Showing 9001 words to 12000 words out of 44561 words
kud’i CFA na gugan CFA har (10000 CFA), fiye da rabin kud’in ta kashe. Bintu ta rasa amsar da za ta bata, ta tsinci kanta tana mai fad’in ‘’Na ga ba na buk’ata ne Iya Dije.’’
Ba ta ankara ba sai ganin Iya Dije ta yi ta d’aga hannunta tana mai k’ok’arin cusa hancin ta k’ark’ashin hammatar Bintu. Da sauri Bintu ta ja da baya ta na k’ok’arin kwatar kanta, fad’i ta ke ‘’Iye Dije ya haka?” Iya Dije kuwa duk da babu abinda ta shak’a na wari daga jikin Bintu don kuwa Bintu irin mutanen nan ne wanda sam ba su da warin jiki, sai ga ta ta yi baya da sauri ta na mai toshe hanci ‘’Kin ji yanda ki ke bugawa ki na hamami kuwa? Har ki ce ba kya buk’ata? Shi kan shi Malam Aisar d’in wannan hamamin na ki ya ji shi ya sa ya ce na tambaya ko ki na da buk’atar turaren.’’
Jin haka kunya ta rufe Bintu, kamar k’asa ta bud’e ta shige. Ta na mai yin k’asa da ido ta ce ‘’Ai idan Gimbiya ta gani ko ta ji ina kamshin turare ma su k’amshi haka Iya Dije kashi na ya bushe’’ Sai a sannan hankalin Iya Dije ya fara kwanciya, ta ce ‘’Yo ba sai ki 6oye yanda ba za ta gani ba, sai ki na sawa kad’an haka, ni dai ba zan mayar da wanga turare ba’’ Ajiyar zuci Bintu ta saki ganin babu yanda za ta yi dole ta hakura ta kar6a ta na mai godiya. Ita kuwa Iya Dije ko da ta samu ta cusawa Bintu turare sai ta sami kwanciyar hankali, dan da ba ta san yanda za ta yi ta biya da kud’in Aisar da ta ci ba.
Aisar kuwa sai da ya tabbatar ya kaiwa Malam Hamisu k’orafinsa kan rashin tarbiyar d’alibai da kuma zaman wata d’aliba a waje lokacin cin abinci ba tare da ya ambaci sunan Bintu ba. Malam Hamisu ya nuna rashin saninshi kan maganar yanayin cin abincin d’aliban, kuma ya yi masa alk’awarin d’aukar mataki. Saidai batun rashin tarbiyar d’aliban ya ce su ma hakuri su ke da su kasancewar kowani tsuntsu kukan gidansu ya ke, amma In sha Allahu za su k’ara tsauri kan lamarin.
Washagari da safe wajan taron d’alibai (Assembly), Mallam Hamisu ya ja kunnan d’alibai akan bin duka, musammam wanda ba sa halartar wajan cin abinci idan lokacin yayi, ya kuma tsawatar da hukunci mai tsanani muddin aka ga d’aya daga cikin d’aliban na aikata hakan. Da wannan Bintu ta sami saukin samin cin abinci tare da yan uwan ta d’alibai duk da kuwa sai da ta sha tuhuma gun Gimbiya akan zargin ko ita ta kai k’arar ta.
Kwanci tashi haka rayuwa ta kasancewa Bintu cikin makaranta. Gaba d’aya gudun Aisar ta ke, tun shi ma bai gane ba har ya zo ya gane ya daina nemanta. Ita kuwa Zahira hakuri ta je ta bashi tare da sa bakin Malam Hamisu ya hak’ura ya bari ta koma ajin na shi. Gimbiya Binta babu irin cusa kai da ba ta yiwa Aisar, amma sam ba ta gabansa bare ya san ta na yi, manyanta ma yan aji biyar da shida fama su ke bare ita karan kad’a miya acikin jerin ‘yan mata.
Da yammacin ranar lahadi, ana saura sati biyu su Bintu su fara jarabawa. Yanda garin yayi wasai, gajimare yayi lub-lub, ciyawa da bishin da ke cikin lambun sun yi kore shar, ga wani ni’imatacciyar iskar da ked’awa wanda sanya rassa da ganyayyakin bishiyun da ke cikin lambun rausayawa suna mai fuzar da feshin ruwa sanadiyar ruwan sama da ya sauka ya kuma tsaya mintina talatin da su ka wuce ne ya sanya Aisar da ke kwance kan kujerar hutun da ke k'ark’ashin d’aya daga cikin rumfunan lambun, in banda kukan tsuntsaye da kuma k’arar saukar sauran ruwan sama da yayi ragowa bisa kwanan rumfar lambun babu abun da ke tashi.
Sanye ya ke cikin bakar riga mai k’aramin hannu, da wando wanda ya ke shi ba gajere ba bai kuma kai masa har k’asa ba. Idanunsa lumshe tamkar mai bacci, ko da yake da zai sami bacci da hakan zai fi so dan kuwa tunanin da ya dad’e ya na damun sa yanzun ma shi ya sa shi gaba. Ba kuma tunanin kowa bane, face na Bintu, musammam yanzu da aikin binciken su ya k’are, Bintun ce ta zaunar da shi a makarantar da tuni ma ya dakatar da koyarwa, dan kuwa dai hakin su ya riga ya cimma ruwa a game da aikin su. Abin takaicin shi ne tsakanin sa da Bintu sai dai a aji, duk yanda zai yi ya ganta bayan aji ya gwada amma abu ya faskara, don kuwa dai Bintu gudun sa ta ke k’iri k’iri. Shi kan shi bai san meyasa ya kasa cire yarinyar daga ransa ba, amma dai yau idan har bai sa ta a idanunsa ba zai iya shiga damuwa. Gashi kuma yau lahadi ko makarantar bai shiga ba bare ya ganta a aji. Nan fa wata dabara ta fad’o masa, ya tsinci kansa ya na mai murmusawa.
Ajiyar zuci ya saki yayin da ya bud’e idanu a hankali jin d’igar ruwa bisa fuskarsa sanadiyar iska da ta kad’o wani reshe zuwa cikin rumfar. Tashi ya yi zaune ya na mai duba lokaci, k’arfe biyar daidai, ya aje hannu inda ya tashi cikin azama ya na mai k’ok’arin zura takalmi cikin k’afafunsa. Kai tsaye ya fice daga cikin lambun, ya bi ta farfajiyar gidan ya shige falonsa wanda zai sada sa da d’akin baccinsa. Cikin k’ank’anin lokaci ya sauya kaya izuwa farar jamfa da hula tare da farin takalmi. Ya gama fesa turaren sa mai kamshin gaske ya wuce cikin motarsa. Hankali kwance ya fito daga gidansa, sai gashi kan titin francophonie, kai tsaye ya nufi makarantar Soverign.
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
©Khadija Sidi.....✍🏼
0⃣6⃣
Minti goma kacal ya kai shi makarantar, Allah ya taimake shi ya had’u da Iya Dije a bakin gate ta na shirin fita kenan. Tsaida Ita ya yi, ya nemi alfarmar ganin Bintu. Iya Dije da tun da ta ga Aisar da yamma haka, gashi ranar lahadi ta san banza ba ta kawo zomo kasuwa, ta yi kud’irin samun wani abu daga aljihun sa. Jin buk’atar ta sa sai ta yi hamdala cikin ran ta, ta na mai gyara tsayuwa ta ce ‘’ai kasan yanayin dokar makarantar ne Malam, an hana d’alibai kebewa da Malamai musammam irin wannan lokacin da ba na d’aukar darasi ba’’
Duk da maganar ta Iya Dije ta yiwa Aisar wani iri, jin ta yi amfani da kalmar ‘’ke6ewa’’ amma sai ya basar, ya na mai murmusawa ya ce ‘’ba ki fahimce ni ba Iya Dije, ba wai tsayar da ita zan yi ba, kawai dai sak'o zan bata, na ga fita ma za ki yi ko?’’ nan fa Iya Dije ta samu mafaka, ta amsa da ‘’eh wlh kasuwa zani, zan saro kaya duk da dai ba wani jarin arziki gare ni ba’’ ganin Aisar ya sanya hannu cikin aljihu jikin ta har rawa ya ke. Ilai kuwa sai gashi ya fito da kud’i CFA na gugan CFA, ba tare da ya k'irga ba ya mik’awa Iya dije ya na mai fad’in ‘’gashi ki k’ara kan jarin na ki’’
nan Iya Dije ta cafe kud’i saura kiris ta had’a da hannun Aisar, fad’i ta ke ‘’kai dai ba ka gajiya, madallah, yo ai in da yarda ai na yarda da kai, bara na kira maka Bintu Bala Mahuta, amma dan Allah kar ta dad’e ka ga dai ni fita zan yi’’
Aisar na murmushin nuna jin dad’i ya amsa da ‘’toh, ina nan kusa da ofishin malamai ina jira.’’ da azar6a6in jiki Iya Dije ta koma ciki ta na k'irga kud’in da aka ba ta.
Bintu na zaune cikin d’aki, kasancewar Gimbiya Binta ba ta nan ta je karatu, itama ta sami damar yin na ta karatun. Sanye ta ke cikin shigar su na bayin Sa’ayrasa dan ba ta isa ta sa kayan gida ba duk da dai yau d’in kowa ado ya ke yi. Sai ga Iya Dije ta shigo, kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Ta na mai washe baki ta ce
‘’Bintu tashi maza ki biyo ni, Malamin ku ne ya ke neman ki, eh! Malam Aisar’’
jin sunan Aisar Bintu ta fidda Ido tare da fad’in ‘’Iye?’’
Iya Dije ba ta damu da yanayin tsoron da ya bayya na fuskar Bintu ba, ita dai burin ta shi ne ta kai ta ga Aisar ta samu ita ma ta fita,
ta ce; ‘’ke tashi mana, ni kasuwa zani kin ga dai yamma ta yi sosai, shida na yi ba lalle na samu shiga ba, kuma kayan abincin ku na sati zan kar6o’’
‘’Iya Dije dan Allah ki ce ba ki ganni ba’’ ta fad’a ta na yin rau-rau da idanu kamar mai shirin yin kuka.
Baki bud’e Iya Dije ta ce ‘’kun ji ni da yarinya, yo me zai mi ki da za ki sa ni yin k’arya da tsufa ta, na k’i na ce ban gan ki ba d’in’’
Bintu ta ce ‘’Iya Dije aradun Allah Gimbiya ta ce idan ta ganni da shi sai na lahira ya fi ni jin dad’i, ki min afuwa ki taimake ni’’
‘’wannan kuma ke ki ka sani, idan dai ba ke ki fad’a ma ta ba ina za ta san ma kin gan shi? Ko ta na nan ne?’’ Bintu ta girgiza kai alamar aha ah. ‘’toh maza yafa mayafin ki mu je’’ Bintu ta ce ai ba ta da mayafi. ‘’ai kuwa dai ba na tafi da ke ti6i ti6i da ke haka ba, budurwa kamar ki ki ce ba ki da mayafi? A garin na ku haka ki ke yawo?’’ Iya Dije ta tambaya ta na mai duban ta.
Kana Bintu ta amsa mata da ‘’ina da su, su na gida ne Gimbiya ta hana ni zuwa da kayan gida’’
Cike da nuna Allah wadai da halin Gimbiya Binta, Iya Dudu ta ce "wannan shi ne zancen 6ir in ji tusa, menene amfanin hana ki ado ko rufe jikin ki ? Ke tashi mu je ko aran zani ne na baki ki yafa ko ma d'auko wannan d’an hijabin nan da ku ke sawa ki yafa, ai yafi babu kaka ta wajan uba’’ .
Hakan ko Bintu ta yi, ta na magiya amma Iya Dije ba ta fasa jan ta ba su ka fito daga 6angaran d’akin kwanan d’alibai, tun suna wuce d’alibai wanda ke zaune farfajiyar wajan har ya zama tsilla tsilla kad’ai ake gani, musammam da ka baro sashin kwanan d'alibai su ka shigo farfajiyar makarantar. Ganin sun nufi ofishin malamai gaban Bintu ya fara fad’uwa.
***
Wata baranda gaban ofshin malamai su ka hangi Aisar zaune kan kujera, ganin Bintu tuni wani farin ciki ya lullu6e shi har cikin ran sa. Da kyar ya iya jira su ka k’araso in da Iya Dije ta bar shi ta na mai yiwa Aisar kashedin kar fa Bintu ta dad'e. Ba tare da wata damuwa ba tun da ita dai ta cika jakarta da kud’i ta yi gaba ta bar Bintu da Aisar. Ganin yanda Bintu ta bi bayan Iya Dudu da ido, Aisar ya ce Bintu ko bin ta za ki yi ne?”
Da sauri ta mayar da hankalin ta gare shi, ta gaishe shi cike da girmamawa. Ya amsa a takaice tare da mata nuni da wata kujera da ke gaban ta sa ya ce ta zauna dan kar ta b’ata k’afar ta cikin ca6in ruwan sama. Ba musu ta ja kujerar can nesa da tashi sannan ta zauna, kan ta sunkuye ta na wasa da yan yatsun hannun ta, ita dai Allah Allah ta ke Aisar ya sallame ta ko ba dan Gimbiya da sauran d’alibai ba, ko dan sanyin iskar damina da ke kad’awa.
Jin shiru be tanka ba ya sa ta yanke hukuncin tambayar dalilin kiran na ta, amma ko da ta d’aga kai, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ashe duk zaman nan kallo yake k’are mata. Da sauri ta k’ara yin k’asa da ido, ganin haka ya murmusa ya ce "Bintu gudu na ki ke ko?’’
Shiru ba ta amsa masa ba, ya k’ara da ‘’ya karatu? Ki na dai yi sosai ko? Ko da ya ke na ga kin ci gwajin da na mu ku sosai’’ kamar ya na magana da dutse Bintu ta k’i amsa masa. Be gushe ba ya ce ‘’daga wannan zangon zan dena koyarwa a makarantar ku, ban san me ya sa na ke fad’a mi ki ba, amma ina jin ya dace ki sani ne’’
Jin haka Bintu ta tsinci kan ta da fad’uwar gaba, ba ta san sanda ta ce "saboda me? Ba dai laifi mu ka maka ba ko?’’
kai ya girgiza mata sannan ya ce "yanayin aiki ya sa, amma inshaAllahu zan sa a maido da k'anwata makarantar nan kin ga sai ki sami k’awa ko?’’ murmushi Bintu ta yi wanda ke k’ara bayyana kyan ta, hakan ya sa Aisar fad’in
"dama haka ki ka iya murmushi?’’
sai kuma Bintu ta tsuke fuska, ta na shirin tambayar dalilin kiran na ta, wayar shi da ta hau k’ararrawa ta tsaida ita. Da ke wayar tafi da gidan ka(handset) be gama cika gari ba, hannun wane da wane kad’ai ake gani, waya ce kirar (Nokia 3310), dan haka baki bud’e ta tsaya ta na kallan wayar har ya d’aga ya kara bisa kunan sa, ji take da zai bata ta d’an kara kunan ta da ba haka ba.
Bintu ba ta dad’a shagala ba sai da ta ji ya ambaci sunan Barde, nan da nan ta manta da wani nauyin Aisar da ta ke ji, ta fara Allah Allah ya gama wayar.
Ta gani ya kashe ta ce "Malam dama kasan Yaremi Barde na Fabarusa?’’
‘’ Na san Barde, amma yanzu ba da shi na yi magana ba’’ sai da ya ba ta amsa sannan kuma mamakin yanda aka yi ta san Barde ya kama shi, be san sanda ya ce ‘’Yerima Barde ke? Ina ki ka san Barde ke kuma ki na yar masarautar Sa’ayrasa?’’ ya tambaya cike da mamaki.
Nan fa Bintu ta fara jero bayani cike da nuna gwanintar yan ajin su ma ba a barsu baya ba ta ce "ai rannan a aji aka yi hirar shi, ance shi ne mai kyawun duniya kuma k'asar nan kaf babu wanda zai gwada masa k'asaita, rabin yan ajin sun ta6a ganin shi, ni ma ina so na gan shi ko da sau d’aya ne a rayuwa ta’’
Jin kalaman Bintu tuni Aisar ya had’e rai, yayi k’icin k’icin ya fara fad’a "wato a shekarun ku har kun san ku zauna ku yi hirar samari ko? Ba ku san komai ba sai kula samari da karanta littafin soyayya ko?’’
"wallahi malam ba na kula samari ni ba yar iska ba ce’’ furucin Bintu kenan yayinda idanun Bintu su ka fara kawo ruwa, sai a sannan ta ankare da 6aran6aramar da ta yi na tambayar Barde, duk da dai ita ba da wata manufa ta yi. Ganin Bintu na shirin masa kuka har da batun ita ba yar iska bace ya sa hankalin sa kwanciya, wato kenan ba ta kula samarin tun da har ta masa wata fassara na da ban, hakan ya masa daidai har ya na mai murmusawa. Ita ko Bintu ta shi ta yi da sauri ganin wasu d’alibai sun fito daga d’akin karatu, ta ce malam dama karatu na ke Iya Dije ta ce za ka bani sak’o’’
Sai a sannan ya tuna fa ashe ba ranar makaran ta ba ne, gashi shi babu wani sak’o da ya kawo mata dama ganin ta kawai ya ke san yi. Amma gudun kar ta d’auke shi sakarai fakewa yayi da dama ya zo wucewa ne ta makarantar ya ce bara ya tsaya ya ji ta na karatu kuwa, maza ta koma ta cigaba da karatun. Da wannan ta masa sallama, har ta na fad’awa cikin ca6i dan saurin kar wannan d’aliban da ta hango su gan ta tare da Aisar. Shi kuwa gogan na ta ko ganin su be yi da ke su ma d’in lab’ewa su ka yi domin su tabbatar da abun da su ke gani.
***
Sai da Bintu ta k'urewa ganin sa sannan ya tashi ya nufi motar sa, ya gifta ta gaban wannan d’alibai da ke leb’e bayan wata yar katanga sam be lura da su ba har ya kai ga motar shi ya shige ya fice daga makarantar.
"kut yau kuwa za yi bantan uwa a makarantar’’ fad’in d’aya daga cikin d’aliban kenan wacce su ke Marry yayinda su ke fitowa daga wajan 6uyan su ganin Aisar ya fice. Su uku ne, kuma dukan su yan aji shida ne ma su mik’amin. Marry ita ce mai ruk’e da muk’amin horo, sai shedigyal da kuma mai kula da tsafta da lafiyar d’alibai, wacce su ke kira da Sikanti.
Marry ba ta gushe ba jiki na rawa tsabagen masifa ta k’ara da "wai ido na ne ke zagi ko kuwa Malam Aisar na gani da wata kwaila a makarantar nan?’’ Cikin Jimami Shedigyal ta ce ‘’ni ma dai abun nan ya ban mamaki, ki ga yanda mu ke bin sa ya na mana wulakanci amma ya rasa wacce zai bi sai Bintu d’iyar bayi’’ sikanta dan mamaki ta ma kasa magana. Marry ta d’aga k’afa ta doka k’asa cikin ca6ali, nan da nan zanin ta ya 6aci amma ko aji kin ta, idanun ta ya rufe, kana ta ce ‘’ba d’iyar bayi, ko d’iyar saraki ce yau sai ta ci Uban ta, za ta min bayanin dalilin