saurara ka ji Barde’’
Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya doki kunnan Barde, fad’i ya ke
‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya Fatima....’’
Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu abokannasa sun girgiza kwaran gaske.
Daga cikin masallaci, ana gama d'aurin auren, inda kowa ya ke mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar Sa'ayrasa, shi kuwa Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a yake, domin zuwa neman Bintu ba tare da Junaidu ya ankare ba. Bayin Sa'ayrasa ne d’auke da farantin goro da alawa, su ke bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d'iba san ran su.
Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk'ata, har bawan zai wuce, nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa Bintu ne cikin yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko shakka babu ya san tawagar shugaban k’asa ne gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran ‘yan tawagar garesu. Aisar na mai duban idanun bawan ya furta
‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’
Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau kwarai cikin jajayen kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo kar6ar mabudin wajan aje baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde.
Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko mata mabud'in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni hanjin cikin Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an yiwa mai dami d’aya sata, aure dai an aura. Tuni ta fashe da kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta.
Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo jiki na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami. Jakadiya ce ta tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya koma gareta.
Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai fad’in
‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata hud’u.’’
Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’
‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya k’arewa sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na Fabarusa cike ya ke da abin mamaki, wani lamari sai shi.....’’
‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’
Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce
‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata, sai ya amrawa d'ansa Barde Bintu.....’’
Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta. Bintu kuwa yanda maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta zama kurma, don kuwa ba ta jin hayaniyar da ake gabanta
‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu....’’
Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan.
Tammat Bihamdillah
Nan na kawo k’arshen Bintu d’yar bayi ce kashi na farkon, sai a dakace ni zuwa bayan sallah da rai da lafiya. Ina mai mu ku fatan yin azumi cikin k'oshin lafiya. Dan Allah ku saka kawuna marigayi Alhaji Aliyu Abdullahi Sidi (A.A Sidi) cikin addu’a, Allah ya ji kan sa da rahama.
Allah ya sada mu da alkhairin sa. Sidiya ce ke mu ku fatan alkhairi.
HASKE
Sa'ayrasa
S anah
Ay aisha
Ra shida
Saƙlma
Fabarusa
FA=Fatima/Farida
B=Batool
R=Rufaida
U=Ummuabdoul
S=Sidiya
A=Asma'u/Bingel.
Monsieur Malam
École Makaranta
Madame Malama
Ciseaux Almakashi
Gide Ke
Hallo Kuma/ haka zalika
Rariya Waje
Aratta kashe ni
Kwankwatsi
Aradu Rantsuwa
Kwana Bacci
Amre. Aure
Wagga/wanga Wannan
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪