Showing 12001 words to 15000 words out of 44561 words

Chapter 5 - Bintu Diyar Bayi Ce 1 Complete Hausa Novel

06 Jan 2025

149

da ya sa ta kyebewa d Malami, kut Malamin ma wanda na ke so dan uban ta? Yau sai ta lashi kashin b’and’akin k’asa dan uban ta Bintu ta ke kowa? Ta yanki tsiya!" ta wuce fuu, dama ga ta jibgegiya tabarakallah. Su shedigyal su ka rufa mata baya, kai tsaye sashin kwanan d’alibai su ka nufa.

***
Bintu kuwa komawar ta d’aki ta tadda Gimbiya ta dawo tare da k'awayen ta, ko da ta tambaye ta daga in da ta ke sai ta mata k’aryar Iya Dije ce ta aike ta. Ta ci sa’a yan masifar Gimbiya ba sa kusa, hankalin ta na kan labarin da Zahira ta ke ba su. Can gefe Bintu ta zauna ta na mai mamakin dalilin da Aisar ya fad’a mata na zuwa ganin ta. Zaman ta ke da wuya ta ji ana kwala mata kira "Bintu Bala Mahuta dan uban ki sauko!’’

Ba Bintu ba hatta su Gimbiya sai da su ka kasa kunne su na jiran tsammani. ita kuwa Bintu jikin ta ne ya hau b’ari jin muryar Marry da gaba d’aya ya 6angaran d'akin kwanan d'alibai. Gimbiya ce ta kai kallan ta ga Bintu ta na mai tambayar ‘’yar nema me kuma ki ka yiwa wannan mai fasalin mazan?’’ Bintu ta kasa magana tsabar tsoro, nan fa su ka k’ara jiyo har gowar Marry ta na mai fad’an ‘’dan uban ki na ce ki sauko kimin bayanin wani malami ki ka kyebe a bayan aji!’’

Nan fa Bunti ta kware saboda firgici da tsoran maganar da Marry ta furta, inda Gimbiya, Zahira da Ruqayya su ka tashi tsaye a a tare, Gimbiya na fad’in ‘’ki tabbatar wannan malamin da ake magana akai ba Malam Aisar ba ne!’’

Can waje kuwa tuni d’alibai kowa ya fito jin shela da tonan siririn Marry, wasu ma babu cikakken sitiran arziki jikin su haka su ka fito bawa idanun su abinci dan kuwa sun san koma wacece wannan ta shiga hannun Marry ta kad’e har ganyen ta, musammam jin ance "ta kyebe da Malami."

"BINTU BALA MAHUTA! Ko ki sauko ko na zo na sauko da ke ta!’’ fad’in Marry ta na mai kumfar baki.
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

©Khadija Sidi.....✍🏼

0⃣7⃣

Babu shiri Bintu ta tashi da sauri, jin Mary na maganar sauko da ita ta ka ta san muguntar Mary za ta aika. Hanyar fita ta nufa ta na jera adduoi iri-iri, ta kama wannan ta saki, wani ma ko k’arshen shi ma ba ta iya kai wa. Su  Gimbiya ma ba su yi k’asa a gwiwa ba, biye su ke da ita, ita dai burin Gimbiya ta ji shin da wa Bintu ta ke6e, idan kuwa Aisar ne sai na lahira ya fita jin dad’i, dan kuwa a daren ranar kwanan Sa’ayrasa ne ya kama ta.

Ganin Bintu ba ta jira ta k’arasa gabanta ba, ta na haki kamar zakanya ta fizgo ta, ta hard’e kafar ta sai ga Bintu zube gabanta cikin ca6al6alin ruwan sama "Rage tsinannan tsayin naki dan ubanki,  shiyasa ki ke tunanin kin balaga kin isa ke6ewa da malamai." Fad’in Mary ta na mai shararawa Bintu mari. Bintu durkushe bisa gwiwowinta,  hannunta bisa kuncinta inda hawaye ke gangarowa daga idanunta, fad’i ta ke ‘’Ina tuba  Anty Marry, ki gafarce ni, kimin rai’’

Fili ya cika maki’il da d’alibai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa, da masu tausayawa Bintu musammam da su ka san ita ba ‘yar kowa ba ce ta shiga hannun Marry, da ma dai ita d’iyar masu mulki ko sarauta ce da duk jarabar Marry sai ta saurara mata gudun abun da zai je ya dawo. Sai  kuma masu mata Allah shi k’ara. Wani wawan mari da Marry ta dad’a kaiwa Bintu, sai ga Bintu a k’asa, sunkuyawa Marry ta yi, hannu bisa kan Bintu ta kama gashinta, ta fisgo ta cikin zafin nama, sai da Bintu ta runtse ido tsabagen azaba. Cikin rad'a ta ce "Ke da wani Malami ki ka ke6e a sashen karatu?’’
Idanun Bintu runtse, da kyar ta iya furta ‘’Ina tuba Anty Marry’’ Cike da mugunta Marry ta fizgi gashin Bintu kamar mai shirin raba gashin da fatar kan Bintu, wani kuka Bintu ta saki, sai ga kallabin ta hannun Marry, inda gashin da dama nad’e shi ta yi cikin kallabi ya warware, sai gashi ya sauka har gadon bayan ta. Ba Marry da su shedigyal ba, hatta sauran d'alibai sai da su ka yi mamakin kyawun gashin Bintu, da ke kullum kanta d’aure ya ke da kallabi, idan ba tsautsayi ba, babu wanda ta ke bari ya gani.

Sikanti ba ta san sanda ta ce ‘’Car uban nan, gide akwai mai irin wannan gashin cikin makarantar nanniya?” Shedigyal da wani bakin kishi ya rufe ta ganin gashin Bintu cewa ta yi ‘’Wannan har wani gashin azo a gani ne?’’

Marry kuwa da tuni ta yi mutuwar tsaye, hannun ta rik’e da kallabin Bintu, murmushin mugunta ta saki, ta na mai jinjina kai ta ce ‘’Sikanti ba ni aran almakashina  ki.’’ Gaban Bintu ne yayi mummunar  fad’uwa, ta d’ago idanunta da su ka yi jajur ta na mai duban Marry. Marry na murmushi ta gyad’a mata kai ta ce "Gashinki zan yanke muddin ba ki fad'a min da wanda mu ka ganki ba, bayan kuma kin fad’amin na kai  bayin k’asa ki lashe kashin yan aji d'aya da su ka yi da harshen ki.’’

Wani sabon kuka Bintu ta saki, musamman jin Sikanta ta tura wata yar aji d’aya ta d’auko mu su almakashi. ‘Dalibai ta bi da kallo cikin neman d’auki, amma sam ba ta ga mai niyar taimakon ta ba, kowa na tsoran sa baki kada gobe idan an je wajan matemakiyar shugaban makaranta wacce ta ke mace ce, a ce har da su, suna ji suna gani a had’a da su. Idanunta ya sauka kan Gimbiya, ta watsa mata harara dan ita ko a jikin ta, Ita so ta ke ma a zo a yanke gashin Bintu ko ta samu ta ji wani Malami ne aka gan shi da Bintu, dan kuwa ta san tun da Bintu ba ta musa ba ko shakka babu da gaske an gan ta d’in ne.

Hankalin Bintu be dad’a tashi ba sai da ta ga an mik’awa Marry almakashi, yayinda ta tsugunna, ta sa hannu ta tattare gashin Bintu cikin hannun ta, wanda rabi kad’ai ta iya kamawa tsabar cikar gashin Bintu,  tsakiyar gashin ta sai ta almakashin na ta, ta na mai fad’in ‘’Gide da wani Malami mu ka gan ki?’’

Bintu da ta za6i masifar da hukuncin Marry akan na Gimbiya, ta kasa bud'ar baki ta furta sunan Aisar, sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’Ki yi hakuri, ina tuba, ba zan k’ara ba.....’’

Jin sautin almakashi ya na ratsawa cikin gashin ta, da kuma sautin mamaki da ya fito daga bakin d’alibai ne ya katse amsar da ta ke bata, idanu runtse yayinda zafafan hawaye su ka zubo daga idanun ta, jin saukar jelar rabin gashin ta k’asa.

‘’Lah'ilaha'illallahu’’ Fad’in Iya Dije wacce dawowar ta kenan ta shigo dan ganin ko Bintu ta koma d’akin ta, ta tadda d’alibai sun yu da'ira, ta na kutsawa ciki Marry na yanke jelar rabin gashin Bintu. Da saurin ta k'arasa in da Bintu ke tsugunne gaban Marry, Shedigyal da Sikanti, ta yi saurin d’ago Bintu ta na mai fad’in ‘’Yo menene zan gani ni Dije?!! Gide wannan wani irin rashin hankali da zalinci ku ke yiwa yarinyar nan?!!! Gide   akan wani dalili?!!! Gide  wa ya ba ku wannan lasisin?!!’’ Ta shiga jera mu su tambayoyi kamar mai shirin taya Bintu kuka ta na mai duban gashin Bintu da su ka yanke.

Ba tare da nuna nadamar abun da ta yi ba Marry ta amsa mata da ‘’Kama ta mu ka yi ta ke6e da Malam Aisar....’’ Waje ya kaure da hayaniyar d'alibai, Gimbiya kuwa kukan kura ne kad’ai ba ta yi ba ta je ta shak’o wuyar Bintu.

Ran Iya Dije idan yayi dubu ya 6aci, kallabin Bintu ta fizge daga hannun Marry yayinda ta mik’awa Bintu ta na mai fad’in ‘’Gide daura ki koma d’aki, kar ki damu ni Dije sai na bi mi ki hakkin ki, aradu ma kuwa" A sanyaye Bintu ta karbi kallabin, har lokacin kuka ta ke, gaba d’aya kayan ta ya b’aci da ta6on ruwan sama da ta kwaso, kan ta sun kuye ta shige ciki. Bayan tafiyar ta Iya Dije ta mayar da kallan ta ga su Marry kana ta ce ‘’Ni Dije ni na ce Malam Aisar ya bar min sak’o wajan Bintu kasancewar ba zai same ni ba, kuma sak’on ba na kowa ba ne face sak’on Malam Hashim.’’

Wato daga Marry, har shedigyal da Sikanti babu wanda bai tsorata ba cikinsu, dan tabbas sun san matsayin Iya Dije gun Malam Hashim, da sun san da sa hannunta da ba su yiwa Bintu abun da su ka yi mata ba. Tuni idanunsu ya raina fata, cikin kame-kame Shedigyal ta ce ‘’Yetto Allah shi an sheda na hallau daliban nanniya su assheda na, yatsa ban kai ga jikin yarinyar ga ba, idan k’arya na kai aratta kashe ni."

Ko da jin haka Sikanti ma ta yi saurin d’age hannu sama ta na mai fa’d’in ‘’Balanta  ni hallau Marry na rako’’ Marry kuwa da ta san k’iri-k’iri Iya Dije ta ganta tana yanke sumar Bintu, jikin ta ne ya hau b’ari, kana ta yi k’ok’arin jan Iya Dije gefe domin bata wani abu dan kuwa kowa ya san Iya Dije da san abun duniya. Amma Iya Dije ta yi kyememe ta k’i sauraronta, sai ma barin ta ta yi awajan ta yi tafiyar ta. Tuni makaranta ta d’auka gobe Marry za ta sha horo, har da masu shagali dan murna. Gimbiya kuwa duk da jin Iya Dije ce ta tura Bintu gun Aisar ba ta fasa mata bambamin wai akan me ya sa ba ta fad’a mata ba ita je a madadin ta tun da ta san ta na san shi, ko damuwa da abun da Marry ta yiwa Bintu ba ta yi ba bare ta saurara mata.

Da daddare Iya Dije ta kira Bintu ta na mai jaddada mata kar ta damu, ita za ta tsaya har sai an bi mata hakkin ta, ita dai duk abun da Iya Dije ta ce gaban Malam Hashim ta amsa mata da eh. Da ke Bintu mace ce mai yafiya sai cewa ta yi ‘’Dan Allah Iya Dije ki bar ta kawai ba sai kin wani bi min hakkina ba, Inna ta tace kowa yayi na gari dan kan sa’’

Iya Dije na mai girgiza kai ta ce ‘’Wagga gaskiya d’aita, amma wannan maganar ban barin ta ko dan rufin asirin kai na, aradu ma kuwa!  Yo ki na tunanin idan shi Malam Aisar d’in ya ji bari zai yi? Abun da dai ya fi sauki ki yi yanda na ce kin ji ya?'’

Da wannan su ka yi sallama. Daren ranar Marry kuwa kasa bacci ta yi tsabagen fargaba, gashi ta cire wa d'iyar mutane suna, gashi duk abun nan da ta yi a banza tun da da sanin Iya Dije, babban tashin hankalin ta shi ne matakin da Malam Aisar zai d'auka idan ya ji abin da ta aikata. "Kar dai fa ace ita d’in sai an yanki rabin gashin kan ta!'’ Abin da zuciyar ta ke raya mata kenan, yayinda ta ke kwance bisa gadan ta, kowa yayi bacci ya bar ta. Sai shafa d’an gajeran gashin da be ma kai kamu d'aya ba ta ke, ta san lalle idan da za a cire shi duka ko kwatan wanda ta cirewa Bintu ba zai kai ba. Girman kai ya hana ta iya zuwa ta bawa Bintu hakuri ko ta sami rangwame, "Ni Marry gide tawa ta same ni kishiya tara rana d’aya’’ Ta fad’a a fili yayinda ta tashi zaune ta na mai d'aura han[truncated by WhatsApp]
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



©Khadija Sidi.....✍🏼

0⃣8⃣






Tin da Iya Dije ta fara jawabi idanun Aisar da ya k’ada yayi jajur ke bisa fuskar Bintu, wacce ke zaune kusa da Iya Dije kan ta sunkuye. Zaune su ke offishin Malam Hashim, dan kuwa gari na wayewa ko taron d’alibai(Asembly) ba a yi ba Iya Dije ta ja Buntu zuwa ofishin, ta na cikin masa jawabi ne Aisar ya shigo sanye da wannan shigar na sa da ya saba, wato (suite) amma wannan karan ruwan k’asa ya saka.

Shigowar Aisar babu alamar da Malam Hashim be yiwa Iya Dije na ta yi shiru ba,
amma ina ta kasa d’aukan haske. Hankalin sa ba k’aramin tashi yayi ba ganin Asar ya tashi tsaye a fusace ya na mai maimata ‘’ta saka Ciseaux (Almakashi) ta yanke sumar Bintu!’’ shima Malam Hashim d’in tashi yayi, ya na yiwa Iya Dije alama da ido na ta rufa asiri ya ce "Ciseaux kuwa uwa Iya Diya?’’

Ita kuwa Iya Dije amsawa ta yi "kwankwatsi ma kuwa, ba mai bi na bashin rantsuwa, ai ga d’iyar nanniya(ai ga yarinyar nan), gani ya kori ji’’ kan Bintu ta ankara iya dije ta ja dan hijabin jikin ta, sai ga daga hijabin har kallabin na ta hannun Iya Dije, dan kunya kamar k’asa ta tsage ta rufe, musammam yanda rabin gashin na ta ya sauka har gadan baya, rabi ya tsaya iya wuya. Ta so yanke sauran dan ta daidai ta su amma sammakon da Iya Dije ta doka mata ya sa ba ta sami dama ba.

Cike da tausayi Aisar ya ke duban ta, ji yake kamar ya ruke ta ya kwashe mata gaba d’aya damuwar ya mayar zuwa kan shi. Gashi saboda shi an wulak’an ta ta, har aka mata cin zarafi ta hanyar yanke mata suma. Malam Hashim kuwa duban sa ga Aisar ya ke, in da zuciyar sa ke jaddada masa lalle watan rufe wannan makaran ta tasu ce ta tsaya...


"Bintu....’’ ya kira sunan ta cikin wani yanayi ya na mai sassauta kullin nakatayal (Neck-tie) din wuyar sa, dan ji yake kamar numfashi ba ya isar sa tsabagen 6acin rai. Hatta Iya Dije da Malam Hashim sai da su ka kai kallan su ga Aisar, ita kuwa Bintu kasa d’aga ido ta kalle shi ta yi. Malam Hashim ya gyara murya ganin yanayin 6acin ran da Aisar ya shiga ya ce "Ina Iya Dije, zai fi kyau ku d’an ba mu hili (fili) mu zanta da Malam Aisar’’ ta na mai mik’awa Bintu kallabi da hijabin ta, ta ce ‘’ye to ai sai mu fita rariya (sai mu fita waje), Bintu mu tahi ko?’’

Da saurin ta, ta karb’a ta d’aura kallabin kafin ta sanya hijabin na ta, Iya Dije a gaba ta na biye da ita, idanun Aisar kan Bintu har su ka fita. Shiru ne ya biyo baya na wani d’an mintina, kafin Malam Hashim ya d’aure ya ce ‘’na san abun da ke ran ka, amma ina mai tabbatar ma ka makamancin haka be ta6a faruwa a wanga École ba, wanga da ya faru ma tsautsayi ne Monsieur Aisar (Malam Aisar)’’

‘’ka na nufin baka san d’aliban ka su na aje makami a tare da su ba Monsieur (Malam)? Ai na zaci k’aida ne hukumar makaranta ta na bibiyan d’akin d’alibai lokaci lokaci dan binciken kayan su domin gudun irin haka? Me ke faruwa a wanga École ? (me ke faruwa a makarantar nan?) Shin me ku ke yi da har irin haka ka iya faru? Ya ilahi da ta kashe d’iyar mutane fa!!!’’ fad’in Aisar wanda tun da ya fara maganar kansa ke kallan silin. Malam Hashim kuwa zufa ne ya lullub’e shi kana ya ce ‘’lillahi warasulihi Monsieur (Malam) abin ga da ya faru tsautsayi nai, na kuma yi maka alkawarin duk matakin da za ka d’auka daidai ta (daidai ne), amma kar ya shafi wanga École(Makaranta) ’’

Sai a sannan Aisar ya mayar da kallan sa ga Malam Hashim, kana ya ce ‘’wannan laifi ne da ba zan iya d’auke ido akai ba, kasan k’asar mu ta Nijar k’asa ce da ke san jama’ar cikin ta, mai daraja dukkan abu mai numfashin da ke cikin ta, a matsayi na na d’an k’asa mai kishin k’asan ga, na ga irin haka na d’auke kai tabbas na ci amanar k’asa ta’’. Jin haka hankalin Malam Hashim ne ya tashi. Sai gashi ya taso ya zo gaban Aisar ya na mai ruk’o hannun sa ya ce "wanga École (makaranta) ta kunshi d’alibai daga kowani sassa da yankunan jamhuriyar Nijar, ruhe (rufe) ta ba k’aramin asara ba ce ga k’asar ga, kai ka sani k’asar mu na buk’atar makarantu ma su inganci irin Sovereign.......’’

"ka na nufin ita kad’ai ta École mai inganci a wanga k’asa ta mu? (ita kad’ai ce makaranta mai inganci a wanga k’asa ta mu?) Kada fa ka nemi ka zagi k’asa ta Monsieur Hashim!’’ Aisar ya katse shi cike da nuna 6acin rai. Cikin sauri Malam Hashim ya girgiza kai ya ce ‘’ba haka na ke nufi ba Monsieur Aisar, yo to na fad’i haka ban yi ma k’asa ta adalci ba, aradu ma kuwa, École (Makaranta) kuwa masu inganci mu ke da su a k’asar mu, amma ruheta kan iya jawo asarar d’aya daga cikin su, sabida Allahu da manzan sa wanga batu ka duba, duk hukunci da za yiwa wannan d’alibar ka mata ita ta jawa kan ta, yo mi zan ce zanin aro ya toye? amma kada laifin wani ya shafi wani’’

Bayan nazari na wani d’an lokaci Aisar ya ce "ko wani hukumci ka ce Monsieur Hashim?’’ Malam Hashim ya jinjina kai kafin ya ce ‘’ko wani hukunci muddin ba zai shafi wanga École ba, ba zai kuma shafi jarabawar gama sakandiri da d’iyar ta ke rubutawa ba....’’ wani irin kallo Aisar ya watsa masa jin maganar ta sa. Da sauri Malam Hashim ya ce ‘’ba dan d’yar ba Monsieur Aisar, dan cigban k’asar mu, ka ga idan ya shafi jarabawar hallau ya shafi cigaban k’asa ta fannin karatu, k’ak’a ka gani?’’

Tashi yayi ya na bai gyara nakatayal(neck-tie) d’in sa, sannan ya ce ‘’na fahimce ka, zan mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login